← Book details Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 65

Sashe 7

Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Rayuwata tana min wuya yanzu, ina jin bani da wata hanya da zan bi, gaba ɗaya sunana ya lalace a idan duniya amma ni na san Allah shi ne mai jiƙan bayinsa yana sane da ni, kuma Allah shi ne zai saka min da abinda haka aikata min. Amma a yanzu bani da madogaro ji nake dama ban yi kuɗi ba, ji nake dama a talaka na zo ina jin cewa dama banzo duniya ba, duk ta dalili na waɗan nan yara suka mutu, wannan yana sanya ni jin cewa na yi ɓarnar da ba zan iya gyara wa ba, na saka al'umma kuka duk kuma ni ina jin cewa tabbas kashe ni ɗin shi ne zai zama adalci domin bani da wata dama da zan samu yanzu a wajan al'umma". Ta faɗa cikin raunatacciyar murya yayin da hawaye ke bin kan ƙuncinta.

Kallonta nayi cikin tausaya wa na ce. "Kada ki furta irin waɗan nan kalaman, wannan yanayin yana iya faruwa ga kowa a kowane lokaci. Kamar yadda rana ke bayyana bayan duhun dare, hakan yana nuna cewa aikwai sabuwar dama da za ta zo, ki bawa kanki dama ki fuskanci sabon hasken da zai shigo rayuwar ki. Ni ɗin nan zan taimaka miki. Yanzu ki tawo mu bar nan wajan na kai ki gida, Aliyu yana chan yana neman ki ".

Kallo na ta yi ta ce da ni. "Wane ne ni?, ta ya ya na san Aliyu?, kuma shin zata iya ganin fuskana". Na ba ta da cewa. "A'a sanin ko ni wane ne bashi ba ne abu mai mahimmanci. Abu mai mahimmancin shi ne bayyanar da gaskiya sannan da wanke kanta domin dama tsarkakkiya ce a wajan Allah yanzu saura kuma ga mutane".

Girgiza min kai ta yi ta ce. Ina jin cewa bani da inda zan tafi a cikin wannan yanayin da na tsinci kaina a ciki".

Jin furucinta ya sa na ba ta martani da cewa. "Rayuwa tana da hanya mai yawa kamar keke mai jujjuya wa. Wasu lokuta, za ka samu damammaki ne a wuraren da ba ka za ta ba. Ko da kuwa kina jin kamar babu wata hanya, toh akwai hanyoyi da dama da za su buɗe a gaba. This is not the end of the road".

Jin kalamai na ya sa ta ji ƙarfin ƙwarin gwiwa tattare da ita hakan ya sa ta biyo ni na mai da ta gida ba tare da kuwa na bari ta ga fuskana ba, sannan nayi mata alƙawarin cewa indai tana cikin matsala to zan bayyana. Duk da cewar ba ta ganni ba amma ta ɗora yarda a kaina sannan ta faɗa min komai da komai dangane da dukiyarta da ke cikin wani daji sa'anan da hujjojin cewar ba ita ce ta aikata abin da ake zargin ta da shi ba. Nayi mata alƙawarin cewa duk rintsi duk wuya zan taimaka mata.

Bayan tafiyata da wasu kwanaki, Abdullahi ya sanar da ni cewa zai faɗa wa ƴan sanda cewa Lailah an ganta domin kuwa mahaifinta ne ya umarce shi da ya yi hakan sannan ya ce min bayan ƴan sanda sun kama ta ni da shi za mu je mu nemo inda takardun hujjojin abinda ya faru suke amma dole sai da fingerprint ɗinta hakan zai kasance.

Bayan Abdullahi ya sanar da ƴan sanda inda Lailah take hakan ya sa suka biyo shi har gida sannan suka kamata nan ta yi tunanin cewa kenan mijinta ya haɗa baki da Abdullahi haka ta ci kuka harta gode wa Allah ta sanadin ta kuma Aliyu ya samu cutar mantau dalilin hakan ya sa mahaifinta da yayanta Yusuf wato mahaifin Aliyu suka ɗora tsanar duniya a kanta. Ibrahim da matarsa Zainab kuwa samm basu yi goyon bayan abinda mahaifin su Salisu ya aikata ba.

Bayan ƴan sanda sun tafi da ita station ta sa ƴan sanda su kawo ta inda gidan ta yake kafin a zartar mata da hukunci domin ganin mijinta dan ta tambaye shi dalilin da ya sa ya butulce masa, amma tana zuwa ta tarar ko ina a rufe harma an siyar da gidan. Hakan ya sa ta yi tunanin cewa Abdullahi ne ya siyar ba tare da sanin cewa mahaifin ta shi ne wanda ya siyar da gidan bayan ya sa mutane suka yi wa Abdullahi duka sannan ya sa haka jefar da shi a titi. Kai tsaye Lailah ta sa haka kaita asibiti domin ganin Aliyu amma basu barta ta ganshi ba hakan ya sa ta koma police station. Ta yi kwanaki mai tarin yawa a chan yayin da haka sha zama da ita a kotu, Abdullahi ya nemi lauyoyi su tsaya Lailah a kotu amma babu wanda ya iya tsaya mata domin gaba ɗaya Musa ya siye su. Hakan ya sa haka dinga yin Shari'a a kotu ba tare da tana da hujja ko mai tsaya mata ba. Babu wanda ya je kotu a gidan su sai Ibrahim da Zainab domin Ibrahim yana qaunar ƙanwarsa kuma ya yarda ba ta aikata abin da ake zargin ta da shi ba.

Musa ya je gidan marayu ba tare da sanin kowa ba sannan ya ɗauko Usman, Ramlat khairat yaranda second wife ɗinsa ta haifa masa a lokacin baya iita ma kuma ta mutu ne a hatsarin mota hakan ya sa ya kai yaran gidan marayu domin kada matarsa khadija ta san yana wasu yaran. Bayan kuma mutuwar Khadijah ya je ya ɗauko yaran sannan ya kai su gida ya faɗa wa Umar cewa ƴaƴan da mahaifiyar sa ta haifa kenen, hakan ya sa Umar ya ja su a jiki kasancewar shi kaɗai yake rayuwa ba tare da ƙanne ba.

Musa ya fara neman thumbprint ɗin Lailah domin buɗe ɗakin ajiyar da na bashi bayani wanda kuma na ƙarya ne domin kuwa ni ne nan ba bashi bayanin ƙarya na cewa ga inda dukiyoyin ta suke.

Abdullahi ya yi iya bakin ƙoƙarin shi domin ganin ya sa kotu bata yanke mata hukunci ba amma duk abinda ya yi suka tashi a banza.

Ana tsaka da haka ya ji labarin cewar an yanke wa Lailah hukuncin kisa. Nan take ya kamu da yawan jini da tashin hankali hakan ya sa ya tattara komai nasa ya koma ƙasar China.

Ana tsaka da haka muka ji labarin cewa ba za'a yanke mata hukunci kisa ba kasancewar tana da juna biyu. Hakan ya sani shiga cikin farin ciki. Bayan wasu watanni naje kurkuku domin ganin ta zuwa na keda wuya na tarar tana naƙuda sannan ta haifo Zahra wacce ke ɗauke da brown eyes. Nan haka ce ba za ta iya haihuwa da kanta ba dole sai an kaita asibiti. A gaba na ta bawa Hajiya Binta amanar Zahra sannan haka wuce da ita asibiti. Nan ta haifo sauran biyun Amrah da kuma Safira. Nan ta bawa Nurse Nadiya Safira sannan ta ɗauki Amrah. Ta fita da ita, nan naji ana sanar cewa Lailah ta gudu hakan ya sa naje a matsayin mai napep don taimaka mata domin ta gudu, duk da na san cewar ita ce Lailah amma na tsaya tambayarta wace ce ita. Nan ta bani bayanin komai. Ni kuma na bayyana mata cewar ni ɗan sanda ne amma mijinta ne ya turo ni gare ta. Naga ɓacin rai tsantsa kan fuskarta lokacin da na ambaci sunan mijinta. Harta gaya min cewa ba ta da buƙatar taimakon da za ta fito daga wajan mijinta. Nan masu neman ta suka ganmu a take muka fara guduwa izuwa cikin daji, cikin rashin sa'a ɗaya daga cikin su ya harbe ni a ƙafa. Nan na ce ta gudu bayan ta gudu ta faɗa cikin wani ruwa inda dabbobi ke rayuwa a wajan a nan dai ta saka wa yarinyar suna Amrah cikin rashin sa'a naji ƙarar harbi an harbeta. Hankali na ya yi matuƙar tashi yayin da na fara yi musu hauka nan muka ga wasu daga ciki sun tawo a guje sakamakon birurruka da namun jejin da suka biyo su bayan sun kaini cell suka dinga gana min azaba iri-iri domin na faɗa musu mene ne halaƙar da ke tsakani na da Lailah amma na ƙi faɗa hakan ya sa suka yi tunanin bani da laifin komai a ƙarshe suka sake ni. Nan na cigaba da bibiyar rayuwar Safira da Zahra domin ni a lokacin nayi tunanin cewa Lailah da Amrah sun mutu.

Ibrahim ya yanke shawarar barin gidan Mahaifin su salisu domin kuwa shi baya goyon bayan abinda ke faruwa ga kuma gori da ake masa na ƙin samun haihuwa da bai yi ba da wuri. Hakan ya sa ya tattara komai na sa shi da matarsa Zainab suka bar gidan.

Mijin Nurse Nadiya Bai amince Nadiya ta ajiye Safira a gidan ba hakan ya sa ya karɓi yarinyar ba tare da nurse Nadiya na da ƙarfin cetar ta ba ya kaita bakin hanyar titi cikin akwati. Su Ibrahim na tafiya suka ji kukan jariri hakan ya sa suka ɗauke ta sannan suka wuce ƙasar America cikin cikin farkon shekarar 2006 domin kuwa a 2005 haka yanke wa Lailah hukuncin zama a kurkuku har sai ta haihu sai a yanke mata hukunci.

Ina bibiyar rayuwar Zahra da irin ƙalubalen da take fuskanta wajan al'umma na muzanta mata da suke yi. Bayan2 nan kuma kawai naji cewar muddin ina son na dinga ganin Zahra dole saina kasance a kurkuku hakan ya sa naje na aikata laifin sata domin a kaini chan, kamar yadda na so haka aka kaini chan kurkukun yayin da ɓangaren mata da ban, na maza ma da ban, ita kuwa Zahra babu inda bata shiga.

Bayan wasu shekaru haka yi ƙoƙarin fito da ni amma naje na ƙara aikata laifi duk dan ba na san barin cikin kurkuku. Hakan ya sa na ci-gaba da rayuwa tsawon shekaru goma sha hudu wanda izuwa lokacin Zahra nada shekaru sha tara a duniya. Lokacin da Aliyu ya zo waje na a kurkuku nayi mamaki sosai domin kuwa tabbas na gane shi ne ɗan yusuf yayan Lailah ban nuna cewar na san shi ba shima kuma bai gane ni ba. Yadda faɗar su ta fara shi da Zahra gaba ɗaya ina wajan.
Chapter 7 · 0% Book details