← Book details Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 65

Sashe 30

Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"A shekarun baya da suka gabata lokacin ina da shekaru sha biyar a duniya, ni da iyaye na muka yi hatsarin mota a hanyar mu ta zuwa garin Abuja wajan ƙanin babana yayin da suka mutu ni kuma na rayu. Na sha wahala sosai, yayin da na rasa mafaka na rasa ina ne zan sa kaina, mutane sun taimaka min wajan bani kuɗaɗe yayin da gomnati ta ɗauki nauyin karatu na, bayan na gama karatu ne na soma neman aiki amma naƙi samun aiki ganin takardun karatu na ba su zama daidai yadda ake so ba. Ganin ba zan iya jure wa na zauna ba aiki ba ne ya sa na fara aiki a gidan mai abinci matsayin ƴar aiki, yayin da nake musu wanke-wanke da shara, ina zaman lafiya da su babu abin ke haɗa ni da su sai sannu. Kwatsam ana zaune wata rana aka yi satan kuɗi a gidan abincin nan kimanin dubu ɗari, nan mai wajan ta tayar da hankalinta yayin da ta ce sai an fito mata da kuɗin ta in ba haka ba ta kira ƴan sanda. Na shiga cikin damuwa sosai domin ni ce kawai ke shiga inda take ajiyan kuɗi kuma babu abinda yake kaini sai yin shara. A nan ne dai ta fara zargi na ta ce na fito mata da kuɗaɗen ta ko kuma na rasa aiki na, nayi rantsuwar duniyar nan cewa bani na ɗauki kuɗi ba amma haka ta je fa ni waje ta ce ta sallame ni. Na sha kuka domin da wannan aiki nake ciyar da kaina. A nan ne na haɗu da Kamal wanda ya kasance ɗan kasuwa kuma manomi, a nan ne muka fara soyayya da shi harta kai ga cewa yana son ya aure ni, ni da shi mum faɗa soyayya wanda muke ji cewa mutuwa ce kawai za ta raba mu, amma iyayensa sunƙi amince wa ya aure ni kasancewar bani da iyaye kuma bansan dangi na ba, hakan ya sa suka ce ba za su bari ɗan su ya auri wanda ba ta dangi ba, haka na ci kuka na na gode wa Allah. A haka iyayen Kamal suka rabani da shi. Nan na cigaba da tafiyar da rayuwata yayin da naji gaba ɗaya duniyar ta ishe ni. Hakan ya sa na yanke shawarar cewa kawai na faɗa a ruwa na mutu. A wajan ƙoƙarin kashe kaina a wajan gona, nan ne wani manomi ya zo ya ceci rayuwata, yayin da ya tambayi wace ce ni, kuma me ya sa nake son na kashe kaina. Nan na faɗa masa komai dangane da rayuwata babu abinda na ɓoye masa. Ya tausaya min sosai yayin da ya bayyana min cewa shi manomi ne kuma sunansa Imran yana da aure saidai matarsa ta rasu, kuma yana da yara uku mace ɗaya namiji biyu kuma duk manya ne. Ya ce min idan ba damuwa na zauna tare da su zai kula da ni tamkar yadda zai kula da kansa. Na amince domin ni a gani na sabuwar rayuwa ya bani. A haka na shiga gudanar da rayuwata tare da Imran da kuma ƴaƴan sa, saidai rashin dace ya sa yaransa samm basua ƙaunata. Abin ya dame ni sosai, har na kasa ɓoye hakan na faɗa wa Imran, jin hakan ya sa Imran ya yi musu faɗa sannan ya ce su dinga girmama ni tamkar yadda suke girmama mahaifiyar su kafin ta rasu. Na ɗauka abin da Imran ya faɗa musu zai kashe tsanata da suke yi, ashe wata wutar gobarar tsana ta Imran ya kunna musu a zuciyoyinsu. Kwatsam wata rana ya zo ya same ni a zaune ina tsintar wake ya ce min a gaskiya yana son zai aure ni saboda na dinga kula da yaransa koda a ce bayan mutuwarsa ne, kuma bai tursasa min ba idan ina so to, ina kuma bana so shi ke nen. Nayi tunani sannan naga dai Imran ya kasance mutumin kirki ne wanda ya san ya kamata. Ba tare da wani tunanin abin da zai je ya dawo ba na amince da buƙatar sa. Ya yi farin ciki sosai da na amince a nan ne haka ɗaura mana aure inda ya biya sadaki na a dubu goma kasancewarsa mai matsakaicin ƙarfi. Yaransa sunji haushi sosai ganin mahaifinsu ya aure ni, hakan ya sa mazan suka shigo ɗaki na bayan sun gama shan kayan mayen su sannan suka yi gargaɗi a kan cewar na rabu da mahaifin su in na haka ba su bani mamaki. Na shiga damuwa sosai domin a gaskiya na ɗaukar wa Imran alqawarin ba zan taɓa rabuwa da shi ba. Na yi nasarar shawo kan kanwar su mace yayin da ta zama kamar ƴar da na haifa da ciki na. Ƙanwar su wato Rahama ta kasance tana son karatun boko ta gama secondary amma tana son cigaba da karatu, saidai mahaifinsu bashi da ƙarfin da zai sata a jami'a. Wata rana muna zaune da ita naji labarin cewa Company miss Lailah Abdullahi suna ɗaukar yara ana basu scholarship. A nan ne na ɗauki Rahama muka je saidai munsha zuwa basua bari mu shiga daga ƙarshe dai wani baba mai gadi ya bar mu muka shiga cikin Company domin haɗuwa da miss Lailah dan Rahama ta samu scholarship. Bamu samu damar haɗuwa da Lailah ba mun haɗu da manager yayin da haka saka sunan Rahama a list ɗin yaran da za'a ɗauka. Mun koma gida cikin farin ciki nake sanar da mahaifinsu abin da ke faruwa, Imran ya yi farin ciki sosai domin yana son yarsa ta yi karatu amma bashi da kuɗi. Su kuwa ƴan uwanta maza samm basu yi murna da hakan ba domin gani suke so nake na cutar da ƴar uwar su. Bayan kwana biyu aka kira mu aka sanar mana da cewa Rahama ta samu scholarship. Cikin farin ciki muka je muka karɓi form yayin da haka yi mata passport da komai da komai. Nan dai suka tafi da su Rahama ƙasar waje karatu. Nasha zuwa gidan miss Lailah domin nayi mata godiya saidai duk lokacin da naje mai gadi sai ya ce bata nan. Nasha ganin hoton ta jarida a matsayin shaharriyar mai kuɗi da take tashe a lokacin, ni kuma a lokacin buri na shi ne kawai na ganta ni ma ta ɗauke ni aiki a kamfanin ta, nasha gwagwarmaya sosai wajan ganin na haɗu da ita saidai duk a banza. Muna zaune haka ce mana su Rahama sun dawo daga ƙasar waje. Munyi mamaki sosai jin dawowarsu domin basu fi watanni zuwa shekara ba da tafiya. Munje da farin ciki domin ganin Rahama amma muna zuwa muka tarar da gawar Rahama kwance gaba ɗaya babu kyan gani. Mutuwar tsaye nayi lokacin da nayi arba da Rahama da sauran gawauwakin da ke kwance. Bansan lokacin da na fashe da kuka ba. Yayin da Imran kuwa ya kamu da ciwon zuciya a take. Nan hankali na ya ƙara tashi. Daidai lokacin motocin Lailah da Ita kanta Lailah ta iso wajan nan naji soyayyar da nake yi mata ya juya ya koma tsantsar tsana, a nan ne mutane tare da ni muka soma jifanta. A nan ne dai ta samu ta bar wajan. Bayan koma war mu gida haka je haka yi jana'izar Rahama, nan mutanen layi, maƙota da yaran Imran suka shiga zagi na, suna cewa ni ce silar mutuwar Rahama. Nayi kuka sosai har na gode wa Allah. Nan na cigaba da kulawa da Imran wanda ko tafiya baya iya yi. Bayan wasu kwanaku naji labarin cewa a kama miss Lailah kuma za'a yanke mata hukunci a kotu daidai da laifin da ta aikata. Nayi farin ciki sosai na fara shirye-shiryen cewa harda ni za'a kalli shari'a. Amma kafin ayi nata haka yi nawa shari'a dalilin kuwa mutuwar Imran, yaransa sun bashi guba ya ci yayin da suka laƙaba min cewa ni na kashe shi da hannu na. Na yarda da cewa ni na kashe shi domin idan naje kurkuku naga Lailah na ɗauki fansar abinda ta yi min. Nan kotu ta yanke min hukuncin rataya, a lokacin ne yaran suka fito suka faɗi gaskiya cewa sune suka kashe mahaifin su domin suyi min sharri, nayi mamakin ganin su fito sun faɗi gaskiya, raina bai so hakan ba domin bana son a ƙyale ni hakan ya sa nace ƙarya suke haɗa hannu muka yi da su muka kashe Imran, nan dai kotu ta yanke min zaman kurkuku na shekaru ashirin tare da biyan tara, yayin da su kuma ƴaƴan Imran haka yanke musu hukuncin kisa. Bayan an kaini kurkuku na shiga tsimayi zuwan Lailah kurkuku, nan dai ta shigo kurkuku da juna biyu. Nayi ƙoƙarin shiga jikinta na kwanakin da ta yi, nan ne ta bani wani littafi ta ce idan ta haifi ɗa ko ƴa in bata wannan littafin, na karɓi littafin sannan naje a ɓoye na karanta shi. Sai a lokacin na gane cewar ashe sharri haka yi mata ba laifin ta ba ne ba, na ji tausayin ta sosai. Nan duk tsanar da nake mata ya gushe. Daga ƙarshe dai ta haihu ta bar Zahra a waje na tace na kula mata da ita a nan ne da haka tafi da ita asibiti naji labarin ta haifi wasu yaran, kuma ta gudu, nan ne kuma naji labarin cewa ƴan sanda sunyi nasarar harbin ta. Sai kuma yanzu dana ji cewar tana raye abin ya bani mamaki kuma yanzu ina cikin farin ciki".

Ajiyan zuciya matar da ke sauraronta ta yi ta ce. "Lallai wato kenen kin zo ne domin ɗaukar fansa, daga ƙarshe ki ka koma taimakon ta har ki ka raini ƴar da ta haifa".

"Girgiza kai Hajiya Binta ta yi ta ce. "Eh nayi hakan ne domin na cika mata alƙawarin da na ɗaukar mata".

________________
Sooraj kuwa gajiya ya soma yi da riƙe Zahra a hannu, hakan ya sa ya ajiye Zahra sannan ya juya bayansa tare da goyata sannan ya tashi ya cigaba da tafiya chan ya hangi parrot ɗin da ya taimaka masa lokacin shigowar sa cikin daji. Da sauri ya isa inda yake sannan ya ce. "Ka fitar da mu daga nan kaji".
Chapter 30 · 0% Book details