← Book details Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 65

Sashe 17

Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Abdullahi dama kana raye tsawon waɗan nan shekaru?, ina ka shiga ka ɓoye?".

Su Mom da Daddy kuwa mamaki kawai suke domin kuwa ko a mafarki basu yi tsanmanin ganin Abdullahi a wannan lokacin ba.

Daidai lokacin Grandpa ya fito daga cikin gidan. Nan take idanunsa suka sauka kan Mk.

Rai a ɓace ya ƙaraso wajan cikin wheel chair da yake zaune sannan ya ce. "Me ya dawo da kai?, bana ce la tafi bana son sake ganin ka ba?, bayan tozarcin da matar ka ta jawo mana kai kuma yanzu ka dawo ne domin ka yi mana dariya ko kuma la dawo ne domin ƙara kunyatar da mu bayan wanda kai da matar ka ku ka yi mana a baya".

Girgiza kai Alhaji Abdullahi ya yi ya ce. "Dan Allah Abba ka saurari abin da zan faɗa maka".

Dakatar da shi Grandpa ta yi da cewar. "Bana da bukatar jin komai daga bakin ka. Yanzu abin da nake so da kai shi ne ka ja mutanen nan daka ɗauko ku fice min daga gida kafin na ɗauki mataki a kanku".

Kallonsa Grandma ta yi ta ce. "Mai gida tunda ya ce ka tsaya ka saurare shi ya kamata kayi hakan, domin bamu san abin da yake son faɗa ba".

"Yi min shiru ko na saɓa miki albarka, ina ruwan ki da abin da yake son furtawa?, ni nake da iko a kan kowa a gidan nan kuma ina da ikon yanke duk abin da na gadama dan aka ku fice min daga gida, idan kuma kema binsu za ki yi to ƙofa a buɗe take za ki iya fice min daga gida".

Sakin baki kawai Grandma ta yi tana kallonsa.

A fusa ce Alhaji Abdullahi ya ce. "Ka tsaya ka saurare ni ƴarka Lailah tana nan a raye ba ta mutu ba".

Nan take gurin ya yi tsit yayin da gaban kowannensu ya yanke ya faɗi!.

"Ƙwarai da gaske ƴarka Lailah tana nan raye". Alhaji Abdullahi ya faɗa a karo na biyu.

Tari Grandpa ya soma yi. Nan take hawaye ya fara bin kan ƙuncin Grandma.

**************
"Mu kamm sai yaushe ne za mu kai inda muke son zuwa ne?". Cewar Safira.

Zahra da gaba ki ɗaya ta gaji da tafiyar yayin da gefe ɗaya kuma tsoro fal ya cika zuciyarta ta ce.

"Yanzu ta ya ya ne za mu san inda dukiyar mahaifiyar ta mu suke?, dajin nan yana da matuƙar hatsarin gaske, tunda muka shigo muke ta harba da sababbin abubuwa masu ban al'ajabi. Ni fa ban shirya mutuwa ba, kawai ku tawo mu tafi, tunda yanzu mun gane cewar mu ƴan uku ne bamua da buƙatar wata dukiya, domin idan muka ce zamu cigaba da nufar cikin wannan dajin ba lallai mu dawo da rai ba. Ni dai gaskiya koma wa zan yi". Ta faɗa tana mai wurgi da kundin littafin da ke hannunta.

Binta da kallo su Safira suka yi sannan Amrah ta ce. "Kin manta abinda ki ka furta kafin mu shigo cikin wannan dajin?, kince za ki iya yin komai a kan mahaifiyar ki. In kin manta bara na tuna miki. Da bakin ki kika ce, bamu san tsananin ƙaunar da ki ke wa mahaifiyar mu ba, duk da cewar baki taɓa sanya ta a cikin idanunki ba, amma kina matuƙar ƙaunarta, to a kan me ya ba za ki iya cetan ta ba bayan ita ce wacce ta tsugunna ta haife ki, idan har za mu iya juyawa mu tafi saboda an ce ɗaya daga cikin mu zai mutu, to tabbas mu ɗin ƴaƴan bogi ne ba na gaskiya ba. Yanzu kin tuna?, kenen idan ki ka juya ki ka tafi hakan na nufin ke ba ƴarta ba ce".

Sauke ajiyan zuciya Zahra ta yi! ta ce . "Shi ke nen naji mu cigaba da tafiya". Ta faɗa tana mai ɗaukar littafin da ta wurgar.

Nan take suka fara jiyo ƙara daga jikin bishiyoyin cikin dajin. Wannan ƙarar tana cigaba da ƙaruwa, kamar wata dabba mai girma tana neman farauta.

Kallon su Amrah ta yi ta ce. "Wannan ƙarar yana nufin cewa zamu fuskanci wani haɗari a nan gaba. Maza kuyi sauri mu cigaba da tafiya.

Saida suka yi nisa a tafiyar su sannan gaba ki ɗaya suka tsaya chak sakamakon harba da suka yi da hanya wacce ta kasu gida uku.

Kallon su Zahra ta yi ta ce. " wannan hanyoyin wanne zamu bi a ciki?".

Kallonta Safira ta yi ta ce. "Ki duba cikin littafin hannunki.

Da sauri Zahra ta duba cikin littafin nan ta tarar an rubuta cewa. "Ku ukun za ku rabu izuwa hanyoyi uku ne, kowaccen ku za ta shiga hanyar ta da ban. Yanzu kun kai lokacin da hanya za ta raba ku, a cikin wannan hanyoyin idan ku ka shiga to ɗaya daga cikin ku ba za ta samu damar dawo wa ba, kuma a cikin wannan hanyoyi guda uku ne za ku ɗaya za ta samu hujjoji, yayin da ita kuma ɗaya za ta samu dukiyoyi, ita kuma ta ɗayar cikin naku za ta mutu".

Nan take cikin kowannensu ya ɗuri ruwa.

Da sauri Zahra ta buɗe shafin gaba domin ganin mene ne abin da za su na gaba. Da mamakin ta ta ga babu komai a page na gaba.

Nan take gabanta ya yanke ya faɗi!.

"Yanzu shi ke nen ta mu ta ƙare". Cewar Zahra.

Kallon su Safira ta yi hankali tashe ta ce. "Ni dama na san wannan littafintarko aka haɗa mana da shi, yanzu kenen mu ukun rabuwa za mu yi kowa ta kama hanyar ta da ban. Kuma idan ma wani abin cutarwa ne yake ƙoƙarin cutar da kai saidai kai kaɗai ka kare kanka ba tare da an taimaka maka ba, ni fa gaskiya tsoro nake ji maybe ma ni ce wacce zan shiga kuma ba zan ƙara fitowa ba".

Kallon Zahra Amrah ta yi ta ce. "Idan har rabuwa za mu yi kowa ya shiga hanyarsa da ban hakan yana nufin cewa dole wani abu sai ya sami ɗaya daga cikin mu kuma dole ne mutum da kansa ya kare kansa".

Girgiza kai Zahra ta yi ta ce. "Yanzu bamu da wani zaɓi dole kowaccen mu ta kama gabanta, a cikin waɗan nan hanyoyi ukun dole akwai na mutuwa a ciki dan aka in dai har muna son mu cika burin mu ya zama dole mu daure mu ta fi".

Ƙwallah Safira ta fara yi da sauri ta share sannan ta ce. "Shi ke nen yanzu babu wanda ya san wanda zai mutu a cikin mu, gashi ban yi su Grandma da su Mom ganin ƙarshe ba zan mutu ba tare da na gansu ba". Ta faɗa tana mai share hawayenta.

Kallonta Zahra ta yi ta ce. "Ki kwantar da hankalin ki, mutuwa gaskiya ce in dai har lokacin ka ya yi dole ka mutu in dan kuwa lokacin ka bai yi ba babu wanda ya isa ya ce zai kashe ka kuma ka mutu wannan rubuttaciya ce".

"Shi ke nen yanzu kawai kowa ya zaɓi hanyar da zai shiga kuma ya shiga". Cewar Safira

Nan Amrah ta zaɓi hanya wacce ta kasance a hannun dama, yayin da ita kuma Safira ta zaɓi hanyar da ta kasance ta hannun hagu.

Ita kuma Zahra ta zaɓi hanya ta tsakiya. Suna gama wa kowaccen su ta shiga cikin hanyar da ta zaɓa. Nan take hanyar ta rufe tare da ɓace wa kamar ba ta taɓa wanzuwa a wajan ba.

KADA KU MANTA DA LIKE, COMMENTS, AND SHARE FISABILILLAH 🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏

ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞💞
ZINARIYAR JAJIRTATTU

بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎

*BOOK 2*
PAGE 7️⃣7️⃣▶️7️⃣8️⃣

_________________________
"Ta ya ya hakan za ta kasance?, an tabbatar mana da cewa wai bindiga ya sami zuciyarta garin ya ya ta rayu?". Cewar Grandpa.

Ajiyan zuciya Alhaji Abdullahi ya sauke!, kana ya ce. "Allah ne ya dubi zuciyarta ta aiko mata da mutanen ƙwarai suka ceci rayuwarta, na faɗa maka cewa Lailah ba ta da laifi a kan abin da ake zargin ta da shi".

"Idan babu damuwa ku shigo daga ciki idan ya so sai ku faɗa mana me cece asalin gaskiya". Cewar Mom.

Kamar yadda Mom ta faɗa aka su Alhaji Abdullahi suka shiga ciki yayin da suka samu guri suka zauna.

******
Nurse Nadiya ce kwance duk ta birkice saboda farin ciki dalilin hakan kuwa shi ne ta ji labarin cewar har kawo izuwa wannan lokaci Lailah tana raye ba ta mutu ba.

"Allah sarki Lailah mutuniyar kirki ashe da rabon zamu sake haɗuwa da ke. Kin taimakawa rayuwata da ba dan ke ba da har yanzu ina tare da mijina yana gasa min aya a hannu, amma dalilin ɗaya daga cikin ƴarki ya sa ya sake ni".

Jin ana kiran sallah magrib hakan ya sa ta mike wa tsaye sannan ta nufi toilet.

******
Tun daga abin da ya faru har izuwa ƙarshen abin da ya sani Alhaji Abdullahi ya faɗa yayin da shima Mk ya ɗora daga inda Alhaji Abdullahi ya tsaya sannan ya kai har ƙarshe.

Nan take gaba ɗaya gidan ya ɗauki shiru yayin da jikin kowa ya yi sanyi.

Cike da dana sani da nadama Grandpa ya ce. "Tabbas na aikata babban kuskuren da zai yi wuya Lailah ta iya yafe min".

"Ashe duk abin da aka faɗa a kan ƴata ƙarya ne. Na zalunce ta da zargi, da shakku, da yanke hukunci kafin bincike. A matsayina na uba, na kasa zama garkuwa, sai na zamo silar raɗaɗinta. Yanzu na fahimci cewa faɗan da na yi ba ya nuna ƙauna, illa ciwo. Kalamaina sun jikkata zuciya mai laushi wadda ke buƙatar fahimta, ba fushi ba. Idan uwa ta fi daɗin nuna ƙauna, to uba ya kamata ya fi daɗin fahimta. Amma ni na zamo dutsen da ya ana ruwa gudu. Na kasa tsayawa a matsayina na uba."

"Ban cancanci a kira ni uba ba idan zuciyata ba ta da haƙuri, idan kunnuwana sun ƙi sauraro, idan bakina ya fi saurin zargi fiye da karɓar uzuri."
Chapter 17 · 0% Book details