← Book details Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 65

Sashe 65

Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Girgiza kai Mami ta yi ta ce. "Ƙwarai kuwa, ina son a bani jikata ta zauna tare da ni". Nan Zeenat ta dubi babanta ta ce. "Daddy ka bari na zauna tare da Grandma please Daddy". Ta faɗa cikin shagwaɓa.

Ajiyan zuciya Sooraj ya sauke sannan ya ce. "Shi ke nen ya na iya tunda kuna so ai shi ke nen".

Murmushi Zahra ta yi ta ce. "Kada ka damu Mahmud ai zai zauna tare da mu".

Nan suka ji Mahmud ya ce. "Ni ma zan tafi wajan Grandma na naje nayi hutu".,

Zaro ido waje Zahra ta yi ta ce. "Mahmud mu kuma ai za ku bar mu cikin kaɗaici".

Murmushi Miss Lailah ta yi ta ce. "Kada ki damu za ki ƙara samun wasu yaran ai".

Girgiza kai Zahra ta yi ta ce. "Ai ni na gama haihuwa wallahi, ba zan so na ƙara shan wahalar da na sha a baya ba".

Nan gaba ɗaya suka kwashe da dariya.

Kallonta Safira ta yi ta ce. "Zahra kin san me na tuna, lokacin da ki ke wannan masifa da bala'i, amma kalle ki yanzu kamar ba ke ba".

Kunya ne ya kama Zahra ta ce. "Kin san an ce in mace ta yi aure tana ƙara hankali kuma tana nutsuwa".

A haka dai suka shiga hira cikin farin ciki da annashuwa. Inda kowa ya watse. Nan Umar da Aliyu suka faɗa wa su Mami cewa za su fita outside country zasu je aikin hajji a gobe. Sosai su Miss Lailah suka yi farin ciki yayin da suka yi musu fatan alheri.

Yayin da su Zahra suka nufi hanyar gida cikin farin ciki ba tare da su twins ba. A nan Zahra take faɗa masa cewa Aljana Farira ce likitar da ta karɓi haihuwarta. Sosai Sooraj ya yi mamaki a gefe guda kuma ya ji daɗi domin ta taimaka musu.

Bayan sunyi nisa a tafiyar ya sa Sooraj kallon fuskar ta.

Ganin ranta a ɓace ya sa Sooraj faɗin. "Me ya faru?".

Shiru ta yi rai ɓace ta ce. "Sai da na ce maka muyi family planning amma yanzu gashi na samu juna biyu, ni yanzu haka zan ta haihu kamar akuya".

Nan farij ciki ya lulluɓe fuskar Sooraj ya ce. "Wow! da gaske?, kuma shi ne baki gaya min ba, amma fa nayi farin ciki sosai, shi ya sa nake sonki my one and only wife, da ke babu ƙari".

Murmushi Zahra ta yi ta ce. "Yanzu sati ɗaya kenen da sanin cewa ina da juna biyu amma naƙi faɗa maka, saboda ina jin kunya. Amma yanzu komai ya wuce na daina jin kunya. Ina sonka my Habibi".

Nan ya riƙe hannunta tare da yi mata light kiss a goshinta ya ce. "Love you more my wifey".

Mintsininsa ta yi ta ce. "Muje gida ai yanzu su Mahmud basua nan zan samu damar koya maka hankali".

Ɗan ƙara Sooraj ya yi jin mintsinin da ta yi masa murmushi ya yi ya ce. "Daga nan kuma mu sha love ɗin mu abun mu, babu twins a gida".

Kallonsa Zahra ta yi ta ce. "Wane irin love kuma?".

Murmushin gefen baki Sooraj ya yi ya ce. "Kin fini sani ai ko kin manta abinda ake yi a ɗaki ne?".

Zaro ido waje Zahra ta yi ta ce. "A'a ni dai babu abinda zanyi".

Dariya Sooraj ya yi ya ce. "Za ki yi bayani ne ai muje gida tukunan, ina son ki min wannan rawar India da ki ke yi kullum a ɗaki".

Kunya ne ya kama Zahra ta ce. "Kenen kana ganin lokacin da nake rawa?".

Girgiza kai Sooraj ya yi ya ce. "Ƙwarai ma kuwa".

Dariya Zahra ta yi sannan ta ce. "Toh ni dai ba zan yi maka rawa ba".

Girgiza kai Sooraj ya yi ya ce. "Au so ki ke na ce na fasa zuwa da ke aikin hajji ko, toh shi ke nen na fasa".

Da sauri Zahra ta kalle shi tare da sakin murmushi ta ce. "Ni na isa na ce ba zan yi maka rawa ba. Ai karka damu harda twerking zanyi maka kaji mijina abin alfahari na".

Ta faɗa tana mai sumbatar sa a kumatu.

Farin ciki ne ya lulluɓe fuskar Sooraj ya ce. "Tom shi ke nen, ki ce yau akwai shagali". Ya faɗa tare da ƙara wa motar gudu.

A haka rayuwar su ya kasance cikin farin ciki mai ɗorewa.

*THE END*💃💃💃💃

Alhamdulillahi! Ina gode wa Allah Maɗaukaki da ya bani ikon kammala wannan littafi cikin ƙoshin lafiya da natsuwa. Ba tare da taimakonsa ba, da ba zai yiwu ba.

Ina roƙon Allah ya rufa asiri, ya yafe duk wani kuskure da ke ciki, ya kuma sa mu amfana da kyawawan abubuwan ciki.

SAI MUN HAƊU A LITTAFI NA GABA🤸‍♀️🤸‍♀️🤸‍♀️.

ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞
ZINARIYAR JAJIRTATTU
Chapter 65 · 0% Book details