← Book details Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 65

Sashe 61

Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sanyi ne ya ratsa jikinta, ta rintse idanunta tana jin jikinta na rawa. A hankali ta ce. "Yanzu me ka ke son nayi?".

Nan Sooraj ya ce. "Zan fita yanzu ɗaki na zuwa bayan sallar i'sha zan zo. Ina son ka kasance a shirye". Ya faɗa tare da fita daga ɗakin. Baki sake Zahra ta bishi da kallo.

Ɓangaren Umar

A can gidan Umar, bayan dawowarsu daga Kano, ya ajiye Amrah a gida, ya je gidan su Miss Lailah suka gaisa yayin da yake ganin Miss Lailah tamkar mahaifiyar sa. Bayan sun gaisa ya dawo gida, ya shiga falonsa inda Amrah ta tarbe shi da murmushi. Hannunta na kan cikinta tana taɓa shi.

“Yahya Umar, yau zuciyata cike take da farin ciki. Tun da naji ina da juna biyu sai naji kamar sabon rayuwa na samu.”

Umar ya riƙo hannunta ya ce. “Wallahi Amrah, wannan ne farin cikin da na daɗe ina nema. In sha Allah zamu yi duk mai yiwuwa mu reni wannan cikin, cikin soyayya har ki haife shi.”

Sai suka zauna tare suna tattaunawa kan yadda za su tsara rayuwar gaba, Umar na koya mata darasi na addini kamar yadda ya saba, hakan na ƙara ƙarfafa soyayyarsu. Yayin da suke ƙara jin ƙaunar junansu.

_________________
Ɓangaren Zubaida

Bayan an mata bulalai kamar yadda Sarki ya umarta suka cinciɓe ta suka kaita gida.

Gidan su Zubaida ya rikiɗe tamkar gidan makoki. Tana kulle a ɗaki, idanunta sun kumbura, fuskarta ta rame saboda kuka da nadama.

Tana tuna bulalar da aka yi mata ɗari, kowane duka kamar ana zane mata zuciya ne. Sai kuma yadda haka korota gida aka ajiye ta tamkar kaya da aka ƙi sayarwa.

Tana kuka tana ta ce.
“Da na san haka zai faru, da ban taɓa shiga rayuwar Junaid ba. Ashe sharrin da na ɗora kan wani zai dawo ya cinna min wuta. Yanzu ina zan saka kaina? ni wace ce a idon jama’a?, da wane ido zan kalli Babana?, tabbas na aikata babban kuskure".

Nan kukan ta ya ƙara tsananta, hawayenta na sauka kamar ruwan sama, zuciyarta na karyewa da nadama.

Ɓangaren Su Sooraj

Da dare ya rufe gari, Sooraj ya shigo ɗakin zahra Zuciyarsa cike da murna da kuma jin nauyin alhakin aure. Yayin da Zahra ta kasance cikin rigar bacci zuciyar ta sai dukan uku-uku take.

Bayan shigar sa ɗakin
ya tsaya cak yana duban ta da ido. “Zahra, yau darenmu ne na farko a matsayin miji da mata. Amma kafin wani abu, mu fara da abin da zai sa albarka ta sauka a cikin mu.”

Zahra ta sunkuyar da kai, kunya na lulluɓe da ita. Nan murmushi ya bayyana kan fuskarta. Ta ce cikin siririyar murya. "Tom".

Nan suka yi alwala tare. Aka jera sallar nafila raka’a biyu cikin nutsuwa, kowannensu yana mai neman albarka daga Allah.

Bayan sun idar, Sooraj ya daga hannuwansa da tsoron Allah a zuciyarsa ya yi addu’a.

“Ya Allah, ka albarkaci zaman mu, ka cusa soyayya da fahimta a tsakanina da Zahra. Ka ba mu zuriyar da za ta zama masu biyayya a gare ka da kuma mu. Ka tsare mu daga sharrin zuciya da fitinar duniya. Ya Allah, Ka sa wannan dare ya kasance farkon sabuwar rayuwa mai tsafta da albarka a gare mu.”

Zahra ta share ƙwallah da ya cika idonta, taji zuciyarta ta yi sanyi.

Sooraj ya ɗan rungume hannunta cikin natsuwa, yana murmushi mai cike da shauƙi da alhini.
“Zahra, daga yau, ni ba kawai mijinki ba ne, ni abokin tafiyarki ne har zuwa Lahira. Zan nuna miki soyayya a bisa tsari, ba kawai don zuciya ta ba, sai don Allah.”

Nan ya kama kanta yayi addu'ar saduwa da iyali. Sannan suka kwanta.

Washe Gari.

Da asuba ta farka da wani irin zafi da ciwo, jikinta tamkar an watsa mata wuta. Sai hawaye suka soma sauka a hankali yayin da take zaune cikin ruwan zafi, tana jin zafin wankan yana huda ta.

A gefe guda kuma Sooraj yana tsaye yana kallonta da wani irin murmushi mai cike da natsuwa. Zuciyarsa cike da farin ciki, ya ji tamkar ya mallaki duniya gaba ɗaya. Wannan farin cikin kuwa ya samo asali ne daga tabbacin da ya samu na Zahra budurwa ce, wanda hakan ya ƙara masa ƙwarin gwiwa da alfahari yayin da ya shiga saka mata albarka.

Bayan ta fito daga cikin ruwan, suka yi wanka tare cikin nishaɗi.

Nan ya ɗauko turaren wuta. Ya kusanto da kyau, ya ɗaga turaren wuta ya ƙyasta, turaren na tashi sama yana gauraya da ƙamshin Zahra. Sai ya rufe mata bayanta da tawul, yana gasata a hankali cikin nutsuwa da kulawa. Murmushin Zahra da lumshe idanunta ya ƙara masa daɗi fiye da komai.

Sooraj ya shiga kitchen ɗin gidan da kansa ya dafa musu karin kumallo. Ya kawo mata farantin soyayyen kwai da burodi, sannan ya zuba mata shayi mai zafi a cikin kofi. Yana mika mata yana kallon yadda take ɗaga kofin a hankali tana sha, zuciyarsa ta cika da farin ciki fiye da kowane lokaci.

Zahra kuwa ta ji kamar wannan rana ta zama farkon sabon rayuwa gareta, rayuwar da kulawa, ƙaunar Sooraj ya mamaye zuciyarta.

Rayuwarsu ta fara shiga sabon babi na farin ciki da soyayya mai ƙamshi, wadda kowanne dariya, kallo ko taɓawa ke ƙara musu daɗin rayuwa.

Bayan kwanaki sun shuɗe cikin annashuwa da soyayya, Zahra ta soma jin wani canji a jikinta. Sau da dama sai ta ji amai ya taso mata, ko da ta ci abu kaɗan sai ta kasa riƙewa. Wannan ya sanya Sooraj cikin damuwa amma bai nuna ba, sai ya ɗauki alhakin kula wa da ita.

Ranar Lahadi da safe, yayin da take ta amai, sai ya kalleta cikin damuwa, ya ce.

“Zahra, ki bari in duba ki. Ni likita ne, kuma bana so ki wahala kina ɓoye min.”

Ya ja hannunta cikin tausayi, suka zauna a ɗaki. Da kulawa da kwarewa ya bincika ta, zuciyarsa na buga wa da sauri. Bayan ƴan mintuna, ya ɗago yana murmushi, idonsa cike da farin ciki.

“Zahra jikin ki ba ciwo bane. Alhamdulillah kina da juna biyu.”

Zahra ta tsaya cak kamar ba ta fahimta ba. Idonta ya cika da hawaye, ta rufe bakinta da tafin hannu, tana girgiza kai cikin kaduwa ta ce.

“Ni... ni zan zama uwa?”.

Sooraj ya kama hannunta ya ɗora a kirjin sa, yana jin bugun zuciyarta sannan yace. “Eh, masoyiyata zamu zama iyaye! Wannan shi ne kyautar da Allah ya ba mu, alamar ƙaunarmu ta tabbata.”

Hawayen farin ciki suka gangaro daga idanun Zahra, ta zuba kanta a kafaɗarsa. Shi kuwa yana jin kamar ya mallaki duniyar gaba ɗaya, farin ciki ya lullube shi har ba shi da kalmomin da za su iya bayyana wannan ni’ima.

Bayan tabbatar da juna biyu na Zahra, rayuwarsu ta shiga sabon babi na annashuwa da shiri. Kowacce rana suna tattaunawa game da sunan jaririn, kayan da za su saya, da kuma yadda za su kula da shi cikin soyayya da ladabi. Yayin da Zahra ke cewa mace take so shi kuma ya ce namiji yake so.

Kwanaki sun shuɗe, ciki na Zahra yana girma, amma hakan bai rage murna da farin ciki ba. Kowace safiya, Sooraj zai tashi da wuri, ya shirya mata kayan sanyi, ya kawo mata shayi mai ɗumi, sannan ya zauna kusa da ita yana kallon yadda take jin daɗi ko zafi.

Bayan wasu watanni, labari mai daɗi ya iso ga Sooraj da Zahra. Safira ta haihu, kuma ta samu ƴa mace. Wannan labari ya cika gidan su da farin ciki mara misaltuwa. Sooraj da Zahra ba za su iya boye murnar da ke cikin zukatansu ba, idanuwansu sun cika da annashuwa yayin da suke yiwa Allah godiya.

Nan suka fara shirye-shiryen zuwa yayin da Aliyu baki har kunne saboda murna. Nan Sooraj ya sanar wa Mami. Nan Mami ta kama hanyar zuwa jigawa cikin farin ciki.

Murna wajan wannan ahalin abin sai wanda ya gani. Yayin da Zahra ta ɗebi wasu daga kayanta ta ce kwanaki zata yi. Nan suka je Jigawa inda Safira ta yi farin cikin ganinsu.

Nan Mami ta sa haka yi mata wankan jego haka turara ta da magunguna.

Ranar suna kuwa haka saka wa yarinyar sunan Grandma wato Amina inda ake ce mata Meenal. Bayan suna Safira ta koma gidan su Miss Lailah domin yin arba'in ɗin ta.

Ana tsaka da wannan shagalin haka ƙara jin cewa Amrah ta haihu. Wayyo zo ka ga farin ciki wajan wannan ahalin.

Su Mami suka tafi gidan Amrah domin taya ta murna. An yi mata wankan jego, an tsaftace jaririya mace da kyakkyawan turare, sannan aka sanya mata suna mai daraja Khadijah, wato sunan mahaifiyar Umar. Yayin da Umar da Amrah suka kasance cikin annashuwa.

A wannan rana, Ramlah da Khairiya sun nemi a basu hutu daga makaranta domin murnar haihuwar matar yayan su. Dukan gida ya cika da murna, farin ciki wajan wannan ahalin ba'a cewa komai.

Bayan an gama suna suka wuce gidan Mom da Amrah domin yin arba’in. A can, ana yi wa Amrah gyara da wankan jego tare da Safira, suna ɗaukar lokacinsu cikin annashuwa da ƙauna. Sooraj da Zahra suna kallon wannan al’amari cikin murna, suna jin cewa albarka da soyayya sun mamaye gidan gaba ɗaya.

Sai dai, bayan abubuwan sun lafa, Zahra ta yi shawara. Zata zauna wajan Mamanta na kwanaki. Ba yadda Sooraj ya iya haka ya haƙura ya dawo Kano yayin da ya kasance cikin kewar Zahra.

Yayin da gefe guda take samun kulawa daga gurin Miss Lailah.

DAN ALLAH KUYI LIKE, COMMENTS, AND SHARE FISABILILLAH. SABODA ALLAH PLEASE🥹 🙏🙏🙏🙏🙏🙏

ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞
ZINARIYAR JAJIRTATTU

*🔥KUNDIN CINIKAYYA*
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*BOOK 2 PAGE2️⃣0️⃣*

*LAST PAGE*
________________________
Bayan kwanaki Zahra ta zauna wajen Mrs Lailah, Sooraj ya kasa zama. Ko a aiki ba ya samun nutsuwa, zuciyarsa kullum na kewar matarsa.

Ranar Asabar ya zauna a falonsa yana ta tunani, ya ɗauki waya ya kira Zahra amma bata ɗauka ba. Sai zuciyarsa ta ƙara masa zafi.

A hankali ya ce da kansa
"Ba zan iya jurewa ba, dole na dawo da ita gida."
Chapter 61 · 0% Book details