Sashe 56
Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Wani lokacin nakan tambayi kaina, mene ne muke murna a zagayowar shekara? Shin saboda mun ƙara tsufa ne, ko saboda muna ƙara raguwa a lokacin da ya rage mana?”
“A ganin mutane zagayowar shekara alama ce ta sabuwar dama amma a gare nu, alama ce ta ƙarewar lokaci.”
Sannan ya maida kallonta kan Mrs Lailah ta ce. "Ummah kiyi haƙuri ban so ki ka ganni a irin wannan yanayin ba, banason aikata wani da zai ɗaga miki hankali, yanzu bana cikin sukuni, ba zan iya yin wani hira ko abi na farin ciki ba, yanzu haka zuciyata hutu take buƙata. Ummah zan tafi. Kuyi haƙuri gaba ɗaya".
Jikin kowanensu ta mutun jin furucin Zahra.
Ta faɗa da zimmar zata tafi. Nan kuma saita tsaya, tare da maida kallonta kan mahaifiyarta tare da sakin fuska ta ce. "Amma matsalar Ummah ba zan iya tafiya ba tare da kin min magana ba". Ta faɗa tare da zuwa wajan Miss Lailah sannan ta rungume ta.
Murmushi miss Lailah ta yi ta ce. "Allah ya yi miki albarka".
Shi kuwa Sooraj mamaki ma ya sa ya kasa furta komai.
Daga cikin rungumar da suka yi, Mrs Lailah ta dafa bayanta a hankali, tana shafa kanta. Sannan cikin nutsuwa ta ce. "Zahra ni na haife ki, na fi kowa sanin lokacin da ki ke buƙatar shiru. Amma kada ki manta da wannan, ba kowane hawaye ba ne rashin sa'a, wasu hawaye alama ce ta tsarkakkiyar zuciya, ta zuciyar da ke jin komai da gaske. Ki yarda da zuciyarki, amma kada ki kashe farin ciki gaba ɗaya".
Zahra ta ɗaga kai ta dubi Mahaifiyarsu da ido mai cike da kwalla cikin tsantsar girmamawa. "Ummah, na gode. Ina jin kalamanki har cikin ƙasusuwana. Zan yi ƙoƙari. Amma ki bari na sami ɗan natsuwa, kawai wuri da zan zauna ni kaɗai, da tunanina, ba tare da kowa ba. Sai an jima". Ta faɗa.
Safira ta riƙe hannun Amrah tana cewa. "Wallahi na taɓa jin an ce idan mace mai taushin zuciya ta fara magana da zafi to akwai abinda ke huda zuciyarta".
Nan Mami ta janyo Zahra yayin da suka sa ta manta abinda ya faru. Nan haka haɗa babban shagali. Bayan an gama shagulgula da murnar zagayowar ranar haihuwar ƴan uku, kowa ya watse cikin farin ciki. Masarauta ta cika da dariya da nishaɗi. An ci an sha, an raira wakoki, yara da manya sun more. Daga karshe, Mami ta cika jakunkuna goma na arziki, kayan kyaututtuka, tsabar kuɗi, da kayan marmari, ta ba Miss Lailah da su tafi da su zuwa Jigawa.
Su Zubaida, Zahra da Sooraj kuwa sun nufi gida cikin motar Sooraj. Zahra na gefe, ta yi shiru cikin nazari. Zubaida kuwa bata ce uffan ba, tana nazarin abubuwan da ke faruwa. Daga fuskar ta, akwai abin da ke damunta.
Sun isa gida lafiya. Amma tuni Zubaida ta fara canzawa. Zuciyarta ta cika da ƙiyayya da fargaba, tana zargin cewa Sooraj yana son Zahra. Kullum idan Sooraj ya dubi Zahra, idan ya yi mata murmushi, idan Zubaida na jin zuciyarta kamar ta fashe.
Wata rana Zahra na zaune a falonsu tana karanta wani littafi, cikin rigar atamfa mai kyau da kwalliya irin ta mata masu tsafta da iya gyaran kai. Sooraj ya shigo falon, yana ta kokarin gyara waya a hannunsa, sannan ya ce da ita.
"My Zahra, kin ƙara kyau wallahi." Ya faɗa murmushi kan fuskarsa. Zahra ta saki murmushi ta ce. "Na gode".
Nan Zubaida ta ce.
"Zahra, dan Allah ki rage sa irin waɗannan kayan. Idan kin san kina da aure, ki dinga kamun kai. Kin fi dacewa da sutura mai da’a."
Nan Zahra ta juyo da idanta gare ta ta ce. "Wallahi kinyi ƙarya."
Zubaida ta zaro ido. "Me ki ke nufi da ƙarya?"
Zahra ta ce da girmamawa mara laifi,
"Kinyi ƙarya idan kina tunanin ni zan canza saboda ke. Idan kuma saboda kaya ne kike jin ciwon zuciya, to yanzu na fara. Ki daure ki ƙara kishi har ya hure miki ido."
Zubaida ta kasa amsa. Maganganun Zahra sun fada mata zuciya kamar ƙibiyar da aka sa wa wuta. Zahra ta ci gaba da cewa.
"Kina yawo kina nuna Sooraj naki ne, naki ne. An gaya miki duk abin da ki ka shirya a kaina ban sani ba?, duk shige da ficen ki dan ki mallake shi duk babu wanda ban sani ba. Saboda haka idan kina da damuwa, sai ki shafa man zafi. Ni kuwa zan yi duk abin da nake so a gabansa har ki yi kuka ki sha hawaye."
Zubaida ta runtse ido, hawaye na neman zubo mata amma sai ta juya ba tare da ta ce uffan ba.
Daga wannan rana, Zahra ta sauya gaba ɗaya. Duk inda Zubaida ke, sai Zahra ta gwada ta da kulawa fiye da yadda kowacce mata za ta so a nuna wa mijinta. Idan suna zaune suna cin abinci, Zahra kan ce. "My love, ƙara tuwon nan kaɗan mana, ina so ka ƙara kiba."
Zubaida na gefe, zucisrta yana cike da wuta.
Wannan sauyin na Zahra ba haka kawai ba ne, hakan ya faru ne a dalilin wata rana lokacin da Zahra ke shirin fita zuwa Garden, ta tsaya kusa da ƙofar ɗakin Zubaida domin ɗaukar takalminta. Bai kamata ta ji ba, amma sai ta jiyo murya daga cikin ɗakin, kamar ana waya, kuma kamar ana magana da zuciya.
Zubaida ce ke magana a waya tana faɗin. "Wallahi sai na mallaki Yarima Sooraj. Ko me zai faru. Zahra ba komai bace a gabana. Da sannu zan kore ta daga gidan nan. Ina da yanda zan yi."
Zahra ta tsaya kamar an dasa ta. Idonta ya cika da ƙwalla, amma ta dannata. Ta juya ba tare da ta yi magana ba. Amma zuciyarta ta ƙona kamar wutar daji.
Tun daga wannan rana, Zahra ta ɗaura ɗamara. Bata sake zama irin Zahra mai jurewa ba.
Wannan shi ne.
Zubaida ba ta iya cin wannan maganar haka ba. Ta wuce ɗaki, tana kukan rai. Washe gari ta tura saƙo zuwa wayar Zahra da nufin barazana.
"Zahra, idan kika ci gaba da wannan hali, sai na tabbatar kin fita daga gidan nan da kuka da nadama. Ki dinga rike baki da kamun kai. Kar ki farka da bala’i."
Zahra ta karanta saƙon tana dariya mai ɓacin rai. Ta ce a ranta:
"To, yanzu ne farawa. Ba ke kika fara ba? Muje zuwa."
A daren ranar, Zahra na zaune cikin ɗakin Sooraj, fuskar ta ɗaure tamkar wacce aka ci amanarta. Ta kalle shi, sannan cikin murya mai cike da ciwo da daci ta ce,
"Ka san kuwa har yanzu fushi nake da kai? Duk wannan wasa da muke a gaban Zubaida, bana jin daɗi da kai ko kaɗan."
Murmushi Sooraj ya yi ya ce. "Hmm nima na sani shi ya sa na biye miki".
Ajiyan zuciya Zahra ta sauke sannan ta dube shi ta ce. "Me ya sa ba za ka so Zubaida ba?, kada ka manta ita ma fa matar ka ce, ni ko ba zaka so ni ba ban damu ba, amma ya kamata a ce kana faranta mata rai tare da kyautata wa zuciyarta domin kai ɗin mijinta ne. Bana jin daɗi yadda baka sakar mata fuska baka mata wasa da dariya ba mata da miji. Ya kamata a ce ka gyara domin samm wannan ba hali ba ne". Tana kaiwa nan ta fice ta bar shi a ɗakin.
Ajiyar zuciya Sooraj ya yi yayin da ya shiga tunanin maganar Zahra. Sauke nannauyan ajiyar zuciya ya yi sannan ya ce. "Ta yi gaskiya, ko ba komai Zubaida kamar ƴar uwa ta ce kuma ya ci a ce ina sakar mata fuska". Miƙe wa ya yi tare da fice wa daga cikin ɗakin da ksi tsaye ya nufi ɗakin Zubaida. Ba tare da ƙwanƙwasa ba ya shiga ciki.
Nan ya tarar da ita a zaune ta yi tagumi. Shiru ya yi yaji a rashi cewar tabbas tana cikin kaɗaici. Nan ya ji ta bashi tausayi. Gyaraj murya ya yi. Sai a lokacin Zubaida ta lura da shigowar sa.
Da sauri ya miƙe ta ce. "Yarima kai ne?, ba laifi dai nayi ba ko?".
Murmushi ya sakar mata sannan ya ce. "Shin kina jin aushi na?".
Zaro ido ya yi ya ce. "Haushin ka kuma saboda me?".
Amsa ya ba ta da cewar. "Saboda irin abubuwan da na dinga yi miki wanda na tabbata baki ji daɗin su ba".
Ɗan jimm Zubaida ta yi ta ce. "Kayi gaskiya, amma ni yanzu komai ya riga ya wuce a waje na, saidai na ce Allah ya kiyaye gaba".
Murmushi ya yi ya ce. "Yanzu me ki ke yi?".
Amsa ta bashi da cewa. "Babu abin da nake yi".
Gyaɗa kai ya yi ya ce. "Toh ki shirya zamu fita".
Zaro ido waje ta yi ta ce. "Fita kuma da ni?".
Gyaɗa mata kai ya yi ya ce. "Eh da ke, ko da akwai laifi miji ya fita da matarsa".
Girgiza masa kai ta yi ta ce. "A'a babi laifi, ai ni a shirye nake na saina shiga na chanza ba".
Nan ya dube ta ya ce. "Je ki saka hijab toh".
Da sauri ta shiga ɗakin ta tare da ɗauko hijabi jiki na rawa ta saka. Yayin da zuciyarta ya cika da farin ciki kamar wacce haka yi wa albishir da gidan aljanna".
Bayan ya saka hijabin ta fito da sauri ta dube shi ta ce. "Na saka".
Nan ya dube ta tare da hijabi maroon da ke jikinta sannan ya ce. "Da wuri haka?. Kin san me?".
Girgiza masa kai ta yi ta ce. "A'a".
Amsa ya ba ta da cewa. "Kinyi kyau sosai".
Washe haƙora Zubaida ta yi sannan ta ce. "Da gaske?, naji daɗin hakan, amma duk kyau na ban kai ba".
Girgiza kai Sooraj ya yi ya ce. "A'a ban kai ki ba, karki manta fa bayan ƙyawun ɗawisu sai mace, to ta ina zan kai ki kyau".
Murmushi Zubaida ta yi ta ce. "Naji daɗi hakan amma dai kai ma ka san ka fini kyau, duk inda za'a zaga ni za'a ce nayi dacen miji ba kai ba".
Shiru Sooraj ya yi ya ce. "Toh shi ke nen zamu iya tafiya?".