Sashe 25
Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Murmushin mugunta Gimbiya Saratu da Talatu suka saki yayin da Talatu ta ce. "Da ba Zahra da Sooraj ne gatan ki a gidan nan ba, to yanzu kuma basua nan, muna da damar yi miki duk abin da muka gadama, kuma ki sani cewa a baya ma ba ƙyale ki muka yi, kawai dan ɗanki shegen nan haihuwar asar..... Maganarta ne ya dakata sakamakon saukar mari da ta ji kan fuskarta.
Zaro idanuwa waje suka yi ganin abinda ya faru.
Cikin huci Mami ta ce. "Idan har ki ka ƙara kiran ɗana da haihuwar asara sai na lahira ya fiki jin dad'i. Aba!, aba!, wai sai kace a kaina aka fara kishiyoyi, da har za ku bi ku addabi rayuwata, kun daɗe kuna yi min abinda ranku ya gadama a gidan nan, amma kusani cewa yanzu haƙuri na ya ƙare, da ina yin shiru ne kawai domin samun zaman lafiya amma ku naga ba hakan ku ke so ba. To ku kuji na faɗa muku na girme ku nesa ba kusa ba, duk wata shegiya da ta ƙara kawo min rainin hankali saina yi maganinta. Ke kuma Zubaida na rabu da ke ne saboda Uncle Sadiq wato mahaifinki da ba dan aka ba da saikin yaba wa aya zaƙin nata. Aba mutum yana haƙuri da ku amma saida ku ka tirje ku ka yi mai yuwa har ku ka kaishi bango".
"Maza ku fice min daga ɗakin ƴan wahala kawai".
Jikin kowannensu ne ya yi sanyi ganin a karo na farko Mami ta tsawatar musu. Simi-simi suka fita ba tare da wanin su ya ce ƙala ba.
Zama Mami ta yi a bakin kujera tana mai maida numfashi. Hawaye ne ya sauka kan fuskarta.
Duk abinda ya faru su Amrah naji yayin da Safira ta kalli Amrah ta ce. "Lallai Mami tana fuskantar kalubale, hanya ba za mu taimaka mata ba?".
Murmushi Amrah ta yi ta ce. "Hmm wai shin kin manta akwai Zahra, indai har Zahra na raye ba ta mutu ba, to tabbas ita ɗaya ta ishe su, bama sai mun taimaka mata ba, Zahra ai ita ce daidai da su".
Murmushi Safira ta yi ta ce. "Haka ne, nidai fata na shi ne Allah ya sa Zahra tana cikin ƙoshin lafiya, sannan Allah ya bawa yarima Sooraj ikon fito da ita lafiya daga wannan dajin".
Jin su Aliyu na kiran sunayensu daga waje ya sanya su suka fita daga ɗakin tare da nufar inda suke.
Da sauri suka karasa inda suke. Kallonsu Umar ya yi ya ce. "Maza ku ɗauko hujjojin yanzu zamu wuce Jigawa za'a dawo da case ɗin sannan ayi wa gov. Musa hukunci".
Kallonsa Aliyu ya yi ya ce. "Amma ai naga wannan mutumin da ka ke magana a kansa mahaifinka na, shin ba za ka ji babu dad'i ba idan aka ce maka kotu ta yi yanke masa hukuncin zaman kurkuku?".
Kallonsa Umar ya yi ido na ganin ido sannan ya ce. "Ko hukuncin rataya haka yanke masa bani da matsala da hakan".
Ya karashe maganar tare da fice wa daga cikin fadan.
Da sauri su Amrah da Aliyu suka bi bayanshi.
Junaid da ke kallon duk abinda ke faruwa ne ya yi saurin bin bayansu yayin da ya dakatar da su da faɗin. "Ku tsaya mana, ku bari mai martaba ya fito da Mami, kada ku tafi hannu a bushe babu komai".
Murmushi Umar ya yi masa sannan ya ce. "Kada ka samu damuwa bro mu wanda ku kayi mana ma ya ishe mu, kace da Mami ta yi haƙuri bamu sanar mata da zamu tafi ba, domin idan muka faɗa mata ba za ta bari mu tafi ba sai ta jiƙa mana hannu da abubuwan ci, yanzu dai ka faɗa mata cewa mun tafi".
Girgiza kai kawai Junaid ya yi.
Suna gama magana gaba ɗaya suka shiga mota tare da barin masarauta baki ɗaya.
Ganin cewa babu fetur cikin motarsu ya sanya Umar nufa gidan mai domin ya sha mai a motarsu.
********
Sooraj na isa dajin, ko ƙwaƙwarar parking bai yi ba ya fito daga cikin motan. Yayin da ya fara neman inda rijiyar take. Daga nesa ya hango rijiyar. Da sauri ya fara tafiya har yana tuntuɓe. A haka ya isa wajan daga bisani ya tsaya da tafiya.
Kallon rijiyar ya yi ba tare da ba ta lokaci ba ya faɗa cikin rijiyar. Saida ya ɗau wajan mintuna ashirin bai sauka ƙasa ba. Kafin daga bisani ya faɗi a ƙasa kan ciyawa. Jiri ne ya ɗebe shi ya faɗi a wajan sumamme.
Ɓangaren Zahra kuwa, a cikin kejin ƙarfe halittun wajan suka saka ta yayin da suka zagaye ta da sarƙoƙi.
A galaibaice take kallon munanan halittun da ke gabanta wanda babu abinda suke faman yi sai zagaye ta suna ihuu suna kururuwa. Kallonsu ta yi ta ce. "Wai me ku ke da buƙata a gare ni, ku sake ni nayi tafiya ta". Ta faɗa murya a galabaice.
Dariya halittun suka babbake da shi yayin da suka ce. "Tunda ki ka shigo kin shigo kenen, dama kafin ku shigo littafin hannun ku ya gaya muku cewa dole a cikin ku mutum ɗaya za ta mutu, to kece wannan mutum ɗayar".
Take gaban Zahra ya yanke ya faɗi, nan take ta saki wani marayan kuka.
"Dan Allah ku barni naje naga mahaifiyata
KADA KU MANTA DA LIKE, COMMENTS, AND SHARE FISABILILLAH 🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏
ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞💞
ZINARIYAR JAJIRTATTU
بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!
*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎
*BOOK 2 PAGE8️⃣3️⃣▶️8️⃣4️⃣*
*************************
Dariya halittun suka yi suna yi suna zagaye ta yayin da suka saka kacoci suka nannaɗe kejin da shi. Nan take jikin Zahra ya fara rawa.
Faɗuwa ta yi kan gwiwowinta yayin da ta rasa yadda za ta iya kuɓuta daga gare su. Ƙanƙame kanta ta yi tare da fauwala wa Allah lamuranta.
Ƙoƙarin kunna wuta suke yi a ƙarƙashin kejin da Zahra ke ciki. Take Zahra ta ƙwalalo idanuwa waje ganin abin da ke shirin faruwa.
"Wayyo dan Allah kada kuyi min irin wannan azabtarwar, idan kashe ni za ku yi ku kashe ni amma kada ku wahalar da ni kafin ku kashe ni".
Nan take ɗaya daga cikin su ya ce. "Yin hakan yana daga cikin tsarin mu, domin azabtarwar ita ce kan gaba kafin mutuwa, kema kuma irin wannan hukunci za ki fuskanta".
Take wutar ta kama. Nan take Zahra ta fasa ihuu.
****
Ɓangaren Sooraj kuwa farkawa ya yi daga cikin suman da ya yi sannan ya miƙe tare da fara tafiya. Ganin yadda dajin keda matuƙar ƙayatarwa.
Chan ya ga wani aku ya a kwance da alama yana ji ciwo. Da sauri ya inda parrot ɗin nan yake. Yayin da ya ga ya ji ciwo sosai domin ƙafarta tana ta fidda jini.
Da sauri Sooraj ya samu ya tsinki ganye tare da yanka rigarsa sannan ya saka masa a wajan ciwon nasa. Kasancewar shi ɗin likita ne hakan bai bashi wahala ba.
Ajiyan zuciya ya sauke kana daga bisani ya tashi domin cigaba da tafiya.
Babu zato ya ji an ce. "Ka zo nan ne domin neman inda masoyiyar ka take?".
Da sauri Sooraj ya juya domin ganin wane ne, da mamakin da kuwa ya ga cewar aku ne.
Tsungunna wa ya yi kusada akun sannan ya ce. "Dama kana magana?".
Girgiza masa kai akun ya yi ya ce. "Ƙwarai kuwa domin ni ɗin aljani ne, duba da yanayin yadda ka ke da tausayi ka manta da abin da ka zo nema ka ceci rayuwata hakan ya sa na ce zan taimaka maka wajan cimma abin da ka zo nema".
Murmushi Sooraj ya yi ya ce. "A'a na gode, ni na ceci rayuwarka ne kawai saboda naga kana cikin raɗaɗi ba dan wai ka saka min da wani abun ba, kada ka damu kanka domin ni ma zan iya ji da lamurana".
Girgiza kai Akun ya yi ya ce. "Kada ka ce za ka ƙi karɓar ceto daga waje na kawai ka yarda da ni, waɗan da suka zo sun kasance suna da littafin nuna hanya a wajan su ne, shi ya sa suka yi samun hanyar tafiya, kai kuma ba kada shi. Ni ne kawai zan iya taimaka maka domin samun inda wacce ka zo nema take, idan kuma kace baka so to za ka sha wahala ne kawai a nan daga ƙarshe ma kaima a ji labarin ka mutu domin kai ɗin bil adama ne kawai a wai jinsi biyu ba. Dan haka kawai ka biyo ni".
Kamar yadda Akun ya buƙata haka Sooraj ya bishi suka fara tafiya tare.
Saida suka yi tafiya mai nisan gaske kafin daga bisani suka hangi bishiyar tsamiya wanda ke ta sheƙi kamar yadda su Zahra suka hanga a lokacin da suka zo.
Tsaya wa Akun ya yi tare da kallon Sooraj sannan ya ce. "A wannan bishiyar masoyiyarka ta yanka hannunta jini ya ɗisa. Saboda wannan jini da ta ɗisa hakan ya sa aljanu suka zaɓe ta matsayin wacce suke da buƙatar ta, hakan ya sa suka rabu da sauran ƴan uwanta guda biyu sannan suka riƙe ta, ba wai don su kashe ta ba kawai su dinga azabtar da ita suna jin dad'i sannan kuma yin hakan yana sanya su farin ciki domin jininta suke da muradi ba wani abun ba".
Ajiyan zuciya Sooraj ya sauke sannan ya ce. "To mu cigaba da tafiya ko".
Kamar yadda Sooraj ya buƙata haka suka cigaba da tafiya.
Saida suka yi tafiya mai nisan gaske kafin daga bisani suka hangi kogo wacce keda girma.
Kallonsa Akun ya sake yi sannan ya dube shi ya ce. "Daidai nan wajan masoyiyar ka da ƴan uwanta suka zauna suka huta, ko kaima za ka huta ne?".
Girgiza kai Sooraj ya yi ya ce. "Ba hutu ne ya kawo ni nan ba dan haka mu cigaba da tafiya".
Cigaba da tafiya suka yi yayin da suka ƙarasa inda ƙogon yake sosai suka yi tafiya mai nisa daga nan ne Sooraj ya hangl gada mai matukar tsayin gaske.
Kallon Akun Sooraj ya yi ya ce. "Ta ya ya zan bi kan wannan gadar?, kana ganin ruwa ce a ƙasar ta kuma cike take da halittun ruwa masu cutarwa".