Sashe 11
Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Wannan wace iriyar jahilci ne, wanna dama shi ne halin illiterate ɗin da ake gaya miki aikin banza kawai". Safira ta ƙarashe maganar tana mai ƙara toshe hancin ta.
Harara Zahra ta galla musu ta ce. "Bana som iya shege, a cikin ku waye zai ce baya tusa?, kema da ki ke cewa jahilci ai naji ɗazu kin saki taki mai iska ba mai ƙara ba, shi ne ni dan nayi sai ya zama laifi?, ko a nan akwai wanda zai ce baya tusa?. Ni wallahi hankali na ne ya tashi jin cewar wani a cikin mu zai mutu, tashin hankali ne ya sa ban san sanda na saki tusa ba".
"Shi ke nen dai yanzu mene abun yi?". Cewar Umar.
Kallon su Safira ta yi ta ce. "Mafita ɗaya ce, shi ne mu fasa zuwa shi mahaifin na mu da kuma Nurse ɗin da aka ce ta ceci mahaifiyar mu sai su zama hujja. Domin ni gaskiya ba zan iya bayar da rayuwata wa ƴar prisoner ba".
Kallon tara saura kwata Zahra ta bi Safira da shi ta ce. "An gaya miki nima zan iya bayar da rayuwata a kanki ne?, ai ba sunana saratu ba da zan zama asararriyar da za ta bada rayuwarta ga ke. Gwara-gwara ma Amrah zan iya bata tawa rayuwar amma ke kam koda wasa wallahi".
Kallon su Amrah ta yi ta ce. "Gaskiya nima ba zan iya shiga cikin wannan rijiyar da za ta kai mu cikin dajin nan ba, mu haƙura kawai gaskiya". Ta faɗa tana mai juyawa.
Juyawa suka yi gaba ɗaya da zimmar tafiya.
Muryar Zahra suka jiyo daga baya tana faɗin. "Ku dakata!".
Da sauri suka juya. Da mamakin su suka ga ta au kan rijiyar. Zaro idanuwa gaba ɗaya suka yi waje. Sannan suka ce. "Zahra mene aka?".
Murmushi Zahra ta yi ta ce. "Baku san irin tsananin ƙaunar da nake yi wa mahaifiyata ba, duk da cewar ban taɓa sanya ta a cikin idanuna ba amma ina matuƙar ƙaunarta, to a kan me ya sa ba zan iya cetan ta ba bayan ita ce wacce ta tsugunna ta haife ni?, idan har za mu iya juyawa mu tafi saboda an ce wai ɗaya a cikin mu zai yi mutu, to tabbas mu ɗin ƴaƴan bogi ne ba na gaskiya ba". Tana ƙarashe maganar ta saki ƙara sannan ta faɗa cikin rijiyar.
Da gudu su ma su Amrah suka ƙarasa wajan yayin da su biyun suka riƙe hannun juna tare da awa kan rijiyar suka faɗa ciki.
Tsayawa su Sooraj suka yi suna bin rijiyar da kallo domin basua iya hango komai da ke cikin wajan.
Addu'a Sooraj ya shiga yi cikin ranshi. "Ya Allah kasa ba Zahra ce zata mutu ba". Yayin da suma su Umar da abinda suke saƙawa a ransu.
Guri suka samu gaba ɗaya suka zauna
Saida suka ɗau lokaci mai tsayi suna yawo kan iskan rijiya kafin daga bisani suka faɗi a wajan gaba ɗaya a sume. A yayin da littafin da ke hannun Zahra ya bada wani irin farin haske.
MANAGE PAGE🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏
SHIN A GANIN KU A CIKINSU WACE CE ZATA MUTU?. WANE SIRRI A DAJIN DA SAFIRA TA CE MAHAIFIYAR SU TA ƁOYE?. MUJE ZUWA DOMIN JIN YADDA AL'AMARIN ZAI KASANCE
KADA KU MANTA DA LIKE, COMMENTS, AND SHARE FISABILILLAH 🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏
ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞💞
ZINARIYAR JAJIRTATTU
بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!
*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎
*BOOK 2*
PAGE 6️⃣9️⃣▶️7️⃣0️⃣
Saida suka ɗau fiye da minti goma kafin daga bisani Amrah da Safira suka buɗe idanuwansu.
Zaro idanuwa suka yi waje ganin daji mai matuƙar kyawun gaske. "Wow!". Safira ta ce yayin da tana mai cigaba da bin dajin da kallo.
Amrah kuwan maida kallonta ta yi kan Zahra da ke kwance sannan ta ƙarasa in da take tare da girgiza ta. A razane Zahra ta farfaɗo tana mai faɗin. "Wayyo shin ina raye ne ko na mutu?".
Kallonta Safira ta yi ta ce. "Da kin mutu za ki na ganin mu ne, aikin banza".
Miƙe wa tsaye Zahra ta yi tana mai karkaɗe jikinta da kuma littafin da ke hannunta. Kallon su biyun ta yi ta ce. "An ce sai mun shiga dajin nan zamu fara buɗe littafin nan muna karantawa shi ne zai dinga yi mana nuni ga hanya".
Ta faɗa tana mai buɗe littafin, kamar jira ake ta buɗe littafin aka fara wata iriyar iska mai haɗe da guguwa yayin da ko ina na dajin ya karaɗe da ƙura.
Kallon Safira Zahra ta yi ta ce. "Bakin ce kina da baiwar matsar da abu ba?, toh ki matsar mana da iskar nan".
Kallonta Safira ta yi ta ce. "Ke ni fa bana jin abin da ki ke cewa iska ya yi yawa bana jin ki".
Kama kunnenta Zahra ta yi da ƙarfi, nan Safira ta saki ƙara mai ƙarfi jin irin riƙon da Zahra ta yi wa kunnenta. Ƙara Zahra ta ƙwalla a kunnen Safira ta ce. "Kina ji na, na ce tunda kina da baiwar matsar da abu ki matsar da wannan iskan kinji ko baki ji ba?". Ta faɗa a tsawa ce. "Na ce kinji ko baki ji ba".
"Naji, naji. Amma ba zan iya ba gaskiya". Cewar Safira
Sakar mata kunne Zahra ta yi ta ce. "Kina nufin ba za ki iya ba kenen?, toh wallahi sai kin yi, tunda ki ka furta cewar kina da wannan baiwar saikin matsar da iskar nan gefe idan kuma ba aka ba, saina miki shegen duka".
Jin hakan ya sa Safira ta gyara tsayuwar ta sannan ta haɗa hannayenta guri guda tana mai tura su gaba sannan a hankali ta fara ware hannayenta. Nan take iskar ta washe kamar bata taɓa wanzuwa a wajan ba.
Ajiyar zuciya gaba ɗaya suka sauke sannan Amrah ta dube su ta ce. "Maza ku tawo mu yi abin da yake gaban mu bamua da isashen lokacin".
Duban cikin littafin Zahra ta yi yayin da su Amrah suma suka ƙara inda Zahra take tare da zuba wa littafin idanu.
A cikin littafin Zahra ta ga an sa. "Barkan ku dai ƴan uku, kafin ku kaiga kun fara tafiya dole a cikin ku ɗaya ta yi muku jagorar tafiyar ku".
Kallon juna su ukun suka yi yayin da Amrah ta ce. "Wace ce za ta yi mana jagora?".
Kallon Zahra Safira ta yi ta ce. "Tunda kece mai riƙe da littafin dole kece za ki yi mana jagora".
Kallon kanta Zahra ta yi ta ce. "Ni kuma?, in karanta littafi sannan kuma nayi jagora, samm ba zai yiwu ba. Ku fa kuna da baiwa a cikin ku ya kamata a zaɓi wacce za ta yi jagora amma bani ba".
"A'a Zahra tabbas kece ki ka fi cancanta da kiyi mana jagora mu kuma zamu dinga kawar da duk wani abu da zai kawo mana hari". Cewar Amrah.
Girgiza kai Zahra ta yi ta ce. "Tom shi ke nan". Ta faɗa tana mai maida kallonta kan littafin. A cikin littafin ta ga an sa. "Ku miƙe kan hanyar da ku ke kada ku tsaya har sai kun ci karo da bishiyar tsamiya".
Jin hakan ya sa Zahra ta tsaya a gaba yayin da su biyun suka tsaya daga bayanta. Nan suka fara tafiya.
***********
"Mu yanzu zaman me muke a nan?". Cewar Aliyu.
Amsa Sooraj ya bashi da cewa. "Zaman jiran su mana".
"Kasan yaushe ne za su dawo ne?, ba fa lallai su dawo yau ba". Cewar Umar.
Kallonsu Sooraj ya yi ya ce. "To ku tawo mu je fadar mu mu dan ci abinci sai mu huta".
Ya faɗa yana mai nufar inda motarsa take. Nan su Aliyu suka bishi a baya.
Shiga cikin motar suka yi tare da barin harabar wajan baki ɗaya.
*****
"Yallaɓai zamanka a China yanzu ya ƙare, domin kuwa ƴaƴan ka sun tafi nemo hujjoji kuma za'a dawo da shari'ar matar ka".
Cikin farin Alhj Abdullahi ya miƙe tsaye daga kan kujerar da yake. "Mk, ina nufin Mubarak da gaske ka ke wannan maganar".
Murmushi Mk ya yi ya ce. "Yau dai ka kira ni da cikakken sunana, ai ka san ba zan taɓa yi maka ƙarya ba yanzu aka ma mun kusa isa garin jigawa muna tare da dpo shi zai taimaka mana sannan dole mu samo ƙwararren lawyer wanda zai tsaya mata a gaban kotu. Dan aka yanzu ka shafa wa zuciyar ka ruwan sanyi domin gaskiya ta kusa ta yi halinta. Lokacin Gov. Musa yanzu ya ƙare".
Cike da farin ciki Alhj Abdullahi ya ce. "Kasan yadda nake ji yanzu kuwa?, da faɗa min wannan zancen ji nayi tamkar anyi min albishir da gidan aljannah, yanzu nan zan fara shirya wa na dawo Nigeria". Yana kaiwa nan ya katse wayar.
Mintuna ƙalilan su Sooraj suka ɗauka kafin su isa ga fada.
Shiga cikin masarautar ya yi yayin da fadawa suka nufi inda su Sooraj suka yi parking yayin da suka tsungunna.
Fitowa su Sooraj suka yi, suna ganin ya fito suka fara yiwa Sooraj kirari. "Wane ne idan ba ɗan sarki ba? mai jinin sarauta da halin mazan jiya, wanda mulki ke binsa kamar inuwa,
mai hangen nesa fiye da hasken rana, ɗan jarumi, mai sulhu da yaƙi,
Mai murya ɗaya da ta fi karfi ƙarar ganga,
Mai fuska ɗaya amma zuciya kamar zinariya,
Gatan talakawa, garkuwar masarauta,
Wanda ba a yi kamarsa a gaban tarihi!".
Murmushi Sooraj ya yi yayin da ya dube su ya ce. "Wannan kirarin naku kaɗai ya isa ya tsuma zuciyar mutum".
Murmushi Umar ya yi ya ce. "Dole wannan kirarin ya tsuma zuciyar mutum, kamar ruwan sama a tsakiyar hamada, yana shiga kai tsaye zuciya ba tare da izininta ba, yana tayar da jarumta da tunani cikin zuciyar mai sauraro,
Kirarin da ke ɗaga gwiwa, ya sa mutum ya manta da gajiya, maganar da ba a faɗa don kunne ba — an faɗa ne don rai!"
Murmushi gaba ɗaya suka yi yayin da suka shiga kai tsaye cikin parlour. Nan suka tarar da kowa a zaune. Mamaki ne ya kama Sooraj ganin family gaba ɗaya a zaune.
Daga nesa Sooraj ya hangi Zubaida ta yi shaɓe-shaɓe da hawaye. Cikin zuciyar sa ya ce. "Me kuma Zubaida take yi a masarautar nan"