Sashe 40
Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nan gayen ya ce. "Tun farko ke ki ka tursasa ni nayi miki wannan ciki, ban sani ba kuma ba da san raina ba, dan haka ke ki ka san yadda za ki yi".
Dubansa Zubaida ta yi ta ce. "Kamar ya bangane ba, so ka ke asiri na ya tonu kenen ka lalata min suna?, ka sani muddin haka san ina ɗauke da juna biyu ba za'a ƙyale ni ba kuma kaima haka. Yanzu haka ma wata daga cikin ƴar aikin masarautar mu ta sani, kuma tsoro na shi ne kada ta faɗa wa kowa. Ni duk ba wannan bama, ina son kafin aure na da Sooraj ka san yadda za'a kawar da wannan cikin kafin komai ya lalace".
"Toh ni me ki ke san nayi miki?, ni fa gaba ɗaya nayi dana sanin saninki a rayuwata, domin ke kinfi maciji mugun dafi, idan haka ganki haka ga maciji, to zai fi a fara kashe ki In ya so a kashe macijin, domin ke kinfi maciji guba". Ya faɗa tare da miƙe wa tsaye sannan ya ce.
"Cikin da ke jikin ki ke ki ka ja bani ba, dan haka ke za ki san yadda za ki kawar da shi. In kuma baki daina bibiyar rayuwata ba, ni da kaina zanje na tona miki asiri, in ya so a haɗamu mu biyun a hukunta mu".
Ya faɗa tare da buga tsaki sannan ya bar wajan.
Wani baƙin ciki Zubaida ta ji ya tsaya mata a maƙoshinta. Nan take hawaye ya fara zirya bisa ƙuncinta.
Da sauri ta share hawayenta da handkerchief sannan ta miƙe tsaye ta fita.
*****
Bayan Zahra ta nunnuna musu fadar masarautar, suka koma ciki.
Daidai lokacin Aliyu ya fito. Duban Safira Aliyu ya yi sannan ya ce. "Ki same ni a garden ina son magana da ke". Ya faɗa tare da fice wa.
Taɓe baki Safira ta yi sannan ta ce. "Ka ji da shi".
Kallonta Zahra ta yi ta ce. "Me ki ke nufi?, kina nufin ba za ki je ba?".
Gyaɗa kai Safira ta yi alamun eh.
"Ai kuwa baki isa ba, dan gidan ku maza kama hanya ki je, wannan ai iskanci ne, je ki kafin na ɓata miki rai". Cewar Zahra.
"Zan je ne kawai dan kince naje, amma da ba dan haka ba da ba zan je ba".
Safira ta faɗa tare da fice wa daga parlourn.
Kai tsaye ta nufi garden. Nan ta tarar da Aliyu zaune. Da sallama ta ƙarasa wajan shi. Nan Aliyu ya amsa. Yayin da ya umarce ta da ta zauna.
Zama Safira ta yi tana mai fuskantar shi ta ce. "Gani".
Ɗan jimm Aliyu ya yi kafin daga bisani ya ɗago da idanuwansa tare da sauke su a kan nata ya ce. "Shin ki na so na?.
Jimm Safira ta yi ta ce. "Bangane abinda ka ke nufi ba".
Nan Aliyu ya ce. "Ki amsa min tambaya ta ki na sona?".
Shiru Safira ta yi tare da sunkuyar da kanta ta ce. "Eh".
Girgiza kai Aliyu ya yi ya ce. "Masha Allah, tom tambaya ta ƙarshe. Shin za ki aure ni ne dan Daddy ya ce saikin aure ni, ko kuwa kece ki ke so ba wai tirsasa miki za'a yi ba. Ki faɗa min gaskiya bana son kiyi min karya".
Dubansa Safira ta yi ta ce. "Nima ban sani ba".
Shiru Aliyu ya yi ya ce. "Okay tom shi ke nen, na gode. Dama ina san zan fita daga cikin rayuwar ki gaba ɗaya, naga alamun bakya sona bacin ni sonki nake kuma so na aure, bana son na tirsasa wa zuciyar da bata ƙaunata sona, dan haka daga yau na fita daga rayuwar ki, ba za ki ƙara ji ko gani anyi magana game da aure na da ke, kinga yanzu Aunty Lailah da mahaifin ku su dawo. Su ke da haƙƙi hakan zaɓa miki duk mijin da ki ke so ba wai Mom ko Daddy ba. Dan haka feel free, yanzu halaƙa ɗaya ke tsakanin mu, shi ne na ƴan uwantaka. Yanzu za ki iya tafiya, you are free to go".
Jikin Safira ne ya yi sanyi. Yayin da ta ji zuciyarta ta karaya. Ƙoƙarin magana take da sauri Aliyu ya dakatar da ita da faɗin. "Please Safira, na riga na yanke hukunci wanda ni na san ya yi miki daɗi, babu buƙatar kuma wata maganar, domin na riga na kawo ƙarshen komai. Yanzu kina da damar yin rayuwar ki yadda ki ke so, daman chan ni ke shishige miki ko, to yanzu na bari ba zan sake ba".
Ya faɗa tare da miƙe wa sannan ya barta a zaune a wajan.
Safira ba ta san sanda kuka ya ci ƙarfin ta ba. Fashe wa da kuka Safira ta yi. Saida ta yi mai isarta sannan ta share hawayenta tare da miƙe wa ta shiga ciki.
Duk abinda ya faru a kan idanuwar Zahra. Nan ta ji cewa ya zama dole ta ƙara haɗa su soyayya.
___
Da daddare da misalin ƙarfe takwas kowa ya zauna ya cin abinci a dining. Inda fuskar kowa ke ɗauke farin ciki da annashuwa, sai dai banda Safira da kuma Aliyu wanda kowannensu ya bawa ɗan uwansa tazara mai nisa.
Suna tsaka da cin abinci Alhaji Abdullahi ya ce. "Gaskiya waɗan da suka girka abincin nan sun iya girki".
Nan miss Lailah ta ce. "Ai ni da Mami ne muka girka".
"Masha Allah". Alhaji Abdullahi ya furta sannan ya ƙara da faɗin. "Shi ya sa naji abincin ya fita da ban. Tsawon shekaru ashirin kenen rabon da naci abinci mai daɗin wannan".
Dariya gaba ɗaya suka kwashe da shi. Su Gimbiya Saratu kuma suna ci suna taunar harshe tsabar masifa na cinsu.
Duban Aliyu Zahra ta yi ta ce. "Malam ɗan sanda lafiya naga fuskarka babu walwala".
Murmushin yaƙe Aliyu ya yi ya ce. "Ba komai, ina lafiya".
Girgiza kai Zahra ta yi ta ce. "A'a ban yarda ba, kowa da ke nan ka kalla fuskar sa da walwala banda kai da Safira. Lafiya kuwa?".
Shiru Aliyu ya yi na ɗan wasu lokuta sannan ya ce. "Ƙalau nake". Ya faɗa tare da miƙe wa ta bar dining ɗin.
Binsa gaba ɗaya suka yi da kallo. Nan Zahra ta miƙe sannan ta ce. "Ina zuwa". Ta faɗa tare da bin sahun ƙafar Aliyu.
Inda ya nufa ta nufa. Da sauri ta nufi inda yake tare da shan gabansa ta ce. "Malam ɗan sanda meke damunka?, da alama lamarin soyayya ne ko".
Haɗe rai Aliyu ya yi sannan ya ce. "Babu komai Zahra, ki matsa na wuce".
Girgiza kai Zahra ta yi ta ce. "Ni fa ba zan matsa ba, in kana son na matsa ka koma ka ƙarasa cin abincin ka".
"Na ƙoshi". Aliyu ya faɗa yana mai ƙoƙarin wuce wa.
Da sauri ta tare shi Zahra ta ce. "Ba fa zan bari ka wuce ba".
Nan take ranshi ya ɓaci inda ya daka mata tsawa. "Maza ki bani hanya na wuce!". Ya faɗa a tsawa ce tare da ture Zahra ta faɗi ƙasa. Hakan ya janyo hankulan su Mami da ke dining.
DAN ALLAH KUYI LIKE, COMMENTS, AND SHARE FISABILILLAH. SABODA ALLAH PLEASE🥹 🙏🙏🙏🙏🙏🙏
ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞
ZINARIYAR JAJIRTATTU
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!
*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎
*A'ISHA M.B*💞💞
*BOOK 2 PAGE1️⃣0️⃣4️⃣▶️1️⃣0️⃣5️⃣*
________________________
Da sauri Zahra ta miƙe gudun kar wani na gidan ya zo ya tarar da su a haka.
Zuwa Sooraj ya yi ya ce. "Lafiya Zahra ihuu wa na ji haka?".
Amsa Zahra ta bashi da cewa bakomai, dama suɓuce wa nayi na faɗi, muna magana ne da Malam ɗan sanda, muna gama wa zan tawo".
Nan take Sooraj ya soma jin kishi a zuciyarsa. "Wace iriyar magana ne ku ke yi?". Cewar Sooraj.
Murmushi Zahra ta yi ta ce. "Sai ka ji?, kai dai kawai ka tafi sirri muke yi".
Ran Sooraj ne ya ɓaci hakan ya sa ya koma dining. Kallonsa Mami ta yi ta ce. "Lafiya Sooraj?".
Amsa ya bata da cewa. "Bakomai Mami wai tuntuɓe ta yi amma bakomai, mu cigaba da cin abincin namu".
Ya faɗa yayin da ya shiga duniyar tunani.
Ɓangaren Zahra kuwa maida kallonta ta yi kan Aliyu ta ce. "Kai kuma na dawo kanka, me nayi maka da za ka ture ni haka?, ko ni ce wacce na ɓata maka rai. Ka ga ka fita idona na rufe, ka san ina ganin girman ka da ba dan haka ba da saina rama. Yanzu maza ka koma ka ƙarasa cin abincin ka".
Kallon baki da hankali Aliyu ya bita da shi ya ce. "Toh Mama sannu, shawara ki ke bani ko umarni?".
Amsa Zahra ta bashi da cewa. "Duk wanda ka zaɓa a ciki".
"Toh ba zan ci ɗin ba, ki je ke ki ci tunda ke abinci kawai ki ka sani". Aliyu ya faɗa yana mai ƙoƙarin wuce wa. Da sauri ta tsaya a gabansa sannan ta ce.
"Wallahi Yahya Aliyu zan ɓata maka rai, maza kafin na irga uku ka je ka ci wannan abincin idan ba haka ba na yi maka ta ƙarfi da yaji".
Harɗe hannuwansa Aliyu ya yi a ƙirji sannan ya ce. "Idan kin fasa baki cika ƴar halak ba".
Murmushi Zahra ta yi tare da fara waige-waige. Kama hannun shi ta yi da zimmar janshi, nan ta ga ya kasa jawu wa.
Ajiyar zuciya Zahra ta sauke sannan ta ce. "Malam ɗan sanda karka sa na fusata".
Nan take Aliyu ya soma ƙoƙarin ƙwace hannun sa daga na Zahra amma ina hakan ya cutura domin gaba ɗaya ƙarfinta ta tattara ta riƙe shi.
Wafce hannunsa ya yi sannan ya ce. " Zahra ki bari, bana son hauka, ana dole ne?".
"Eh ɗin dole ne. Idan kuma baka je ba saina je na faɗa wa Mama na, kuma za ka gani". Ta faɗa tana mai ƙoƙarin nufa hanyar dining.
Da sauri ya dakatar da ita da faɗin. "A'a ba sai an kai ga wannan matakin ba maza muje na ƙarasa ko".
Ya faɗa tare da nufar hanyar dining. Murmushi Zahra ta yi ta ce. "Yaron kirki".
Nan suka koma dining ɗin tare da ƙarasa abincin.