← Book details Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 65

Sashe 23

Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri suka isa wajan tare da ƙwalla wa su Sooraj kira. "Kuna ina sun dawo fa maza ku fito". Nan take mai martaba da su Mami suka fito.

Take gaban Mami ya yanke ya faɗi ganin masu kama da Zahra sakk, ta iya gane babu Zahra a cikin su ne ta hanyar launin idanuwansu.

Daidai lokacin su ma Gimbiya Talatu da yaranta tare da Junaid suka fito. Nan suka yi ido huɗu da su Amrah.

Take suka fasa ihuuu suna faɗin. "Wayyo Allah aljanu, maza mu gudu". Gimbiya Saratu ta faɗa daidai lokacin da Sooraj ke ƙoƙarin fitowa. Yayin da ita ma Zubaida wacce fuskarta ke a rufe ta fito tare da masu aiki.

Baki sake jama'ar wajan ke binsu da kallo.

Kallonsu Umar ya yi ya ce. "Ina kuma Zahra take na ga ban ganta a nan ba?".

Fashe wa da kuka Amrah ta yi ta ce. "Zahra ta tafi ba zata sake dawo wa ba, Zahra ta riga ta tafi tafiya ta har abada".

Chakk maganar Amrah ya sauka a kunnen Sooraj. Nan take ya ji zuciyarsa ta tsaya yayin da ƙwaƙwalwar da kansa ya shiga sarawa.

Da sauri ya fito jiki na rawa ya ce. "Me ku ke nufi?, kenen Zahra ta mutu?".

Share hawayenta Safira ta yi ta ce. "Bamu sani ba ko ta mutu ko tana raye".

Jikin kowa ne a wajan ya yi sanyi.

Nan take idanuwan Sooraj suka ƙada suka yi jajir tamkar an kunna garwashi.

Maida kallonsa ya yi kan Umar baki na rawa ya ce. "Bani maƙullin mota?".

Girgiza kai Umar ya yi ya ce. "Ta ya ya zan baka Sooraj yanzu fa one hour ya rage a ɗaura maka aure, ka bari bayan an ɗaura maka".

Huci Sooraj ya fara yi tamkar wani tsohon zaki. Cikin daka tsawa ya ce. "Maza ka bani maƙullin mota kafin nayi maka abin da baka yi zato ba?".

Ganin ranshi a ɓace ya sa Umar ya zaro maƙulli daga aljihun sa sannan ya miƙa wa Sooraj.

Karɓa Sooraj ya yi tare da juyawa da zimmar tafiya.

Dakatar da shi Mami ta yi da faɗin. "Ina zaka je?, auran ka fa za'a ɗaura".

Nan take hawaye ya gangaro kan fuskarsa sannan ya dube ta ya ce. "Auren banza auren wofi, Zahra ita ce duniya ta, ita ce komai tawa, ba zan iya taɓa rayuwa ba tare da ita ba, indai ta mutu to tabbas nima na zama muttacce. Idan babu ita mene ne amfanin rayuwata?".

Yana kammala faɗin hakan ya nufi inda motarsa take. Tare da tada wa. Dakarai sunyi ƙoƙarin dakatar da shi amma ina ya citura domin kuwa da mugun gudu ya figi motar tare da barin cikin masarautar.

THE WAR JUST STARTED🥺🥺🥺🥺.

KADA KU MANTA DA LIKE, COMMENTS, AND SHARE FISABILILLAH 🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏

ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞💞
ZINARIYAR JAJIRTATTU
بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎

*BOOK 2*
PAGE 8️⃣2️⃣▶️8️⃣3️⃣

_________________________
Mamaki ne ya kama kowannensu a wajan. Fashe wa da kuka Zubaida ta yi tana mai faɗin. "Kenen ba za'a yi aure na ba da Yarima Sooraj?, ya fifita wata ƴar aiki sama da ni".

Kallonta sarki ya yi ya ce. "Ki kwantar da hankalin ki, auren ki da Sooraj babu fashi wannan alƙawari na ne, yana dawo wa za'a ɗaura miki aure da shi".

Kallonsa Gimbiya Saratu ta yi ta ce. "Ai tunda lokaci ya kusa me zai ana a ɗaura masa auren naga dai ana yin hakan, a ɗaura mai aure a masallaci yana dawo wa kawai saidai ya wuce gidan matarsa.

"Wannan ba shawara ba ce mai kyau gwara a ce yana wajan kuma ya bada sadaki da kansa ba tare da wani ya yi masa hakan ba". Cewar sarki.

Nan sarki ya bawa duk wanɗan da suka hallaci masarauta domin auren Sooraj haƙuri. Yayin da gaba ɗaya suka wuce masallaci kawai don sallah juma'a.

Da sauri Mami ta nufi inda su Amrah suke murmushi kan fuskarta. Ƙarasawa ta yi wajan su ta ce. "Yara na ku shigo ciki nan gidan sarki ne ku ɗauka tamkar kuna gidan ku kunji. Ki shigo".

Murmushi Safira ta yi ta ce. "Mun gode da kulawa, amma a halin yanzu bamu ga ta zama ba. Munje waccan dajin ne domin nema wa mahaifiyar mu ƴanci yanzu tunda mun samu abin da ya kai mu shi ke nen tafiya zamu yi".

Girgiza kai Mami ta yi ta ce. "Tafiya kuma, daga zuwanku fa ko hutawa baku yi ba. To tun da sun tafi masallaci ki ku shigo kuyi sallah sai kuyi wanka ko, kafin nan kunci abinci".

Girgiza kai suka yi ba tare da sun musa da abinda ta ce ba suka bita izuwa ciki.

Kai tsaye ɗakin da aka bawa Zahra suka nufa yayin da take nan da chan da su.

Murmushi ta yi ta ce. "Karfa ku ƙullace ni na wahalar da ku da nake, ina yin hakan ne saboda ina farin cikin ganin ƴan uwan Zahra. Kunga wannan ɗakin shi ne ɗakin da Zahra ta zauna a ciki. Tunda ta shigo masarautar nan rayuwata ta sauya daga ƙunci zuwa farin ciki. Gaba ɗaya saida ta saita wa kowa zama a gidan nan, shi ya sa nake alfahari da ita".

Murmushi kawai suka sakar mata. Nan Safira ta miƙe tare da kama hannun Amrah suka je suka yi alwala duk da cewar Amrah bawani sanin addini ta yi ba hakan ya sa duk abin da ta ga Safira ta yi ita ma saita yi. A haka har suka yi sallah.

Suna zaune a ɗaƙi masu aiki suka kawo musu abinci. Nan suka zaune suka fara ci domin dama yunwa suke ji.

B
Ita kuwa Mami bar musu ɗakin ta yi ta nufi hanyar part ɗin ta.

*****
Kuka kawai Zubaida ke faman yi ganin yadda ta ga soyayyar Zahra ƙarara cikin idanuwan Sooraj.

A daidai lokacin ne su kuma Gimbiya Saratu suka shigo ɗakin nata, nan suka sa ƴan aikin su fita daga cikin ɗakin. Ba tare da ɓata lokacin ba suka fice daga ɗakin.

Kallon Zubaida suka yi wacce ta yi shaɓe-shaɓe da hawaye. Ba tare da ɓata lokaci ba suka bushe da dariya.

Cikin dariya Gimbiya Talatu ta ce. "Wai ke ƴar soyayya ko?, maganinki kenen ai, gashi nan wata ƴar aiki ta zo ta kama zuciyar Sooraj ke kina nan zaune tamkar wata bahamagiya. Dama an ce wanda yaƙi ji ba zaiƙi gani ba".

"Rabu da ita Talatu, dama ai na gaya miki duk wanda ya ci tuwo da mu miya yasha, ba da kina wani jijida kanki ba kina wani cewa babu mai raba ki da Sooraj, gashi a gaban kowa ya ce Zahra ita rayuwar sa ce. Hmm Allah sarki amma fa naju miki ba dad'i". Cewar Gimbiya Saratu wanda ta ƙara kwashe wa da dariya a karo mara adadi.

Share hawayenta Zubaida ta yi ta ce. "Dan Allah kuyi haƙuri tabbas na gane kuskure na, yanzu ina son nima na zama ɗaya daga cikin ku, dan Allah ku taimaka min please".

Kallon juna Saratu da Talatu suka yi sannan Talatu ta ce. "shi ke nen zamu taimaka miki, amma kiyi alƙawarin cewa ba za ki juya mana baya ba kuma ba za ki ci amanar mu ba".

Girgiza kai Zubaida ta yi ta ce. "Nayi alƙawarin cewa ba zan juya muku baya ba, na rantse".

Murmushi Saratu ta yi ta ce. "Good girl, yanzu abin da za mu yi shi ne ki tawo mu je ɗakin A'isha".

Tana idda maganarta suka nufi hanyar ɗaƙin Mami.

Banka ƙofar da ƙarfi Zubaida ta yi wanda ya sanya Mami razana.

Da sauri Mami wacce ke kwance kan gado ta miƙe tana mai binsu da idanuwa. "Lafiya?, me ya faru naga kunzo a wannan lokacin?".

Tsaki Zubaida ta buga sannan ta ce. "Munafuka algunguma, ni dama na san ba san aure na ki ke yi da Sooraj ba shi ya sa lokacin da ya tafi baki dakatar da shi ba matsayin ki na uwarsa".

Sakin baki Mami ta yi yayin da ta ji maganganunta tamkar saukar aradu. Nuna kanta Mami ta yi yayin da ta ce. "Zubaida ni ki ka buɗe baki ki ka cewa munafuka algunguma?, kina cikin hayyacin ki kuwa?".

Amsa Zubaida ta ba ta da cewar. "Ƙwarai ina cikin hayyaci na ba giya nasha ba balle ki ce na bugu, wallahi idan baki bari aurena da Sooraj ya faru ba sai na nuna miki cewa tabbas ni ƴar ƙwalta ce, kuma ki sani muddin Sooraj ya dawo da wannan tsinanniyar yarinyar nan gidan baki ce ta bar masarautar nan ba, saina nuna miki cewa ruwa ba sa'ar kwando ba ne".

Sakin baki Mami kawai ta yi tana kallon Zubaida da su Saratu. Ji take tamkar a mafarki, wai Zubaida da ce ke kallon tsabar idanuwanta take gaya mata maganganu masu ɗaci.

Murmushin mugunta Gimbiya Saratu da Talatu suka saki yayin da Talatu ta ce. "Da ba Zahra da Sooraj ne gatan ki a gidan nan ba, to yanzu kuma basua nan, muna da damar yi miki duk abin da muka gadama, kuma ki sani cewa a baya ma ba ƙyale ki muka yi, kawai dan ɗanki shegen nan haihuwar asar..... Maganarta ne ya dakata sakamakon saukar mari da ta ji kan fuskarta.

Zaro idanuwa waje suka yi ganin abinda ya faru.

Cikin huci Mami ta ce. "Idan har ki ka ƙara kiran ɗana da haihuwar asara sai na lahira ya fiki jin dad'i. Aba!, aba!, wai sai kace a kaina aka fara kishiyoyi, da har za ku bi ku addabi rayuwata, kun daɗe kuna yi min abinda ranku ya gadama a gidan nan, amma kusani cewa yanzu haƙuri na ya ƙare, da ina yin shiru ne kawai domin samun zaman lafiya amma ku naga ba hakan ku ke so ba. To ku kuji na faɗa muku na girme ku nesa ba kusa ba, duk wata shegiya da ta ƙara kawo min rainin hankali saina yi maganinta. Ke kuma Zubaida na rabu da ke ne saboda Uncle Sadiq wato mahaifinki da ba dan aka ba da saikin yaba wa aya zaƙin nata. Aba mutum yana haƙuri da ku amma saida ku ka tirje ku ka yi mai yuwa har ku ka kaishi bango".
Chapter 23 · 0% Book details