← Book details Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 65

Sashe 42

Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su Gimbiya Saratu kuwa sun fito tamkar su ne ma amaren, inda su Samira suka ci ture kaga tsiya. Ɓangaren su Khairiya kuwa suma sunyi kyau cikin shigar su ta alfarma less ce mai tsada suka saka wacce bata da hayaniya. Yayin da suke ta walwala da farin ciki. Yayin da ita ma kuma Miss Lailah da Alhaji Abdullahi suka kasance cikin shigar su ta alfarma. Yayin da Mami ta ci gwargwaro sai kai kawo take a cikin fada, tana ta tarbar baƙinta.

Lefen su Zahra kuwa kowaccen su set guda ashirin da huɗu. Kuma duk iri ɗaya haka yi musu. Ɓangaren Zubaida ita kuma hakan take.

Haka aka shafe kwanaki bakwai ana biki yayin da haka yi kamu, yayin da haka fara ɗaura auren Zahra da Sooraj a sadaki dubu ɗari biyar da zoben zinare guda uku sannan haka ɗaura nashi da na Zubaida ita ma sadaki dubu biyar da zoben zinare guda uku. Yayin da Aliyu ya biya sadakin Safira a sadaki dubu ɗari uku. Shima kuma Umar hakan ta kasance ya biya sadakin Amrah a dubu dari uku.

Bayan an sanar da ɗaurin auren ya kasance. Haka yi gagarumar walima. Yayin da haka yi wa Zahra da Zubaida rakiya zuwa wajan mai martaba. Nan mai martaba ya yi musu nasiha tare da fatan alheri a zaman su. Nan haka fita da su yayin da haka yi wa Zahra rakiya wacce ta kasance uwar gida da motoci masu tambarin masarsuta, raƙuma da kiɗa na musanman. Yayin da haka saka Zahra a mota mai alfarma na Rolls Royce mai launin gold. Nan Zahra ta soma kuka a haka aka raka ta zuwa gidanta haka kaita part ɗin ta yayin da ita ma kuma Zubaida wacce ta kasance kishiyar Zahra haka kaita ita ma part ɗin ta. Gaba ɗaya gidan ya cunkushe da hayaniyar ƴan kawo amare.

Nan haka zaunar da Zahra da Zubaida guri guda Inda parlourn ya yi tsit. Yayin da Mami ta fara musu nasiha tana faɗin.

"Ku biyu Allah ha ɗaukaka da aure a rana guda, ku sani zaman kishiya ba gaba ba ne, gwaji ne daga Allah. Ku kalli juna da zuciyar kirki, ku girmama juna, ku riƙe aure da tawali’u."

"Kar ku tsaya kallon wacce aka fara ɗaura wa aure, ko wacce aka fara kai wa ɗaki. Aurenku duk daidai yake a wurin Allah, wanda ya fi ladabi da biyayya shi Allah zai ɗaukaka."

"Ku guji magana da kishi, kiɗa da gasa. Ku zauna da addu’a, da fahimta. Ku bar Allah Ya daidaita zukatanku."

Nan Miss Lailah ta ce. "
Ni dai fata na shi ne ku haɗa kawunan ku guri guda, ku guji saɓon Allah, kuyi wa mijin ku biyayya, sannan kuyi haƙuri da juna, duk halin da za ku kasance a ciki ku kasance masi haƙuri da juriya, ku kasance masu tawwakali da juna. Ku bi mijin ku domin samin aljannar ku".

Nan Mami ta maida kallonta kan Zahra wacce ke sanye cikin alƙabba ta rufe fuskarta da mayafi ta ce. "Zahra na sanki, dan Allah kiyi haƙuri, duk abinda zai faru kada kiyi komai, ki maida komai ba komai ba".

Girgiza kai kawai Zahra ta yi yayin da ta kasa magana sai faman kuka take yi.

A sa'inda ɓangaren zubaida baƙin ciki ne ya mamaye ta. Nan su Gimbiya Saratu suka ce. "Zubaida kiyi haƙuri, amma karki bari haƙurin ki ya yi yawa domin idan haƙuri ya yi yawa cuta ce, indai yarinya ta miki ba daidai ba ke ma kiyi mata, karki yarda ta raina ki dan ta zo a uwar gida, kina ji na ba, ki nuna mata cewa kin fita wayewa".

Kallon Gimbiya Saratu Mami ta yi ta ce. "Wannan wane irin abu ne haka Saratu?, shin nasiha ki ka zo yi ko kuwa ki haɗa su faɗa?".

Nan Gimbiya Saratu ta buga tsaki ta ce. "Ina ruwan ki, tunda ba da ke nake ba kiyi shiru".

Tashi su Miss Lailah suka yi domin ana jiran su a waje za'a kai su Amrah su ma gidajensu.

Sallama suka yi da juna yayinda suka fita suka kai su Amrah gidansu, kowacce gidanta da ban.

Da kaɗan kaɗan mutane suka fara watse wa.

Inda ya rage Zahra da kuma Zubaida Aliyu. Shiru bake ji babu wacce ta tanka wa ƴar uwarta.

Cikin zuciyar Zubaida kuwa tana ta tunanin irin sharin mutuncin da za ta ƙula wa Zahra, yayin da ita kuwa Zahra ranta fes.

Ana haka suka ji shigowar Sooraj hannayensa riƙe da leda. Da sallama ya shigo gidan tare da bawa kowaccen su ledarta.

Zama ya yi a three seater yana mai fuskantar su .

Sauke nannauyan ajiyan zuciya ya yi sannan ya ce.

“Amaryata uwar gida, amaryata kishiya. Yau Allah ya haɗa ku da ni a cikin aure. Wannan ni’ima ce daga Ubangiji, kuma nauyi ne a kaina da ku duka. Ina so ku sani, ni zan yi ƙoƙarin zama adali. Zan ƙaunace ku bisa gaskiya, ba son zuciya ba".

“Ban aure ku don kuyi gasa da juna ba, na aure ku ne domin ku zama ginshiƙan gida. Wanda ta riƙe kanta da natsuwa, da mutunci, ita ce za ta fi samun farin ciki. Ina roƙon ku da ku zauna lafiya. Ku bar gaba, ku karɓi juna da zuciyar kirki".

“Zan yi adalci a kowane dare, ba zan nuna bambanci ba. Kuma ina roƙon ku, idan na fi zama da ɗaya wani lokaci, ku ɗauka da zuciya mai sauƙi, domin zuciya tana tafiya da yanayi, amma adalci zai tabbata. Kowanne ɗaki yana da lokacinsa, kowane dare yana da sahibinsa. Ku kasance da hakuri, ku taimaka min, ku gina gidana da addu’a da fahimta.”

Sannan ya ƙara da cewa. Tsarin kwanakin da zanna yi da ku shi ne.

“Zan kwana dare ɗaya a ɗakin uwar gida, gobe a ɗakin kishiya tunda sabon aure ne. Haka zan ci gaba, daga baya kuma ya koma kowacce zan nayin kwana uku a ɗakinta. Idan akwai wani abu da ya sa na ɓata rana, zan rama. Kuma duk lokacin da na ga akwai buƙatar gyara, za mu tattauna da nutsuwa daga baya".

“Allah Ya albarkaci zaman mu. Ya raya mana gidan auren mu da salama da fahimta.”

Nan gaba ɗaya suka amsa da amin. A sa'inda kowacce ta tashi ta shiga ɗakin ta.

TOH FA WANNAN SABON BABI KENEN, SHIN WANNAN RAYUWAR AUREN NASU YA ZAI KASANCE A TSAKANIN SU UKUN?, ME KU KE TUNANIN ZAI FARU A GABA, ZA SU ZAUNA LAFIYA NE KO A'A, SHIN SOORAJ ZAI GANO CEWAR ZUBAIDA TANA ƊAUKE DA JUNA BIYU KO A'A, SANNAN WANE NE MAI CIKIN ZUBAIDA?. DOMIN JIN YACCE ZATA KASANCE MUJE ZUWA

DAN ALLAH KUYI LIKE, COMMENTS, AND SHARE FISABILILLAH. SABODA ALLAH PLEASE🥹 🙏🙏🙏🙏🙏🙏

ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞
ZINARIYAR JAJIRTATTU
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎

*A'ISHA M.B*💞💞

*BOOK 2 PAGE1️⃣0️⃣6️⃣▶️1️⃣0️⃣7️⃣*

________________________

Nan su Mami suka wuce garin jigawa, hawanni biyu zuwa uku ya kai su chan yayin da haka kai kowacce gidan ta na aure.

Amrah haka fara kaiwa gidanta na sunnah. Babban gida ne wanda ya haɗa da kayan zamani tare da furnitures na royals. Gaba ɗaya kallon kayan ɗakin Amrah Onion colour ne. Ko ina na gidan yana da matuƙar ban sha'awa. Ba laifi Umar da su Alhaji Abdullahi sunyi ƙoƙarin wajan ganin an ƙawata gidan Amrah. Nan haka zaunar da ita da Umar yayin da haka yi musu nasiha tare da wa'azi. Sannan a ƙarshe haka yi musu fatan alheri, tare da yi musu addu'ar Allah ya basu zuri'ar ɗayyiba.

Ɓangaren gidan Safira ma haka. Ita ma gidan ta babba ne wanda ya haɗa da duplex. Gaba ɗaya colour na kayan gidan light purple ne da milk. Ko ina anyi decorating din shi da kaya masu tsada. Kamar yadda haka yi wa su Umar nasiha suma ɓangaren su haka, inda a ƙarshe suka yi musu fatan alheri tare da barin gidan.

Nan Miss Lailah ta ja Mami izuwa gidan ta domin ta kwana. Gaba ɗaya wannan ahalin sun kasance a cikin farin ciki mara misaltuwa.

____________

Zahra kuwa, bayan shigar ta ɗaki ta baje kan gado tana mai saukar nannauyan ajiyan zuciya.

Furzar da iska ta yi waje tare da bin ɗakin da kallo sannan ta ce. "Wayyo daɗi kashe ni, wai da gaske nan ɗin ɗaƙi na ne?, oh ni jikar wa zance, gaskiya yau ina cikin farin cikin".

Miƙe wa ta yi tare da bin kazar da Sooraj ya bata da ido sannan ta ce. "Yanzu ita ma wannan kazar tawa ce, gaskiya Zahra kina cikin alheri dumu-dumu". Ta faɗa tashi tsaye sannan ta nufi kitchen tare da bin kitchen ɗin da kallo. Jinjina kai kawai ta yi ganin irin ƙawata kitchen ɗin da haka yi da kayan alatu da sauransu. Cikin zuciyarta ta ce. "Ba laifi kuɗi sunyi kuka wajan ƙawata gidan nan da haka yi". Ana haka ta ɗauko plate da cup tare da koma wa ɗakinta.

Nan ta samu guri a ƙasa ta baje tare da ɗaukar kaji biyu da ke cikin leda da kuma rufaida yoghurt guda biyu ta ajiye a ƙasa.

Nan ta saki wani murmushi ta ce. "Waya gan mu su uwar gida mai capacity".

Ta faɗa tana mai ɗaukar kaza ɗaya ta saka a plate. Nan ta ce. "Kassh!, na manta ban ɗauko chokali ba, kuma shin na jira yahya Sooraj ne ko a'a?". Ta tambayi kanta.

Basarwa ta yi ta ce. "Ba buƙata tunda ga tashi chan sai ya ci shi ɗaya. Ta faɗa tare da ware hannayenta ta soma cin kazan. Haka ta shiga ci babu gaggauta wa, tana ci tana sumbatu. "Masha Allah gaskiya aure akwai dad'i, dama irin daɗin da ake ci kenen, ai da na sani tun ina da shekaru sha biyu a duniya zan ce a min aure, irin wannan jin daɗi haka". Haka ta shiga yin surutai ita ɗaya.

Ɓangaren Zubaida kuwa bayan shigar ta ɗaki. Yaye kayan da ta sa ta fara yi tare da shiga toilet ta watsa ruwa, daga bisa ni kuma ta saka sleeping dress wanda yake transparent. Sannan ta koma kan gado ta baje a kai. Nan ta ɗauki wayarta ta fara chatting.
Chapter 42 · 0% Book details