Sashe 12
Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kallonsu ya yi ya ce. "Mene abinda yake faruwa?".
Jin muryar sa ya sa gaba ɗaya suka jiyo suna mai fuskantar sa. Murmushi Mami ta yi tana mai faɗin. "Sannu da zuwa, ran uwar gida,
Idon idaniyata, hasken zuciyata, ka dawo lafiya kamar yadda na roƙa,
ɗana mai kamanni da mahaifinsa,mai tafiya cikin nutsuwa, mai dawowa da albarka,
na haife ka da ƙauna, na raineka da addu'a,
ka dawo kamar alfijir mai dauke da rahma,
Allah ya ƙara maka lafiya da daraja, domin ka fi ƙarfin sharri".
Kallon Mami Sooraj ya yi ya ce. "Wannan kirarin da Mami?, kamar wanda nayi shekara bana gida".
Tsaki Gimbiya Saratu ta ja tana mai rafta tagumi ta ce. "Mu da idan ba za'a faɗa mana dalilin da ya sa aka tara mu a nan ba zamu tashi mu tafi, domin ba zaman banza muka zo yi nan ba".
Kallon Sooraj mai martaba ya yi ya ce. "Sooraj ƙaraso nan kaji".
Ƙarasowa wajan su Sooraj ya yi ya ce. "Gani ya shugabana".
Ya faɗa yana mai zama kan hannun kujera. Kallonsa Mami ta yi ta ce. "Ba ka ga Zubaida a zaune ba?".
Maida kallonsa ya yi kan Zubaida tare da kawar da kansa sannan ya ce. "Na ganta mene abinda ya faru, naga ma harda su Uncle Sadiq iyayenta a zaune. Fatan dai babu wata matsala".
Murmushi Uncle Sadiq ya yi ya ce. "Babu abinda ya zaunar da mu face alkhairy".
Kallonsa Mami ta yi ta ce. "Kayi farin ciki ɗana, Zubaida ta ce a shirye take zata aure ka yanzu aka ma kuka take na tsoron kada ka ƙi amince wa, ta ɗauka ko kai da Zahra kuna soyayya ne a lokacin da ta ganku a asibiti sai daga baya kuma ta ga ba aka ba ne ta yi muku rashin fahimta ne. Yanzu abinda za'a yi shi ne mu fara shirye-shiryen saka muku rana kawai a ɗaura muku aure tun da kaima kana sonta, kuma ka ga ƴar kawun ka ce bai kamata ka watsa musu ƙasa a ido ba".
Furzar da iska mai zafi Sooraj ya yi waje sannan ya miƙe tsaye tare da da bin gaba ki ɗayan su da kallo ya ce. "Inda wasu ke cikin matsala suna neman hanyar da za su warware matsalolin su basu samu ba, shi ne kuma yanzu za ku zo min da maganar auren wata Zubaida. To ni samm bana sonta".
Jin kalaman Sooraj kowanne su ya yi tamkar saukar aradu.
"Me ka ke nufi?, kamar ya baka sonta?, ba da soyayya ku ke ba?". Cewar Mami.
Kallon Mami ya yi ya ce. "Ni samm ban taɓa soyayya da Zubaida ba, asali ma ita ce wacce ta dinga naniƙe min harta zo ta faɗa miki cewar ni ɗin saurayinta ne ke kuma Mami ki ka yarda saboda kina ganin hakan yana da kyau zai ƙara danƙon zumunci tsakanin mu da Uncle Sadiq. Ni ban taɓa ji a raina ina sonta ba".
Fashe wa Zubaida ta yi da kuka sannan ta ce. "Wallahi Mami ƙarya yake yi, kema kin san ba zan taɓa zuwa nayi miki ƙarya ba, a lokacin muna ƙasar london ma har club yake zuwa shi da wannan abokin na shi Umar, domin na taɓa ganinsu a chan kuma ƴan mata suke zuwa kulawa".
Zaro idanuwa waje gaba ki ɗayan su suka yi . A yayin da Gimbiya Saratu da Talatu suka kalli juna suna mai kwashe wa da dariya tare da faɗin. "An yanka ta tashi, dama an ce ramin ƙarya ƙurarre ne, ashe har club yana zuwa idan ya zo nan kuma ya dinga nuna wa kamar babu wanda ya kai shi son addini".
Miƙe wa tsaye Mami ta yi hawaye kan ƙuncinta ta ce. "Sooraj ka faɗa min cewar maganar da Zubaida ta faɗa ƙarya ne ba gaskiya ba. Sooraj wannan ba ita ce tarbiyyar da na ɗora ka a kai ba, dama abinda kai da abokin ka ku ke zuwa aikata wa kenen a London shi ya sa idan na ce ka dawo gida sai ka ce min kana da ayyuka da yawa da ka ke yi, dama wannan shi ne ayyukan da ka ke tsayawa yi?".
Girgiza kai Sooraj ya yi yayin da hankalin shi ya yi matuƙar tashi ganin hawaye kan fuskar Mami. "Mami dan Allah ki saurare... Bai ƙarasa magana ba ya ji Mami ta daka masa tsawa yayin da ta ɗaga hannunta ta kwashe shi da mari.
Dafa fuskarsa Sooraj ya yi karo na farko a rayuwarsa da Mami ta ɗaga hannu ta mare shi.
Farin ciki wajan su Gimbiya Saratu kuwa kamar za su shiɗe su nutse ƙasa tsabar dad'i.
"Kayi min shiru Sooraj, ban taɓa zaton da irin wannan abin za ka saka min ba a matsayina na mahaifiya a gare ka, kai ne ɗa ɗaya tilo da Allah ya bani, baka taɓa tambaya ta abu na ana ka ba, a kan me za ka watsa min ƙasa a ido?".
Kallon Sooraj Umar ya yi ya ce. "Kai Sooraj mene aka?, me ya sa ba za ka gaya musu gaskiya ba?".
Girgiza kai Sooraj ya yi ya ce. "A'a Umar kawai kayi shiru".
Kallonsa Umar ya yi ya ce. "Wallahi ba zan iya kallon hakan na faruwa ba in yi shiru. Ba za ka taɓa aikata hakan ba, ni na san inda muka je, ni na san me muka yi, kuma ba laifi muka je nema ba, kana rayuwa da gaskiya, kuma yanzu kuna son ku ɗauke masa sunan da bai cancanta ba. So ka ke ta yanke yardar da ta yi a gare ka?,
kana da zuciya mai taushi, ba za ka iya jure ganin mahaifiyar ka ta daina yarda da kai ba.
Kada ka je fa kanka cikin duhu saboda zargin da babu tushe.Ni abokin ka ne, kuma sai na tsaya tsayin daka har ku su gane gaskiya!"
Mayar da kallonsa Umar ya yi kan mutanen parlour ya ce. "Ku saurare ni da kyau,
ba don ina so na shiga maganar nan ba, amma gaskiya ba ta da murya, sai wani ya ba ta. Wanda kuke zargi Na san shi, na san yadda zuciyarsa take. Wallahi ba irin waɗan can mutanen ba ne. Mun tafi wuri guda, mun dawo lafiya a tare, ba mu taɓa wani abu da zai jawo mana sharri ba.
Kuna so ya zauna yana kallo mahaifiyarsa ta daina dariya saboda abin da bai aikata ba?,
kuna so ya ga mahaifinsa yana shakkarsa?, shi da Sooraj wani mutum ne da idan ya ce maka 'Na rantse', sai ka ji gaskiya na fitowa daga numfashinsa. Sooraj Kada ka bari shiru na ya zama dalilin ɓarnar rayuwarka. Idan kun kasa yarda da shi, to ku yarda da ni. Na fi so a yi min hukunci domin duk laifi na ne, ba zan iya bari ana tuhumar ka a kan abinda baka aikata ba".
"Bara kuji, ni ɗin jami'i ne a ƙasar London kuma a asibitin da Sooraj yake aiki an kawo wata yarinya ƙarama ƴar shekara sha biyu an kawo ta cikin jini yayin da aka yi mata aiki aka tarar da cewar wani ne ya yi mata fyaɗe. Jinin yarinyar ya zuba sosai har ta kai ga ba ta iya numfashi daga nan kuma yarinyar ba ta ƙara motsi ba su Sooraj suka tarar da cewa ta mutu.
Hakan ya sa ran Sooraj bai yi masa dad'i ba har ta kaiga ya kasa ɓoye damuwarsa ya sanar da ni. Naji babu dad'i game da rashin adalcin da aka yi mata hakan ya sa na yi masa alƙawarin saina kama wanda ya aikata mata hakan. Mun samu bayanai daga wajan iyayen yarinyar yayin da suka sanar mana da cewa yana zuwa club sosai nan suka bami hoton mutumin muka tafi club a lokacin mun ga Zubaida tana ta bibiyar mu hakan ya sa Sooraj ya yi kamar yana kula ƴan mata a cikin club ɗin saboda Zubaida ta ji bata son shi. Ganin Sooraj da Zubaida ta yi sai ta yi tunanin cewa yana bin matan banza ne. Nan ta tafi tana tafiya kuma muka kama mutum yayin da muka miƙa shi wa ƴan sanda da ya ci duka sosai yake sanar mana da cewa bawai kama yarinyar ya yi ba siyar masa da yarinyar aka yi aka aiko masa da ita tun daga ƙasar Nigeria. A lokacin da na ji hakan nayi mamaki sosai na fara bincike a ka wane ne yake sakawa ake aiko da yara ƙanana kasashen waje. An hukunta mutumin bisa laifin da ya aikata. Nayi ta bincike a kan wane ne yake saka wa ake aiko da yara amma ban samu ba. Hakan ya sa ni da Sooraj muka ce za mu koma Nigeria sannan muyi tamkar bamu san juna ba yayin da zamu dinga bincike a kan wane ne yake safaran yara. Amma daga ƙarshe yanzu saina gano cewar mahaifi na ne yake sanyawa ake yin hakan. Naji ba dad'i da na gano hakan. Amma shi Sooraj ba wai mutumin banza ba ne shi ɗin walihi ne".
Ajiyan zuciya gaba ɗaya suka sauke!, Sannan Mami ta ce. "Kayi hakuri Sooraj nayi maka gurguwar fahimta, sam ban yi maka adalci ba da har ban tsaya na tabbatar da gaskiyar ba kuma na yanke hukunci a kanka, samm ban cancanci zama uwa a gare ka ba".
"A'a Mami samm ba laifin ki ba ne, laifi na ne da ban sanar da ke hakan ba tuntuni, kiyi haƙuri na sanya hannunki ciwo ta hanyar mari da ki ka yi". Cewar Sooraj.
Kallonsa Zubaida ta yi ta ce. "Ka ya ƙuri yahya Sooraj ni ɗin shasha ce kishi ne ya ana ni tambayar ka me kaje yi chan, amma dai ba za ka ƙi aure na ba ko?".
Kallonta Sooraj ya yi ya ce. "Ba zan fa aure ki ba domin bana sonki?".
"Toh idan baka aure ta ba wa za ka aura Sooraj?, Girma ka ke fa, ya kamata kayi wa kanka faɗa, idan ba ka sonta to wa ka ke so". Cewar Gimbiya Saratu.