← Book details Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 65

Sashe 35

Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai a lokacin Zahra ta buɗe baki ta ce. "Wasu sun zo da nufin su kashe ni, kuma wani daga cikin masarauta ne ya turo su kashe ni".

Kalllonta Sooraj ya yi cikin rashin fahimta ya ce. "Bangane abin da ki ke magana a kai ba. Su waye su ka zo domin su kashe ki?, kuma me ki ka musu da za su kashe ki?".

Amsa Zahra ta bashi da cewa. "Ni ma ban sani ba, amma dai sun zo ne da zimmar cutar da ni, ban san ya haka yi suka tafi ba. Ni dai yanzu ina son na kai ni inda ƴan uwa na da mahaifiyata suke yanzu kaji".

Ajiyan zuciya Sooraj ya sauke!, sannan ya ce. "Karki damu yanzu dai ga abinci nan ki fara ci zan je wani guri yanzu na dawo".

"Ina za ka je?". Zahra ta tambaya.

Amsa ya ba ta da cewa. "Karki da mu da sanin inda zan je, ke dai kawai ki ci abincin ki yanzu zan je na dawo kafin ki gama na dawo".

Ya faɗa yayin da fuskar sa ke ɗauke da ɓacin rai. Ajiye mata ledar ya yi tare da fita daga cikin ɗakin.

Taɓe baki Zahra ta yi tare da ɗaukar ledar sannan ta ba za a kan gado, nan ta ci karo da fried rice wanda haka yi sealing ɗin shi a plastic plate ya ji naman kaji, yayin da gefe ɗaya rufaida ne guda biyu.
Ba ta san sanda ta ce. "Alhmadullihi rabbil alamin, gaskiya kuɗi duniya ne".

Ta faɗa tare da ba za ƙafafuwan ta sannan ta ya ga ledar da haka yi sealing ɗin fried rice ɗin da shi sannan ta yi bissmillah ta fara ci.

_________________________
Bayan su Aliyu sun isa gida hakan ya sa kowa ya samu guri ya zauna. Gaba ɗaya gidan ya yi shiru kamar ana zaman makoki.

Ɓangaren Umar kuwa babu abin da yake iya tunano wa sai fuskar mahaifinshi da yake neman gafara wajan miss Lailah. Hakan ya ƙara sa zuciyarsa ta ƙara karaya. Kallon su ya yi ya ce. "Nayi farin cikin ganin kunyi nasara a wannan case ɗin, dan haka ina ganin ni zan tafi, zan je gida yanzu sai kuma wata rana idan Allah ya ƙara haɗa mu da ku, nayi farin cikin kasancewa da ku sannan na ilimantu sosai da abubuwa game rayuwarku, sai an jima ni zan tafi". Ya faɗa yana mai ƙoƙarin fita daga gidan.

Daga sama ya ji muryar miss Lailah na faɗin. "Me ya sa za ka tafi?, ko dan saboda abin da ya faru ne?. Na san cewa dole za ka ci babu dad'i a zuciyarka kasancewarsa mahaifi a gare ka, kayi haƙuri dan Allah kada kayi min gurguwar fahimta, ni na riga na yafe masa, ba a kai na nake faɗa ba, ina faɗa ne a kan yaran da suka mutum sanadiyar sa. Dan haka ina mai baka haƙuri".

Murmushin yaƙe kawai Umar ya saki sannan ya ce. "Ka da kii bani haƙuri, domin babu wani a cikin ku da ya cutar da zuciyata, ni ne ya kamata na baku haƙuri kan abin da mahaifina ya aikata wa wannan ahalin mai cike da haɗin kai da farin ciki. Dan haka ina mai baku haƙuri".

Ya faɗa hawaye na sauka kan fuskarsa. Nan take ya fita da sauri.

Ganin haka ya sa Amrah ta yi saurin bin bayansa. Tare da rungume shi ta baya. "Dan Allah kada ka tafi ka barni". Ta faɗa hawaye kan fuskarta.

Juyowa ya yi yana mai fuskantar ta ya ce. "A'a Amrah dole na tafi, domin zama na yanzu a gidan nan ya kare, karki da mu zan dinga kawo miki ziyara kinji. Kinga da, muna tare ne saboda ahalinki da iyayenki basua nan, yanzu kuma kinga kuma yanzu suna nan, za ki yi rayuwar farin ciki tare da su. Bana tunanin bi na shi ne solution a gare ki, ki zauna tare da mahaifiyarki ki rayuwa cikin farin ciki har lokacin da Allah zai kawo miki miji na gari".

Girgiza kai Amrah ta yi ta ce. "Ni ba zan iya auren kowa ba in ba kai ba, kada ka manta fa ka ɗauko ni a lokacin da bani da kowa, bani da komai. Me ya sa to za ka rabu da ni a lokacin da na samu komai?. Shin baka so na ne?".

Murmushi wanda ya fi kuka ciwo Umar ya yi sannan ya ce. "Ina sonki Amrah, amma iyayenki ba za su bani ke ba kasancewata ɗa a wajan azzalumi, makashi, kuma macuci
Ba za su bani ke ba gudun kar ni a ce irin halin mahaifina ne da ni, kuma banga laifin su ba. Kiyi haƙuri ki bar wa Allah kowa. Allah zai bayyana miki wanda ya fi alkhairy a gare ki wanda za ki yi rayuwar farin ciki da shi na har abada". Ya faɗa tare da kwace jikinsa daga gare ta sannan ya shige cikin mota. Sannan ya tada ya fice daga gidan.

Tsugunnawa ta yi tare da fashe wa da kuka.

Duk abin da ya faru a kan idanuwan miss Lailah. Nan ta ji tausayin Umar ya kamata. Nan ta yanke shawarar cewa babu wanda ya fi dace wa da Amrah in ba shi ba.

Takawa ta fara yi tare da nufar inda Amrah take. Nan ta tayar da ita. Kallonta miss Lailah ta yi ta ce. "Ki na sonsa?".

Girgiza mata kai ta yi ta ce. "Eh Mama, dan Allah kada ki ana shi aure na, domin yana so na sosai, shi ya ci da ni ya suturta ni lokacin da ban san kowa ba, sannan ya jure duk wani abu da nayi wanda ba daidai ba".

Murmushi miss Lailah ta yi ta ce. "Karki da mu ƴata za ki aure shi kinji".,

Nan murmushi ya bayyana kan fuskar Amrah. "Na gode Mama, ina sonki sosai". Ta faɗa tana mai ƙara kankame mahaifiyar Tata a jiki. Nan miss Lailah ta ja ta cikin gida.

________________________
Ɓangaren Sooraj kuwa kai tsaye hanyar masarauta ya nufa, abu ɗaya ne kawai yake yawo a ƙogon kansa, shi ne maganar Zubaida na cewar sai ta kashe Zahra. Hakan ya sa shi ƙara gudu na motar tamkar zai tashi sama.

Bai ɗauke shi lokaci mai tsayi ba ya isa masarauta. Ko tsaya wa ya yi kyakyawan parking bai yi ba, ya fito daga cikin mota sannan ya shiga cikin parlour na family gaba ɗaya.

Kallon parlour ya yi ya ga ba kowa. Nan ya soma ƙwalla wa ƴan gidan suna. "Samira, Fasma, Yusrah, Zubaida, Gimbiya Saratu da Talatu, Junaid, Mami gaba ɗaya ku fito".

Su Gimbiya Saratu da ke shirya makircin su a ɗaki jin murya Sooraj ya sanya su fito wa babu shiri. Nan da nan kowa ya hallara a parlourn.

Kallonsa Mami ta yi ta ce. "Lafiya Sooraj na ganka a cikin irin wannan yanayin?".

Kallonsa Zubaida ta yi wacce ta dage sai taunar chewgum take kamar tsohuwar karuwa sannan ta ce. "Kema dai kya faɗa, lafiya ya tara mu a nan kamar wasu kaji".

Kallonta Mami ta yi ta ce. "Ke kuma Zubaida ki kama kanki, ba da ke nake ba, tohh".

Kallon Mami Sooraj ya yi ya ce. "Mami ki rabu da ita, a lokacin da zan fara jibgar su a lokacin za su gane cewar Sooraj ba kanwanlasa ba ne ba". Ya faɗa sannan ya ƙara da cewa.

"Ina son ku faɗa min gaskiya, a cikin ku wace ce ta tura ƴan daba domin su kashe Zahra a asibiti?".

Nan take cikin Zubaida ya ɗuri ruwa. Nan take zufa ya fara ƙeto mata.

Nan take su Mami da su Gimbiya Saratu suka shiga ƙoƙanto.

Kallonsu ya yi a karo na biyu sannan ya ce. "Zan ƙara tambayar ku a karo na ƙarshe, wa ya tura mutane su kashe Zahra a asibiti?".

Nan Gimbiya Saratu ta ce. "Toh ta ya za'a yi mu ma mu sani, ita Zahra me ya aikata mana da za mu tura ƴan daba domin su kashe ta, ina ga dai ka saɓa lamba ne".

Murmushi Sooraj ya yi sannan ya ce. "Shi ke nen, karku fito ku faɗa, amma wallahi duk ranar da na gano wacce ta shirya hakan a cikin ku, sai na lahira ya fita jin dad'i". Ya faɗa idanunsa a kan Zubaida.

Nan ta ji gabanta ya yanke ya faɗi!, cikin ranta ta ce. "Ko dai ya gane ni ce na tura ƴan daban nan ne"

Sooraj kuwa fita jan hannun Mami ya yi ya shigar da ita part ɗin ta, zaunar da ita ya yi kan gado sannan ya ce. "Mami za ki ji yau shiru ba zan dawo ba saboda zan kai Zahra domin ta ga mahaifiyarta, bana son ki shiga damuwa shi ya sa na gaya miki".

Murmushi Mami ta yi ta ce. "Tom shi ke nen Allah ya kai ku ya dawo da ku lafiya".
Nan ta saka masa albarka, daga bisani ya bar gidan baki ɗaya tare da komawa asibiti wajan Zahra.

Yana zuwa ya tarar da Zahra ta cinye abincin, kallonta ya yi ya ce. "Tawo mu tafi na kai ki wajan mahaifiyar ki".

Kallonsa ta yi sannan ta ce. "Baka cika alkawarin ka ba, kace za ka dawo kafin na gama cin abinci kuma tun ɗazu na gama ci baka dawo ba, me ya sa?".

Furzar da iska Sooraj ya yi waje sannan ya ce. "Shi ke nen hajiya Zahra kiyi hakuri na yarda ban cika alkawarina ba, ayi min afuwa".

Murmushi Zahra ta yi ta ce. "Ba zan haƙura ba in dai baka goya ni ba".

Zaro ido ya yi waje ya ce. "Goyo!, ina zan iya ɗaukar ki?, kinga kawai tawo mu tafi".

Girgiza kai Zahra ta yi ta ce. "Ni fa ba zan yarda ba".

"Tom shi ke nen ki bari in munyi aure, har abinda ya fi goyo zan miki, harda ma lilo duk zan yi miki".

Washe haƙora Zahra ta yi ta ce. "Da gaske ka ke kayi alƙawari?".

Gyaɗa kai Sooraj ya yi ya ce. "Eh nayi". Ya faɗa tare da jan hannunta. Nan suka je haka sallame su yayin da haka yi mata prescribing magunguna.

Nan suka fita daga asibitin yayin da suka kama hanyar garin Jigawa.
Chapter 35 · 0% Book details