← Book details Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 65

Sashe 44

Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɗago wa Zahra ta yi a fusa ce ta ce. "Kai baka ji kunyar abin da ka ke furta wa ba?, aba!, ban taɓa tunanin haka daga gare ka ba. Nan taɓa sanin cewa kana da sankan ka ba sai yau, wato saboda farin cikin ka shi ne ni kuma za ka tauye nawa farin cikin?, me ya sa tun farko ka sa zuciyata ta aminta da kai bayan ka san ƙarya ka ke min?, me ya sa ka tusa min sonka lokacin da ban shirya ba?, me ya sa baka faɗa min gaskiya ba tun kafin lokaci ya ƙure?. Yanzu me ka ke shirin faɗa min?, na cigaba da zama da kai ko me?".
Ta faɗa hawaye na sauka bisa ƙuncinta.

Kallonta ya yi ya ce. "A'a ni na faɗa miki gaskiya ne kawai saboda bana son na cigaba da yaudarar ki da kalaman ƙarya, Zahra wallahi ban aure ki ba domin cutar da zuciyar ki, nayi ne do...

Bai ƙarasa ba Zahra ta ce. "Ka ga Yarima, dan Allah ka ƙyale ni, yanzu haka kaina ciwo yake min, ka rabu da ni ka fita na kwanta, bana son wani hayaniya da daddaren nan. Kowacce mace na farin cikin ganin ta a gidan mijinta na sunnah sai gashi ni yau ta kasance min mummunar rana a gare ni, Yarima ka ƙyale ni ". Ta ƙarashe maganar tare da fashe wa da kuka.

Share hawayenta ta yi tare da nufar hanyar waje sannan ya buɗe masa ƙofa tare da maida dubanta kansa ta ce. "Ka fita dan Allah".

Zama Sooraj ya yi ya ce. "Ba zan fita ba har sai kin yafe min abinda na miki ".

Murmushi wanda ya fi kuka ciwo Zahra ta saki kana ta girgiza kai ta ce. "Tunda kai ba za ka fita ba to ni zan fita na bar maka ɗakin".

Ta faɗa tare da ƙoƙarin barin ɗakin. Da saurin Sooraj ya nufi inda take tare da janyo ta. Nan take ta faɗa jikinsa.

Nan take kowannensu bugun zuciyarsa ya ƙaru. Da sauri Zahra ta ƙwace jikinta daga gare shi sannan ta ce ." Me ya sa za ka jawo ni jikin ka?".

Murmushi Sooraj ya yi ya ce. "Karki manta fa ni mijinki ne, kuma kin san ina da iko s kanki ko. Toh yanzu ina son ke ki koma ki kwanta ni zan tafi ɗaki na".

Ya faɗa tare da barin ɗakin.

Koma wa kan gado Zahra ta yi tare da kwanciya kana ta sauke nannauyan ajiyar zuciya!.

Kwanciya ta yi inda a ƙarshe baccin ɓarawo ya sace ta.

*******
ZUBAIDA POV
Zubaida kuwa hannunta riƙe yake da waya ta kara a kunne alamu kira take yi .
"Hmm kai dai bari yanzu anyi aure hankali na ya kwanta, yanzu zan fara kodimo, yanzu haka yana ɗakin waccan shegiyar yarinyar, bakiji haushin da nake ji ba wallahi, ko kazar da ya kawo min ma kasa ci nayi".

Daga ɗayan ɓangaren haka sauke ajiyar zuciya aka ce. "Zubaida yanzu fa ke matar wani ce, me ya sa ki ke min magana a ranar auren ki?, me ya sa ki ka rasa wanda za ki kira sai ni?".

Nan take Zubaida ta haɗe rai tamkar tana gaban wanda take wa magana.

"Ka ga bana son rainin hankali, ina ruwanka?, aure na ne ko naka?, ni na ga zan iya dan haka baka da hurumin shiga rayuwata, tohm".

Shiru mutumin ya yi mata sannan ya ce. "Allah ya shirye ki". Yana kaiwa nan ya katse wayar.

Nan take taja dogon tsaki sannan ta ce. "Aikin banza kawai, mutane in ban da shishishigi babu abinda suka yi.

Washe gari da sassafe. Haka aiko wa amaren Sooraj abinci daga masarauta.

Nan Zubaida ta fito dining domin nata, a sa'inda shima Sooraj ya fito. Nan ya tarar cewa Zahra ba ta fito ba, hakan ya sa hankalin da yaƙi kwanciya. Duban Zubaida ya yi ya ce. "Zubaida Please je ki kira Zahra ta zo ta yi karin kummallo".

Nan take Zubaida ta haɗe rai sannan ta ce. "Kamar ya bangane ba?, ita ba ta san hanyar dining ɗin ba ne da sai naje na kira ta?, toh ba zan je ba".

Nan Sooraj ya nuna kansa ya ce. "Zubaida ni nake miki magana ki ke mayar min da martani?, toh umarni nake baki ba shawara ba maza ki je ki kira ta".

Ba tare da ranta na son hakan ba ta tashi taje part ɗin Zahra. Tana zuwa kai tsaye ta ƙusa kai cikin parlourn ta. Nan take ta tsaya tana bin harabar parlourn da kallo, mamaki ne ya kamata ganin abubuwa yadda parlourn ya haɗu, domin ita kanta ta san parlourn ya tattaka nata kyau nesa ba kusa ba. Chan ta hangi Zahra ta yi ruff da ciki a kan kujera.

Yamutse fuska Zubaida ta yi ta ce. "Toh sai a fito a ci abinci ko, a daina noƙe-noƙe, ko kunya ki ke ji ne, bayan kun gama duk abinda za ku yi?".

Nan take Zahra ta ɗago da kanta rai ɓace ta miƙe tsaye ta dube ta ta ce. "Kin san Allah, kin ci darajar Mami da mahaifiyata kan nasihar da haka yi min, da ba dan haka ba, wallahi da sai an ji mu da ke a gidan nan. Maza fitar mun daga parlour kuma kice ba zan ci abincin ba".

Nan Zubaida ta juya ta tafi ta koma dining tare da faɗa wa Sooraj gaskiya da ƙarya. Girgiza kai kawai ya yi yayin da ya tashi daga kan abinci ya fice daga gidan.

Ɓangaren su Aliyu kuwa, bayan sun tashi suka yi wanka tare da sallah. Aliyu ya yi farin ciki sosai domin ya samu Safira da budurcin ta.
Nan Mami da Miss Lailah ta suka kawo musu break fast, yayin da Mami ta baiwa Safira magunguna na gargajiya da sauransu. Bayan sun gaisa ne suka bar gidan sannan suka je gidan Umar.

Ɓangaren Umar kuwa bayan sun tashi ya gasa jikin Amrah da ruwan zafi yayin da ya shiga saka mata albarka domin yana cikin farin ciki mara misaltuwa kasancewar ta budurwa.
Bayan sun gama wanka. Suka yi Sallah, nan suka ji ana Kwankwass ƙofa. Tashi Umar ya yi domin kuwa Amrah bata da ƙarfin da zata iya zuwa buɗe ƙofa yayin da ba abin da take faman yi sai kuka, domin a ganinta Umar ya yaudare ta jiya ya mata ƙarya.

Bayan sun kawo abincin suka gaisa da juna yayin da Mami da kanta ta ƙara tsaftace Amrah tare da bata magunguna na gargajiya wanda zasu taimaka mata wajan rage raɗaɗi.
Bayan sun gama ne suka bar gidan.

Da rana misalin ƙarfe 1 haka ƙara kaiwa kowaccen su abinci daga kan su Zahra har su Amrah. Inda su Amrah wannan karan driver ne ya kai musu abincin. Yayin da su Zahra kuwa haka kai musu daga masarauta. Sai dai a wannan karon ma Zahra ba ta ci abincin ba, Zubaida ce kawai ta ci.

Bayan Mami sunyi sallama da kowa ne, ta kama hanyar tawo wa Kano.

******
Haka Zahra ta zauna da yunwa har zuwa dare inda babu abinda ta saka a bakinta.

Daidai lokacin Sooraj ya dawo daga fada hannunsa riƙe da ledoji guda biyu nan ya nufi ɗakin Zahra ya ajiye mata ba tare da ya yi mata magana ba. Kana daga bisani ya nufi ɗakin Zubaida.

Nan Zahra ta galla wa ledar harara tamkar shi ne a gabanta. Ganin ba zata iya ba ya sanya ta ɗauki ledar tare da buɗe wa, nan ta ga kula nan ta buɗe take ta yi harba da tuwon shinkafa miyan taushe yaji nama da kayan lambu. Lumshe idanuwanta ta yi lokacin da ƙamshin abincin ya bugi hancinta. Ba ta yi wata- wata ba ta fara cin abinci, tana ci tana siɗe hannu. Nan ta ce. "Yunwa bata da hankali, ba ta san yaro da babba ba". Tana kaiwa nan ta nufi kitchen tare da shan ruwa daga bisani ya wanke hannu kana ta koma ta kwanta.

Ɓangaren Sooraj kuwa bayan ya kaiwa Zubaida abincin ta ci. Ya tafi kan gado tare da kashe wutar ɗakin ya kwanta da zimmar bacci. Duban sa Zubaida ta yi rai ɓace ta kunna fitilar.

Ɗago da kansa Sooraj ya yi ya ce. "Lafiya ki ka kunna fitila?".

Kau da kai Zubaida ta yi ta ce. "Wai saina tuna maka tukun zaka gane?, ya za ka yi shirin bacci kuma?".

Dafe kansa Sooraj ya yi sai a lokacin hankalin ya tuna.

WASHE GARIN RANAR.
A matuƙar fusa ce Sooraj ya dube ta ya ce. "Zubaida dama ke ba budurwa bace?, dama ke ragowar wani ce, maza gaya min gaskiya".

Fashe wa da kuka Zubaida ta yi tana mai faɗin. "Wallahi ba abinda ka ke tunani ba ne, ni samm ba haka nake ba, ka fahimce ni ".

"What are you trying to say Zubaida?, za ki ce min bishiya ki ke awa, ko awa machine ki ke yi ko kuwa ɗaukar abu mai nauyi ki ke? , da sauransu, duk babu wanda ki ke yi a ciki. So how comes?".

Sosa kai Zubaida ta yi ta ce. "Na taɓa yin cuta ne a baya shi ya sa".

Girgiza kai Sooraj ya yi ya ce. "Ƙarya ki ke Zubaida babu wani cuta da ke sa mace ta rasa budurcinta in ba fasiƙanci ta je ta yi ba. Amma shi ke nen, ai ramin ƙarya ƙurarre ne, kuma na san Allah ba azzalumin bawansa ba ne".

Yana kaiwa nan ya shiga toilet ɗin ta ta yi wanka sannan ya fito ya nufi part ɗin domin saka kaya.

Zubaida kuwa gabanta ne ya tsananta faɗuwa. Nan take gabanta ya yanke ya faɗi!, baki na rawa ta ce. "Ko dai ya san ina da juna biyu ne?".

MANAGE PAGE

DAN ALLAH KUYI LIKE, COMMENTS, AND SHARE FISABILILLAH. SABODA ALLAH PLEASE🥹 🙏🙏🙏🙏🙏🙏

ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞
ZINARIYAR JAJIRTATTU

[8/21, 8:02 AM] AyeesherM B: [8/21, 8:01 AM] AYEESHER MB💞💞💞: BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎

*A'ISHA M.B*💞💞
Chapter 44 · 0% Book details