← Book details Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 65

Sashe 6

Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

PAGE 6️⃣3️⃣▶️6️⃣4️⃣
_______________________
Ƙarasowa wajan Mk ya yi sa'anan ya sauke nannauyan ajiyan zuciya ya ce. "Duniya mai cike da ruɗani, tana ɗauke da launin zafi da sanyi, a wannan duniyar kowane ɗan adam yana rayuwar a irin wannan matsayar, wasu zukatan sukan kasance masu zafi, wasu kuma sukan kasance masu sanyi, idan ka so chanza rauninka, zaka juyar da shi da muhimmin abu domin gyara manufofi, domin ƙalubalantar wasu masu zuwa dole ka kasance mai taka tsantsan tare da kiyaye abubuwa da yawa na rayuwa, ire-iren duniyoyi sukan bambanta kuma mukan samun labarbarin su, duniya mafi hatsari a ciki ita ce duniyar da muke a cikin ta, ita ce ba ka iya ka bambance maƙiyi da masoyin ka. A dai wannan duniyar, maƙiyi ya kan zama amini na tsohon shekara da shekarunka baka sani ba, ita wannan duniyar ba duniya bace na hutawa ko na jin daɗi ba, duniya ce da haka samar da ita domin mu tafiyar da rayuwar mu da tunani mai kyau, idan ka aikata daidai a cikinta, toh za ka ga daidai, idan ka aikata saɓanin haka toh zaka riski saɓanin haka, lokaci baya jiran mutum a wannan duniyar, sai dai mutum ya jira shi, da zarar ya zo kuma zai tafi. Al'amarin da ya fi bani tsoro shi ne labarin Mrs Lailah. Abinda ta sani kawai ta rubuta wa a wannan littafi amma bashi ba ne ainihin gaskiyar ba, abinda ya faru da ita gaskiya ne domin ni kaina na shaida hakan amma kan mijinta ba gaskiya ba ne ta yi masa gurguwar fahimta".

Kallonsa Umar ya yi sa'anan ya ce. "Toh mene ne ainihin gaskiyar?".

Sauke ajiyan zuciya Mk ya yi a karo na biyu sannan ya ce. "A lokutan da suka shuɗe, bayan Lailah ta zo ta sanar wa Abdullahi cewar abokinsa Musa ya ci amanarta ya karɓi sa hannunta domin safaran mata ba tare da saninta ba, hakan ya sa Abdullahi wato mai gida na ya tafi izuwa gidan Musa. Shigar shi ke da wuya ya ga sun kafa hujjojin su a kan kujera na cewar da amincewar Lailah aka yi safaran mata. Ganin hakan ya sa ran mai gida na ya ɓaci sannan ya ce wa Musa da kada ya aikata hakan a gare ta domin kuwa bai cancanci ya samu irin wannan sakayyar daga gare shi ba bayan duk gwagwarmayar da shi da Lailah suka sha wajan samar masa gurbi na karatu sannan har ya kai matakin da yake kai a lokacin. Musa ya nuna girman kai sannan ya ce shi ba zai faɗi gaskiya ba muddin bai bashi kujerar sa na shugaba ba. Jin hakan ya sa hankalin Abdullahi ya rabu izuwa gida biyu sa'anan ya ce ya amince zai sauka daga kan wannan kujerar shi ya au amma ya tabbatar da cewa bai furta wa mutane cewar Lailah ita ce take safaran yara. A gaba na da gaban mutanensa Musa ya yi wa Abdullahi alƙawarin cewa ba zai yaɗa abinda ya faru ba, muddin ya saka hannu to zai dawo da yaran da suka ɗauka. Jin hakan ya sa Abdullahi ya tafi office ɗinsa sannan ya rubuta ya ajiye aikin sa kuma yana son Musa ya au kujerar a maimakon sa. Nan letter da Abdullahi ya rubuta ya je hannun prime minister yayin da haka haɗa zama na politics ana tattaunawa ga me da hukuncin da Abdullahi ya yanke. Kuma shi Abdullahi ya yanke hakan ne ba dan komai ba sai dan samun kwanciyar hankalin matar sa mafi soyuwa a gare sa, ya bar dukkanin abu wanda ya shafi siyasa ba tare da ya sanar da Lailah hakan ba domin idan ta sani ba za ta ji daɗi ba.

Bayan kwanaki da faruwar hakan kwatsam Musa ya watsa wa gari cewar Lailah na safaran yaran mutane har maganar ta kai kotu. Hankalin Lailah da Abdullahi sunyi matuƙar tashi sosai, amma hankalin mai gida na duk ya fi tashi domin kuwa sabo da wannan abun ya sauka daga kan kujerar siyasa. Ana haka suka ji labarin an kawo gawauwakin yaran da haka tafi da su ƙasar waje. Nan suka je kamfanin Lailah yayin da mutane suka fara jifan su. Nan ma'aikatan wajan suka samu fetir suka babbakawa kamfaninta wuta suka ƙona shi ƙurmus sannan suka sawa Abdullahi da Lailah duka a titi. Lailah kuka shima yana yi yayin da suka rasa inda za su sa kansu. Da ƙyar suka iya cetar kansu. Bayan sun koma gida Abdullahi ya je wajan Musa sannan ya yi masa faɗa hakan me ya sa zai ci amanarsa bayan ya yi masa alƙawarin cewa zai ajiye sirrin ba zai fitar ba sannan ya ce zai dawo da su cikin ƙoshin lafiya. Kun san wane martani Musa ya bashi?".

Da sauri su Aliyu suka girgiza kai sannan suka ce . "A'a".

Amsa Mk ya basu da cewa. "Martani da ya basa da cewa, dama chan faɗuwar ka nake son gani ba cigaban ka ba, kai a waye za ka sani abin da zuciyata ba ta yi niyar yi ba?, ina zaune da kai ne kawai saboda dukiyar matarka, kuma ya yanzu na samu domin da bakinka ka faɗa min cewa dukiyoyin matarka suna cikin wani daji a garin nan amma baka san ina ba ne. Ni kuma yanzu ka gama yi min amfani domin dama chan faɗuwar ka nake so ba cigabar ka ba". Abdullahi bai san sanda hawaye suka fara bin kan ƙuncin sa ba ya ce da shi. "Ban taɓa tunanin cewa za ka iya zama maƙiyi na ba, duk da cewar an ce masoyinka na yau na iya zama maƙiyin ka na gobe sannan kuma maƙiyin ka na yau kan iya zama masoyin ka na gobe, amma kai ka zama maƙiyi na kawai dan abin duniya!. Ban taɓa zaton kai amini na zai so ganin faɗuwa ta ba, ni a koda yaushe nasarar ka nake son gani amma kai ba hakan ne a zuciyarka ba na zauna da kai da zuciya ɗaya tilo kai kuma da mummunar zuciya da kuma mummunar manufa a gare mu ni da matata".

Musa ya girgiza kai ya ce mishi. "Wannan kujerar ni ya kamata na au amma kai ka au tun daga lokacin na ƙudiri aniyar cewa saina kawo ƙarshen ka, da kai nayi niyyar na yi wa sharrin abin da nayi wa matarka sai kuma na chanza ra'ayi na ya koma kanta".

"Toh me ya sa ba ka tsaya iya ni kaɗai ba ka saka da matata?, ni ne abokin ka bai kamata wannan al'amarin ya shafi Lailah ba". Cewar mai gida na. Jin hakan ya sa musa ya daka masa tsawa! ya ce da shi. "Dole ne ya taɓa ta domin ni duk wanda ya haɗa halaƙa da kai toh maƙiyi na ne, koda kuwa a ce wanda ya kawo ni duniya ne, matata ma na kashe ta ba dan ta gano ko ni wane ne ba sai dan mu'amala da take yi da Lailah hakan ya sa ita ma na aikata barzau wato lahira, yanzu kuma ina zaune ne da Umar iya ɗan da ta haifa min".

Nan take gaban mu ya yanke ya faɗi jin abinda ya faɗi. Tsugunnawa mai gida na ya yi ya fara bashi haƙuri ganin hakan ya sa nima na tsugguna na taya mai gida na bada haƙuri Kasancewar sa mai taimako kuma dogaro a gare ni. Babu irin roƙon da ba mu yi masa ba amma bai yarda ba hakan ya sa muka je kotu ba tare da sanin kowa ba domin mu nemar wa Lailah adalci amma alƙali ya ce ba zai karɓi ƙorafin mu ba muddin ba mu da hujja".

Ajiyan zuciya Umar ya sauke!, sa'anan ya ce. "Ka saka ni cikin ruɗani!, ban gane abin da ka ke faɗi ba, kana nufin iya ni kaɗai mahaifiyata ta haifa?".

Amsa Mk ya bashi da cewa. "Ƙwarai da gaske kai kaɗai ne ɗansa sauran ukun ba ƴaƴansa ba ne shi ya sa ya fi baka kulawa fiye da su".

Furzar da iska mai zafi Umar ya yi waje ya ce. "Toh a ina ya same su kenen?".

Martani Mk ya ba wa Umar da cewa. "Ai ban ƙarasa labarin ba tukun nan ko, ka bari na ƙarasa a nan za ka san inda mahaifinka ya same su".

Ya faɗa sannan ya cigaba daga inda ya tsaya.

"Ana haka Abdullahi ya kai Lailah izuwa wani guri mai hatsari sabo da kada ƴan sandan da suke neman ta a gari su kamata ko kuma jama'a su ganta domin za su hallaka ta ne kai tsaye.

mahaifin Lailah ya buƙaci yana son ganin mai gida na hakan ya sa na kai mai gida na wajan sa. Samun mai gida na ya yi ya ce ya samu labarin duk abubuwan da suke yawo a gari kan ƴarsa Lailah, kuma ya san da cewa mai gida na ya je ya ɓoye Lailah a wani guri, idan yana son cetar kansa ya fito da Lailah ya miƙa wa ƴan sanda ita domin ta karɓi hukunci daidai da laifin da aikata idan ba haka ba zai sa ƴan sanda su kama shi. Abdullahi ya ji tsoro sosai da jin kalamansa, hakan ya sa ya rasa duk wata nutsuwa da kwanciyar hankali. Babu abin da yake tunani sama da rayuwar matarsa domin gaba ɗaya gari ita ake nema. Bai kamata mace mai daraja da kima da kuma taimako ta shiga irin wannan hali ba amma kaddara tana iya faruwa ga kowa. Bai san a wace hali Lailah take ba burinsa kawai shi ne Allah ya sa tana cikin ƙoshin lafiya.

Ɓangaren Lailah kuwa ta yi rayuwa a cikin daji na tsawon sati ɗaya a yayin da babu abin da take ci in banda ganyayyakin cikin daji. Duk ta bi ta rame ta yi baƙi gaba ɗayanta. Naje na same ta lokacin Abdullahi ya sani naje na dawo da ita amma na rufe fuskata da ƙyalle domin ba ta taɓa sani na da mijinta ba naje a matsayin mai taimaka mata. Na ce ta biyo ni muje amma ta ce min.
Chapter 6 · 0% Book details