Sashe 64
Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ganin sun shiga tunani ya sa likitar cewa. "Kada ku ji tsoro, in sha Allah babu abinda zai same ta kuma zata haife su cikin ƙoshin lafiya.
Jin hakan ya sa gaba ɗaya suka fita suka barta daga ita sai Zahra.
Ganin likitoci sun fito daga labour room ya sa Mami faɗin. "Mene abinda ke faruwa?".
Nan ɗaya daga cikin likitocin ya ce. "Likita ta ce tana buƙatar a barta da mai nakuɗar kaɗai a room ɗin".
Mamaki ne ya kama su jin abinda suka faɗa.
Ɓangaren likitan kuwa bin Zahra ta yi da ido sannan ta ɗora hannunta kan cikin jikin Zahra. Nan take Zahra ta kurma ihuu. Yayin da jaririya ta fito.
Jin ihuun Zahra ya sa hankalin su Sooraj ya ƙara tashi.
Ɓangaren likitar kuwa cikin ikon Allah ya juyar da kan jajirirn ya dawo daidai yayin da numfashi Zahra ya fara sama-sama. A ƙarshe dai da ƙyar ta samu ta haifi ɗayan jaririn. Yayin da kukan jariran ya karaɗe ɗakin.
Bayan ta haihu likitar ta yi murmushi yayin da Zahra ta shiga sauke ajiyar zuciya.
Kallonta Zahra ta yi ta ce. "Amma wace ce ke?".
Murmushi likitar ta yi tare da cire face mask ɗin fuskar ta. Nan take Zahra ta zaro idanuwa waje. "Aljana Farira kece?".
Girgiza kai Aljana Farira ta yi ta ce. "Ƙwarai kuwa Zahra ni ce, naga kina cikin mawuyacin hali ne hakan ya sa na zo domin taimaka miki". Nan ta yi wa Zahra allurar bacci.
Cikin ƙankanin lokaci bacci ya yi awon gaba da Zahra.
Ganin ta yi bacci ya sa ta fito daga cikin labour room ɗin sannan ta hangi su Sooraj. Da sauri suka isa gare ta sannan suka ce lafiya. Nan ta ce musu Zahra ta yi kuma babu abinda ya samu ƴaƴanta. Tana kaiwa nan ta bar asibitin.
Nan farin ciki ya lulluɓe fuskokin su gaba ɗaya yayin da nurses suka shiga suka tsaftace jariran tare da jira jinin da ke wajan umblical cord ya tsaya sannan suka yanke shi.
Bayan mintuna Talatin Zahra ta farka inda ta bawa jariran abinci. Yayin da likita ya auna blood pressure da mahaunin bugun zuciyarta. Nan ya ga komai na lafiya.
Nan haka wuce da ita Postnatal ward, wato ɗakin kula da uwaye wanda suka haihu.
Shigo wa Mami da su Sooraj suka yi cikin wajan yayin da farin ciki ke lulluɓe kan fuskokin su.
"Maman twins". Cewar Sooraj. Yayin da Mami ta yi wa jariran wanka sannan ta sa haka haɗa wa Zahra shayi mai kauri.
Bayan an sallame su daga asibiti kai tsaye masarauta suka nufa, domin Mami ta ce a masarauta za'a yi suna kuma ta yi arba'in a chan. Ba tare da Sooraj ya so hakan ba suka nufi masarauta.
Gaba ɗaya masarauta ta amsa cewar matar Yarima ta haihu. Nan Sooraj ya kira su Miss Lailah a waya ta sanar da su halin da ake ciki. Sosai Miss Lailah ta yi farin cikin samun wannan ƙaruwar.
Washe gari kuwa da sassafe haka ga zuwan miss Lailah. Inda su Umar da Aliyu suka ce ranar suna za su zo.
Shagali sosai ba buga wa a jarida haka yi masarauta.
Ranar suna kuwa kowa ya hallara a masarauta inda haka ci aka sha. Yayin da haka saka wa jariran suna Ahmad da Zainab, sai dai ana kiran Ahmad da Mahmud, yayin da jaririya Zainab kuma Zeenat.
Haka rayuwa ta cigaba har Zahra ta yi arba'in ta koma gidan auren ta. Inda suka cigaba da rayuwar su cikin farin ciki.
BAYAN SHEKARU SHIDA
Cikin farin ciki da nishadi, na hangi yara na ta guje-guje a falon gidan suna dariya. Yayin da gefe guda Zahra ce ke bin su bulala.
Da sauri suka shiga ɗakin Sooraj tare da ɓuya a bayansa. Nan yaron wato Ahmad wanda suke matuƙar kama da Sooraj ya ce cikin ƙaramar murya. "Daddy ka ga Mommy za ta dake mu ko".
Kallonsa Sooraj ya yi ya ce. "Saboda za ta dake ku?, ai in dai ina nan babu mai taɓa ku".
Haɗe rai Zahra ta yi ta ce. "Ai dama kai ka ke lalata waɗan nan yaran, ka san abinda suka yi ne, sun ce za su sha ragowar lemo cikin fridge na ana su. Wallahi bayan ana su da nayi, tun da safe nake dafa shinkafa amma taƙi dawuwa, shi ya sa haifar ƴan biyu na wallahi aiki ne, wajan haihuwa kasha wahala wajan raino ma haka, aba dan Allah".
Dariya Sooraj ya kwashe da shi sannan ya dubi twins ɗin nasa ya ce. "Ba na ce ku daina wahalar min da Mommyn ku ba?, me ya sa ku ke wahalar da ita?".
Nan Zeenat ta dubi Mommynta ta ce. "Mommy kiyi haƙuri amma ba mu ne muka saka shinkafa taƙi dawuwa ba".
Ta faɗa tare da nufar wajan Zahra sannan ta riƙe hannunta ta ce. "Mommy mu koma kitchen zai dawu".
Dafe kanta Zahra ta yi alamun ta fara gajiya da halin ƴan biyun nan. Kallonta Sooraj ya yi ya ce. "Ashe babu daɗi, nima irin wannan wahalar ki ka bani lokacin da ki ke da juna biyu, yanzu kuma su suke rama mun".
Jin abinda ya ce ya sa Zahra nufar inda yake da bulala. Da sauri ya tashi tare da fita a guje ya nufi falo. Nan Zahra ta bishi da bulalar tana faɗin. "Ba za ka tsaya ba, yau duk saina koya muku hankali, duk kun bi kun maida ni kamar wata mahaukaciya". Haka suka dinga guje-guje a cikin gidan cikin farin ciki da annashuwa.
Suna tsaka da haka ne suka ji ana ƙwaƙwasa ƙofa. Nan kowanensu ya tsaya yayin da Zahra ta nufi hanyar waje domin ganin wane ne.
Tana buɗe wa kuwa ta tarar da budurwa tsaye a bakin ƙofa.
Cikin kallon rashin sani Zahra ta ce. "Lafiya?, wace ce ke?".
Kallonta budurwar ta yi ta ce. "Zahra baki gane ni ba?, ni ce fa Zubaida".
Zaro ido waje Zahra ta yi ta ce. "Ya salam, na shiga uku, me ya same ki haka?, ya naga kinyi baƙi, kin lalace, me ya sa me ki haka. Shigo ciki kinji".
Shigo wa ciki ta yi tana mai share ƙwallah.
Nan Sooraj wanda ke riƙe da twins ɗin sa suka samu suka zauna. Kallon Zahra Sooraj ya yi ya ce. "Wace ce wannan?".
Kallonsa Zahra ta yi ta ce. "Zubaida ce fa".
Zumbur Sooraj ya miƙe tsaye ya ce. "What!". Mamaki kan fuskarsa.
Ganin da yara a wajan hakan ya sa shi kallonsu ya ce. "Ku shiga ciki kunji, kuje kuyi wasa, ni da Mommyn ku zamu zo daga baya".
Nan Mahmud da Zeenat suka riƙe hannunsu tare da awa upstairs suka nufi ɗakin wasa.
Maida kallonsa Sooraj ya yi kan Zubaida ya ce. "Me ya kawo ki kuma?, maza fice mana daga gida".
Durƙusawa Zubaida ta yi kan gwiwowinta tare da fashe wa da kuka. Cikin shesheƙar kuka ta ce. "Dan Allah kada ku kare ni, na zo nan ne domin neman gafarar ku, tun lokacin da ka sake ni haka maida ni gida ban ƙara samun kwanciyar hankali ba, gaba ɗaya rayuwata ta lalace, nayi aure amma na kasa samun kwanciyar hankali mijin da na aura ya kasance mai kule-kulen mata, kullum cikin duka da hattara ta yake. Har ya zo daga baya ya sake ni. Ban sani ba ko saboda abinda na aikata a baya ne ya sa nake fuskantar irin wannan ƙalubalen. Na san na cutar da ku da yawa, shi ya sa na zo domin neman gafarar ku ko zan samu sauƙi a raina, shima Junaid naje gidansa sannan na bashi haƙuri kuma ya ce ya yafe min, dan Allah ku yafe min". Ta faɗa tana mai fashe wa da matsanancin kuka.
Nan take tausayin ta ya kama su. Ɗaga ta Zahra ta yi tare da share mata hawaye sannan ta ce. "Ai mu tuntuni muka yafe miki, Allah ma muna masa laifi yana yafe mana shi ne kuma mu ba za mu iya yafe miki ba?, ki kwantar da hankalin ki Zubaida Allah zai baki wani mijin wanda zai tarairaya ki sannan ya so kuyi rayuwar farin ciki na har abada".
Murmushi wanda yafi kuka ciwo Zubaida ta yi sannan ya ce. "Zan so hakan amma hakan ba za ta kasance ba".
Cikin mamaki Zahra ta ce. "Saboda me?".
Nan Zubaida ta amsa da cewa. "Saboda ina da cutar heart disease, a kowane lokaci zan iya mutuwa".
"In sha Allah babu abinda zai same ki". Cewar Sooraj.
Tashi Zubaida ta yi tare da yi musu sallama tace zata tafi. Nan Zahra tace ta zauna ta ci abinci amma sai tace ta ƙoshi. A haka ta bar gidan ba tare da ta taɓa komai ba.
Ajiyan zuciya Zahra ta sauke!, ta ce. "Allah sarki, wallahi ta bani tausayi sosai".
Girgiza kai Sooraj ya yi ya ce. "Allah ya sa muyi kyakkyawar ƙarshe".
Nan Zahra ta amsa da Amin.
Nan Sooraj ya ce. "Mami ta kira ni ta ce Za'a yi taron family gobe". ya faɗa tare da shiga part ɗinsa.
WASHE GARI
Su Zahra suka shirya Tare da twins suka nufi masarauta.
Cikin farij ciki haka tarbe su. Nan Sooraj ya yi mamakin ganin su Miss Lailah, su Umar gaba ɗaya suna wajan. Da sauri Mahmud ya nufi wajan Miss Lailah ya ce. "Oyoyo Grandma nayi missing ɗinki, ina tsaraba ta?".
Murmushi Miss Lailah ta yi ta ce. "Tsarabar ka tana nan kaji na siyo maka mai yawa".
Zeenat kuwa wajan Mami ta tafi tare da zama kan cinyar ta. Da murmushi Mami ta rungume ta.
Su Samira da su Fasma suka shigo da ruwa da lemo sannan suka yi serving kowa murmushi kan fuskokin su. Yayin da Junaid da matarsa Ramlat tare da ɗansu mai suna Yusuf ke zaune murmushi kan fuskarsu.
Bayan an ci a sha haka yi hirar yaushe rabo sannan. Mami ta kalli kowa ta ce. "Dama ba wani abu ne ya sa muka tara ku a nan ba sai saboda jikata Zeenat, ina son a bani ita ina kula da ita amma Sooraj ya ce ba zai bani ita ba".
Dariya kowa ya kwashe da shi inda Sooraj ya ce. "Yanzu Mami saboda Zeenat ki ka kira ni ki ka ce Za'a yi family meeting?".