← Book details Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 65

Sashe 63

Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Miƙe wa ta yi daga kan cinyarsa ta ce. "Ni fa yau gurasa nake son ci ya za'a yi ne?".

Kawar da kansa Sooraj ya yi gefe kamar bai ji abinda ta ce ba. Cikin shagwaɓe fuska ta ce. "Au ina maka magana shi ne za ka juya min fuska?".

Kallonta ya yi da idanuwansa masu ɗaukar hankali ya ce. "Ni yanzu a ina zan samu gurasa, ki bark na dafa miki indomie ki ci".

Tashi ta yi tare da bubbuga ƙafa a ƙasa cikin shagwaɓa ta ce. "Ni wallahi gurasa nake so, in ba haka ba muyi faɗa".

Ajiyar zuciya Sooraj ya sauke!, tare da girgiza kai ya ce. "Kowa Allah ya na haɗa shi da jarabawa, ni kuwa ke ce jarabawar da Allah ya haɗa ni da ita. Ni yanzu a ina zan samu gurasa?".

Kallon sa ta yi tare da washe baki ta ce. "A wajan Audu mai balangu a wajan sa za ka siya kuma wallahi yana mutunci har Aunty yake ce min, ni kuma in ce mai ƙanina".

Nan take kishi ya kama Sooraj kallonta ya yi ya ce. "Saboda me zai dinga kiran ki Aunty?, bai san kina da aure ba ne, ai kuwa zai gane kuransa, saboda me zai dinga cewa matata Antinsa".

Rufe bakinta Zahra ta yi tana dariya ta ce. "Toh ai banga wani abu a nan ba, kuma fa Audu ɗin fa tsoho ne, dan na san sai dai ya yi jika da kai, mutunci ne kawai".

Murmushi Sooraj ya yi jin Zahra ta ce tsoho ne. Hakan ya sa ya ce zai je ya siyo mata. Nan ya tashi ya ɗauki key ɗin motarsa tare da fita daga gidan. Saida ya ɗan yi tafiya kafin daga bisani ya ga wajan Baba Audu mai balangu. Nan ya yi parking ya sauka tare da zuwa, ai kuwa yana zuwa ya ga tabbas tsoho ne sosai. Hakan ya sa kawai ya siyi gurasar dubu ɗaya sannan ya nufo hanyar gida.

Zahra kuwa bayan fitar Sooraj ta ƙara jin tana sha'awar cin goruba.

Bayan Sooraj ya shigo da gurasar ya kalle ta tare da miƙa mata sannan ya ce. "Gashi na siyo miki gurasar, yanzu kinyi farin ciki?". Ya faɗa fuskar sa ɗauke da murmushi.

Ƙwaƙulo murmushi Zahra ta yi ta ce. "Yanzu naji gurasar ta fita a raina, yanzu goruba nake son ci".

Zaro ido waje Sooraj ya yi ya ce. "Me?, bangane ba, ke fa ki ka ce kina son gurasa kuma na siyo yanzu kuma ki ce Goruba ki ke so".

Shagwaɓe fuska Zahra ta yi ta ce. "Ba fa laifi na ba ne ba, laifin Baby Zee ne, ta ce min gurasa muka ci jiya yanzu kuma Goruba take son mu ci".

Nannauyan ajiyan zuciya Sooraj ya yi ya ce. "Ni dai naga ta kaina, da ke da Baby Zee ɗin ba za ku ci goruban ba. Kenen shi gurasar ya za ku yi da shi?".

Washe haƙora Zahra ta yi ta ce. "Ai wannan abu mai sauƙi ne, kawai sai ka zauna ina kallon ka kana ci, idan ka ci kamar na ci ne, bayan ka gama ci saika je shagon ɗan aljanna ka siyo min goruba".

Jinjina kai Sooraj ya yi ranshi a haɗe ya ce. "Wato ni yanzu na zama ɗan aiken ki ko?, saboda kina da juna biyu shi ne ki ka yi amfani da opportunity ɗin domin ku dinga bani wahala. Da na san haka masu juna biyun nan ku ke da munyi family planning. Allah ne ya sa irin wahalar da su Umar da Aliyu su ma suka sha. Ai na san duk wahalar da za su sha ba za su kai ni ba".

Taɓe baki Zahra ta yi ta ce. "Ni kuma wane wahalar nake baka?".

Girgiza kai Sooraj ya yi ya ce. "Au ba ki ma sani ba kenan, kullum haka ki ke ana ni bacci, idan na kwanta ki tashe ni ki ce ke baki samu bacci ba amma ni kuma zanyi bacci, ki saka ni na zauna da ke saboda bakya jin bacci nima ba zan yi bacci ba".

Sosa ƙeya Zahra ta yi ta ce. "Ai ba laifi na ba ne, laifin Baby Zee ne".

Cije leɓensa na ƙasa Sooraj ya yi ya ce. "Komai sai ki ce ba laifin ki ba ne, laifin Baby Zee, ita Baby Zee ɗin ba ta tausayin Baban ta ne da zata sa ana bashi wahala. Gaba ɗaya kin maida ni ɗan aiki a gidan nan. Farko ki saka ni na goya ki nayi ta yawo da ke cikin gida, ki saka ni muyi wasan ɓarawo da ɗan sanda a cikin gida, harda tausa fa ki ke sa nake miki. Ni gaba ɗaya na koma kamar wani mara wayo". Nan ya tuna da wani abu take ya kwashe da dariya sannan ya ce. "Gaskiya ke fa abin naki ya wuce misali, ranar nan ma muna zaune da ke salin halin kawai naga kin tashi wai wallahi warin tusa ki ke son kiji, in ba kazanta ba ta ina mutum zai so jin warin tusa". Ya faɗa yana mai kwashe wa da dariya.

Ƙasa Zahra ta yi da kanta alamun kunya ta ce. "Ka daina min dariya, in ba haka ba, Baby Zee zata yi fushi da kai".

Kawar da kansa Sooraj ya yi ya ce. "Ta daɗe ba ta yi fushi ba, ni wallahi har na matsu wannan Baby Zee ɗin ta zo duniya, ta ga irin abinda Maman ta ke yi".

Maida kallonsa ya yi kan gurasar ya ce. "Ni ba zan ci wannan gurasar ba, ki ɗauka ki ajiye a fridge idan kin tashi sha'awar sa, sai ki ɗauka ki ɗumama ki ci".

Girgiza kai Zahra ta yi alamun to, sannan ta ce. "Shin za ka siyo min gorubar?".

Jim ta ƙara ambatar sunan goruba ya sa Sooraj ji kamar ya kurma ihuu. Kallonta ya yi ya ce. "Ba zan siya ba, ki je ki sha shayin goruba da ke kitchen"..
.
Taɓe baki ta yi tare da haɗe giranta ta ce. "Ni ba shayin goruba nake so ba, shi kanshi goruba nake so, in ba haka ba na tayar maka da aljanu".

Girgiza kai Sooraj ya yi sannan ya ce. "Kin daɗe baki tayar da aljanu ba".

Ya faɗa tare da miƙe wa ya nufi hanyar ɗakinsa.

Nan take ya ji ta kurma ihuuu tare da faɗuwa ƙasa.

Da sauri ya juya tare da kallonta, ganin ta zuɓe a ƙasa ya sa shi faɗin. "Aljanun sun ƙaraso kenen". Jin gurnani ya sa shi yin tunanin ko da gaske ne ta tada aljanu. Da sauri ya nufi inda take.

Nan ya ga halin da take ciki, kasancewar sa likita hakan ya sa shi ganin cewa naƙuda ne ya zo mata. Da sauri ya nufe ta tare da ɗaga ta. Fashe wa ta yi da kuka tana faɗin.

"Wayyo na shiga uku na lalace, baya na, ƙafa na, marata zafi suke min, ka taimake ni, wayyo zan mutu".

Ganin yadda ya ɓare baki tana kuka hakan ya bashi dariya. Ganin dariya yake yi hakan ya sa Zahra jan kunnensa da mugun ƙarfi. Hakan ya sa Sooraj sakin ƙara.

Ɗaukarta ya yi chakk ya nufi mota da ita. Bayan ya saka ta a cikin mota.

Ya shiga mazaunin driver sannan ya tada mota tare da fita daga gidan. Ɗaukar wayarsa ya yi tare da sanar da Mami halin da ake ciki. Hakan ya saka Mami ta tambaye shi a wane asibiti zai kaita. Nan ya sanar da ita sannan ya ce gata nan zuwa. Bayan sun gama wayar Mami ta saka ruwan zafi a flask tare da ɗaukar towel da kuma meternity pad da towel. Nan ta sanar da su Talatu da Saratu. Nan kuwa su ukun suka nufi hanyar asibitin.

Bayan su Sooraj sun isa asibitin Sooraj ya fito da ita tare da kiran nurses, nan da nan suka fito da patient bed sannan suka ɗora ta kai a shigar da ita labour room.

Babu abinda Sooraj ke faman yi sai addu'a. Ɓangaren Zahra kuwa kuka sosai ta ke yi yayin da ta shiga jera kalmar shahada tare da istighfari domin a ganinta mutuwa za ta yi.

Bayan mintuna ashirin da zuwansu Sooraj asibiti su Mami suka iso. Yayin da suka nufi inda Sooraj yake suka tambaye shi a jikin Zahra.

Saida suka shafe hour 2 a tsaye inda Sooraj ya ga nurses ɗin sai kai kawo suke a asibitin. Nan Sooraj ya tambayi ɗaya daga cikin nurses ɗin a wane hali ake ciki. Nan ta faɗa masa cewa gaba ɗaya Zahra ta kasa yinkuri kan jaririn cikin mahaifa ya juya yana a breech position, kuma sunyi scanning an ga ƴan biyu ne namiji da mace, a cikin su ɗaya ne a breech position, wacce kanta ba'a breech position take ba ta kasa fito wa saboda dalilin ɗayan. Yanzu addu'ar da muke yi shi ne Allah ya sa kada wani abun ya samu jariran kuma ita kada wani abu ya same ta.

Jin wannan maganar ya sa hankalin Sooraj da su ya tashi. Bai san sanda idanunsa suka ciko da ƙwalla ba. Saurin share wa ya yi ya ce. "Ina son ku bani dama na karɓi haihuwar nan, ni ɗin likita ne, hanyar da za'a iya dawo da kan jariran daidai shi ne External Cephalic version".

Nan nurse ɗin ta ce. "Eh yanzu zuwa zan yi na kira babban likita domin hakan. Sannan kuma ba duka biyun ne a breech position ba, ɗaya kansa daidai yake ɗayan kuma breech position".

Daidai lokacin wata likita ta shigo wajan fuskarta sanye da mask ta dube su ta ce. "Ina mai naƙudar take?".

Nan nurse ɗin ta gaya mata cewa tana a labour room. Nan likitar ta nufi labour room ɗin yayin da ita kuma nurse ɗin ta bi bayanta.

Likitar na shiga labour room ɗin ta kalli sauran nurse da likitoci sannan ta ce musu su fita su barta ita ɗaya.

Maganar ya yi musu bambaraƙwai domin ta ya za su bar likita wacce basu san daga ina take ba ta karɓi haihuwa gashi Zahra na halin tsaka mai wuya.
Chapter 63 · 0% Book details