← Book details Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 65

Sashe 55

Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Me ya faru?”. Ya tambaye ta.
Kallonsa Zahra ta yi ta ce.
“Na karanta saƙonka. A wayar Zubaida. Ka ce cikin da take da shi naka ne... amma ba da yardarka ba. Ka ce ta cuce ka. Kuma kai da bakinka ka ce zaka tona asiri idan bata bar ka ba. Da gaske kake?. Wato duk ka shirya mata hakan ne saboda ta auri yayanka, kai wane irin mugun mutum ne haka?".

Junaid ya tsaya cak. Idonsa ya sauka ƙasa. Zahra ta matso.

"Junaid, ka faɗa min gaskiya. Kai ne mahaifin cikin nan?”

Shiru ya cika ɗakin. Sai daga bisani Junaid ya ja numfashi ya ce. "Eh. Na san ba zan iya ɓoyewa ba, na san zaki gano. Ina ƙoƙarin kare sunana ne, kare kai na daga abin da ban aikata da nufina ba”

Girgiza kai Zahra ta yi ta ce. "Ban yarda da kai ba Junaid, tabbas kai ne ka tirsasa mata, ta ya ya za'a ce mace ce zata sa namiji ya kusance ta ba tare da izinin sa ba, kasan ba abu ba ne mai yiwuwa".
“Zahra,” ya katse ta, “Na shiga firgici. A daren nan ta zo, ta kawo min juice, sai barci. Na farka da jiki ba kaya, zuciyata a bige, da ita tana kuka tana cewa wai nayi mata fyaɗe, na ƙeta mata haddi duk da bana cikin hayyaci na amma ban yarda zan aikata hakan ba".

Zahra ta tsaya tsaye a gaban Junaid, zuciyarta na ambaliya da hargowa. Tana jin kamar duniya na juyawa a kansa. Bayan ya gama bayani, ta girgiza kai da takaici.

"Kai kake cewa ba ka aikata ba, amma cikin ya fito daga kai? Haba Junaid, wannan wace irin magana ce? Ashe ka iya ƙarya da sauƙi haka?”.

Junaid ya kalleta cikin razana. “Zahra, me kike nufi? Ni ba ƙarya nake miki ba".

“Shut up!” Ta ɗaka masa tsawa. “Kayi shiru! Zubaida ba irin wannan yarinya bace da zata aikata abinda kake faɗa. Ka san cewa Sooraj ya amince da kai, kuma yanzu kana son tonawa yarinyar mutane asiri da ƙarya?”.

Junaid ya ce “Amma..... Bai ƙarasa ba ya ji ta ce. “Enough!” Idonta ya kaɗa ja. “Na san irin ku. Idan mace ta fara samun kulawa, sai ku so ku ruɗata da munafunci. In dai haka ne, to ina gaya maka bazan yarda da wannan karyar taka ba. Zubaida bata aikata hakan ba".

“Zahra kina tunanin zan ƙirƙiri wannan azabar?”. Cewar Junaid

Nan Zahra ta ce. "Na fi yarda da Zubaida akan kai!”

Shiru ya ɗauki dakin, sai ga wani motsi. sai ta ji kamar motsi. Zahra ta kalli can, bata lura da komai ba. Sai dai duk wannan maganar Talatu da Saratu suna maƙale a bakin taga suna saurarawa kamar katuwar masifa.

Saratu da Talatu, waɗanda suka ɓuya a bayyane, suka kalli juna da murmushin ɓarna. Sun jiyo komai. Talatu ta ce,

“Kinyi sauraron kalmomin Zahra kuwa? Wannan dama ce, kawai sai mu saka wuta a ƙasa, ita ta ƙone.”
Gimbiya Saratu ta raɗa wa Talatu cewa. “Ai yau masarauta zata ga hazo,” cewar Saratu tana gyara gyale".

Suka fito da sauri suna kuka da ihu kamar masu alhini. sun fito cikin sauri suna haki kamar wanda aka kai wa farmaki

"Kuje ku ji! Zahra da Junaid suna cikin ɗaki, suna jayayya akan cikin da Zahra take da shi! Ai wallahi mun jiyo da kunnuwanmu.”

Mutane suka tsaya cak. Mami ta ce. “Cikin wa kika ce?”
Saratu ta girgiza kai cikin munafurci ta ce

“Cikin Junaid fa, yanzu fa suka kammala faɗa akan cewa wai Zahra ta zubar da ciki ne saboda yana tsoron abun ya tonu.”.

Gimbiya Talatu ta daura hannu a kirji.
"Wai ita ce mai ladabi? Ashe 'yar iska ce!”.
Ɗaya daga cikin masu aikin masarauta ya gaggauta aika sako zuwa gidan su Sooraj
“Yarima Sooraj! Gimbiya! Ku zo masarauta da gaggawa, matsala ce babba!, Gimbiya Zahra tana cikin zargi mai tsanani, wai tana da ciki daga Junaid!”

Sooraj ya mike da hanzari, jini ya hau kansa.

"What nonsense are you talking about?!” ya faɗa rai ɓace.
Zubaida ta tsaya cak, jikinta ya ɗau zafi.
"Me kake nufi?!”

“Ana cewa tana ciki… kuma fa sun ce da kunnensu suka ji tana faɗa da Junaid.”
Sooraj ya farka gaba ɗaya daga duk wani soyayya da sauƙi da ke jikinsa. Ya sanya babban rigarsa cikin hanzari, Zubaida ma ta ɗaura gyale da takalmi. Dukkan su suka kama hanyar komawa masarauta cikin gudu.

Masu masarauta sun rufe Zahra a ɗakin bak'i. Ana jiran zuwan Sooraj da Zubaida. Gaba ɗaya gari ya fara cika da zancen "cikin Zahra da Junaid". Amma ashe babu gaskiya ko kaɗan, sharri ne kawai, daga ƙiyayya da haushin soyayyar Sooraj da Zahra.

Zahra tana zaune ciki, ta rasa yadda aka yi aka jefa ta cikin sharrin da bata zato ba. Har yanzu bata san su Talatu da Saratu suka sa aka jefa ta a cikin wannan ƙazamar makircin ba.

Su Zubaida da Sooraj suka iso cikin hanzari. Su biyu suka tarar da taron mutane a cikin masarauta. Duk inda suka wuce ana kallon su, ana raɗa.

Sooraj ya daka tsawa “Waye ya ƙirƙiro wannan sharri?”.

Talatu ta matsa gaba da kwaɓaƙƙen fuska.

“Ka tambayi masoyiyarka Sooraj. Zahra ce ke da ciki, kuma ciki na Junaid ne!”

Zubaida ta tsaya cak.

“What?!”

Junaid ya fito daga cikin ƙofar ɗakin baki, yana tsaye a nesa. Fuskar sa babu walwala.

Zahra na kwance a ƙasa, tana kuka tana ƙoƙarin yin bayani amma babu wanda ke saurara.

Wani maigadi ya nufi Zahra da niyyar ja ta a jiki su fitar da ita daga masarauta, kamar matacciya. Amma kafin ya taɓa ta.

Sooraj ya tsayar da shi. “Ba wanda zai fitar da kowa ba sai an ji gaskiya!”
Ya juya ya kalli Zahra, da mamaki da tambaya a fuskarsa,

“Zahra me ke faruwa?”.

Zahra ta kalle shi da hawaye:

“Wallahi Sooraj, ni babu ciki. Karya suke. Su Talatu ne suka jefa ni cikin wannan sharri. Su suka jiyo ni ina faɗa da Junaid ne akan wani zargi da ya yi wa Zubaida, amma sai suka canza maganar gaba ɗaya!”.

Zubaida ta juya da sauri ta kalli Zahra, zuciyarta na bugu da sauri.

"Me ya ce game da ni?”. Ta tambayi Zahra

Zahra ta kalle ta cikin zuciya mai rauni tana so ta kareta amma shine sai Sooraj ya kalli Junaid kai tsaye.
"Junaid me kake ɓoye wa? Gaskiya kawai muke buƙata.”
Junaid ya ɗan juya kansa gefe, kafin ya zaro wayarsa ya mika wa Sooraj.

“Ga saƙon da na tura wa Zubaida, warning ne. Kuma cikin nan tabbas nawa ne. Amma ba da yardata na same ta ba.”

Sai kowa ya tsaya cak. Zubaida ta lumshe ido, Zahra ta rufe bakinta da hannu. Sooraj yana riƙe da wayar, yana karanta saƙon.

Da sauri Zahra ta nufi inda yake tare da ƙwace wayar ta fasa.

Dariya Zubaida ta kwashe da shi ta ce. "Hakan me ya sa za ki fasa wayar, dama kenen da gaske kina da cikin Junaid bamu sani ba, dama ke ƴar iska ce ba budurwa ba, tirr da wannan halin ki, ya kamata a hukunta ki, domin wanda yayi hakan hukunci yana kansa, banza ƴar talakawa ashe haka ki ke".

Nan take hawaye ya fara gangaro wa kan fuskar Zahra. Nuna kanta Zahra ta yi ta ce. "Zubaida ke da nake ƙoƙarin kare wa za ki maida abin ya juye kaina?".

MANAGE PAGE. HAR YANZU WAYATA BATA GYARU BA
TOH ME SOORAJ ZAI YANKE? YAYA JAMA'A ZA SU ƊAUKI WANNAN SABON BAYANI? SHIN ZAI GOYI BAYAN ZUBAIDA KO YA RUNGUMI GASKIYA.

ALƘALAMIN
A'ISHA MB
ZINARIYAR JAJIRTATTU
[8/21, 8:03 AM] AyeesherM B: 🔥KUNDIN CINIKAYYA🌍

A’ISHA M.B 💞
BOOK 2 – Page
1️⃣1️⃣4️⃣➡️1️⃣1️⃣5️⃣
Nan take ga baki ɗaya suka kalli juna tare da fashe wa da dariya. Sannan suka ce. "Prank me". Daidai lokacin su Mrs Lailah da su Umar tare da su Aliyu suka shigo masarauta. Bayan sauko warsu daga cikin mota. Su Safira da Amrah suka nufi inda Zahra take. Nan Masarautar ta amsa da muryoyin mutane. Suna faɗin. "Happy birthday to you, happy birthday to you, happy birthday, happy birthday, to you". Nan Sooraj ya ce. "Triplet Allah ya ƙaro shekaru masu albarka".

Share hawayenta Zahra ta yi sannan ta ce. "Kenan kuna nufin duk wannan abin da ya faru prank me?".

Nan Zubaida ta ce. "Kwarai kuwa, duk abin da ki ka ga ya faru to da sanin mu kuma duk shirin mu ne munyi hakan ne domin muyi pranking ɗin ki sannan mutaya ke da 'yan uwanki murnar ƙarin shekara".

Share hawayenta Zahra ta yi sannan ta kalle su ɗaya bayan ɗaya ta girgiza kai ta ce. "Wato shi ne kuka sa nai asaran hawaye na, kuka sa na shiga damuwa, da a ce zuciyata ta buga na mutu fa kenan duk wannan haka za ku ce prank ne?, lallai ma wallahi kun bani mamaki, to ni ba na so, Kuma kada a ƙara yi min irin wannan abun".

Kallonta Mami ta yi ta ce. "Ni kaina ban san prank suka yi miki ba, dai daga baya. Kiyi haƙuri don Allah, wallahi ban sani ba da a ce na sani da bazan biye musu ba sannan ga mahaifiyarku ma ta zo ya kamata a ce kin haƙura kuma omai ya wuce".

Kallonta Zubaida ta yi ta ce. "Yau fa ranar zagayowar haihuwar ki ne, kamata ai a ce yanzu kina farin ciki ba sai ɓacin rai ba. Kiyi farin ciki Zahra ga ƴan uwanki ma sun zo kinga wani ƙarin farin cikin ne".

Murmushi wanda yafi kuka ciwo Zahra ta yi ta ce. "Nayi farin ciki?, nayi farin cikin ne fa ki ka ce. Hmmm, kowanne birthday, kamar sabuwar ƙafa ce da nake ɗauka ina takawa kusa da kabarina.”
Chapter 55 · 0% Book details