← Book details Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 65

Sashe 15

Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallonsu Safira ta yi ta ce. "Ta ya ya zamu wuce yanzu?".

Amsa Zahra ta bata da cewa. "Ta kan wannan gadar zamu wuce".

Kallonta Safira ta yi ta ce. "To idan by mistake wani a cikin mu ya zame fa ya faɗa cikin ruwan da ke ƙasar gadar fa?, kin san duk wanda ya faɗa mutuwa zai yi fa".

Murmushi Zahra ta yi ta ce. "Da ki ka san ba za ki iya ba me ya sa ki ka biyo mu?, a cikin littafin nan abun da aka rubuta a ciki shi ne dole sai mu bi ta kan wannan gadar idan baki shirya mutuwa ba to ki juya ki koma inda kika fito bamua da buƙatar ragwaye a tafiyar mu". Ta ƙarashe maganar tana mai yin gaba ta fara bin kan gadar.

Ran Safira idan ya kai dubu to ya ɓaci!, cikin ɓacin rai ta soma tafiya yayin da ta fara tunanin yadda zata koya wa Zahra hankali.

Kallonta kawai Amrah keyi domin ta gama karantar abinda ta faɗa a zuciyarta.

Tafiya mai nisa suka yi kan gadar. Babu zato suka ji gadar ta fara girgiza. Nan take hankalin kowanensu ya tashi!.

Nan take halittun ruwan suka fara yowa sama Kasancewar sunji kamshin mutane.

Danne tsoron ta Zahra ta yi yayin da ta cigaba da karanta littafin. Nan take suka fara jiyo muryoyi masu matuƙar ban tsoro.

Cikin rashin sa'a Safira ta zame yayin da ta kusan faɗa wa ƙasa cikin ruwa. "Wayyo Allah ku ce ce ni zan faɗa". Ta faɗa tsoro cikin tsananin tsoro. Ganin hakan ya sa Zahra ta yi saurin nufar inda take tare da kamo hannayenta. Ajiye littafin hannunta ta yi tare da fara ƙoƙarin janyo Safira. Sa hannu Amrah ta yi. Cikin sa'a suka janyo ta kan gadar.

Ajiyan zuciya dukansu suka sauke!. Kallonta Zahra ta yi cikin fusata ta ce. "Ke ba za ki iya kula da kanki ba?, kin san koda mutum ɗaya wani abu ya same shi mahaifiyar ba zata jura ba, ya kamata ki kula. Aikin banza kawai ta inda bana kusa da ku da tuni kin faɗa".

Ta faɗa tana mai cigaba da tafiya. Sosai Safira ta yi farin ciki game da abin da Zahra ta yi.

A karo na biyu suka kara jin sautin da suka ji ɗazu. Tsayawa chak kowanensu ya yi kan gadar. Kallonsu Amrah ta yi sannan ta ce. "Ina da shawara ɗaya daya kamata muyi".

"Me ce ce?". Zahra ta tambaya.

Kallon Safira Amrah ta yi ta ce. "Kinga ke kina da baiwar matsar abu daga guri ɗaya zuwa wani wajan, ni kuma inada baiwar tsalle-tsalle, gudu da kuma karantar zuciya. Dan aka abinda ya kamata muyi shi ne ni zan ɗauke ki a baya na sannan nayi gudu da ke mu tsallaka mu wuce kan wannan gadar. Sai kuma ki tura ni da baiwar ki na zo wajan Zahra sannan muyi gudu saiki ɗaga mu baki ɗaya ki tsallakar da mu ta hakan ne kawai zamu yi sauri, domin naga idan zamu cigaba da tafiya kan wannan gadar, sai mun wuni muna tafiya kan wannan gadar domin tana da tsayi sosai".

Girgiza kai Safira ta yi ta ce. Wannan shawara ce mai kyau dan aka maza muyi hakan ko".

Girgiza kai Zahra ta yi ta ce. "Ni gaskiya shawarar nan ba ta yi min ba, yanzu idan ku ka tafi ni kuma idan wani abu ya same ni fa?".

"Babu abun da zai same ki kinji". Cewar Safira.

Kamar yadda suka tsara aka Amrah ta ɗauki Safira sannan ta karɓi littafin hannun Zahra. Sannan ta fara gudu da Safira kan wannan gadar sai da ta yi gudu mai nisan gaske kafin daga bisani suka kai ƙarshen gadar.

Saukar da Safira ƙasa Amrah ta yi. Cikin rashin sa'a suka ga gadar ta fara wargaje wa yayin da itatuwan suka fara ciccirewa.

Nan take gaban su ya faɗi! ɓangaren Zahra kuwa gaba ki ɗaya ya ruɗe yayin da hankalin ta ya yi matuƙar tashi!.

faɗuwa ta yi yayin da ta ririƙe itatuwan ƙamm. Daga nesa Amrah ta ce. "Zahra ki dakata ina zuwa". Ta faɗa tare da maida kallonta kan Safira ta ce. "Maza kiyi amfani da baiwar ki wajan tura ni inda take, kiyi sauri bamu da isashen lokaci.

Girgiza kai Safira ta yi sannan ta fara ƙoƙarin tura Amrah amma samm wannan baiwar tata yaƙi yin aiki.

Cikin tashin hankali Safira ta dube ta ta ce. "Samm fa yaƙi yin aiki bansan me ya sa".

Jin hakan ya sa hankalin Amrah ya tashi. "Shi ke nen yanzu kenen Zahra mutuwa za ta yi?".

Ɓangaren Zahra kuwa tsoron da take ƙoƙarin ɓoye wa ne ya bayyana. Nan take ta fara ƙwalla wa su Amrah kira domin su zo su cece ta.

Aka gadar ta cigaba da tsinkewa yayin da halittun ruwan suka cika sama ruwa suna jiran faɗowar Zahra cikin ruwan.

Nan take numfashin Zahra ya fara yin sama yayin da jikin ta ta soma kakkarwa haƙoranta na sama yana dukan na ƙasa.

Nan laulayi ya ɗauke ta sa'anan ta faɗa cikin ruwan.

Nan take su Amrah suka yi suman tsaye. Nan da nan suka fashe da kuka.

Zahra na faɗa wa cikin ruwan kuwa halittun ruwan suka rufu a kanta. Nan take gaba ki dayansu suka ja da baya yayin da suka kasa yi mata komai. Sunyi ƙoƙarin cin namarta amma da zarar sun kusance ta suke jin wani irin azaba tamkar wutan garwashi.

"Yanzu shi ke nen zahra ta mutu, innalillahi wa innahilaihi rajihun!". Cewar Safira wacce ta yi shaɓe-shaɓe da hawaye.

Nan take suka ga haske ya cika cikin ruwan wanda ya sanya halittun ruwan suka ja da baya.

Buɗe idanuwanta Zahra ta yi tare da kurma wani irin ihuu mai matuƙar tsoratarwa. Nan take tsoro ya kama halittun ruwan. Nan take Zahra ta yi sama yayin da ta soma tafiya kan iska.

Mamaki ne ƙarara ya bayyana kan fuskokin su Amrah.

Yayin da kowanensu ya saki baki yana kallon Zahra.

Kafin giftawar ido suka ga Zahra a kusa da da su.

Nam take Zahra ta dawo cikin hayyacin ta.

Kallonsu Zahra ta yi ta ce. "Na kasa gane wa, ya aka yi halittun ruwan suka kasa yi min komai?".

Murmushi Amrah ta yi ta ce. "Saboda ke ma kina da baiwa saidai naki yafi namu".

"A'a ni samm bani da wani baiwa, Allah ne dai kawai ya yi zan kuɓuta daga hannunsu, tunda ku kun kasa aiwatar da komai, in badan ikon Allah da ƙarfin addu'ar da nake yi ba da shi ke nen na mutu". Cewar Zahra.

Basu yi aune ba suka ji gurnani daga bayansu. "Ya Allah". Safira ta faɗa ta ƙara da cewa. "Yanzu muka fita daga matsala ɗaya ga wata matsalar ta kuma kunno kai".

Ta faɗa suna mai juyawa a tare.

Nan suka ci karo da wani babban zaki, yana tsaye yana kallonsu yayin da idanunsa suka kasance wuta mai ci. Da sauri suka ja da baya. Murmushi Amrah ta yi domin ita samm ba ta tsoron dabbobi saboda ta yi rayuwa da su. Da ƙarfin zuciya da jarumta ta soma ƙoƙarin yin masa wasa yayin da ta isa inda yake tana mai shafar bayansa. Nan suka ga zakin ya tashi cikin iska yana mai ɓace wa daga harabar wajan.

Sauke ajiyan zuciya suka yi yayin da gaba ɗaya suka samu guri suka zauna. Cikin gajiya Zahra ta miƙar da ƙafarta tana mai kwanciya.

Ƙara mai matuƙar tsoratarwa suka jiyo da sauri gaba ki ɗayansu suka miƙe tsaye suna mai kallon ta ina wannan ƙara ke fitowa. Nan suka ji muryar na faɗin. "Ku koma ko kuma ku mutu".

Nan kowannensu ya shiga cikin tashin hankali.

Wannan murya tana ƙara musu tsoro a zuciyoyinsu domin basu san daga wane ɓangare na wajan muryar ke fitowa ba, kuma kowanne su yana jinta sosai a cikin zuciyarsa.

Maida kallonta Zahra ta yi kansu ta ce. "Yanzu mene ne abun yi?".

"Kawai mu juya mu tafi, ni fa ina tunanin ma ba'a wannan dajin dukiyar mahaifiyar ta mu da hujjojin suke ba, saboda ta za'a yi mahaifiyar mu ta kawo dukiyoyinta da hujjoji cikin wannan dajin mai matuƙar hatsari, tunda muka shigo muke ta harba da abubuwa masu matuƙar tayar da hankalin mutum. Ni fa ina ganin kamar tarko a kayi mana, tabbas wani ne zai shirya hakan".

Girgiza kai Zahra ta yi ta ce. "Tabbas maganarki gaskiya ce, ta ya ya mahaifiyar mu ta iya shiga dajin nan harta fita ba tare da wani abu ya same ta ba, tabbas na yarda akwai abin da yake tafiya ba daidai ba".

Nan take gaban Zahra ya yanke ya faɗin!, Kallonsu ta yi hankali tashe ta ce. "Ko dai ba ita bace mahaifiyar mu?, ina ga fa wanda ta bada wannan bayanan ba mahaifiyar mu bace. Na yarda samm ba mahaifiyar mu bace kuma wannan littafin ma duk shirya shi aka yi bana gaskiya ba ne".

Girgiza kai Safira ta yi ta ce. "Ƙwarai da gaske ita ɗin samm ba mahaifiyar mu bace ba, gaba ɗaya tarko aka haɗa mana domin mu mutu, kuma wani ne zai yi hakan".

Kallonsu Zahra ta yi ta ce. "In har muna son mu tsira da rayukan mu, ya zama dole mu yi gaggawar barin wannan dajin yanzun nan".

Nan take suka yi sauri juyawa da zimmar barin daji. Da mamakin su kuwa suka ga gurin ruwan da gurin hanya gaba ɗaya ta washe tamkar babu wani abu da ya taɓa wanzuwa a wajan".

Girgiza kai Safira ta yi tana mai ja da baya. "Shi ke nen mun riga mun faɗa a tarko, babu wanda zai tsira a cikin mu domin gaba ɗaya mutuwa za mu yi".

Nan take suka ji an kwashe da wata mummunar dariya mara daɗin sauraro.

MANAGE PAGE PLEASE👏🏽😌😌😌😌😌😍

KUYI HAƘURI DA NI, YANZU WAYATA BATA TYPING SBD TA SAMU MATSALA INA YI NE A WAYAR ƳAR UWATA HAR LOKACIN DA ZAN GYARA, SHI YA SA BAKUA SAMUN UPDATE A KAI A KAI, DOMIN SAINA ARI WAYAR TAKE BANI NAYI MUKU TYPING. IN SHA ALLAHU KOMAI YA KUSA ZUWA ƘARSHE DA ZARAR NA CHANZA WAYA.🙏🙏🙏🙏🙏🙏

KADA KU MANTA DA LIKE, COMMENTS, AND SHARE FISABILILLAH 🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏

ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞💞
ZINARIYAR JAJIRTATTU
Chapter 15 · 0% Book details