← Book details Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 65

Sashe 4

Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Girgiza kai Zahra ta yi. "Uhmm yaro bai san wuta ba saiya taka. Tirrr shashashar banza kawai mara hankali. Ni na faɗa miki nafi ƙarfin ki wallahi, na gani na bari ƙwalelen agalawa. Idan kina takama da kuɗi ni da Allah na dogara Kuma idan kin isa kizo ki gafza faɗa da ni kiga yadda zan yi miki shegen duka.

Tsaki Safira ta buga. A sa'inda Amrah na gefe tana karantar zuciyoyin Zahra da Safira. Yayin da Zahra na faɗin."wallahi yarinyar nan ta shigo hannu na ko saina yi mata dukan kawu wuka, domin saina chanza mata kamanni, shegiya mai bakin triangle".

Yayin da ɓangaren Safira ke faɗin. "This girl is crazy, wannan daga ganinta ƴar daba ce, ya kamata naja baki na domin wannan tafi ƙarfin a kirata ƴar jagaliya, wannan shugaba ce a jagaliyan ci".

Murmushi kawai Amrah ta yi bayan gama karantar kowanensu da ta yi.

Maida kallonsa Sooraj ya yi kan Aliyu ya ce. "Mene haɗin ka da Mrs Lailah?, ɗazu naji kana cewa Mrs Lailah ƴar Uwar ka ce?".

Shiru Aliyu ya yi na ɗan wasu lokuta kana daga bisani ya ce. "Eh ita ɗin ƙanwar mahaifina ce".

Ana tsaka da haka tsayuwar mota a wajan. Fitowa Dpo ya yi daga cikin motan tare da fara waige-waige.

Hango shi da Zahra ta yi ya sa ta saurin koma wa bayan Sooraj ta ce. "Dan Allah ka ɓoye ni, wannan mutumin yana zuwa zai ce zai tafi da ni".

******
"Har yanzu fa mun kasa samun diddigin du Aliyu, ni fa damuwata kada muje wani abu ya cutar da su". Cewar Daddy.

Tagumi Mom ta yi yayin da zuciyarta ya cika fal da tsoro.

"Allah ka sa duk inda suka shiga ya kasance suna cikin tsaro". Cewar Grandma.

**********
Gov. Musa na zaune parlour yana shirya mugayen plan kan yaran Mrs Lailah ya ji ƴan sanda sun shigo parlour tare da yaransa.

Miƙe wa Gov. Musa ya yi ya ce. "Me ya kawo ƴan sanda kuma a gida na".

Nuna shi Usman ya yi ya ce. "Officers shi ne wannan ki tafi da shi har sai ya fito mana da ɗan uwan mu da ya sace".

Kallonsa Gov. Musa ya yi ya ce. "Usman are you okay?, is something wrong with your brain?, ni kaida ƙannenka za ku kawo wa ƴan sanda?".

"Eh mun kawo ɗin". Cewar Ramlat sannan ta ƙara da cewa. "Am sorry to say, Abba you are heartless, samm bamu yi dacen mahaifi ba. Police maza ku ɗauke shi ku tafi da shi".

Kallon sa ƴan sandan suka yi tare da nuna police warrant ɗin su.

Kallon ƴan sandan Gov. Musa ya yi ya ce. "Dan Allah kada ku biye musu, ta ya Uba zai sace ɗansa?".

Amsa ɗaya daga cikin police ɗin ya basa da cewa. "Sanin hakan ne ya sa muka zo. Ya kamata kayi cooperate da mu. Domin duk abinda ka faɗa a nan will be use in court".

Miƙe wa tsaye Gov. Musa ya yi ya ce. "Ku faɗa duk abinda ku ke da buƙata ni zan baku, amma dan Allah kada ku kaini kotu domin ni ɗin babban mutum ne kuma ba zan so mutunci na ya zube a gaban mutane ba".

"Ka bamu haɗin kai, dan ka kasance babban mutum ɗin ne ya sa ka ga muna maka magana a haka da a ce wani ne da tuni mun tasa ƙeyar sa gaba da bindiga dan haka kayi surrender kawai".

"Shi ke nan". Gov. Musa ya faɗa yayin da ya bisu suka tafi police station.

*******
Hango su da Dpo ya yi ne ya sa ya nufi inda suke. Cike da zallar mamaki yake bin Amrah da Safira da kallo. Cikin ransa ya ce. "Dama ƴan uwan Zahra na raye, dole na sanar da Hajiya Binta wannan lamari".

Ƙarasawa inda suke ya yi sallama riƙe a bakinsa. Amsa sallamar suka yi gaba ɗaya.

Kallon su ya yi ya ce. "Wane ne Sooraj a nan wajan?".

Ɗaga hannun sa Sooraj ya yi ya ce. "Ni ne me ya faru".

Amsa Dpo ya bashi da cewa. "Dama zuwa nayi saboda Zahra, tana Ina?".

Amsa wa Sooraj ya yi da cewa. "Ga Zahra kana kallo". Ya faɗa yana mai nuna Safira.

Murmushi Dpo ya yi ya ce. "Ni fa ba yaro ba ne ba, Zahra idanuwanta ba blue ba ne brown ne ka ga wannan ba Zahra bace. Dama Hajiya Binta ce ta ce na kawo mata wannan littafin amma tunda bata nan bara na koma".

Jin ya ambaci Hajiya Binta ya sa Zahra ta yi saurin fito wa daga bayan Sooraj. Sannan ta ce. "Gani nan Dpo".

Kallonta Dpo ya yi ya ce. "Dama kina nan laɓe wa ki ka yi?, tom shi ke nen dama Hajiya Binta ce ta ce. "Na kawo miki wannan littafin yanzu kuma naga harda ƴan uwanki kinga da su za ki karanta wannan littafin mahaifiyar taku".

Dariya Zahra ta kwashe da shi sannan ta ce. "Dpo ba fa ƴan uwa na ba ne ba, su ɗin kawai kama suke da ni bakomai ba".

"Tabbas ƴan uwan ki ne su ɗin, kuma kema ƴar uwar su ce". Waigawa gaba ɗaya suka yi domin ganin waye.

MK suka gani zaune kan dutse tashi ya yi tare da ƙarasawa inda suke.

Kallonsa Safira ta yi ta ce. "Ta ya ya muka zama ƴan uwa ɗaya?".

Amsa wa Mk ya yi da cewa. "Ta hanyar mahaifiyar ku, wacce take tare da ke a gida ita ɗin ba ita ce asalin mahaifiyar ki ba, ita ɗin kawai ta raine ki ne a matsayin ƴar cikinta".

"Ta ya ya to hakan zata kasance?". Cewar Amrah.

Amsa wa Mk ya yi ya ce. "Ku karɓi littafin da ke hannun Dpo daga nan za ku fahimci komai da komai".

Miƙa hannu suka yi tare da karɓar littafin sannan su ukun suka samu guri suka zauna.

Jikin kowanensu ne ya yi sanyi. A hankali Zahra ta fara ƙoƙarin buɗe wannan littafi.

*BARKA DA SHIGOWA SABUWAR SHEKARA, ALLAH KA SA MUGA ALKHAIRY DA KE CIKINTA🙏🙏🙏*

*MU HAƊU A PAGE NA GAMA DOMIN GANIN MENE NE CIKIN WANNAN LITTAFI*

LIKE AND SHARE FISABILILLAH 🙏🙏🙏

ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞💞
ZINARIYAR JAJIRTATTU.

بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎

*BOOK 2*

PAGE 6️⃣1️⃣▶️6️⃣2️⃣
_______________________
Buɗe littafin da Zahra ta yi keda wuya ta ga an rubuta . "Ban yarda wani ya buɗe littafin nan in ba jini na ba".

Ajiyan zuciya su Zahra suka sauke sannan ta buɗe ɗayan page ɗin.

"Duk abinda zan rubuta ina rubuta wa ne cikin ƙunci da dana sanin yarda da na ɗora wa Mutane ne, sannan ina rubuta wa da jini na da kuma hawaye na, ban sani ba ko daidai nake aikata wa ko ba daidai ba"

"Da farko dai sunana Lailah Abdullahi wanda haka fi sani da Mrs Lailah, ni ɗin haifaffiyar garin Jigawa ce. An haife ni ne a shekara ta alif ɗari tara da saba'in (1970). Na gama makarantar secondary ina da shekaru sha shida wato a shekarar ta alif ɗari tara da tamanin da bakwai(1987). Mahaifina da mahaifiyata suna matuƙar ƙaunata kasance wa ta mace ɗaya tilo cikin ƴan uwa na, ina da yayyi maza wanda suke matuƙar ji da ni Yahya Yusuf sai kuma Ibrahim. Yaya yusuf shi ne babban ɗa ga mahaifin mu mai suna Salisu, sai kuma ya'ya Ibrahim na biyu ni kuma ta ƙarshe. Gaba ɗaya muna nuna wa juna sosai fiye da yadda muke ƙaunar kanmu. Mahaifin mu ya kasance babban ɗan kasuwa yayin da ya mallaki duniyoyi masu tarin yawa, hakan ya sa ya kudiri aniyar cewa dole ɗaya daga cikin yaransa su gaje shi. Amma yayyi na guda biyu sam basu da ra'ayin yin aiki irin na mahaifin mu. Amma fuskantar cewa mahaifin mu yana son ɗaya daga cikin mu ya gaje shi, hakan ya sa na nemi admission yayin da na zaɓi course ɗin business administration wato (Gudanar da kasuwanci). Ba dan raina yana son hakan ba sai dan kawai na faranta wa mahaifina rai. Na fara karatu na a University wanda ke a Zaria wato Ahmadu Bello Zaria (ABU) wanda aka kafa a shekara ta alif ɗari tara da sittin da biyu (1962). Bayan fara wa ta Ya'ya Yusuf ya yi aure a (1988) wanda haka ci aka sha. Bayan shekara ɗaya matar yayana ta haifo ɗa namiji wanda ya ci suna Aliyu. Haka komai ya cigaba ba tare da samun wata matsala ba, ana tsaka da haka na haɗu da Abdullahi wanda shima yake karatu a Ahmadu Bello saidai yana karantar political science shi da babban abokinsa mai suna Musa Muhammad wanda mahaifinsa burinsa shi ne ya karanci engineering amma saboda tunanin cewa siyasa ta fi kawo kuɗi sai ya chanza course ya koma political science. shima yana da budurwa mai suna Khadijah. Gaba ɗaya mu huɗun muka zama aminai na kud da kud, ko ina tare muke zuwa idan haka ganni za'a ga Abdullahi idan haka ga musa ba za'a ga Khadijah, haka rayuwa ta cigaba yayin da kanmu ya kasance a haɗe. Musa ya bayyana wa khadija soyayyar sa, a sa'inda ya kai kuɗin ta haka saka musu rana, cikin kwanaki ƙalilan haka ɗaura musu aure. Ni da Abdullahi muna son juna yayin da ita kanta makaranta ta shaida hakan.

A lokacin Abdullahi da Musa suka riga ni gama University yayin da su biyun suka nemi takarar shiga siyasa, cikin sa'a Abdullahi ya yi nasara yayin da shi kuma Musa bai yi nasara ba domin babu wanda ya karɓe sa hannu biyu".

Abdullahi ya zama babban ɗan siyasa ya yi alƙawarin gyara ƙasar sa da mutanen cikin ta. Musa ya ji aushi sosai ganin abokin saya samu takara shi bai samu ba, hakan ya sa ya ɗora tsanar duniya a kan abokin nasa, a yayin da yake zuwa wajan Abdullahi da fuska biyu na kirki da kuma na mugunta".

"Bayan na gama makarantar University na karanta master's da degree tareda yin PhD na fito da first class upper, na fara business, cikin ikon Allah na tara dukiyoyi na cikin shekaru uku na gina kamfanoni na kaina guda goma manya-manya a ƙasashe da ban da ban. yayin da duk suke ɗauke da sunana.
Chapter 4 · 0% Book details