← Book details Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 65

Sashe 26

Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Girgiza masa kai Akun ya yi ya ce. "Ka faɗi gaskiya, domin kuwa saida Zahra ta faɗa cikin wannan ruwan kasancewar abin gadar ta fara tsinkewa hakan ya sa ta faɗa, saidai koda ta faɗa halittun ruwan basu iya yi mata komai ba kasancewar tana tattare da wata baiwa a jikinta wanda ko ƴan uwanta basua da irin wannan baiwar da take da shi".

"To ni ya za'ayi na wuce ta wannan gadar?". Sooraj ya tambayi Akun.

Girgiza masa kai Akun ya yi ya ce. "Ka zuba ido ka ga abin da zan yi". Yana kaiwa nan ya fara girgiza jikinsa. Nan take ya koma jibgegiyar Aku mai fuka fuki masu tsayi.

Da sauri Sooraj ya ja da baya ganin abin al'ajabi da ya farj yanzu a gaban shi.

Kallonsa Akun ya yi ya ce. "Kada ka tsorata kaji, maza yanzu ka au kaina, ni nan zan tsallakar da kai".

Kallonsa Sooraj ya yi ta ce. "Ta ya ya zan iya yin irin wannan sakacin na su bayanka?, idan haka samu matsala ka kasa jure nauyi na kuma ka koma ƙaramin Aku ba?, me ka ke tunanin zai faru?, abinda zai faru shi ne ni ban ceci Zahra daga dajin nan ba kuma ban ceci kaina ba, gaskiya ba zan iya awa kanka ba".

Kallonsa Akun ya yi ya ce. "Idan har baka au bayana na tsallakar da kai ba, to babu ta yadda za ka bi ta kan wannan gadar lafiya, domin kuwa dole sai ka fuskanci kalubale, kuma babu wata hanya sai wannan gadar. Ya kamata ka saurare ni ka tawo muje".

Nannauyan ajiyan zuciya Sooraj ya sauke!, lumshe idanuwansa ya yi nan take fuskar Zahra ya fara yi masa gizo. Da sauri ya buɗe idanuwansa tare da kallon Akun.

Ba tare da ransa ya so hakan ba, haka ya su bayan wannan Akun yana mai rintse idanuwansa.

Kafin giftawar ido ya ga sun tashi sama tare da fara bin ta saman wannan gadar. Nan take halittun ruwan da ke cikin ruwa suka fara yowa sama domin kai farmaki saidai ko kaɗan sun kasa cimma abin da suke da ƙudirin yi.

A haka har su Sooraj suka tsallake wannan gada.

Nan Akun ya sauke shi sannan ya koma yadda yake. Godiya Sooraj ya yi masa sannan suka cigaba da tafiya.

Saida suka kwashe mintuna ashirin suna tafiya yayin da Sooraj yake jin ƙafarsa gaba ɗaya kamar ba a jikinsa ba saboda tsananin tafiya, tunda yake bai taɓa yin tafiyar makamanciyar irin ta yau ba.

Chan suka hangi ƙofofi guda uku.

Da sauri suka ƙarasa inda ƙofofin suke. Kallon Sooraj Akun ya yi ya ce. "Wannan ƙofa ta tsakiyar ne wacce ka ke nema ta shiga, dan haka muma nan zamu shiga.

Nan take Sooraj ya zaɓi ya shiga na tsakiyar. Nan suka yi yinƙurin shiga. Nan Sooraj ya ga Akun ya kasa shiga cikin wajan. Kallon sa Akun ya yi ya ce. "To ɗan uwa ni na riga nayi maka wanda ƙarfi na zai iya, kai saika ƙarasa sauran aikin, ba zan iya bin wannan hanyar ba domin ba a bani damar yin hakan ba, dan haka ina yi maka fatan nasara".

Murmushi Sooraj ya yi ya ce. "Na gode sosai Aku zan so na sake ganinka, na gode da taimako". Yana kaiwa nan ya shiga cikin wannan ƙofar. Nan take ƙofar ta haɗe.

********
Ɓangaren su Umar kuwa bayan sun isa garin Jigawa kai tsaye gidan su Aliyu suka nufa tare da parking a ƙofar gidan.

Ƙwanƙwasa ƙofar Aliyu ya shiga yi. Nan baba mai gadi ya buɗe musu. Ganin su Aliyu ne ya sa shi yin farin ciki sannan ya ce. "La Hajiya ku zo ku ga su Aliyu ya sun dawo".

Shiga cikin gidan su Aliyu suka yi yayin da suka shiga cikin parlourn gidan. Nan suka tarar da kowa ya fito izuwa falo jin abinda mai gadi ya furta.

Fitowa Alhaji Abdullahi ya yi tare da ɗora idanuwansa kansu Safira da Amrah.

Da sauri Mom ta isa inda Safira take tare da rungume ta . Rungume ta ita ma Safira ta yi tana mai fashe wa da kuka.

Kallon Amrah suka shiga yi ganin yadda suke matuƙar kama da Safira.

Kallon Amrah Daddy ya yi ya ce. "Kenen wannan ƴar Lailah mu ce".

Kallonsa Alhaji Abdullahi ya yi ya ce. "Kana nufin waɗan nan yara na ne?". Ya faɗa murya na rawa.

Girgiza masa kai Aliyu ya yi ya ce. "Kawu waɗan nan su ne ƴaƴanka amma su uku ne ta ukun ba ta nan".

Bin Alhaji Abdullahi su Amrah suka shiga yi da idanu. Kallonsu Grandma ta yi ta ce. "Me ku ke jira muka kuje gurin mahaifin ku mana, shi ne fa mahaifinku".

Nan Amrah da Safira suka haɗa baki wajan faɗin. "Mu mahaifiyar mu muke da buƙatar gani yanzu".

Kallon su Grandpa ya yi ya ce. "Ai mahaifiyar ku har yanzu tana Kano, ba'a zo mana da ita nan ba".

Zaro idanuwa waje Aliyu ya yi ya ce. "Me ka ke nufi Grandpa, kana nufin aunty na ba ta nan?, a gaban mu da aka ce a tafi da ita izuwa garin Jigawa, kuma yanzu sai a ce ba ta nan tabbas tana nan garin".

Kallonsu Alhaji Abdullahi ya yi tare da nufar inda yaransa suke. Cikin farin ciki yake bin su Amrah da kallo ganin yadda suke matuƙar kyau ga kama nan ta mahaifiyar su ƙarara a kan fuskokin su hakan ya sa shi kara jin cewa tabbas waɗan nan babu makawa yaransa ne.

Da sauri Safira ta isa inda yake tana neman albarkar shi, ganin Safira ta yi hakan, ya sa ita ma kuma Amrah yin abin da ta yi. Kukan da yake riƙe wa ne ya subuce mishi. Da sauri ya share hawayen shi sannan ya ce. "Kada ku damu yanzu kun dawo gare mu babu wanda zai sake raba mu da ku, yanzu mu fara neman inda mahaifiyar ku take, na san ba zai wuce tana chan tsohon gidan da ta fi ƙauna ba dan haka nan zamu je".

Yana kaiwa nan suka fito daga gidan yayin da suka tada motoci tare da barin gidan. Kai tsaye inda tsohon gidan Mrs Lailah yake suka nufa.

Lokaci ƙalilan ya ɗauke su suka isa izuwa wannan gida.

Nan suka tarar da police ɗin da Dpo ya tura su a tsatsaye.

Ganin Dpo ya sa suka sara masa. Dubansu ya yi ya ce. "Where is she?".

Nan suka nuna cikin gidan. Da sauri su Alhaji Abdullahi suka isa ciki. Nan suka tarar da ita a tsugunne ta yi ruff da ciki.

Ƙarasawa inda take Alhaji Abdullahi ya yi tare da kiran sunanta a hankali. "Lailah!".

Ɗago kai ta yi da sauri ya ja da baya ganin tabbas ita ce.

"Lailah dama kina raye?".

Miƙe wa Mrs Lailah ta yi ta ce. "Eh ina raye, sai kuma aka yi yaya?, Ka zo nan ne domin tabbatar da cewa na mutu ne ko ina raye?, duk me ya kawo ku, gaba ɗaya bana da buƙatar ku a gare ni, domin a lokacin da nake da buƙatar taimakon ku baku taimaka min ba, sai kuma yanzu za ku dawo gare ni?, shin tsawon waɗan nan shekaru akwai wanda ya yi ƙoƙarin waiwaya ta a cikin ku?, ni bana da buƙatar ku?".

A daidai wannan lokaci idanuwanta ya sauka kan su Amrah. Nan kuka ya ci ƙarfin ta . Da sauri su Amrah suka nufi inda take tare da rungume ta. Ƙanƙame su a jikinta ta yi ta ce. "Tabbas waɗan nan ƴaƴa na ne, nayi muku laifin da ba zai yu na iya gyara wa ba. Duniya ta raba ni da ku tun kafin ku mallaki hankalin ku, ban san ta ina ya kamata na fara neman gafarar ku ba. Ko bari basu yi na shayar da ku ba a haka suka raba ni da ku". Ta faɗa tana mai fashe wa da matsanaciyar kuka. Kuka suma su Safira ke yi.

Da sauri Aliyu ya isa inda take sannan ya ce. "Aunty kin gane ni?, ni ne ɗan ki Aliyu".

Share hawayenta ta yi ta ce. "Aliyu kai ne ka zama haka, Allah sarki duk ban samu damar kasancewa da ku ba duk saboda wannan mijin nawan".

Murmushi Alhaji Abdullahi ya yi ya ce. "Lailah kin yi wa abin gurguwar fahimta ne, samm ni ɗin ban haɗa baki da Musa ba, kawai dai ban samu lokaci nayi miki bayani ba ne".

"Wane bayani kuma bayan komai ya riga ya faru?, ni bana da buƙatar ganin kowannne daga cikin ku in ba Aliyu da yara na ba, sai kuma mahaifiyata".

Kuka ne ya ci ƙarfin Grandpa. Nan take ya soma yin kuka cikin tsantsar dana sani da nadama.

"Dan Allah Lailah ki yafe min tabbas mutanen duniya sunyi miki mummunan tabo da ba zai yu ya gogu ba, ina neman gafara a gare ki".

Share hawayenta Mrs Lailah ta yi ta ce. "Allah ma muna masa laifi yana yafe mana balle mutum ɗan adam, ni babu wanda na riƙe a cikin ku, duk na yafe muku, ni kawai abin da nake da buƙata shi ne ku rabu da ni da yara na mu sarara".

Share hawayenta Safira ta yi ta ce. "Mama, mun riga munje wannan dajin domin ɗauko hujjoji da kuma dukiyoyi. Mun samo su saidai bamu samu dukiyar da ki ka faɗa ba, kuma kince wajan saida thumbprint ɗin ki duk bamu samu ba iya box da maƙulli muka samu".

Kallonta Mrs Lailah ta yi ta ce. "Nayi hakan ne saboda gujewa abin da zai zo ya dawo, banason a ƙara yaudara ta a karo na biyu hakan ya sa na ce akwai dukiyata a chan amma babu, dukiyata ba'a nan suke ba. Sannan ina son na tambaye ku wani abu, ina ta ukun ku take?".

Kallon juna Safira da Amrah suka yi yayin da Amrah ta ba ta amsa da cewa. "Tana cikin wannan dajin ba ta samu damar dawo wa ba, hakan na nufin za ta mutu a chan".

Nan take gaban Mrs Lailah ya yanke ya faɗi.

*********
Zahra kuwa ihuu ta fasa wanda ya sanya kejin da suka saka ta a ciki ya tarwatse yayin da jikinta ya soma ƙakkarwa.

MANAGE PAGE PLEASE
Chapter 26 · 0% Book details