Sashe 14
Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ganin Zahra ba ta kula ta ba ya sata jan bakin ta tayi shiru.
*******
Rufe family meeting ɗin mai martaba ya yi yayin da ya sa kowa ya watse.
Serving ɗin su Aliyu abinci Mami ta yi yayin da ta sa Zubaida ta kirawo Sooraj.
Hanyar part ɗin Sooraj Zubaida ta nufa. Tana isa bakin ƙofar ɗakin sa ta ja burki kana ta yi addu'a daga bisani kuwa ta shiga cikin part ɗin kai tsaye.
Tarar da shi ta yi kan kujera, a yayin da kansa yake kallon sama.
Gyaran murya ta yi. Sai a lokacin Sooraj ya lura cewar an shigo part ɗin sa. Maida kallonsa ya yi kanta ya ce. "Who gave you the gut and the audacity to enter my room?".
Murmushi Zubaida ta saki sannan ta ce. "Calm down masoyi".
"Answer my question first!". Ya faɗa a tsawa ce.
Nan take Zubaida ta sha jinin jikinta. Amsa ta bashi da cewa. "Mami ce ta ce na kira ka kazo ka ci abinci, kuma ni ba zan iya cin abinci ba tare da kaci ba".
Murmushin takaici ya yi ya ce."Wow!, really?, you mean indai ban ci abinci ba kema ba za ki ci ba?".
Girgiza kai Zubaida ta yi alamun eh.
Murmushi Sooraj ya yi ya ce. "Toh masha Allah ka ga ƴar soyayyar gaske, wato ko rataye kaina nayi kema saiki rataye kanki ko, lallai abun ya burge ni. Toh ki saurare ni kiji, ina son kafin na irga uku ki fice min daga ɗaki or else am going yo show you my true color".
"Aba yarima ka san fa ina sonka, kuma very soon zamu yi aure, kuma aure ba na lokaci ƙalilan ba ne zama ne na har abada, shi ya sa nake son tun yanzu na koya maka so na a zuciyar ka, wallahi ba zan iya auren kowa ba idan ba kai ba, kuma ba zan iya rayuwa ba tare da kai ba".
Girgiza kai Sooraj ya yi ya ce. "Ai kuwa za ki mutu kina daƙon so na, in dai har ki ka ce ni za ki so, ni fa bana sonki, kuma ba zan taɓa sonki ba, na riga na faɗa miki. Ni fa mutumin kirki ne ma, da wani ne ba zai faɗa miki ba zai aure ki a hakan kuma alhalin ba ƙaunar ki yake ba, ni kuma na fito na gaya miki cewar bana sonki domin bana son ki fuskanci uƙuba ta shi ya sa na gaya miki, amma ke kin nace sai kace mayya. Ni ina da wacce nake so ba ke ba kin gane".
Kallonsa Zubaida ta yi ta ce. "To wace ce ka ke so in ba ni ba?".
Kallonta Sooraj ya yi ya ce. "Kina son ki san wa nake so?, toh saurare ni kiji".
MANAGE PAGE PLEASE👏🏽😌😌😌😌😌😍
KADA KU MANTA DA LIKE, COMMENTS, AND SHARE FISABILILLAH 🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏
ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞💞
ZINARIYAR JAJIRTATTU
بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!
*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎
*BOOK 2*
PAGE 7️⃣3️⃣▶️7️⃣4️⃣
_________________________
"Wacce nake so ni kaɗai ne na santa kuma faɗa miki babu abinda zai ƙare ki da shi". Dan aka ki fice min daga ɗaki.
"Ni fa ba zan fita ba har sai ka gaya min, ni na ma riga na san wace ce. Waccan shegiyar yarinyar da na ganka tare da kai a asibiti ita ce ko?, faɗa min gaskiya shin ita ce?". Cewar Zubaida
Kallonta Sooraj ya yi sannan ya ce. "Idan ma ita ce mene damuwarki?, me zai ƙara miki mai zai rage ki da shi?. Ki sani cewa ni Zahra ma a waje na ta fiki daraja, ke fa ko takalmin ƙafata ya fiki daraja dan aka ba zan so ki ƙara yi min magana kan soyayyar banzar ki ba".
Nan take Zubaida ta fashe da kuka yayin da ta yi saurin barin ɗakin sannan ta nufi parlour wajan dining.
Tana ƙarasowa wajan dining ɗin ta faɗi ƙasa tana mai ƙara rusa wani kukan.
"Subhannallahi!, Zubaida mene ne abinda ya faru?, me Sooraj ya aikata miki, eh maza faɗa min dole na ɗauki mataki a kansa".
Share hawayenta Zubaida ta yi ta ce. "Mami dan Allah ki sa yarima Sooraj ya aure ni, wallahi ba zan iya auran wani inba shi ba, kuma ya ci min mutunci ya ce takalmansa ma sun fi ni daraja".
Jin hakan ya sa ran Mami ya ɓaci!. "Hakan me zai sa Sooraj ta furta miki hakan, aikuwa dole na ɗau mataki a kansa". Maida kallonta ta yi kan Zubaida ta ce. "Kina ji na ba, nayi miki alƙawarin cewa zan sa ya aure ki nan da sati ɗaya".
Murmushi Zubaida ta yi ta ce. "Da gaske ki ke Mami?".
Amsa Mami ta ba ta da cewa. "Ƙwarai da gaske yanzu ma zan nufi hanyar part ɗin mai martaba". Tana kaiwa nan ta nufi hanyar ɗakin mai martaba kamar yadda ta faɗa.
Tashi tsaye Zubaida ta yi sannan ta buga tsalle cikin farin ciki. Binta kawai su Aliyu da umar suke yi da kallo. Yayin da suke mamakin halin irin na Zubaida.
Mami kuwa tana kaiwa kan ƙofar ɗakin mai martaba ta shiga ciki. Nan ta tarar da mai martaba da Gimbiya Saratu a zaune da alama suna tattauna wa ne. Sunkuyar da kanta Mami ta yi ta ce. "Ranka shi daɗe ina son zamu yi magana".
Kallon sama da ƙasa Gimbiya Saratu ta bita da shi ta ce. "Iyyee uwar gida sannunki. Kina gani na a zaune za ki wani shigo ki ce za ku yi magana, ko kin manta cewa yau kwana ta ne, to ba za ki yi maganar da shi ba, ki bari sanda kwana ta zagayo kanki sai kiyi masa magana". Ta ƙarashe maganar tana mai jan tsaki.
Kallonta mai martaba ya yi ya ce. "Ke Saratu mene ne aka?, shin ita ɗin sa'ar ki ce da har za ki na faɗa mata irin waɗan nan maganganun?, kuma a gaban nawa ma ki ke faɗa mata hakan saboda baki da kunya?. Ki sani cewa gaba ki ɗaya ku ukun babu wacce bana so. Dan aka maza ki bawa A'isha haƙuri".
Sosa ƙeya Saratu ta yi ta ce. "Ka gafarce ni mai martaba amma ba zan iya bata haƙuri ba".
Da sauri Mami ta share hawayen da ke ƙoƙarin zubowa sannan ta juya tare da saurin barin ɗakin.
Ganin ta fita ya sa mai martaba ya dubi Gimbiya Saratu sannan ya ce. "Ke ma maza bi ta".
"Bangane ba, korata ka ke yi?"., Cewar Gimbiya Saratu.
Amsa sarki ya bata da cewa. "Eh na kore ki maza ki fice min daga ɗaki ina buƙatar hutawa".
Fuska a yatsine Saratu ta miƙe sannan ta fice daga ɗakin.
_______________
"Wai shin kun manta ki ni waye?, ni ɗin fa Govnor garin nan ne". Cewar Gov. Musa.
Amsa ɗaya daga cikin ƴan sanda suka bashi da cewa. "Koda kai ɗin shugaban ƙasar nan ne muddin aka kama ka laifi kuma aka tabbatar da hujja kan hakan to dole ne kotu ta yi aiki a kansa tunda bai bi dokar wannan ƙasa ba".
Shiru Gov. Musa ya yi yayin da damuwar duniya suka bi suka addabe shi.
"Dama aka ake jin kunya idan aka kama mai laifi aka saka shi a cell?, idan kuwa aka ne wane irin zafi da raɗaɗi Mrs Lailah ta ji ita da ba babu abinda ta yi ni ne nan nayi mata sharri". Gov. Musa ya faɗa yana mai cigaba da sake-sake a ransa.
Su dpo kuwa suna isa dutse kai tsaye police station suka nufa. Yayin da shi da Mk suka shiga buɗe files na mutane masu laifi wanda aka rufe a baya domin rashin samun tabbattacciyar hujja. Nan suka bazama neman file ɗin Mrs Lailah.
________________________
Ganin Amrah su Zahra suka ta dawo da fruit a hannunta. Mamaki ne ya kama su ganin Amrah na riƙe da kayan marmari.
Ƙarasowa Amrah ta yi sannan ta ajiye mangwaro da su tsamiya tare da lemon ɓawo.
Kallonta Safira ta yi ta ce. "A ina ne ki ka samo waɗan nan fruit ɗin?".
Amsa Amrah ta bata da cewa. "Awa kan bishiyun da nayi to a nan na samu".
Nan take Amrah da Safira suka fara cin kayan marmarin hankali kwance.
Kawar da kanta Zahra ta yi cikin zuciyarta kuwa fal yake da jin aushin Safira.
Kallonta Safira ta yi ta ce. "Ke Zahra ba za ki ci ba ne ba koya?".
Maida kallonta Zahra ta yi kanta ta ce. "Umarni ki ke ba ni ne ko me?, Idan da a ce ina da niyyar sha ba za ki ga na sha ba ne, ko an gaya miki ni ɗin ina da ƙwalama ne".
Ajiyan zuciya Safira ta sauke! ta ce. "Koma dai mene ne ke ki ka sani, idan ma zuciya ki ka yi to tun wuri ki sauko domin kuwa bamu sani ba ko daga wannan ba zamu kara samun wani abun taɓawan ba, dan aka ki taimaki kanki ki sako hannu kisha domin babu wanda zai tuhume da yin hakan".
Ɗaukar littafin da ke ƙasa Zahra ta yi sannan ta ce. "Hmm karki manta cewar da Fatima ki ke zance, idan Fatima ta riga ta faɗi magana to ba za ta chanza kalamanta ba kuma babu wani mahaluƙi wanda ya isa chanzawa".
Ta ƙarashe maganar tana mai ɗora wa da tafiya. Ganin ta fara tafiya da littafin tana mai ƙaranta abinda ke ciki.
Da sauri suka miƙe yayin da suka yi saurin bin bayanta.
Kai tsaye cikin ƙogon Zahra ta nufa yayin da su Amrah suka mara mata baya.
Nan suka tarar da duhu gaba ɗaya ilahirin ƙogon. Ba tare da tsoron abun da zai je ya dawo ba suka cigaba da tafiya cikin duhun ƙogon. Nan take suka fara jiyo sautin tsuntsaye masu matuƙar ban tsoro.
Nan take kowanensu ya shiga cikin tsoro. Cikin daƙewa suka cigaba da tafiya.
Saida suka yi tafiya mai nisan gaske kafin daga bisani suka tsinci kansu a wani waje da basu taɓa ganin irinsa ba. Gurin na ɗauke da gada ta itatuwa da suka gungure a juna mai matuƙar tsawon gaske. Yayin da ƙasar gadar yake fal da ruwa yayin da kada da halittun ruwa suka cika cikin ruwan.