Sashe 2
Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tun daga kan Sooraj Mami bata sake haihuwa ba har shekaru goma suka gifta hakan ya sa Mami ta fara bawa sarki shawarar da ya ƙaro aure amma ina sarki yaƙi amincewa da hakan.
Suraj yana matuƙar son mahaifiyarsa fiye da yadda yake son kansa yayin da yake ganin taɓa mahaifiyarsa tamkar taɓa rayuwar sa ne hakan ya sa a duk sa'in da mami ta shiga damuwa yakan zuwa gare ta sannan ya durƙusa kan gwiwowin ysa ya shiga bata hakuri yana kuka hawaye na bin kan ƙuncin sa, hakan ya sa Mami take shiga damuwa a duk sanda ya yi mata aka domin kuwa bata son ganin yaronta cikin bakin ciki.
Mamy bata gajiya wajen rokan mai martaba ba domin ya kara aure saboda ba zata kara iya haihuwa ba hakan yasa mai martaba shiga damuwa domin a duk sanda Mami ta zo gareshi da hawaye da kuka take zuwa tuna ce da shi ya kara mata aure amma shi kuwa mai martaba bashi da burin kara aure gaba ɗaya ganin hakan ya sa mai martaba ya yanke hukuncin cewar tun da hakan shi ne burin Mami to zai faranta mata rai sannan zai kara auren. Hakan ya sa yaje ƙauye neman auren Saratu. Saratu ta kasance mace mai fitina da kuma ƙyamatar mutane, duda irin cewar mahaifinta talaka ne amma hakan bai sata dinga yin fake life ba, bayan auren ta da wata biyu. Ta samu juna biyu. Farin ciki gun Mami ba'a magana saika rantse cewar cikin nan nata ne.
Ɓangaren Sooraj kuwa ya yi farin ciki domin bashi da wani buri sai ya ga yana da ƙani ko ƙanwa. A sa'inda yake ganin Saratu tamkar mahaifiyar sa. Ana aka kwatsam wata rana Sooraj ya dawo daga makaranta ya tadda Mami tana wanke wa Saratu kaya hakan ya sa ran Sooraj ya ɓaci. Cikin ɓacin rai ya gaggayawa Saratu maganganu masu ɗaci. Cikin jin aushi Gimbiya Saratu ta kai ƙarashi wajan sarki. Sarki bai jira cewar Sooraj ba ya yanke wa Sooraj hukuncin barin ƙasar Nigeria ya tura shi ƙasar London wajan babban abokinsa domin ya ƙarashe karatun sa a Chan, a sa'inda sarki ya ce muddin bai kammala karatun sa ba kada ya dawo masa gida. Bayan wasu watanni Saratu ta haifo kyakkyawan ɗanta wanda ya ci suna Junaid. Bayan wasu shekaru ta haifi Samira daga nan bata ƙara haihuwa ba.
Mami ta kasance tana iya ɗaukar duk abinda Saratu zata yi mata domin mace ce mai neman zaman lafiya ba tashin hankali ba. A ɓangare ɗaya kuma tana mai kewan ɗanta Sooraj.
Bayan wasu shekaru Sarki ya ƙara aure wato Talatu, Talatu ta kasance mace mai kimala da kamun kai sannan mai haƙuri a komai, amma saidai tun lokacin da sarki ya aure ta Saratu ta hure mata kunne, yayin da ta sata suka haɗa hannu wajan gallaza wa Mami suna mai gasa mata aya a hannu. Talatu ta haifar wa sarki yara mata biyu ta farko Yusra sai kuma ta ƙarshe Fasma.
Ɓangaren Sooraj kuwa a ƙasar London ya kasance yana karanta Medicine ne domin burinsa shi ne ya zama babban likita. Bayan gama University ɗin sa ne ya dawo Nigeria. A yayin da Sarki ya buɗe masa babban asibiti. Sosai Mami ta farin cikin ganin ɗanta cikin ƙoshin lafiya. Sooraj kuwa mamaki ne ya kama shi ganin yadda yake da ƙanne har guda huɗu gashi Sarki ya ƙara aure bayan Saratu. Bayan Sooraj ya fara aiki ne ya dinga samun mutane suna kiranshi a ƙasashe da ban da ban domin kasancewarsa ƙwararren likita.
Hakan ya sa yake tafiya kasashe waje yin aiki sai yayi watanni bai dawo gida ba. Dalilin hakan aka kuwa shi ne saboda Saratu da Talatu domin baya son tarihi ya sake maimaita kansa.
Wannan dai shine cikakken tarihin Sooraj.
**********
Horn Dpo ya yi hakan ya sa fadawa suka fito domin ganin waye. Tambayarsa suka fara yi waye shi hakam ya sa Dpo ya nuna musu police warrant ɗin shi. Ganin hakan ya sa suka barsa ya shiga harabar fadan.
Dakatar da shi daga yunkurin shiga ciki fadawan suka yi sannan suka bashi haƙuri gami da cewa. "Dole sai mun je mun isar wa sarki cewa wani ya zo kafin mu barka ka shiga".
Girgiza kai Dpo ɗin ya yi ya ce. "Shi ke nen nima ba zan dakatar da ku ba kuje ina jira".
Jin hakan ya sa ɗaya daga cikin fadawan ya shiga ciki sannan ya sanarwa sarki cewa yayi baƙo. Jin hakan ya sa sarki ya umarci bawan da ya shigo da baƙon nasa.
Jin hakan ya sa shi fita sannan ya sanar da Dpo cewar zai iya shigowa ciki. Jin hakan ya sa Dpo ya shiga ciki sannan ya gaida sarki tare da Mami. Umarni sarki ya yi masa da ya zauna, sannan ya saka a kawo masa abun taɓawa. Jin hakan ya sa Dpo ya ce
"Ya gode domin a ƙoshe yake".
"Muna san sanin me ya kawo ka". Cewar sarki.
Amsa Dpo ya bashi da cewa. " Dama naji labarim cewa Zahra tana nan ne shi ya sa na zo domin neman ta".
Washe baki Mami ta yi sannan ta ce. "Kai mahaifin Zahra ne?".
Girgiza kai Dpo ya yi ya ce. "A'a bani da ma alaƙa da ita, ita ɗin yarinyar wata mai laifi ce a kurkuku kuma yanzu bata raye. Nazo neman ta ne saboda littafin mahaifiyar ta da tace a bata".
Kallon juna Mami da Sarki suka yi yayin da sarki ya ce . "Sooraj ya kai Zahra asibiti sakamakon wani wani ɗan ƙaramin matsala da ya faru".
"Asibiti kuma?". Dpo ya faɗa cikin rashi. Kallon sarki ya yi sannan ya ce. "Ranka shi daɗe shin wane asibiti ne ya kaita?".
Amsa sarki ya bashi da cewa. "Wallahi mu kanmu bamuda masaniya a kan inda ya kaita. Saidai idan zaka bi diddigin wayarsa".
Nan Dpo ya karɓi number Sooraj sannan ya fita. Shiga cikin motarsa ya yi sannan ya dialing ɗin number sa.
*************
Buɗe idanuwansa Sooraj ya yi sakamakon wayarsa da yaji yana ruri. Waige-waige ya fara yi chan ya hangi su Zahra kwance har izuwa wannan lokaci babu wanda ya buɗe idanuwansa.
Bin diddigin location ɗin da suke Dpo ya fara yi.
Gov. Musa Muhammad ne zaune kan kujera yayin da yake riƙe da tsadaddiyar shisha a hannu yana zuƙa.
Kallon su Sooraj ya yi ya ce. "Wai su waye ku?, me ya sa za ku zo ku ɗaɗɗaure mu?, wai shin ba kai ne govnor Jigawa ba?".
Dariya gov. Musa Muhammad ya yi ya ce. "Ƙwarai da gaske, ni ɗin govnor ne, gaskiya yau ta kasance min babban rana a gare ni, burina na zama amshaƙi mai kuɗi wanda babu kamarsa a duniya ya cika domin ga yaran Mrs Lailah Abdullahi a hannu na".
Zaro idanuwa waje Sooraj ya yi a sa'inda mamaki ya bayyana kan fuskarsa. "Kana nufin waɗan nan mata ukun yaran Mrs Lailah Abdullahi ne?".
Amsa Gov. Musa ya bashi da cewa. "Ƙwarai kuwa, sune kuma sirrin zama amshaƙi, shekaru sha tara kenen ina neman waɗan nan yara sai gashi yau Allah ya nuna min su, lokacin mulkar wannan ƙasar ta yi bayan nayi amfani da su ukun nan wajan neman inda ajiyar kudaɗen Mrs Lailah suke sai nayi safaransu izuwa kasashen waje".
"Me ya sa tun wannan kwanaki ban san da cewar Zahra ƴar Mrs Lailah ba?". Sooraj ya faɗa cikin zuciyarsa.
Buɗe idanuwansu Umar da Aliyu suka yi tare da ɗora wa kan Gov. Musa. Baƙin ciki da takaici ne suka bi suka cunkushe guri guda a zuciyar sa.
"Me ya sa ka kasance mahaifi na?, tabbas babu mai rashin sa'ar mahaifi kamar ni. Ni ɗan naka ma baka ƙyale ba balle kuma ƴaƴan wasu". Cewar Umar.
Dai-dai wannan lokacin su Zahra suka buɗe idanuwansu. Kallon juna su ukun suka shiga yi. Ganin suna a ɗaɗɗaure ya sa Zahra kallon gov. Musa ya ce. "Kai ya zaku wani ɗaɗɗaure mu tamkar wasu akuyoyi?, ku zo ku kunce mu".
Murmushin mugunta Gov. Musa ya yi ya ce. "Kina da taurin kai tamkar mahaifiyar ki, ke ya kamata na fara koya wa hankali tare da waɗan nan ƴan uwan naki".
Taɓe baki Zahra ta yi ta ce. "Toh haka aka ce maka su ɗin ƴan uwa na ne?, dan ka ga muna kama, dama ai kowa yana da mai kama da shi a duniya, ni lokacin haɗuwa da masu kama da ni ɗin ne ya yi, ko kai nan ba za'a rasa mai kama da kai ba, amma ba zan yi fatan hakan ba domin kayi muni da yawa, ga kuɗin haram ka girman kai, ka kunce mu kafin na nuna maka asalin wace ce ni".
Kallonta Safira ta yi ta ce. "Can you just keep quiet, duk kin bi kin ishi mutane da surutu, muna cikin matsala an ɗaɗdaure mu har kin samu bakin magana".
Galla mata harara Zahra ta yi tare da yi mata kallon sama da ƙasa sannan ta ce. "Ke ina ruwanki da ni?, karki ga fa dan muna kama ki samu damar raina min hankali, kina gani na nan bana batin ta kwana yadda nake a ɗaɗdauren kika fusata ni zan iya durza bakin ki a bango".
Daka mata tsawa Sooraj ya yi!, sannan ya ce. "Zahra mene aka?, duk kin bi kin ishi mutane da surutu".
Kallon Safira Aliyu ya yi ya ce. "Safira dan Allah kiyi shiru".
Kallonsa Zahra ta yi ta ce. "Malam ɗan sanda dama wannan ce Safira?, shi ya sa ranar nan da zanje kasuwa siyawa wannan Sooraj ɗin kayan shayi naji kace Shakira, ashe ita ce".
Kallonta Safira ta yi ta ce. "Ke mene aka ya za ki zo kina ɓata min suna, sunana Safira ba Shakira ba".
Duk abinda ke faruwa Amrah da Mk na kallo yayin da suka kasa furta komai.
Saka wa gov. Musa Muhammad ya yi da kidnappers ɗin su kunce su Zahra. Kamar yadda ya umarta aka suka kunce su baki ɗaya.
Ganin sun kunce su ya sa Zahra ta yi saurin buge su kidnappers ɗin. Tare da riƙe hannun Safira da Amrah.
Nan take wani farin haske ya zagaye su ukun. Nan take mamaki ya kama gaba ɗaya mutanen wajan.