Sashe 36
Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
_________________
Umar kuwa yana zuwa gida ya tarar da ƙannensa zaune sun yi tagumi gaba ɗaya fuskokin su ya bayyana suna cikin damuwa.
"Sannu da zuwa Yahya Umar". Ƙannen nasa suka faɗa.
Da kai kawai ya amsa sannan ya shiga part ɗin sa tare da kwanciya kan gado ya na mai kallon silin ɗin ɗakin.
Shigowa cikin ɗakin su Ramlat suka yi sannan suka kalle shi suka ce. "Yahya kenen rataye Abba za'a yi?".
Amsa ya ba ta da cewa. "Ni ma ban sani ba Ramat, ban taɓa jin zuciyata ta karaya ba a kan mahaifin mu sai yau, gaba ɗaya na rasa walwalah da sukuni na, ko ba komai shi ya kasance mahaifin mu ne, amma koma mene ne haka yi masa ya cancanci hakan domin halin sa shi ya ja masa wannan sakamakon".
Khairiya ce ta ce. "Amma za mu je muyi masa kallon ƙarshe ranar Monday ko?".
Amsa Umar ya ba ta da cewa. "Allah masani, ku ɗan bani space please". Jin hakan ya sa suka fita daga cikin ɗakin.
__________________
Awa biyu ya ɗauke su suka isa Dutse. Sooraj bai san ina ne gidan su Aliyu ba hakan ya sa ya kira Umar a waya.
Umar da ke gyare-gyaren files ɗin da yake bincike a kai ne ya jiyo wayarsa na ruri, nan ya ga number Sooraj wanda ya yi saving da my Gee ya bayyana kan fuskar wayar.
Ɗaukar wayar ya yi ya ce. "Hello Sooraj ya ka ke?".
Amsa Sooraj ya bashi da cewa. "Ina lafiya kalau. Dama na kira ka ne domin ka nu na min gidan su Aliyu inda miss Lailah take".
Murmushi Umar ya yi ya ce. "Kai da ka ke Kano, ina ruwanka da sanin inda gidan su Aliyu yake, idan na maka kwatance zuwa za ka yi ne kai da ka ke Kano".
Nan Sooraj ya ce. "A'a, yanzu haka ma ina garin jigawa".
Nan Umar ya miƙe tsaye cikin zallar mamaki ya ce. "Me ya kawo ka kuma a wannan lokaci?".
Nan Sooraj ya kwashe komai ya faɗa masa.
Sauke nannauyan ajiyan zuciya ya yi sannan ya ce. "Ka gaya min inda ka ke zan zo na same ka".
Nan Sooraj ya faɗa masa.
Nan Umar ya shiga bathroom sannan ya yi wanka tare da sauya tufafi, kafin daga bisani ya fice daga gidan.
Nan suka haɗu da Sooraj yayin da ya kai su har gaban gidan su Aliyu.
Nan ya tsaya sannan ya ce. "Nan ne gidan za ku iya shiga".
Kallon sa Sooraj ya yi ta cikin mota yayin da ya ce. "Me ya sa ba za ka shiga ba?".
"Babu komai". Umar ya bashi amsa.
Kallonsa Zahra ta yi ta ce. "Yahya Sooraj zo ka shiga mana kodai kana jin kunyar surukar ka ne?".
Umar bai san sanda murmushi ya subuce masa ba. Nan ya ce toh shikenen ya zan shiga.
Nan suka yi parking a waje yayin da suka ƙwanƙwasa kofar gidan. Nan Baba mai gadi ya buɗe musu kofa. Kai tsaye suka shiga cikin gidan.
Nan Amrah ta hango Zahra, da sauri ta nufi inda take sannan ta rungume ta nan suka rungume juna.
Shiga ciki suka yi gaba ɗaya. Nan Safira ta fasa ihuu ganin Zahra, da sauri ta nufa inda take tare da rungume ta. "Ashe da rabon zan sake ganinki, Allah na gode maka da ya kasance kina raye".
Murmushi Zahra ta yi ta ce. "Nima nayi farin cikin ganin ku".
Nan take idanuwanta ya sauka a kan Miss Lailah.
Nan take gaban Zahra ya yanke ya faɗi. Saurin ture Safira ta yi daga jikin ta tare da ja da baya.
Nan take kanta ya fara jujjuya wa.
Mamaki ne ya kama su, ganin Zahra cikin wannan yanayin. Nan Sooraj ya dube ta ya ce. "Zahra lafiya?".
Nuna miss Lailah Zahra ta yi ta ce. "Ita ce mahaifiyar mu?".
Girgiza mata kai gaba ɗaya suka yi sannan suka ce. "Eh mana".
Nan take Zahra ta ce. "Wannan samm ba mahaifiyar mu bace ba".
Nan take gaban kowa ya yanke ya faɗi.
"Kamar ya ba ita ce mhaifiyar ku ba". Cewar Grandpa.
Nan Zahra ta ce. "Ƙwarai kuwa ita ɗin ba mahaifiyar mu bace ba".
Nan Miss Lailah ta ce. "Tabbas kin yi gaskiya, ni ɗin ba mahaifiyar ku bace ba, ni ɗin na kasance aljana ce".
Nan take kowa da kowa ya ja da baya.
"Ina Lailah take?". Cewar Alhaji Abdullahi.
Nan ta basu amsa da cewa. "Tun a shekaru ashirin da suka gabata Lailah ta daɗe da mutuwa".
Nan take jiri ya ɗibi Grandma ta faɗi a wajan sumammiya.
TASHIN TASHINA, WAI DAMA WANNAN BA MISS LAILAH BACE ALJANA CE?, TOH ME YA SA TA ZO A MATSAYIN MISS LAILAH?, KO DAI AKWAI WANI ƁOYAYYEN AL'AMARI NE?. MU JE DAI ZUWA💃💃💃.
MU HAƊU A PAGE NA GABA🙏🙏🙏🙏
KADA KU MANTA DA LIKE, COMMENTS, AND SHARE FISABILILLAH 🙏🙏🙏🙏🙏🙏
ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞
ZINARIYAR JAJIRTATTU
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!
*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎
*A'ISHA M.B*💞💞
*BOOK 2 PAGE9️⃣8️⃣▶️9️⃣9️⃣*
________________________
Da sauri suka nufi inda Grandma take. Nan Aliyu ya shiga kitchen da sauri tare da ɗebo ruwa a kofi. Kai tsaye inda Grandma ke kwance ya nufa tare da yayyafa mata.
A hankali ta fara buɗe idanuwanta yayin da hawaye suka fara bin kan ƙuncinta.
Ɗaga ta Mom ta yi tare da zaunar da ita kan kujera. Maida kallonsu suka yi kan Aljanar da ya zo matsayin Miss Lailah sannan Aliyu ya ce.
"Shin bake bace Aunty na ba?, ta ya haka yi hakan ta kasance?, ta ya ya ki ka san Aunty na da har ki ka iya ɗaukar sufanta ki ka zo matsayin ke ce ita?".
Kallonta Sooraj ya yi ya ce. "Amma na shiga ƙoƙanto, ya kamata ki warware mana komai domin kin sanya kowane mu cikin duhu da ruɗani".
Murmushi Aljanar ta yi ta ce. "Ni sunana Farira, kuma ni ɗin na kasance ba mutum bace aljana ce. Ba ta ƙarasa ba Zahra ta dakatar da ita da faɗin.
"Kenen sunanki Farira?, ko dai ke ce ƴar uwa matar da na gani a cikin dajin da muka je dan nemo hujjoji da za su wanke mahaifiyar mu".
Girgiza mata kai ta yi sannan ta ce. "Ƙwarai da gaske ita ɗin ta kasance ƴar uwa ta ce. A shekarun baya da suka gabata sarkin aljanu na cikin dajin wato mai suna Saif ya kasance shi ɗin yahyan mahaifin mu ne, mahaifiyar mu ta kasance bil adama sakamakon lokacin baya mahafinmu ya zo duniyar ku ya fara soyayya ba tare da ta san cewar mutum bace. A lokacin iyayen mahaifiyar mu sunƙi aminta da mahaifin mu saboda ya bayyana musu cewa shi ɗin bashi da dangi. Ganin cewar iyayen sunƙi amince wa ya sa sunka yanke shawarar guduwa. Bayan sun gudu suka je suka fara rayuwa a chan wani waje na da ban wanda babu wani wanda zai iya zuwa wajan. A lokacin da mahaifiyar mu ta zo haifar yayata wato Barira ta sha wahala wanda har sai da mahaifin mu ya gayyato dukkannin aljanu domin su taimaka mata wajan haihuwa. Bayan ta haifi Barira. Bayan shekara guda haka haife ni, saidai a lokacin ta mutu.
Saboda tsananin ƙaunar da yake mata hakan ya sa ya saka mani sunanta. A lokacin yahyan sa Saif ya buƙaci a bashi ni domin ɗansa ya aura saidai mahaifin na yaƙi amince wa. Ganin hakan ya sa haka saka mahaifin mu a kurkuku na azaba harta kai ga ya rasa ransa. Ta ƙarfi da yaji suka kama ni da yayata suka sa muka fara rayuwa tamkar bayi a ƙarƙashin su".
Safira ce ta katse ta da faɗin. "Amma labarin mahaifiyar mu muka ce ki bamu, kuma kina bamu naki labarin".
Murmushi aljana Farira ta yi sannan ta ce. "Me ki ke ci na baka na zuba?, nan mafari ne". Ta faɗa sannan ta ɗora da cewa.
"Ni da yayata mu ɗau shekaru muna rayuwa cikin ƙangin bauta. Ana haka wata rana naji ina son zuwa duniyar mutane. Nan na fita izuwa duniyar ku ba tare da kowa ya sani ba. A nan ne na ci karo da wata mata cikin daji alamu tana cikin tashin hankali, kuma sai naga tana cin ganye alamun yunwa a tare da ita, gaba ɗaya ta galabaita. Nan naji tausayi ya kama ni. Daidai nan kuma naga wani ya zo ya ce ta bishi suka tafi wato kai". Ta faɗa tana kallon Mk.
Girgiza kai Mk ya yi ya ce. "Eh ni ne a lokacin".
Nan aljanar ta cigaba daga inda ta tsaya. "Nan na ji ta na ce maka. Rayuwarta yana mata wuya yanzu, tana jin bata da wata hanya da za ta bi, gaba ɗaya sunanta ya lalace a idan duniya amma ta san Allah shi ne mai jiƙan bayinsa, yana sane da ita, kuma Allah shi ne zai saka mata da abin da aka aikata mata. Ta ƙara da cewa vata da madogaro ji take dama ba ta yi kuɗi ba, ji tame dama a talaka ta zo, tana jin cewa ta yi ɓarnar da ba zata iya gyara wa ba, ta saka al'umma kuka duk kuma dalilin ta, ta ji cewa kawai kashe ta shi ne zai zama adalci domin bata da wata dama da zata samu a lokacin a wajan al'umma". Matar take faɗa cikin raunatacciyar murya yayin da hawaye ke sauka kan fuskarta".