← Book details Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 65

Sashe 57

Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gyaɗa masa kai ta yi da sauri. Riƙe hannunta ya yi sannan suka fita waje yayin da suka nufi parking space. Kallon Zubaida ya yi ya ce. "Na manta je ki kira Zahra mu tafi".

Nan walwalar fuskar Zubaida ya gushe. Kallon sa ta yi ta ce. "Dama ba mu biyu zamu tafi ba?".

Amsa ya bata da cewa. "Eh ba zai yu mu barta ita ɗaya a cikin gida ba".

"Shi ke nen". Kawai Zubaida ta iya furta wa sannan ta koma ciki domin kiran Zahra.

Tana zuwa part ɗin zahra ta fara bubbuga mata ƙofa kamar zata ɓalla. Zahra da ke zaune tana kallon "tere bina" a arewa ta jiyo ana bubbuga mata ƙofa. Nan ranta ya ɓaci. Da sauri ta tashi tare da nufar kofar sannan ta buɗe.

"Ya dai ki ke bubbuga min ƙofa kamar wacce ta yi sata?".
Tsaki Zubaida ta ja sannan ta ce. "An buga ɗin ne za ki yi?".

Murmushi Zahra ta yi ta ce. "Kina don ki dan abin da zan yi?, to nan gaba ki ka sake yi min irin wannan sai na cire miki wannan dogon bakin naki mai kama da na jaɓa. Wai ke a rayuwar ki bakya son zaman lafiya ne?, kin san idan rashin ji ne na fiki, na tattaka ki a rashin ji, amma me na watsar da komai. Ni ina ji ana cewa idan mace ta yi aure tana ƙara hankali, amma ke naki hankalin raguwa yake, ki dai bi duniya a sannu dan wallahi zata kaiki ta baro ki".

Zubaida kuwa ji ta yi tamkar zuciyar ta zata fashe. Dubanta ta kai kan Zahra ta ce. "Kin san dai ni ba sa'ar ki bace ba ko?, kin san na fiki aji, class da sarauta, ke da ne ki ka fi ni?".

Murmushi Zahra ta yi ta ce. "Kalle ni da kyau fara nake ba baƙa nake ba. Kina son ki san abin da na fiki da shi?. Toh farko dai kin girme ni amma na fiki hankali, sannan ni ina da sauran mutunci da daraja ta a gidan aure na domin na zo da budurci na, ke da me ki ka zo. Kuma abin aushin ma me makon ki chanza amma abin ƙara tubatsa yake".

Cikin fusata Zubaida ta ce. "Kenen gori za ki yi min?. To ina ruwanki ma idan ban zo da shi ɗin ba, jikin ki ko nawa?. Wallahi in baki bini a sannu ba zanyi miki dukan kawo wuka".

Nan take Zahra ta haɗe rai ta ce. "Ɗan halak ka fasa, idan baki dake ni ba baki cika ƴar halak na".

Sooraj da ke tsaye ya ji komai da suke tattaunawa. Ajiyan zuciya ya sauke!, sannan ya ce. "Me ke faruwa a nan ne?".

Nan take suka juyo tare da kallonsa. Amsa Zubaida ta bashi da cewa. "Babu komai, muna magana ne da ita".

Kallon sa Zahra ta yi ta ce. "Ƙwarai kuwa Zubaida ta yi gaskiya magana muke yi".

Nan Sooraj ya dube su ya ce. "Maganar me?". Shiru kowanensu ta yi . Nan Zahra ta ce. "Maganar sirri ne wanda uwar gida da kishiya suke yi".

"Kenen bani da damar ji?". Cewar Sooraj.

Girgiza kai Zubaida ta yi ta ce. "Kada ka damu ba da maganar a zo a gani ba ne".

Murmushin yaƙe Sooraj ya yi ya ce. "Akwai abinda ku ke ɓoye min, ina son kuma na san mene ne wannan abun da ku ke ɓoye wa".

Shiru kowacce su ta yi. Nan Zahra ta ce. "Ƙwarai kuwa, bamu so gaya maka ba, saboda muna don muyi maka bazata ne. Dama Zubaida yanzu haka tana ɗauke da juna biyu naka, dama cewa ta yi zata maka bazata shi ne muke shirya wa".

"Juna biyu?". Sooraj ya maimaita kalmar a ransa. Nan take zufa ya fara ƙeto wa Zubaida a jiki.

Kallonta Sooraj ya yi ya ce. "Juna biyu kuma a yaushe?".

Amsa Zahra ta bashi da cewa. "Eh mana tana da juna biyu yanzu haka sati ɗaya kenen da sani. Kai da ya kamata kayo farin ciki mene ne naka na damuwa?".

Sosai Zubaida ke yin mamakin ganin yadda Zahra take rufa mata asiri amma hakan bai sa ta ƙiyi mata rashin mutunci ba.

Ajiyar zuciya Sooraj ya sauke ya ce. "Ƙwarai kuwa, kinyi gaskiya ya kamata nayi farin ciki da hakan. Idan kun gama tattaunawar kuzo ina jiranku a cikin mota zamu fita". Yana kaiwa nan ya fice.

Kallon Zahra Zubaida ta yi ta ce. "A kan me za ki gaya masa cewar ina da juna biyu?, shin kinyi hauka ne".

Kallonta Zahra ta yi ta ce. "Lallai sai yanzu na ƙara tabbatar da cewa baki da hankali, yanzu na rufa miki asiri na ce cikinsa ne a jikin ki amma ki ke cewa dan me zan gaya masa?, to so ki ke na gaya masa cewar kina ɗauke da cikin shege a jikin ki me?".

A fusa ce Zubaida ta ce. "To bana son rufa asirin naki, shirme kawai, shin na buƙaci kiyi hakan ne, mara zuciya kawai". Tana kaiwa nan ta fita.

Shiru Zahra ta yi ta ce. "Ikon Allah, yanzu ni nayi laifi dan na rufa miki asiri?. Bakomai, gaba tafi baya yawa, kin kashe kasuwar gobe". Tana kaiwa nan ta shiga ciki ta ɗauki hijabi jalbab ta fito kai tsaye wajan motar ta nufa. Nan ta ga Zubaida a gaban mota. Taɓe baki Zahra ta yi sannan ta koma back seat ta zauna.

Nan Sooraj ya tada mota yayin da mai gadi Ya buɗe musu ƙofa suka fita.

Suna cikin mota suna tafiya Zahra ta fara waƙa. "So suke suga mu tsaya cak, gashi muna ta gaba, sunƙi Allah ya nufa maƙiya ban san me nayi muku ba. Kallon biri suke min, ina musu na ayaba".

Kallonta Zubaida ta yi ta ce. "Ke mene haka za ki zo ki dame mu da waƙa?, ko an ce miki ke kaɗai ki ka iya waƙa, kiyi mana shiru".

Dariya Zahra ta yi ta ce. "Ina ta waƙa uwata bata hanan ba, ina ta waƙa uba na bai hanan ba, ina ta waƙa sarki bai anan ba, ina ta waƙa Malam bai anan ba. To tunda har Malam bai anan ba, kowa ya ce zai ana ni ubansa zanci".

Nan Zubaida da Sooraj suka zaro idanuwa waje. A fusa ce Zubaida ta ce. "Hakan me za ki zagi uba na, banza matsiyaciya kawai".

Murmushi Zahra ta yi ta fara waƙar Ali jita kamar haka. "Dole ne a barki uwar gida, dole ne a biki uwar gida, a ci arzikin ki uwar gida.. dakatar da ita Zubaida ta yi da faɗin.

"Karya ki ke wallahi, bani na ci arzikin ki ba ke ki ka ci arziki na".
Ganin sun ishe shi ya tsaya Sooraj ya daka musu tsawa. "Wai me ke damunku ne haka?, wai ba yanzu na ga kuna hira ba a ciki, wannan wace iriyar shirmen banza ne, toh wallahi duk wacce na ƙara jin bakinta wajen nan saina sauke ta".

Kallonsa Zahra ta yi ta ce. "Sauke ni kawai, domin ni baki na ba zai iya shiru ba, dan Allah ya gani waƙata nake yi kuma ba da kowa nake ba, ya za'a ana ni sukuni?, gaskiya indai zanyi shiru ka kunna mana waƙa ta cikin mota, in ba haka ba ni na cigaba da nawa".

Nan Zubaida ta ce "Ba za'a kunna waƙar ba motar ta ubanki ce sheg....
Bata kai ga idda maganarta ba Zahra ta wanke ta da mari. A fusa ce Zahra ta shaƙe mata wuya.

Da sauri Sooraj ya nemi guri ya yi working.

Cikin huci Zahra ta ce. "A kan me za ki yi magana kan mahaifi na?". Ƙoƙarin ƙwace kanta Zubaida ke yi amma hakan ya cutura.

Cire hannun Zahra Sooraj ya daga jikin Zubaida ya ce. "Baki da hankali ne Zahra dan me za ki mare ta?".

A fusa ce Zahra ta ce. "Dan me na zan mare ta ba, wannan ai rashin mutunci ne". Babu zato ta ji ya wanke ta da mari. A fusa ce ya dube ta ya ce. "Fitar min daga cikin mota".

Dafa fuskarta Zahra ta yi ta ce. "Ni ka mata?". Girgiza kai Sooraj ya yi ya ce. "Ƙwarai kuwa na mare ki domin rama mata nayi, kin san tana ɗauke da juna biyu kuma za ki mata haka saboda baki da tunani?, ke hanya ya kamata a kira ki da matar aure kuwa?, samm rayuwa da irin ku a gidan aure na masifa ne, ban san me ya sa na na yarda haka ɗaura mana aure da ke ba wallahi. gaba ɗaya baki da hankali, kuma wai mata ta, tirr ni dai banyi dace ba samm. Maza fice min daga cikin mota kuma ki juya ki tafi gida".

Sosai maganar da ta ratsa zuciyar Zahra. Share hawayen da ke ƙokarin zubo mata Zahra ta yi ta ce. "Wannan shi ne karo na biyu da ka mare ni. Bakomai ba laifin ka ba ne". Tana kaiwa nan ta buɗe murfin motar tare da fice wa daga ciki. Maida kallonsa Sooraj ya yi kan Zubaida ya ce.
"Kina dai lafiya ko?, dan Allah kiyi haƙuri a kan marin da ta yi miki ba ta da tunani". Cikin hawaye Zubaida ta ce. "Mu koma gida dan Allah".

"Shikenen". Sooraj ya faɗa tare da juya motar suka koma gida.

Ɓangaren Zahra kuwa bayan fitar ta daga cikin motar. Ta samu guri ta zauna hawaye na bin kan fuskarsa. Girgiza kai Zahra ta yi ta ce. "Wato bai yi dacen mata ba ko? Hmmm ba laifin ka ba ne Soo... Ba ta kaiga ƙarasawa ba ta fashe da kuka yayin da ta saka kanta tsakanin cinyoyinta tana ta rusa kuka. Gefe guda kuma mutane suna wuce wa suna kallonta.

Har haka yi sallar Isha'i Zahra bata dawo gida ba, shi kuwa Sooraj ko a jikin da. Ɓangaren Zubaida kuwa ranta fal babu abinda ya dame ta.
Chapter 57 · 0% Book details