← Book details Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 65

Sashe 52

Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Junaid ya rantse min cewa babu abin da ya yi mata. Wannan ya sa na ɗauki mataki na tafi hotel ɗin da aka yi birthday ɗin. Na nemi CCTV footage. Bayan na duba, sai na ga wani abin mamaki."
Umar ya ɗan waiwayo yana kallon kowa da ido.

"Hoton CCTV ya nuna cewa bayan Zubaida ta kawo cake ɗin, wani mutum ya shiga ɗakin bayan ta kwantar da Junaid saboda rashin hayyacinsa. Shi ne ya yi lalata da ita, ba Junaid ba. Bayan mutumin ya fita, ne Junaid ya dawo hayyacinsa, sannan Zubaida ta yi masa sharrin cewa ya yi mata fyaɗe".

A falon, aka ji tsit, sai numfashin mutane kawai ake ji.

Nan Umar ya ce. "Duk da cewar a shari'ar Muslunci indai haka ga mace tayi zina ana da buƙatar hujjoji mutane guda huɗu domin tabbatar da cewa tabbas ta aikata. amma saidai babu wannan huɗun ni ɗaya ne kuma CCTV camera baya ƙarya shi ya bayyana komai. Sannan shi ne asalin gaskiya".

Sooraj ya yi shiru na ɗan lokaci bayan Umar ya gama bayani, numfashinsa yana fita da sauri. Idanunsa sun yi ja, ransa yana tafarfasa.
"Zubaida, duk wannan sharri da kika yi wa Junaid kina sane da irin illar da kika jawo? Kin yi wa mutumin nan barna a suna, kin ƙeta masa martaba! Kin sa ni na zarge shi da abin da bai aikata ba."

Zubaida ta zube a ƙasa tana kuka, hannunta a haɗe tana roƙo.
"Wallahi na yi kuskure, shaiɗan ne ya ruɗar da ni. Ban yi niyyar lalata rayuwar kowa ba. Don Allah ka yafe min Sooraj."

Sooraj ya girgiza kai cikin ɓacin rai
"Yafe miki? Bayan kin sa wani ya sha wahalar abin da bai aikata ba? Yanzu da a ce Umar bai gano gaskiya ba, da har yau muna kallon Junaid a matsayin mai cin amanar aure da kuma masa kallon rashin mutunci. Wannan ba ƙaramin abu bane!"

Zubaida ta ƙara kuka, tana rawar jiki. Amma Sooraj ya miƙe tsaye, muryarsa na nuna ƙarshe.
"Daga yau babu aure tsakanina da ke. Na sake ki saki uku. Ki koma gidanku, ki nemi gafarar Allah da kuma Junaid wanda ki ka yi wa wannan babban sharri."
Ta saki ƙara mai tsuma rai, tare da faɗi ƙasa, yayin da aka ruga aka riƙe ta.

Sooraj ya juyo wurin Junaid, zuciyarsa cike da nadama.
"Junaid, na yi maka babban zargi, na ɗauke ka kamar mai ci amanar aure. Na yanke hukunci a raina ba tare da na bincika ba. Don haka ina roƙon ka, a matsayin ɗan uwa, ka yafe min."
Junaid ya ɗan yi shiru sannan ya ce cikin nutsuwa:
"Na yafe maka Yahya. Abinda ya faru darasi ne ga dukkanmu, cewa dole a binciki gaskiya kafin yanke hukunci sannan ita da taje ta yi zina Allah ya gafarta mata".

Sai Sarki ya yi gyaran murya, yana kallon kowa a falon.
"To, yanzu da gaskiya ta bayyana, dole a yi hukunci bisa shari’ar Musulunci. Zubaida ta yi ƙazafin zina ga wanda bai aikata ba, wanda hukuncin sa a shari’a shi ne bulala tamanin a bainar jama’a. Bayan haka, za a mayar da ita gidan iyayenta. Wannan hukunci zai zama darasi ga duk wanda zai kuskura ya yi irin wannan aiki a cikin masarautar nan."

Ya ɗan yi shiru, sannan ya ƙara da cewa
"Sannan an kore ki daga masarautar nan Allah ya shirya ki. Kuma wannan lamarin ya ƙarfafa mana darasin cewa a cikin masarauta, adalci shi ne ginshiƙin zaman lafiya."

Sosai Zubaida ke kuka da dana sanin abinda ya aikata. Nan fadawa suka fita da ita domin yi mata bulala tamanin. Haka aka fita da ita tana birgima tana kuka.

ALƘALAMIN
A'ISHA MB
ZINARIYAR JAJIRTATTU
[8/21, 8:01 AM] AYEESHER MB💞💞💞: https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎

*_THREE SIBLINGS FROM DIFFERENT PART OF THE WORLD_*🫁

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

*DIAMOND 💎 STAR⭐*
*LADIES 🧝‍♀️🧝🏼‍♀️🧝‍♀️*
(We stand together)
🤝🤝🤝

*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*BOOK 2 PAGE1️⃣1️⃣8️⃣▶️1️⃣1️⃣9️⃣*
________________________
Bayan an tafi da Zubaida, Sarki ya rufe taron. Inda su Sooraj da Aliyu suka ɗan taɓa hira. Gefe guda kuma Amrah na tare da Zahra a garden.

Kallon Amrah Zahra ta yi ta ce. "Amrah fatan kina rayuwa cikin farin ciki".

Girgiza mata kai Amrah ta yi ta ce. "Sosai ma kuwa, ya naki gidan fatan komai lafiya".

Ajiyan zuciya Zahra ta sauke! sannan ta ce. "Toh saidai na ce Alhamdulillah".

Murmushi Amrah ta yi ta ce matso da kunnen ki kiji".

Nan Zahra ta matso da kunnen ta. Nan Amrah ta raɗa mata magana a kunne. Zaro idanuwa waje Zahra ta yi cikin farin ciki ta ce.

"Da gaske ki ke Safira tana da juna biyu kema haka?".

Gyaɗa mata kai Amrah ta yi ta ce. "Eh ko jiya munje asibiti an bani magunguna sakamakon amai da nake yi".

Washe haƙora Zahra ta yi tare da rungume ƴar uwarta ta ce. "Gaskiya na tayaku murna, Allah ya sauke ku lafiya".

"Ameen". Amrah ta amsa. Sannan ya ƙara da cewa. "Kuma yanzu Yahya Umar yana koya min karatu yana min lessons, kasancewar ba a cikin mutane na tashi ba, ban san abubuwa game da karatu ba. Hakan ya sa yake koya min harda na addini".

Murmushi Zahra ta yi ta ce. "Masha Allah, su abin farin ciki ne wannan, gaskiya kin yi sa'a wallahi. Ki cigaba da maida hankali in sha Allah kema wata rana za ki san komai da komai".
[8/21, 8:03 AM] AyeesherM B: BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎

*A'ISHA M.B*💞💞

*BOOK 2 PAGE1️⃣1️⃣0️⃣➡️1️⃣1️⃣1️⃣*
________________________
Da sauri Zubaida ta bi bayan Sooraj domin kada ya tona mata asiri. Daidai lokacin ta ga Zahra ta fito daga part ɗin ta. Da sauri Zubaida ta ja burki kana ta wayance da faɗin. "Wai ina na saka waya na ne?". Ta faɗa tana dube-dube.

Girgiza kai kawai Zahra ta yi ta ce. "Hmmm inda ranka zaka sha kallo, wai ga waya a hannun mutum amma bai san da ita a hannunsa".

Sai a lokacin Zubaida ta tuna cewa da ashe da wayarta a hannunta. Ɓata fuska ta yi ta ce. "Toh sai me?, ina ruwanki da hakan?, aikin banza". Ta faɗa tare da koma wa part ɗin ta.

________________
Dutse
Zaune suke a parlour suna cin abinci kallonta ya yi annuri kan fuskarsa ya ce. "Kin san mene ne my wife?". Girgiza kai Safira ta yi alamun a'a.

Nan ya kalle ta ya ce. "A gaskiya ina cikin farin ciki mara misaltuwa, kin cika min burina, i love you so much my wife, Allah ya bamu kwanciyar hankali da nutsuwa a zaman mu".

Murmushi Safira ta yi tare da amsa wa da. "Ameen". Bayan sun gama cin abincin Safira ta tattara abubuwan da suka ci abinci da su ta kai kitchen tare da wanke wa. Dawo wa ta yi sannan ya dube shi ta ce. "Bari naje na haɗa maka ruwan zafin da za ka yi wanka da shi".

Tashi Aliyu ya yi tare da janyo ta jikinta sannan ya rungume ta yana mai faɗin. "No Safira, bana son ki wahalar min da kanki, tunda safe ki ke ta aiki a gidan nan, ni yanzu ina buƙatar ki a kusa da ni, ina son ki bani lokacin ki".

Cire jikin ta Safira ta yi daga nashi ta ce. "A'a Habibi ni da na ce maka na gaji, ka barni yanzu haka ma wanka nake ƙoƙarin zuwa nayi sai nayi bacci kaɗan kafin nan kuma na san kaima ka dawo daga office ko. Yanzu dai ka tawo na fara saka maka ruwan zafin da za ka yi wanka idan ya so daga baya sai ni naje nayi nawa".

Murmushi Aliyu ya yi ya ce. "Wai wai ya ga ya miki cewar ango yana fita office?, to albishirinki, hutun wata guda haka bani a office dan haka kinga babu inda zani muna tare. Muje yanzu sai kiyi min wankan".

Rufe fuskarta Safira ta yi alamun kunya ta ce. "Ni ba zan iya ba kaje kayi kawai". Ta faɗa tare da saurin shiga ɗakinta. Kallon love kawai ya bita da shi tare da girgiza kansa. Sosa lallausar sumar kansa ya yi cikin wani irin yanayi na farin ciki, kana daga bisani ya bi bayanta.

Ɓangare su Umar kuwa. Babu abin da yake faman yi sai kallon kyakkyawar fuskar matarsa Amrah, yayin da yake ji tamkar yafi kowa sa'ar samun mata a duniya.

Ganin yadda yake ta binta da kallo ya sa Amrah ta kauda fuskarta sannan ta ce. "Yah Umar ka daina min irin wannan kallon". Ta faɗa a shagwaɓe.

Sakin murmushi Umar ya yi ya ce. "Amrah kenan, toh idan ban kalle ki ba wata ki ke so na ke na kalla?, ko so ki ke naje na kalli wata?".

Nan take Amrah ta ɗauki pillow kujerar da ke kusa da ita ta wurga masa sannan ta ce. "Karka ƙara yi min maganar wata".

Fashe wa da dariya Umar ya yi ya ce. "Dama kina da kishi?, chabn lallai, ki ce bani ba ƙara aure".

Haɗe rai Amrah ta yi alamun ta yi fushi. Nan Umar ya haɗiye dariyar da ke cinsa sannan ya tako zuwa har inda take kana ya zauna kusa da ita. Ɗago da haɓarta ya yi sannan ya dube ta ya ce. "Kema kin san babu wata mace a raina ina ba ke ba, wasa fa nake miki kinji".

Mintsinin sa Amrah ta yi ta ce. "Toh ba zan haƙura ba har sai ka goya ni".

Murmushi Umar ya yi tare da tsugunna wa sannan ya ce. "Toh zo na goya ki".

Kunya ne ya kama Amrah inda ta ce. "Ni fa wasa nake maka, ka tashi kaji".

Girgiza kai Umar ya yi alamun ba zai tashi ba har sai ta su bayansa. Ganin yaƙi tashi ya sanya Amrah ta su bayansa sannan ya goya ta tamkar wata ƴar shekara biyar. Inda ya shiga zagaye gida da ita suna tafe yana binta da wasa da dariya.
Chapter 52 · 0% Book details