← Book details Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 65

Sashe 39

Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maida kallonta Zahra ta yi kan Zubaida ta ce. "Kai Zubaida, wai sai ka ce ke ba mace bace, gaba ɗaya baki da tunani. Ni wallahi ba zan ɓoye miki ba dariya ki ke bani, domin a yadda nake gani ke kin fi ƙuda naci, abu sai ka ce asiri. Kin san ina ɗaga miki ƙafa ne kawai saboda Iyaye na da ƴan uwa na suna nan, sannan ina ɗaga miki ƙafa ne saboda mai martaba, da ba dan haka ba da na tona miki asiri a gaban kowa da kowa".

Dariya Zubaida ta kwashe da shi sannan ta ce. "Wane asiri?, ai babu wani abu da ki ka sani dangane da ni, koda kin sani, wannan damuwar ki ce domin babu wanda zai yarda da ke".

Wani miskilin murmushi Zahra ta saki sannan ta zo daff da kunnen Zubaida ta ce. "Kenen kina nufin ban san kina da cikin shege a jikin ki ba?".

Rass! Rass!. Gaban Zubaida ta yanke ya faɗi.nan take zufa ya fara ƙeto wa ya kowace sashi na jikinta. Take cikin ta ya ɗuri ruwa.

Baki na rawa Zubaida ta ce. "Me..me.. ki ke.. nufi?".

Girgiza Zahra ta yi tare da sakin murmushi sannan ta ce. "Kin riga kin san abin da nake nufi ba sai na maimaita miki ba. Hmmm kina mamakin ta yadda na sani ko?, to buɗe kunnuwan ki kiji. A sanda na shigo ɗaki ku na zaune, ido na a kanki ya fara sauka, yadda na karanci fuskarki alama ya nuna kina cikin damuwa, a hannunki naga midstream pregnancy test wanda masu ciki suke fitsari a kai domin su ga ko suna da ciki, ke a matsayin ki na budurwa wacce bata taɓa aure ba, me ki ke da shi?".

Sosa kai Zubaida ta yi yayin da ta kasa furta komai domin borin kunya.

Zahra ta dube ta ta ce.
"Da a ce ni wata ce mai baƙar zuciya, da a gaban kowa da kowa zan tona miki asiri. Amma ni samm ba zan miki haka ba domin hakan ba hali na ba ne, sannan kuma duk wanda ya tona asirin wani ba zai mutu ba har sai shi ma ya yi wannan abun. Dan haka gwara ki kama kanki ki san abinda ke damunki, kin san cewa idan mai martaba da mahaifinki ya ji wannan labari ba za ki tsira ba".

Zahra na kaiwa nan ta wuce ɗakinta.

Suman tsaye Zubaida ta yi yayin da ta kasa koda furuci ɗaya. Jikinta ne ya mutu. Cikin ranta ta ce. "Ta ya hakan ta kasance?, ban so ta san wannan al'amarin ba ya zama dole nayi wani abu a kai". Ta faɗa tare da shiga ɗakinta. Kai tsaye inda wayarta take ta nufa sannan ya shiga wajan lambobin wayarta. Sannan ya yi dialling lamba wanda bata yi saving ɗin shi ba. Ringing biyu zuwa uku haka ɗauka. Nan Zubaida ta ce. "Ina son mu haɗu a five star hotel nan da mintuna talatin".

Tana kaiwa nan ta katse wayar. Da sauri ta nufi inda jerin kayanta suke sannan ta ɗauki wani siririn mayafi wanda da shi gwara babu ta saka a kafaɗarta, sannan ta ɗauki maƙullin mota tare da nufar hanyar waje nan suka ci karo da Umar.

"Lafiya Zubaida naga kina wannan saurin?, kodai da akwai wata matsalar ne?".

Girgiza masa kai Zubaida ta yi da sauri sannan ta ce. "A'a babu komai ina son zan je gidan ƙawata ne".

"Tom shi ke nen a dawo lafiya". Cewar Umar.

Kamar jira take hakan ya sa ta yi saurin fita sannan ta nufi hanyar parking space. Nan driver ya buƙaci ya kaita inda za ta, amma sai ta nuna bata so. Daga ƙarshe dai da kanta ta tada mota sannan ta fice daga masarautar.

Mamaki kawai ke ɗauke kan fuskar Umar domin shi yana zargin Zubaida akwai abinda take shirya wa, sannan alamu ya nuna tabbas ba wajan ƙawa zai je ba. Basarwa ya yi sannan ya fita domin zuwa inda motar Sooraj yake dan ɗauko abu. Nan ya tarar da Junaid na shirin fita.

Kallon Junaid Umar ya yi ya ce. "Ɗan uwa ina zuwa haka?".

Murmushi Junaid ya yi ya ce. "Wallahi zan je asibiti ne yanzu haka kira ni wai wani abokina ya yi hatsarin mota".

"Innalillahi wa innahilaihi rajihun!, Allah ya sauwaƙe ya kiyaye gaba". Cewar Umar.

"Amin". Junaid ya amsa.

Nan Umar ya ce. "Ko in bika mu tafi tare ne, domin na taya ka kula da shi".

"Ayya ɗan uwa babu buƙatar hakan, an ce min ba wani rauni ya ji ba sosai, ni zan iya kula da shi, ka ga kai kana da ayyuka da yawa a gaban ka, kuma ba zan so ta dalilina na katse maka su ba. Kada ka damu ni zan je". Cewar Junaid.

Girgiza kai Umar ya yi ya ce. "Tom shi ke nen tunda kace haka. Kace ina gaishe da mara lafiya?".

"Tom zai ji". Junaid ya faɗa tare da shiga cikin mota sannan ya figi motar tare da fice wa daga gidan.

Jinjina kai Umar ya yi ganin yadda hankalin Junaid ya tashi kan abokin sa. "Kaga abokin ƙwarai kenen". Umar ya faɗa cikin ransa.

Ɓangaren Sooraj kuwa bayan sun gaisa dai mai martaba yake sanar da mai martaba cewa idan babu damuwa kafin su Miss Lailah su tafi ya nemi auren Zahra.

Nan mai martaba ya amince da hakan sannan ya ce. "Zamu tattauna a kan hakan amma ba yanzu ba mu bari zuwa gobe ko jibi, domin ba zai dace daga zuwan su mun fara musu maganar aure ba".

Girgiza kai Sooraj ya yi alamun gaskiya mai martaba ya faɗa.

Tashi ya yi da zimmar fita. Nan ya ji muryar mai martaba ya ce. "Sooraj!".

Nan Sooraj ya juyo sannan ya ce. "Na'am mai martaba".

Magana mai martaba ya fara da cewa. "Me ya sa baka son Zubaida?, sannan me ya sa ka ke son auren Zahra?, Zubaida fa jinin wannan masarautar ce, ƴar sarauta ce, kuma mace ce mai hankali da sanin ya kamata. Me ya sa baka sonta?".

Murmushi Sooraj ya yi ya ce. "Ni kaina mai martaba ban san me ya sa ba, kuma ban san me ya sa nake son Zahra ba, kawai dai ina jin ina son na rayu da Zahra tsawon numfashina na ƙarshe, ita kuma Zubaida ba wai zai nuna mata ƙiyayya ba ne, zan yi bakin ƙoƙari na wajan ganin nan tauye haƙƙin kowanne daga cikin su ba".

Kallonsa mai martaba ya yi ya ce. "Idan har ka san ba za ka iya yin adalci a tsakanin su to ban amince ka auri Zahra ba, amma in har za ka yi adalci kuma kaji tsoron Allah kayi hukunci a kan gaskiya ba tare da tauye haƙƙin wani a cikin su ba to kana da damar auren su biyun".

Gyaɗa kai Sooraj ya yi ya ce. "Na gode mai martaba". Ya faɗa tare da fita daga cikin part ɗin da gaba ɗaya.

****
"Wai Zahra na tambaye ki, haka ki ka yi rayuwa da waɗan nan mutanen marasa mutuncin?". Cewar Safira.

Murmushi Zahra ta yi tana mai gyara zamanta a kan gado ta ce. "Ke dai bari, inda Allah ya taimake ni shi ne, ni ɗin ba kanwanlasa bace ba, ni ba gamagarin mace bace, da tuni sun shafe babi na wallahi. Ai duk hankali nake koya musu domin bana iya jure ganin abu wanda ba daidai ba kuma nayi shiru, dole ne sai na ranka. Ranar farkon da Mami ta kawo ni gidan nan ina ta jin na matsu na koma kurkuku inda nake, amma tunda na haɗu da kishiyoyin Mami da ƴaƴanta naji gaba ki ɗaya bana son tafiya har saina koyar da su darasi, a kan ma fa basu daddara ba. Yanzu jira nake kofin su ya cika, Allah za su gane cewar Allah ɗaya ne".

Maida kallonta Zahra ta yi kan Amrah ta yi. Nan ta ga Amrah ta yi tagumi alama ta shiga tunani. Nan Zahra ta ce. "Ke kuma Amrah tunanin me ki ke?, ko kina tunanin saurayin ki Yahya Umar ne?".

Sai a lokacin Amrah ta dawo daga duniyar tunanin da ta shiga sannan ta ce. "A'a ko ɗaya, ina tunani ne a kan dabbobin da nayi rayuwa da su da haka kashe, su ɗin fa basu aikata laifin komai ba haka kashe su". Ta faɗa hawaye na sauka kan ƙuncinta.

Shiru Zahra ta yi tare da miƙe wa ta nufi inda Amrah take sannan ta share mata hawayenta ta ce. "Aba ƴar uwata kada ki saka wannan a ranki, ki maida komai ba komai ba kinji, abinda ya wuce ya riga ya wuce sai dai mu ce Allah ya tsare gaba, yanzu maza ku ta so na nunnuna muku masarautar nan".
Zahra ta faɗa tana mai jan hannun Amrah yayin da su ukun suka riƙe hannun juna tare da fice wa daga cikin ɗakin.

Nan suka fita harabar masarautar inda Zahra ta shiga zagaye da su. Duk inda suka gifta sai a tsaya a kalle su. Abin har mamaki yake bawa su Zahra domin gaba ɗaya idanuwa jama'ar Masarautar a kansu yake.

______________
Bayan isar Zubaida five star hotel ta shiga ciki sannan ta zauna kan kujera. Nan ɗaya daga cikin ma'aikatan ta tambayi Zubaida mai take da buƙata. Ɗaga mata hannu kawai Zubaida ta yi alamun bata da buƙata.

Tsayuwar motar da ta ji ne ya sata waigawa. Girgiza kai ta yi alamun tana cikin fusata.

Fitowa gaye wanda fuskar sa ke sanye da fecemark ya yi tare da rufe murfin motar. Waige-waige ya soma yi daga nesa ya hangi Zubaida a zaune. Da sauri ya ƙarasa inda take sannan ta samu kujera wanda ke kusa da ita ya zauna. Kallonta ya yi rai ɓace ya ce.

"Me ya sa ki ka kira ni bayan na ce miki ki rabu da rayuwata?, kinga ni na gaya miki bana da buƙatar ki, bana son komai da zai ƙara halaƙanta ni da ke".

Kallonsa Zubaida ta yi ta ce. "Wallahi baka isa ba, kamar ya na fita daga cikin rayuwarka, kayi min ciki kuma ka ke ikirarin cewa in fita daga rayuwarka?, ina ka ke da damar da za ka faɗa cewa na fita a rayuwarka".
Chapter 39 · 0% Book details