← Book details Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 65

Sashe 20

Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri Zahra ta ja da baya ganin yanayin da suke ciki na ban tsoro. Tunanin ta ina za ta ɓullo musu ta shiga yi. Saidai gaba ɗaya ta rasa me ya kamata ta yi.

Ganin sun fara yinƙuro inda take ya sa ta soma ja da baya- baya.

"Dama mun faɗa miki baki san ko mu ɗin su waye ba yanzu kuma za mu nuna miki cewa bakin rijiya ba gurin wasan makaho ba ne".
Suna kaiwa nan suka yinkura tare da kai mata farmaki.

Da sauri Zahra ta tsugunna. Cikin mamakin su kuwa suka ga abin da suka tura mata bai yi tasiri a kanta ba.

Kallon juna suka yi nan suka shiga kai mata farmaki marasa adadi amma a yayin da suke jefarta da shi shi kuma farmakin yake koma wa kansu.

Dubanta suka yi cikin murya mai matuƙar firgitarwa suka ce. "Ta ya ya ki ka iya tsallake wa farmakin mu?, Ke ɗin wace ce?".

Murmushi Zahra ta sakar musu sannan ta ce. "Ni ɗin Zahra ce, kuma wannan kaɗan ku ka gani daga cikin ƙarfi na. Yanzu dai tun da kun tabbatar cewa ba za ku iya yi min komai ba to ku zuba makamanku ku tawo mu zamo abokai kawai kunji ƴan albarka".

Shiru suka yi mata yayin da ɗaya daga cikin su ya ce. "Ki sani cewa wannan mafari ne na tafiyar ki ba wai ƙarshe ba, ya kamata ki san da cewar tafiyar nan bata ƙare ba, idan kinyi nasarar tsallake wa makircin mu to ba za ki iya tsallake na shuwagabannin mu ba".

Suna kaiwa nan suka ɓace daga harabar wajan.

Taɓe baki Zahra ta yi ta ce. "Tunda har na iya ji da ku shuwagabannin ku ba za su wani bani matsala ba". Ta faɗa tana mai ɗora tafiyar ta.

****
Amrah kuwa tafiya ta cigaba da yi ba tare da ta dakata ba. Ganin ba za ta iya cigaba da tafiya ba ya sa fara gudu tamkar wata barewa sannan ta shiga aye wa kan bishiyoyi ɗaya bayan ɗaya a haka ta cigaba da tafiya har saida ta isa wani guri mai ban tsoro.

Babu abinda take har ba da su sai kwarangwal ɗin mutane wanda suka ƙwalalo idanuwa waje. Bin Amrah suke da kallo tamkar wata abincin su.

Sauke ajiyan zuciya Amrah ta yi ba ta ankara ba sai gani ta yi waɗan nan kwarangwal ɗin mutane sun fara rikiɗa izuwa namun jeji.

Da sauri Amrah ta dube su tana mai sakin fuskarta ta ce. "Kada ku cutar da ni, nima ɗaya daga cikin ku ce, na girma ne a tsakanin ku, kuma ina ganin ya kamata ku iya gane ni ɗin ƴar uwar ku ce".

Ba ta ankara ba ta ga wata dabba ta tawo da gudu domin kawo mata farmaki. Da sauri Amrah ta buga tsalle tana mai kauce wa wannan farmakin.

****
Ganin Safira taƙi tashi ya sa wannan dutsen ya rabu izuwa gida biyu yayin da hayaki ya fara fitowa daga cikin wannan dutsen. Nan take kunamu da ƙadangaru suka mamaye wajan suna nufo inda Safira take.

Zaro idanuwa waje Safira ta yi tare da ja da baya.

Nuna su ta yi tana mai faɗin. "Maza ku koma ni ɗin ba abincin ku bace". Nan take suka fara awa jikin ta. Da sauri ta fara karkaɗe su yayin da ta kurma ihuu. Nan take ta fashe da wani marayan kuka. Ganin sunƙi barin jikinta ya sa ta ware hannayenta sannan ta yi amfani da ƙarfin ikonta ta shiga bazar da su.

*******
Cikin rashin sa'a ɗaya daga cikin dabbobin ya buga tsalle sannan ya karce ta a baya. Nan take Amrah ta saki azababbiyar ƙara. Faɗuwa Amrah ta yi yayin da bayanta ya fara fidda jini.

******
Faɗuwa Zahra ta yi ƙasa yayin da ta ji bayanta nayi mata zugi da raɗaɗi.

Mamaki ne ya kamata ganin lokaci ɗaya bayanta ya fara soma mata zafi.

Ɓangaren Safira ma aka kamar yadda Zahra ke jin zafi ita ma haka take jin zafi da raɗaɗi a bayanta.

********
Shiga cikin ɗakin Mami mai martaba ya yi ya tarar da ita a zaune ta yi tagumi. Kallo ɗaya za ka mata ka san cewar tana cikin damuwa.

Har mai martaba ya zo ya wuce ta gabanta ya zauna Mami ba ta sani ba domin gaba ɗaya ta zurfafa cikin damuwa.

Binta da kallo mai martaba ya yi sannan ya fara kiran sunanta. "A'isha". Sai a lokacin Mami ta dawo cikin hayyacin ta. Nan ta dube shi da sauri ta ce.

"Mai martaba yaushe ka shigo?".

Amsa mai martaba ya ba ta da cewa. "Ba jimawa na shigo. A'isha wai me ke faruwa ne?, naga bakya cikin walwala, alamu sun nuna cewa kina cikin damuwa".

Nannauyan ajiyan zuciya Mami ta sauke!, sannan ta ce. "Idan na ce maka bana cikin damuwa to tabbas nayi maka ƙarya. Dama a kan maganar Zubaida ne, yarinyar naga tana matuƙar son Sooraj kuma nayi wa Sooraj magana ya ce ya amince. Amma abinda ya faru ɗazu ya sani a ƙoƙanto, naji yana ambatar sunan Zahra wannan ƴar aikin da na kawo, ina tunanin fa ita yake so. Bana son kuma nayi masa abin da ransa yake so, na tambaye shi shin da akwai wacce yake so a zuciyar sa ya ce min a'a hakan ne ya sa na ce za'a yi musu aure shi da Zubaida. Saidai naga alamu kamar baya sonta, baya so ya ɓata min rai ne shi ya sa ya amince da batun Zubaida".

Murmushi mai martaba ya yi ya ce. "Ai ina ganin wannan ba wani abun tada hankali ba ne, karki manta fa ke ɗin mahaifiyarsa ce kuma kina da ikon yi duk abin da ki ke muradi a kansa. Tunda har da bakin sa ya furta miki cewar babu wacce yake so, ina ganin ai ba matsala ba ne, ni nan zan sa a shirya bikin sa da Zubaida wannan satin mai zuwa. Gida, lefe ko sadaki na san ba abin da zai gagari Sooraj ba ne".

Murmushin jin dad'i Mami ta yi ta ce. "Na gode sosai ranka shi daɗe, na san idan na sanar wa Zubaida wannan maganar saita fi kowa farin ciki".
Mami ta faɗa yayin da ta kirawo wasu masu aiki a masarautar sannan ta sanar da su cewa su kira mata Zubaida. Cikin ƙanƙanin lokaci Zubaida ta shigo cikin ɗakin sallama riƙe a bakinta. Yayin da ta saukar da kai ƙasa tana mai rinsinawa tamkar wata mahauniya.

"Gani ranki shi daɗe".

Murmushi Mami ta yi ta ce. "Ina da wani albishir da zan yi miki, yanzu ki fara shirye-shirye nan da sati ɗaya za'a ɗaura muku aure da ɗana Sooraj".

Washe haƙora Zubaida ta yi sannan ta ce. "Na gode sosai ranki shi daɗe, gaskiya nayi farin ciki sosai bara zan je na sanar da Baba na mu fara shirye-shiryen".

Ta faɗa tare da barin ɗakin. Ji ta yi an janyo hannunta tare da shigar da ita ɗakin.

Da sauri ta ɗago idanuwanta domin ganin wane. Nan suka haɗa ido da Gimbiya Talatu.

Kallon ƴan cikin ɗakin Zubaida ta yi sannan ta maida kallonta kan Gimbiya Saratu ta ce. "Fulani fatan lafiya dai ko?".

Kallon ta Samira ta yi ta ce. "Shin aure za ki yi ke da Yarima Sooraj?".

Girgiza kai Zubaida ta yi ta ce. "Eh mana in sha Allah, me ya faru?".

Inda ƙofar ɗakin yake Gimbiya Saratu ta nufa tare da rufe ɗakin sannan ta maida kallonta kan Zubaida ta ce. "Wato tambayar mu ki ke me ya faru bayan kina soyayya da ɗana Junaid".

Furzar da iska waje Zubaida ta yi tare da riƙe ƙugu sannan ta ce. "Wannan soyayyar baya kenen kuma soyayyar shan minti muka yi da shi, ni nayi soyayya da shi ne kafin naga yarima Sooraj. Amma bayan naga yarima Sooraj ne soyayyar da nake wa Junaid ta koma kansa".

Jinjina kai Talatu ta yi ta ce. "Lallai kin shahara, wato so ki ke ki haɗa wa da ƙaninsa ko?, ke daga gani sheɗaniya ce, kasancewar mahaifinki ƙanin mai martaba ne hakan ba zai sa idan mai martaba ya gano gaskiya ya ƙiyi miki hukunci ba, sannan daɗin daɗawa ke kanki kin san da cewa Sooraj ba sonki yake ba, kuma ki sani cewa ba zai taɓa so ki ba. Tun kafin lokaci ya ƙure kiyi gaggawar fito ki gaya wa kowa cewa Junaid shi ne masoyinki wanda ki ke so ki aura ba Sooraj. Muddin kuma ki ka kuskure ki ka auri Sooraj sannan ku ka shigo gidan nan, to ki sani cewar tamkar kin shigo inda mutuwar ki take ne".

Dariya Zubaida ta kwashe da shi sa'anan ta dube su ɗaya bayan ɗaya ta ce. "Wai me ya sa ni ku ka raina, ita Zahra me ya sa baku yi mata hakan ba, ai naji labarin yadda ta saita muku zama a gidan nan, da a ce ita ce a matsayina kun isa ku ce za ku yi mata wata barazana?, Ita kanta barazana ce balle ku razana ta. Dan aka ku bar tada wani jijiyoyin wuya domin kuwa aure na da Sooraj babu fashi tamkar an ɗaura ne, kuma babu wani mahaluƙi da ya isa ya dakatar da hakan". Ta ƙarashe maganar tare da kan tsaki sannan ta buɗe ƙofar ɗakin tare da ficewa daga ɗakin.

"Gimbiya kada mu rabu da ita, mu koya mata hankali, har tana da bakin da za ta faɗa mana abin da ranta yake so". Cewar Samira tana mai kallon Saratu.

"Ki rabu da ita, duk wanda ya ci tuwo da mu miya ya sha, zamu nuna mata cewa bakin rijiya ba wajan wasan makaho ba ne". Cewar Gimbiya Saratu.

*********
Jami'an ƴan sanda su isa hospital ɗin da Mrs Lailah take lafiya yayin da suka nuna police warrant ID card ɗin su kafin nan likitoci suka yarda ya shiga inda Mrs Lailah take.

Tarar da ita suka yi a ƙasa ta yi ruf da ciki. Kallon juna suka yi yayin da suka yi mata sallama.

A hankali ta ɗago da idanunta tare da sauke su a kansu. Da sauri ta miƙe tare da ja da baya ta ce. "Su waye ku?, me ku ke nema a gare ni?".
Chapter 20 · 0% Book details