← Book details Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 65

Sashe 47

Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nan Zahra ta kalli wayar ta ce. "Kamar wayar Zubaida da Sooraj ya ƙwace". Ta tambayi kanta. Basar da wayar ta yi ta cigaba da abinda ke gabanta .

Zahra ta ci gaba da aikin, amma zuciyarta ba ta yarda ta wuce wayar haka nan ba. Bata taɓa aminta da Zubaida ba. Bata manta yadda komai ya rikice tun shigowarta ba.

Kafin ta ɗauke kai, wayar ta haska.

New Message From JUNAID

Zahra ta tsaya. Sunan da ta gani ya buɗe mata wani bargo na tambaya. Hannunta ya yi sanyi. Ta janyo wayar a hankali zuciyarta na bugawa kamar an saka mata ƙaho. Nan ta ɗauki wayar ta danna.

“Zubaida, na kai iyaka. Wannan cikin da kike ɗauke da shi nawa ne, amma ba da yardata ba. Kin cuce ni, kin saka min magani, sannan kin ƙetare iyaka da jikina. Na yi shiru har yau, amma yanzu sai na faɗa miki gaskiya,
Idan baki bar rayuwata ba, zan fallasa komai. Zan tona asirin ki a gaban duniya. Ki farka daga mafarkin ƙarya, ina da ƙarfi da gaskiya, ki ƙaurace min, ki manta da sunana saboda yanzu ke matar aure ce kuma yayana ki ka aura. Wannan shi ne farkon ƙarshe. Kar ki kuskura ki ƙalubalanci fushina".

Zahra ta runtse idonta da ƙarfi, zuciyarta ya shiga buga wa da sauri. Idonta a lumshe, numfashinta ya rikice. Wannan shine sirrin da ta ke neman fahimta tun farko. Sai kawai ta dafa bango tana sauke ajiyar zuciya mai nauyi. ta maida wayar a inda ta ke kamar ba’a taɓa ta ba.

"Junaid?, ta ya ya hakan ta kasance?, dama cikin Junaid ne a jikin Zubaida, ta ya ya Sooraj zai juri hakan?, cikin ƙanninsa a jikin matarsa, wannan ba ƙaramin abu ba ne, ya zama dole na riƙe wannan sirrin". Zahra ta faɗa tare da goge message ɗin

Kamar a lokaci guda, ƙofa ta yi ƙara da sauti.

Sooraj ya shigo, yana sanye da rigar gida da after dress. Idonsa ya tsaya a kanta.

> “Zahra? Me kike yi haka kin tsaya kamar wata tsintsiya?”
“Eh... A’a. Na goge mirror ne kawai. Na ga wayar Zubaida na mayar.”
“Okay". Sooraj ya faɗa Ya ɗauki wayar ba tare da wani zargi ba, ya juyo da murmushi. Zahra ta ɗan ɗaure fuska tana ƙoƙarin daidaita numfashinta.

Sooraj ya fita, Zahra ta rufe ƙofar da hannunta, sannan ta dafe ƙirjinta. Zuciyarta tana bugawa da irin wutar da sirri ke ƙonewa da shi.

Bayan Sooraj ya fita da wayar, Zahra ta tsaya wani lokaci tana fuskantar madubi, tana kallon fuskarta da ba ta da haske. Duhu ya mamaye zuciyarta. Ta san wannan sirrin ba zata iya haɗiyewa ba.

Zuciyarta ta yanke shawarar abu daya: ta fuskanci Junaid da kanta, a gaban idonsa ta tambaye shi gaskiyar komai.

Tana jin ƙafafunta sun matse, amma zuciyarta ta ƙi juyawa. Ta ɗaura gyalen kanta, ta gyara rigarta sannan ta fita daga ɗakin Sooraj. Ba kowa a waje. Kai tsaye harabar waje ta nufa ta ga Sooraj. Alfarma ta nema tace tana son zuwa gaida Mami. Da ƙyar Sooraj ya amince inda driver ya kaita har masarautar. Nan Zahra ta sauka. Tana zuwa bakin ƙofa, ta tsaya na ɗan lokaci. Jikinta ya yi sanyi. Shiga ta yi ta tarar babu kowa a parlourn hakan ya sa ta nufi hanyar ɗakin Junaid Kai tsaye. Daidai lokacin suma su gimbiya Saratu suka ganta hakan ya sa suka bi bayanta.

Tana zuwa ga yi knocking. Junaid da ke kwance kan gado ya ji ana knocking hakan ya sa ya ce a shigo. Na ta shiga cikin.
Idon Junaid ya cika da mamakin ganin Zahra a wannan lokaci

“Me ya faru?”. Ya tambaye ta.
Kallonsa Zahra ta yi ta ce.
“Na karanta saƙonka. A wayar Zubaida. Ka ce cikin da take da shi naka ne... amma ba da yardarka ba. Ka ce ta cuce ka. Kuma kai da bakinka ka ce zaka tona asiri idan bata bar ka ba. Da gaske kake?. Wato duk ka shirya mata hakan ne saboda ta auri yayanka, kai wane irin mugun mutum ne haka?".

Junaid ya tsaya cak. Idonsa ya sauka ƙasa. Zahra ta matso.

"Junaid, ka faɗa min gaskiya. Kai ne mahaifin cikin nan?”

Shiru ya cika ɗakin. Sai daga bisani Junaid ya ja numfashi ya ce. "Eh. Na san ba zan iya ɓoyewa ba, na san zaki gano. Ina ƙoƙarin kare sunana ne, kare kai na daga abin da ban aikata da nufina ba”

Girgiza kai Zahra ta yi ta ce. "Ban yarda da kai ba Junaid, tabbas kai ne ka tirsasa mata, ta ya ya za'a ce mace ce zata sa namiji ya kusance ta ba tare da izinin sa ba, kasan ba abu ba ne mai yiwuwa".
“Zahra,” ya katse ta, “Na shiga firgici. A daren nan ta zo, ta kawo min juice, sai barci. Na farka da jiki ba kaya, zuciyata a bige, da ita tana kuka tana cewa wai nayi mata fyaɗe, na ƙeta mata haddi duk da bana cikin hayyaci na amma ban yarda zan aikata hakan ba".

Zahra ta tsaya tsaye a gaban Junaid, zuciyarta na ambaliya da hargowa. Tana jin kamar duniya na juyawa a kansa. Bayan ya gama bayani, ta girgiza kai da takaici.

"Kai kake cewa ba ka aikata ba, amma cikin ya fito daga kai? Haba Junaid, wannan wace irin magana ce? Ashe ka iya ƙarya da sauƙi haka?”.

Junaid ya kalleta cikin razana. “Zahra, me kike nufi? Ni ba ƙarya nake miki ba".

“Shut up!” Ta ɗaka masa tsawa. “Kayi shiru! Zubaida ba irin wannan yarinya bace da zata aikata abinda kake faɗa. Ka san cewa Sooraj ya amince da kai, kuma yanzu kana son tonawa yarinyar mutane asiri da ƙarya?”.

Junaid ya ce “Amma..... Bai ƙarasa ba ya ji ta ce. “Enough!” Idonta ya kaɗa ja. “Na san irin ku. Idan mace ta fara samun kulawa, sai ku so ku ruɗata da munafunci. In dai haka ne, to ina gaya maka bazan yarda da wannan karyar taka ba. Zubaida bata aikata hakan ba".

“Zahra kina tunanin zan ƙirƙiri wannan azabar?”. Cewar Junaid

Nan Zahra ta ce. "Na fi yarda da Zubaida akan kai!”

Shiru ya ɗauki dakin, sai ga wani motsi. sai ta ji kamar motsi. Zahra ta kalli can, bata lura da komai ba. Sai dai duk wannan maganar Talatu da Saratu suna maƙale a bakin taga suna saurarawa kamar katuwar masifa.

Saratu da Talatu, waɗanda suka ɓuya a bayyane, suka kalli juna da murmushin ɓarna. Sun jiyo komai. Talatu ta ce,

“Kinyi sauraron kalmomin Zahra kuwa? Wannan dama ce, kawai sai mu saka wuta a ƙasa, ita ta ƙone.”
Gimbiya Saratu ta raɗa wa Talatu cewa. “Ai yau masarauta zata ga hazo,” cewar Saratu tana gyara gyale".

Suka fito da sauri suna kuka da ihu kamar masu alhini. sun fito cikin sauri suna haki kamar wanda aka kai wa farmaki

"Kuje ku ji! Zahra da Junaid suna cikin ɗaki, suna jayayya akan cikin da Zahra take da shi! Ai wallahi mun jiyo da kunnuwanmu.”

Mutane suka tsaya cak. Mami ta ce. “Cikin wa kika ce?”
Saratu ta girgiza kai cikin munafurci ta ce

“Cikin Junaid fa, yanzu fa suka kammala faɗa akan cewa wai Zahra ta zubar da ciki ne saboda yana tsoron abun ya tonu.”.

Gimbiya Talatu ta daura hannu a kirji.
"Wai ita ce mai ladabi? Ashe 'yar iska ce!”.
Ɗaya daga cikin masu aikin masarauta ya gaggauta aika sako zuwa gidan su Sooraj
“Yarima Sooraj! Gimbiya! Ku zo masarauta da gaggawa, matsala ce babba!, Gimbiya Zahra tana cikin zargi mai tsanani, wai tana da ciki daga Junaid!”

Sooraj ya mike da hanzari, jini ya hau kansa.

"What nonsense are you talking about?!” ya faɗa rai ɓace.
Zubaida ta tsaya cak, jikinta ya ɗau zafi.
"Me kake nufi?!”

“Ana cewa tana ciki… kuma fa sun ce da kunnensu suka ji tana faɗa da Junaid.”
Sooraj ya farka gaba ɗaya daga duk wani soyayya da sauƙi da ke jikinsa. Ya sanya babban rigarsa cikin hanzari, Zubaida ma ta ɗaura gyale da takalmi. Dukkan su suka kama hanyar komawa masarauta cikin gudu.

Masu masarauta sun rufe Zahra a ɗakin bak'i. Ana jiran zuwan Sooraj da Zubaida. Gaba ɗaya gari ya fara cika da zancen "cikin Zahra da Junaid". Amma ashe babu gaskiya ko kaɗan, sharri ne kawai, daga ƙiyayya da haushin soyayyar Sooraj da Zahra.

Zahra tana zaune ciki, ta rasa yadda aka yi aka jefa ta cikin sharrin da bata zato ba. Har yanzu bata san su Talatu da Saratu suka sa aka jefa ta a cikin wannan ƙazamar makircin ba.

Su Zubaida da Sooraj suka iso cikin hanzari. Su biyu suka tarar da taron mutane a cikin masarauta. Duk inda suka wuce ana kallon su, ana raɗa.

Sooraj ya daka tsawa “Waye ya ƙirƙiro wannan sharri?”.

Talatu ta matsa gaba da kwaɓaƙƙen fuska.

“Ka tambayi masoyiyarka Sooraj. Zahra ce ke da ciki, kuma ciki na Junaid ne!”

Zubaida ta tsaya cak.

“What?!”

Junaid ya fito daga cikin ƙofar ɗakin baki, yana tsaye a nesa. Fuskar sa babu walwala.

Zahra na kwance a ƙasa, tana kuka tana ƙoƙarin yin bayani amma babu wanda ke saurara.

Wani maigadi ya nufi Zahra da niyyar ja ta a jiki su fitar da ita daga masarauta, kamar matacciya. Amma kafin ya taɓa ta.

Sooraj ya tsayar da shi. “Ba wanda zai fitar da kowa ba sai an ji gaskiya!”
Ya juya ya kalli Zahra, da mamaki da tambaya a fuskarsa,

“Zahra me ke faruwa?”.

Zahra ta kalle shi da hawaye:

“Wallahi Sooraj, ni babu ciki. Karya suke. Su Talatu ne suka jefa ni cikin wannan sharri. Su suka jiyo ni ina faɗa da Junaid ne akan wani zargi da ya yi wa Zubaida, amma sai suka canza maganar gaba ɗaya!”.

Zubaida ta juya da sauri ta kalli Zahra, zuciyarta na bugu da sauri.

"Me ya ce game da ni?”. Ta tambayi Zahra

Zahra ta kalle ta cikin zuciya mai rauni tana so ta kareta amma shine sai Sooraj ya kalli Junaid kai tsaye.
"Junaid me kake ɓoye wa? Gaskiya kawai muke buƙata.”
Junaid ya ɗan juya kansa gefe, kafin ya zaro wayarsa ya mika wa Sooraj.
Chapter 47 · 0% Book details