← Book details Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 65

Sashe 34

Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ka kalli wannan mahaifiyar, idan har za ka iya kallonta. Ka kalli yadda idanuwanta suka bushe da kuka, ta rasa komai, ta rasa gata, ta rasa mafarki, ta rasa mafaka duk saboda zaluncin ka a gare ta. Wannan mugunta ce da za ta biyo ka har gaban Allah. Ka sani cewa babu wani sojoji ko yawan masu tsaro da zai ana ranar lahira. Mutuwa tana nan kuma babu wanda zai tsira daga gare ta. Tambayar da za'a maka na ƙarshe ita ce , ina ka ke lokacin da ka ke da iko?, me ne abin da za ka ce?".

"Ni da ka ke gani, haka na ta so cikin dabbobi, na taso cikin rayuwar jahilci, na ta so ina cin ganyaye, na ta so ina sanya kayan gaye, ko da sau ban san dad'i uwa ko uba ba, ban san zafin rashi da samu ba, ban samu ilimi ba, ka tarwatsa rayuwar mu ta hanyar raba mu, shin kayi mana adalci?, shin kayi wa ni kaina adalci?, A ranar zagayowar haihuwar Umar, shin baka sa mutanen ka su sace ni domin nima a kaini ƙasar waje a siyar da ni, wannan abi da me ya yi kama".

Nan take ya Gov. Musa ya fashe da kuka cikin jin dana sani. "Ku faɗa min duk abin da ku ke so ni kuma zan baku, amma bana son kotu ta yi min hukuncin kisa, bana son na mutu". Maida kallonsa ya yi kan Umar sannan ya ce. "Ɗana dan Allah ka roƙe su ka ce Miss Lailah ta yafe min, wallahi nayi alƙawarin zan biya diyan waɗan da suka mutu ta dalili na, kuma zan ɗauki nauyin iyayeyen su gaba ɗaya".

Shiru kawai Umar ya yi cikin zuciyarsa kuwa kukan zuci yake domin yana jin zugi da raɗaɗi ganin mahaifinshi a irin wannan yanayin. Ko ba komai shi ɗin ya kasance mahaifin sa ne.

Kawai da kansa ya yi gefe danne zuciyarsa ya yi sannan ya ce. "An sorry Abba, ba zan iya ba". Ya faɗa tare da shige wa cikin mota.

Nan take Gov. Musa ya ji komai na duniyar nan ya fitar masa a rai.

Nan ƴan sanda suka kama shi tare da tafiya da shi cell.

Ɓangaren su miss lailah kuwa shiga cikin motar suka yi tare da barin harabar wajan baki ɗaya.

___________________
"Hello guys, ina son zan baku location ɗin asibiti, kuje ku sace wannan wanda zan baku information a kanta, karku ɓata lokaci kawai ku raba ta da rayuwarta".

Daga ɗayan ɓangaren haka je. "Hajiya Zubaida wani aikin ne ya samu kenen, karki samu damuwa kin san raba bawa da rayuwa ƙaramin aikin mu ne, indai a kan wannan ne za ki ga aiki da cikawa".

Murmushin mugunta Zubaida ta yi ta ce. "That's my boy. Ka duba whatsapp ɗin ka za ka ga gaba ɗaya bayanan yarinyar na tura maka, dan Allah bana son kowa ya zargi komai a wajan".

Daga ɗayan ɓangaren haka ce. "In dai wannan ne baki da matsala a kai".

Tana kaiwa nan ta katse wayar tare da sauke nannauyan ajiyan zuciya.

Gyaɗa kai ta soma yi tamkar wata ƙadangariya tana mai faɗin. "Ba dai ya ce ita ce rayuwar sa ba, toh idan na kashe ta sai mu ga abinda zai yi, kuma wallahi aure na da kai babu fashi sai anyi, domin idan na aure ka a nan gaba ni ce zan zamo Sarauniya a wannan fadar na dinga juya kowa yadda na gadama".

_____________________
"Masoyi ni fa yunwa nake ji". Cewar Zahra.

Murmushi Sooraj ya yi ya ce yayin da ya ji wani farin ciki ya mamaye zuciyarsa. Ji ya yi kamar anyi masa albishir da gidan aljannah. Kallonta ya yi ya ce. "Toh yau kuma ni ne masoyi?".

Gyaɗa masa kai ta yi ta ce. "Toh ko dai nayi laifi ne?".

Saurin girgiza kansa Sooraj ya yi sannan ya ce. "Aba dai ai ni dad'i naji ma a hakan. Toh mar'atussaliha me ki ke son ci?".

Amsa ta bashi da cewa. "Ni koma mene ne ka kawo min amma banda tuwo".

Dariya ne ya ci ƙarfin sa. Sannan ya ce. "Zahra kenen sarkin rigima, shi ke nen toh karki samu damuwa bara na tashi yanzu naje".

Tashi ya yi tare da nufa hanyar fita. Daga sama ya ji ta ce. "Yahya Sooraj!".

Tsayawa ya yi sannan ya dube ta ya ce. "Na'am ya aka yi?".

Amsa ta basa da cewa. "Dan Allah karka daɗe kaji".

Girgiza kai ya yi ya ce. "In sha Allah my wife to be". Ta ƙarasa tare da fita daga ɗakin.

________________
Su John kuwa sun iso garin jigawa kasancewar Flight suka bi.

Nan suka fara neman Safira, suna nuna hotunan ta a duk inda suka je, kasancewar su turawa ba kowa ke fahimtar abinda suke faɗi ba, babu abin da ma hausawan dutse ke yi sai faman kallon su.

Daga ƙarshe suka samu location ɗin da za su samu safira.

_________________
Ƴan daban da Zubaida ta sa su kashe Zahra kuwa, basu zarce ko ina ba sai asibitin da Zubaida ta basu location.

Nan suka yi shigar fadawa, yayin da hannunsu ke riƙe da flask na abinci.

Cikin reception suka shiga yayin da tambayi mara lafiya mai suna Zahra, yayin da suka bada bayanan ƙarya na cewa sarki ne ya turo su. Nan haka nuna musu hanyar ɗakin da Zahra ke ciki sannan suka shiga.

Nan suka tarar da ita a kwance ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, yayin da idanuwanta ke saman silin ɗin ɗakin.
f

Rufe ɗakin suka yi hakan ya sa hankalin Zahra ya karkato izuwa gare su.

Binsu ta yi da kallo cikin mamakin ta kuwa ta ce. "Ku kuma su waye?".

Shugaban cikin su ne ya ce. "Turo mu a kai domin mu sheƙe rayuwarki, kuma maƙudan kuɗaɗe aka bamu domin yin hakan".

Binsu Zahra ta yi da ido. Nan take ta fashe da dariya wanda ya sanya ƴan daban Zubaida suka fusata.

Kallonsu ta yi ta ce. "Kaji wata lukutar masifa. Wai kun zo ku kashe ni, toh waya turo ku?".

Amsa ɗaya daga cikin su ya bata da cewa. "Keda za ki mutu ina ruwanki da sanin wa ya turo mu?".

Amsa Zahra ta bashi da cewa. "To ai gwara na sani domin ta yadda idan na mutu zan dawo matsayin fatalwa na na addabi rayuwar wanda ya sa ku kashe ni".

"Hhhhhhh!"., Ƴan daban suka kwashe da dariya.
Sannan suka ce. "Sai kuma Allah ya kama ki babu fatalwa a gaske ba".

Gyara kwanciyar ta Zahra ta yi ta ce. "Toh ko babu sai a fara a kaina". Kunga bacci zan yi kafin rabin raina masoyi na ya dawo na ci abinci. Dan haka gwara ku yi wa kan ku faɗa ku fice daga ɗakin nan". Ta faɗa tare da rufe idanuwanta.

Nan shugaban cikin su ya bawa ɗaya daga cikin order ya kashe Zahra. Da sauri ya nufi kan Zahra tare da ƙoƙarin daɓa mata wuka. Nan take ya ji an zabga masa wata iriyar azababbiyar dorina. Nan take ya kurma ihuu, da sauri ya juya ya kalle su yana mai sosai bayansa ya ce. "Amma fa Allah ya isa na tsakani na da ku, a kan me za ku dake ni da bulala".

Cikin rashin fahimta gaba ɗaya suka dube shi sannan suka ce. "Kamar ya?, mu fa babu wanda ya taɓa ka".

Nan take suma suka fara jin saukar bulalai a jikin su. Nan take suka soma yin ihuu suna kuka wiwi. Yayin da suka dinga burgima a ƙasa.

Babu abin da kake ji a ɗakin sai sautin bulalai wanda ke ratsa jikin kowanensu. Ita kuwa Zahra barcinta take cikin kwanciyar hankali.

Saida suka ɗau fiye da rabin awa aba jibgar su, kafin daga bisani suka ji an dakata. Ganin an daina. Ya sa suka miƙe, ƙafa me na ci nan baka ba, haka suka ruga a guje suka bar cikin ɗakin yayin da jama'a suka bi su da kallo.

Gaba ɗaya sun haɗa zufa.

Shiga cikin motocin da suka zo da shi suka yi tare da barin asibitin baki ɗaya.

Daidai lokacin kiran Zubaida ya shigo. Ɗaukar wayar shugaban nasu ya yi yana huci yana sosa bayansa, tare da saka wa a speaker ya ce. "Ya akai?".

Daga ɗayan ɓangaren Zubaida ta ce. "My guy, aiki na ya kammala ko?".

Nan take ta ji, Ya fara kututtuma mata ashar, ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba. "Shegiya, ƴar kutumar uba, kin sa munje mun daku a banza a wofi, ke kin san yarinyar nan ba mutum bace ki ka tura mu kashe ta?, kin sa munje mun ci duka a banza, wallahi idan ki ka ƙara kira na sai na lahira ya fiki jin dad'i, har da wani cewa my guy, na bi my guy da gudu ba wando. Kuma wallahi Allah ya isa, shegiya fitsararriya, ƴar wahala".

Yana kaiwa nan ya kashe wayar.

Gaba ɗaya hankalin Zubaida ya tashi jin maganganun ɗan dabanta.

MANAGE PAGE PLEASE🙏🙏🙏

MU HAƊU A PAGE NA GABA🙏🙏🙏🙏

KADA KU MANTA DA LIKE, COMMENTS, AND SHARE FISABILILLAH 🙏🙏🙏🙏🙏🙏

ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞
ZINARIYAR JAJIRTATTU

*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎

*A'ISHA M.B*💞💞

*BOOK 2 PAGE9️⃣6️⃣▶️9️⃣7️⃣*
________________________
Zama ta yi tare da fidda iska mai zafi. Girgiza kanta ta soma yi sannan ta kalli sama kamar mai tunani. A take ta miƙe tsaye sannan ta ce.

"Me su ke nufi Zahra ba mutum bace?, dole wannan yarinyar wani makircin ta ƙalla, dole sai nayi maganinta da kai na ba tare da na buƙaci taimakon kowa ba".

______________________
Shigo wa cikin reception Sooraj ya yi hannunsa riƙe da leda alamun ya siyo abu. Kai tsaye ɗakin da Zahra ke ciki ya nufa tare da murɗa handle ɗin kofa sannan ya kutsa kai ciki.

Chakk ya ja burki ganin Zahra a tsaye rai bace ta kama ƙugunta da hannayenta guda biyu.

Mamaki ne ya bayyana kan fuskarsa wanda hakan ya sa shi faɗin. "Lafiya Zahra na ganki a haka?".

Shiru ta yi masa ba tare da ta maida masa da martani ba.

Dubanta ya yi a karo na biyu sannan ya ce. "Zahra tambayar ki fa nake kin yi min shiru".
Chapter 34 · 0% Book details