← Book details Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 65

Sashe 22

Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aka ta cigaba da tura dutsen ba tare da ta gaji ba. Chan daga nesa ta hango ruwa masu kala uku fari, baƙi da kuma ja wanda suka yi zagaye sai suka bada cycle yayin da tsakiyar su kuma ya kasance rami ne mai zurfin gaske.

Ƙarasawa wajan ta yi da dutsen kana daga bisani ta dakata. Kallon dutsen ta yi ta ce. "Gashi nan dai na isa wajan amma ban san a wane ruwa zan jefa ka ba".

Dariya dutsen ya kwashe da shi. Nan take ya rikiɗa izuwa tsohon mutum.

A razane Amrah ta ja da baya.

Girgiza kai tsohon ya yi ya ce. "Kada ki tsorata, tabbas na yaba da irin jajircewa da kuma baiwar da Allah ya yi miki. Tabbas ni ɗin aljani ne amma ba aljanin ruwa ba, na kawo ki nan ne domin nuna miki wannan ruwan".

Kallonsa Amrah ta yi ta ce. "To mene ne alaqa ta da wannan ruwan?".

Amsa tsohon ya ba ta da cewa. "Tabbas kina da alaqa ba ke kaɗai ba harda sauran ƴan uwanki. Kowacce a cikin ku za ta shiga ɗaya daga cikin waɗan nan. Kuma duk wanda kowannen ku ya shiga zai sami abin da yake so. Saidai ɗaya daga cikin wannan ruwan idan aka shiga ba'a dawo wa. Dan haka yanzu zaɓi ya rage naki. A cikin ku uku kece za ki fara zaɓar wanda za ki shiga".

Sauke ajiyan zuciya Amrah ta yi!, cikin rashin tsoro ta ce. "Na zaɓi ruwa fari zan shiga".

Tana gama faɗar hakan ta faɗa a ruwan nan
Ta tarar da ƙaton ƙarfe mai kama da takobi tare da maƙulli mai sheƙi a kansa.

Farin ciki ne ya kamata ganin cewa ta samu muƙulli. Nan take jiri ya ɗebe ta ta suma.

*******
"Muna da bukatar ka yarda mu tafi da Mrs Lailah izuwa garin Jigawa, domin haɗuwa da ahalin ta". Cewar ɗaya daga cikin ƴan sanda.

Girgiza kai Sooraj ya yi ya ce. "Me zai ana indai ta amince bani da matsala da hakan. Nima very soon zanyi joining ɗin ku. Yanzu ana shirye-shiryen aure na ne shiyasa ba zan samu damar binku ba amma zan zo daga baya".

Godiya sosai jami'an suka yi masa daga bisani suka tafi. Nan suka koma asibitin yayin da suka bawa likitoci evidence daga bisani suka ɗauki Mrs Lailah suka nufi hanyar jigawa da ita.

********
"Tunda har kin san ƴar uwata to tabbas zan taimaka miki a wannan tafiyar ta ki. Maza ki cigaba da tafiya a gaba za ki haɗu da dutse mai kuka, zai ce ki taimaka masa kada ki kuskure ki ƙi taimakon sa. Domin shi ne wanda zai kaiki inda ki ke da buƙatar zuwa".

Godiya sosai Zahra ta yi
Kafin daga bisani ta soma tafiya. Saida ta shafe hawanni goma Zahra na tafiya yayin da tana tafe tana waƙe-waƙe.

Ji ta yi gaba ɗaya gabanta yana faɗuwa. Tamkar wani abu na shirin faruwa da ita.

Da mamakin ta kuwa ta hango dutse mai kuka kamar dai yadda dattijuwar aljana ta faɗa mata.

Ƙarasawa ta yi inda dutse yake ta ce. "Toh tabbas babu sarki sai Allah. kai kuma me ya sa ka ku ka?, kuma dama dutse na motsi".

"Eh ina motsi ni ɗin na kasance aljanin ruwa ne shi ne na aikata laifi a ka maida ni dutse. Idan da a ce za ki iya taimako na ki tura ni izuwa cikin ruwa, da nayi farin ciki sosai kuma kema zan taimaka miki, wajan neman abin da ki ka zo nema". Dutsen ya faɗa kamar yadda ya furtawa Amrah a farko".

Girgiza kai Zahra ta yi ta ce. "Ta ya ya ne zan iya tura ka ni da ba Iliya ɗan mai ƙarfi ba ce?".

Amsa dutsen ya ba ta da cewa. "Idan har ki ka sa yaƙini a zuciyarki za ki iya".

"To ta ya ya zan san inda ruwan yake?". Cewar Zahra.

Amsa dutsen ya ba ta da cewa. Hannun dama za ki bi a nan ni kuma zan faɗa miki".

Nan Zahra ta rintse idanuwanta yayin da ta cigaba da jin zuciyarta na faɗuwa!.

Cikin daƙe wa ta fara tura dutsen tare da yin hanyar dama kamar yadda ya buƙata.

Chan ta hangi ruwa guda uku a zagaye masu launuka daban-daban.

Ƙarasawa ta yi wajan sannan ta ce. "To wane ruwa zan saka ka?".

Nan dutsen ya kwashe da dariya tare da rikiɗa izuwa tsoho.

Zaro idanuwa Zahra ta yi waje tare da fasa ihuu!.

Da sauri tsohon ya dakatar da ita da faɗin. "Kiyi haƙuri ni ɗin ba aljanin ruwa ba ne. Ɗaya daga cikin ruwan nan za ki zaɓa ki shiga domin nemo abinda ki ke da buƙata game da mahaifiyar ku. Amma ɗaya daga cikin ruwan nan idan aka shiga ba'a dawo wa, saidai ikon Allah".

Nan Zahra ta shiga tunani. Cikin kasala da faduwar gaba ta rintse idanuwanta. Ba tare da jinkiri ba ta faɗa cikin ɗaya daga cikin ruwan.

********
Ɓangaren Safira ma the same thing abinda ta ya faru da su Zahra ita ma ta haɗu da wannan dutsen mai kuka inda ta shiga ruwa mai launin ja.

Saida kowaccensu ta shafe kwanaki huɗu a cikin wannan ruwan inda Amrah ta tsinci kanta cikin kogo, ita kuma Safira ta tsinci kanta cikin daji mai cike da gold da abubuwa. Ita kuwa Zahra tsintar kanta ta yu cikin wani guri mai matukar duhun gaske.

******
Ɓangaren su Sooraj kuwa biki ake na bugawa a jarida. Yayin da fadar sarki ta cika da mutane, gwamnoni da ƴan majalisa tare da masu kuɗi. Motoci kawai kake gani tare da ƴan sanda da kuma sojoji.

Ko ina ya cika da masu girke-girken abinci. Duk inda ka gifta saidai kaji kamshi na tashi.

Amarya Zubaida ansha lalle da kitson attachment yayin da aka yi henna day da bridal shower.

*****
Ɓangaren Mrs Lailah kuwa a lokacin da jami'an suka tafi da ita. Ta buƙaci kada su kaita gidan su kawai su nufi gidanta da ita. Kamar yadda ta buƙata aka suka kaita take zaune a chan ba tare da su Dpo sun sani ba.

***
Ɓangaren su Alhaji Abdullahi kuwa masaukin baƙi Grandpa ya kai su suke zaune a chan, tun tsawon waɗan nan kwanakin basu san da cewar Mrs Lailah tana garin jigawa ba.

*****
*After two days*

Yau ne ranar da za'a ɗaura auren Sooraj da Zubaida yayin da kowa ya zo massalacin masarauta domin shaida hakan.

Ɓangaren Sooraj kuwa. Shaddar da Zahra ta zaɓar masa maimakon genzna wato ishirinka a kwanakin baya ya saka. Yayin da su Umar ma suka ci shadda sun yi kyau abinsu.

Kallo ɗaya za ka yi wa Sooraj ka san da cewar baya cikin farin ciki da walwala.

Lura da hakan da su Aliyu suka yi ya sa Aliyu faɗin. "Wai ba kai ne ka ce kana son auren nan ba?, ya kuma naga kamar baka cikin farin ciki?".

"Kaima dai ka faɗa Aliyu, ni dai ban san me ke damun wannan abokin nawa ba, gaba ɗayan shi a boɗe yake. Koma dai me za ka yi aure ne babu fashi sai an ɗaura tunda kai ne ka ce kana so, da baka ce kana so ba da ba a baka ita ba. Kuma karka manta yau juma'a bayan an idar da Sallah za'a ɗaura muku aure".

Shiru kawai Sooraj ya yi domin ya rasa abin cewa. Ji yake kamar akwai abin da yake tafiya ba daidai ba".

******

Ɓangaren Zahra kuwa babu abinda take fuskanta sai farmaki daga wajan munanan halittu na inda ta shiga.

Farfaɗo wa Amrah ta yi daga suman da ta yi. Tare da miƙe wa sannan ta nufi inda wannan maƙullin zinaren yake sannan ta ɗauka. Ta ɗaukar wannan maƙullin ta ga wannan takobin ya rikiɗa izuwa ƙofa. Cikin farin cikin ta shiga cikin wannan ƙofar. Nan ta tsinci kanta a ƙofar dajin.

Godiya ta yi wa Allah ganin ta ƙofar da ta shiga nan ta fito.

A dai-dai wannan lokacin ta ga Safira ma ta fito hannunta riƙe da akwatin zinare.

Hamdala Safira ta yi ganin ita ma ta fito ta hanyar da ta shiga. Nan suka haɗa idanuwa da Amrah. Cikin farin ciki ta ce. "Kema kin fito kenen, kenen hakan yana nufin kin rayu".

Murmushi Amrah ta yi mata. Nan take wannan murmushi ya rikiɗa izuwa tsantsar damuwa. Kallonta ta yi hankali tashi ta ce. "Kenen iya ni da ke ne muka samu fitowa?, kenen hakan yana nufin Zahra ita ce wacce za ta mutu, ba zata dawo wa".

Zaro idanuwa waje Safira ta yi sai a lokacin ta lura da hakan. Nan take hankalin su gaba ɗaya ya tashi. Nan da nan suka fara kuka.

Ɓangaren Zahra kuwa. Gaba ɗaya ta galabaita domin waɗan nan halittun sunji mata raunuka masu munin gaske. A halin da take yanzu ko ɗan yatsarta ba za ta iya motsa wa ba domin duk sun galabaita.

Babu abinda take ambata sai sunan Allah da sunan mahaifiyarta.

******
Share hawayenta Safira ta yi da sauri ta ce. "Yanzu ba kuka ne ya kama ce mu ba, maza mu tafi izuwa masarautar su Sooraj domin mu sanar da su".

Girgiza kai Amrah ta yi tare da binta suka fita izuwa bakin titi. Nan suka tsayar da mai adaidaita sannan suka ce ya kai su izuwa gidan sarki.

Cikin ƙanƙanin lokaci suka isa izuwa masarautar. Yayin da mai adaidaita ya shiga ɗaukar su a hoto ba tare da su sani ba, dalilin hakan kuwa shi ne ganin yadda suke matuƙar kama da juna kuma launin idanuwan kowaccensu da ban yake.

Mamaki ne ya kama su ganin ne ya kama su Amrah ganin motoci a jere a ƙofar gidan sarki.

Shiga cikin masarautar suka yi ba tare da su bawa mai napep kuɗinsa ba. Shi kuwa mai napep bai damu ba domin dama ya ce koda sun bashi ba zai karba ba kar ya je ba mutane ba ne".

Tunda suka sanya kafafuwansu cikin masarautar ake binsu da kallo. Yayin da su kuwa gefe ɗaya hankalinsu a matuƙar tashe.

Daga nesa su Aliyu suka hango su gaba ɗaya sun galabaita.
Chapter 22 · 0% Book details