Sashe 37
Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Nan take tausayin ta ya kama ni, na ɗauka cewar ni da yayata ne kaɗai muke fuskantar kalubale ashe a cikin bil adama suma suna fuskanta. Hakan ya sa na kudiri aniyar cewa dole na shiga rayuwarta domin taimaka mata, ban san ta ba amma haka kawai naji ta shiga raina kuma naji ina son taimaka mata. Nan Mk ya karfafa mata gwiwa da kalamansa harta yarda ta bishi. Ba tare da sun sani ba na bi bayansu. Nan naji tana faɗa masa dukiyoyinta da kuma hujjoji, yanayin yadda take bayyana dajin ya nuni da maƙocin dajin da na sani a kano ya kasance yanki ne wanda babu wani abu da ke rayuwa a wajan. Hakan ya sa naje wannan dajin na ƙara masa tsari sannan na saka aljanu waɗan da ba za su yarda wani bil adama ya shiga domin ɗaukar dukiyarta ba. Bayan tsaurara tsaron da nayi hakan ya sa na cigaba da bibiyar Miss Lailah. A lokacin naje kotu nan naji an ce za'a yanke mata hukuncin kisa amma kuma za'a bari sai bayan ta haihu. Bayan an kaita prison. Na cigaba da bibiyarta yayin da nayi shigar ma'aikatan ƴan sandan da ke aiki a wajan sannan naje naga wani kundi na littafi ɗaukar littafin nayi na karanta komai, bayan karanta wa na fahimci duk abinda ya faru. Bayan watanni lokacin ta zo haihuwa ta sha wahala sosai wanda hakan ya sanya iya ƴa guda ɗaya ta haifa wato Zahra a lokacin na shafa goshin Zahra tare da sanya mata ƙarfi na kariya a jikinta. Ganin ta kasa haifar sauran da kanta ya sa haka nufi asibiti nan na bisu asibitin bayan ta haifo biyun, ni kuma saka wa kowaccen su baiwa na kariya a jikinsu. Nan ƙarfi na ya ragu na koma izuwa duniyar mu domin na je na ƙaro wani ƙarfin.
Bayan ba dawo kwatsam naga an harbi Lailah a gefen zuciyarta ta faɗa kogi yayin da ruwa ya tafi da gangar jikinta . Nan na ɗauke gangar jikinta na kai shi dajin da na tsaurara tsaro na garin Kano. Abokina na ya taimaka min wajan ganin na ajiye gangar jikin Lailah a wannan dajin saidai sarki Saif ya gano shirin da muke yi. Hakan ya sa ya mayar da abokina izuwa Aku wato (parrot). Sannan ya saka gangar jikinsa cikin dutse ta yadda babu wanda zai iya fidda ta. Nayi ta roƙonsa amma yaƙi daga ƙarshe ya ce. Na koma izuwa duniyar mutane sannan na yi rayuwa irin nata har izuwa lokacin da zan ga ƴaƴan da ta haifa sannan na kawo su shi ne kawai zan barki ki cigaba da rayuwa muka na ƙyale wannan gangar jikin. Idan kuma ba haka ba na rasa rayuwata. sannan kada na kuskure na aɗa wa koda yayata Barira ne, idan ba haka ba gaba ɗaya zai haɗa ya kashe mu".
Nan na amince da kudirin sa sannan na koma izuwa duniyar ku na mutane na koma daidai wannan kogin na ɗauki suffar Lailah sannan da raunukan da ke jikinta da kuma harbin bindiga da aka yi mata. Nan naci alwashin cewa saina ɗaukar mata fansar abinda haka aikata mata sannan kuma sai na tona asirin wanda ya yi mata hakan. Nan gangar jikina ta fara yawo a ruwa har izuwa kogin ƙauye Ɓabura A nan ne jama'ar ƙauyen suka ganni. Nan haka fito da ni daga ruwan sannan haka kawo ni izuwa tsakiyar ƙauyen. Nan mahaifiyar Sooraj ta ce ya duba ni. Gaba ɗaya abin da ke faruwa ina ji. A nan ne Sooraj ya duba ni nan na dube su ina ta furta kalmomi.
Nan haka ɗauke ni haka kai ni garin Kano. A haka nake ɓace wa na sanar da dutsen da gangar jikin Lailah ke ciki duk abin da ke faruwa. Bayan shekaru. Naji ƙanshin ƴar Lailah a asibitin da nake nan na ga Zahra. Take farin ciki ya mamaye zuciyata.
Hakan ya sa na je na riƙe ta a haka dai likitoci suka ƙwace ta daga hannun na.
Bayan dawowar Sooraj na faɗa masa komai sannan na kirkiri littafi na hatsarin da zasu fuskanta idan zasu shiga dajin. Sannan na bawa Sooraj domin idan ya ga yarana ya basu.
Haka na cigaba da bibiyar rayuwar kowaccen su
Bayan sun je dajin ne na sanya suka fuskanci hatsariruka duk domin naga shin za su iya komai domin ganin an wanke mahaifiyar su. Nan suka cigaba ba tare da sun ja da baya ba. A nan ne na saka aljani su kama Zahra matsayin wacce ita ce za ta mutu domin fitar da hujjojin. Kuma duk anyi hakan ne domin tabbatar da soyayyar da take yi wa mahaifiyar nasu.
Bayan kazo cikin dajin na saka abokina wato Aku domin taimaka maka sannan ya nuna maka hanya. Bayan ka fito da Zahra ka kaita asibiti na tura tsofafin masu maganin cikin mu domin su ceci rayuwar Zahra. Nan ne suka je yayin da suka taimaka wajan dawo mata da numfashin ta. Ana haka ne Zubaida wacce zaka aura ta turo ƴan daba domin su kashe Zahra. Nan tsofafin suka yi musu mugun duka ta yadda ba za su sake ganganci tunanin cewa su dawo. Gaba ɗaya wannan shi ne ni. Kuyi haƙuri idan kunji babu dad'i kasancewar na ɗauki fuskar Lailah.
Nan Sooraj ya ce. "Kenen Zubaida ita ce ta sa a kashe Zahra aikuwa zata gane kuranta".
Nan Zahra ta kalleta sannan ta ce. "Dan Allaht ki kai mu muga mahaifiyar mu".
Nan aljana Farira ta ce su rufe idanunsu. Kamar yadda ta faɗa haka suka rufe idanunsu. Daidai lokacin John ya nufo inda Safira take domin ya cutar da ita. Bai ankara ba ya ga an ririƙe shi ya kasa motsa wa daga inda yake.
Buɗe idanunsu keda wuya suka tsinci kansu cikin daji. Nan aljana Farira ta ce. "Ga inda mahaifiyar ku take". Ta faɗa tana mai nuna duste.
nan Zahra ta ce. "Wannan ba dutse mai kuka ba ne ba wanda yake nuna hanya?".
Amsa aljana Farira ta bata da cewa. "Ƙwarai kuwa shi ne"
"Ta ya zamu iya fito da mahaifiyar ta mu?". Cewar Amrah.
Nan aljana Farira ta ce. "Ta hanyar bada baiwar da ku ke da shi sannan ku tura izuwa wannan dutsen".
Kamar yadda ta faɗa haka su ukun suka ɗora hannayensu kan dutsen sannan suka fara tura duk wani baiwa na kariya da ke tattare da su.
MU HAƊU A PAGE NA GABA🙏🙏🙏🙏
KUNJI SHIRU BANA DA LAFIYA NE. ABIN AUSHIN MA NA MUKU LONG PAGE YA GOGE DUK DA BANA JIN DADI SAIDA NA SAKE WANI🥺🥹. KUYI MANAGE.
DAN ALLAH KUYI LIKE, COMMENTS, AND SHARE FISABILILLAH. SABODA ALLAH PLEASE🥹 🙏🙏🙏🙏🙏🙏
ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞
ZINARIYAR JAJIRTATTU
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!
*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎
*A'ISHA M.B*💞💞
*BOOK 2 PAGE9️⃣9️⃣▶️1️⃣0️⃣1️⃣*
________________________
Da sauri su Zahra suka ja da baya ganin yadda dutsen ya so ma girgiza.
Nan take suka tsaya Tare da zuba wa sarautar Allah ido.
Da mamakin su suka ga dutsen ya rabe gida biyu yayin da haske ya bayyana daga cikin dutsen. Nufar gurin Aljana Farira ta yi tare da fito da miss Lailah.
Sanye take cikin kayan da haka yi da rigar doki yayin da ya kasance tamkar alƙabba. Fuskarta kuwa ɗauke yake da murmushi.
"Baba!". Kalmar da ta fara ambata kenen. Haɗa hannayensa guri ɗaya Grandpa ya yi ya ce. "Ki yafe min kinji ƴata".
Murmushi ta saki sannan ta ce. "Babu abin da kayi min, na san a lokacin kana cikin ɓacin rai ne hakan ya sa ka gaza saurona amma yanzu komai ya wuce".
Da sauri su Zahra suka nufa gare ta tare da rungume ta.
Rungume su ita ma ta yi suna me yin kukan farin ciki.
Kallonsu gaba ɗaya aljana Farira ta yi ta ce. "Ni lokacin tafiya ta ya yi, zan koma izuwa inda na fito, na cika miki dukkanin mafarkin ki Lailah, yanzu baki da damuwa. Ni yanzu zan tafi, kada ku manta a duk sanda ku ke da buƙatar taimako na, to ni kuma zan bayyana gare ku".
Share hawayenta Zahra ta yi ta ce. "Kin dawo mana da mafarkin da muka rasa, kin mayar mana da rayuwar da ta kau, Aljana Farira, ba mu da kalmar da za ta isa godiya face hawaye masu ɗauke da farin ciki."
Kallon Aljana Farira Miss Lailah ta yi ta ce. "Rayuwa ta ba ni darasi, amma ke ki ka dawo da darajar rayuwata. Kin goge min hawaye da kulawa, kin cusa min murmushi mai ma’ana. A lokacin da na rasa mafita, ki ka bayyana da rahama da alheri. Kin zamo tamkar mala'ika da Allah ya aiko min. Sannan gashi sanadiyyar ahalin guda ya dawo, ƴaƴana sun dawo gare ni. Ban san ta ina zan iya saka miki da wannan abu da ki ka yi a gare ni ba na gode Farira". Miss Lailah ta faɗa tare da fashe wa da kuka mai tsuma zuciya.
Nan Alhaji Abdullahi ya ce. "Kinyi abin da ba kowa zai iya ba. Kin dawo mana da abin da zuciyarmu ta daɗe tana kuka a kansa. Mun gode da taimakon mu da ki ka yi, da kuma nuna mana ƙaunar da ba ta da iyaka".
Murmushi kawai Aljana Farira ta yi ta ce. "Na barku lafiya". Ta na kaiwa nan ta ɓace daga ganinsu.
Nan jikin kowanensu ta yi sanyi.
Tsugunnawa Umar ya yi kan gwiwowinsa sannan ya haɗe hannyensa guri guda ya ce.
"Ku gafarta wa mahaifina. Eh, ya yi kuskure, ya cutar da ku, ya zamba ce ku cikin aminci.
Duk da ya ba mu kunya, ba mu daina ƙaunarsa ba. Zuciyarmu na kuka, amma muna roƙon gafara a gare shi. Ba don yana da gaskiya ba, amma don muke neman salama a zukatanmu da nashi.
Ku yafe masa, domin kowa yana da lokutan gazawa. Kuma ina roƙon hakan da hawaye a zuciyata, ku gafarta masa, kubarwa Allah hukunci.idan Allah na gafarta wa bayinsa, me zai hana mu gafarta wa juna?. Dan Allah ki yafe min nima idan na ɓata miki rai. Kuma ina son ki ɗauke ni matsayin ɗanki". Ya faɗa kansa a sunkuye.