Sashe 21
Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ɗaya daga cikin ne ya fara kwantar mata da hankali sannan ya ce. "Mu ɗin jami'an ƴan sanda ne kuma ba wani ne ya turo mu ba fa ce Dpo wanda a halin yanzu yana tare da da mijinki da kuma ahalin ki".
Nan take ran Mrs Lailah ta ɓaci. "Me kuma suke buƙata nayi musu, bayan sun riga sun juya min baya tun da daɗewa ".
Ki ya ƙuri ki saurare mu letter ne aka bamu domin mu baki sannan bayan ki karanta an bamu izinin mu tawo da ke garin jigawa". Cewar ɗaya daga cikin police ɗin sannan ya ɗauko letter ɗin tare da miƙa mata. Karɓa ta yi sannan ta zauna tare da karanta letter ɗin tunda farko har ƙarshe.
Sauke ajiyan zuciya ta yi yayin da ta kama letter ɗin tare da yaga wa. Maida kallonta ta yi kansu ta ce. "Ina mahaifin nawa yake, muje gurin nasa".
"A halin yanzj yana garin jigawa ba zai yu muje yanzu ba sai gobe kuma dole sai an sallame ki daga asibitin nan tukun nan zamu iya tafiya da ke". Cewar police ɗin sannan ya samu likita tare da yi masa bayani. Nan likitar ya sanar da shi cewa ba zai yu su basu Mrs Lailah ba har sai da amincewar yarima Sooraj.
********
Washe garin ranar Zubaida ta zo da mahaifinta da mahaifiyar ta gidan yayin da aka tada family meeting kan shirye-shiryen auren Sooraj da Zubaida.
Shi kuwa Junaid ko a jikinsa domin yana da wacce yake so.
Tara jama'ar masarautar mai martaba ya yi yayin da ya sanar da kowa cewar za'a yi gagarumin biki na babban ɗa kuma magajin wannan masarauta. Farin ciki wajan mutane abun sai wanda ya gani. Nan Junaid ya sa aka raba invitation card. Nan labarin auren Yarima Sooraj ya bazu garin Kano.
*********
Suma Amrah ta yi sakamakon raɗaɗi ciwon da dabbar ta ji mata. A hankali ta Buɗe idanuwanta ta ga gari ya yi haske alamun cewa gari ya waye.
***
Zahra da ke kwance yunwa ta addabe ta ce ta miƙe tana mai kalle-kalle.
Chan ta hangi wata dattijuwa tana suya saidai ba ta iya ganin mene ne abin da dattijuwar ke soyawa ba sakamakon ta kasance daga nesa.
Da sauri Zahra ta ƙarasa inda wannan dattijuwa take sallama a bakinta. Jin ba'a amsa sallamar ba ya sa ta ƙokwanto. Basarwa ta yi ta ce. "Mama nawa ne wannan ƙosai".
Murmushi dattijuwar ta yi ta ce. "Ai duk abin da ki ka ci a nan kyauta ce".
Zaro ido waje Zahra ta yi jin cewar kyauta ne ya sa ta baje wa a ƙasa sannan ta sa dattijuwar ta zuba mata ƙosai cikin faranti. Nan Zahra ta shiga cin wannan ƙosan saida ta ci mai isarta sannan ta dubi dattijuwar ta ce. "Ina ruwa yake?". Nan dattijuwar ta ɗauko mata ruwa wanda ke cikin ƙwarya sannan ta bawa Zahra. Karɓa Zahra ta yi tana mai yin bissmillah sannan ta sha ruwan.
Gyatsa Zahra ta yi tare da yi wa Allah godiya. Maida kallonta ta yi kan matar sannan ta ce. "Amma me ya sa ki ke suyan kosai a nan maimakon ki je cikin mutane sai kin fi samun kuɗi".
Murmushi dattijuwar ta yi ta ce. "Ai ni ba mutum ba ce kamar kowa, wannan ma ba ƙosai ba ne a idon ki kawai yake ƙosai".
Binta da kallo Zahra ta yi ta ce. "Me ki ke nufi? Yaushe ki ka fara suyan ma ƙosan a nan?".
Amsa matar ta ba ta da cewa. *Ba yanzu na fara ba domin yanzu a ƙalla na kai shekaru ɗari takwas ina suya kuma ƴan uwa suna siya, a kaff cikin mutanen mu ni kaɗai aka fi son suyarta domin nafi kowa iya wa".
Dariya Zahra ta kwashe da shi sannan ta ce. "Keda baki wuce sa'ar mahaifiyata ba shi ne za ki ce wani shekarun ki dari takwas sai kace a tatsuniya".
Murmushi matar ta yi ta ce. "Shi ya sa na ce da ke ni ɗin ba kamar ku nake ba domin ni ɗin aljana ce mutum ba".
Zaro idanuwa waje Zahra ta yi ta ce. "Na banu, kenen hakan yana nufin wannan ba ƙosai ba ne. Faɗa min mene ne waɗan nan abubuwan".
Girgiza kai matar ta yi sannan ta rikiɗa ƙosan ya koma asalin kashin ƙadangaru yayin da ruwan kuma ya kasance na kwata.
Nan take Zahra ta fara kwarara amai.
MANAGE PAGE PLEASE🙏🙏🙏🙏
KADA KU MANTA DA LIKE, COMMENTS, AND SHARE FISABILILLAH 🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏
ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞💞
ZINARIYAR JAJIRTATTU
بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!
*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎
*BOOK 2*
PAGE 8️⃣1️⃣▶️8️⃣2️⃣
_________________________
Babu abinda Zahra ke faman yi sai amai yayin da hawaye suka yi shaɓe-shaɓe kan fuskarta.
"Wallahi Allah ya isa na tsakani na da ke, muguwa azzaluma. Ta ya za ki bani kashin ƙadangaru a matsayin ƙosai, wallahi ba zan yafe miki ba". Cewar Zahra yayin da gefe ɗaya zuciyarta sai tashi yake.
Murmushi matar ta yi ta ce. "Ai bani na gayyace ki ba, ke ki ka kawo kanki da kanki, ki ka ce kina son na zuba miki. Ni kuma dana ga hakan ya sa na zuba miki". Sannan ta kara da cewa. "Yayin dad'i ko?, shin na ƙaro miki ne?".
Nan take Zahra ta ji kamar ta rotsa wa matar dutse a kai saboda takaici. A halin yanzu Zahra ji take tamkar zuciyarta zata fashe.
Mike wa tsaye Zahra ta yi ta ce. "Allah ya kiyaye na ci wannan ƙazantar, ɗazun ma na ci ne kawai saboda na ɗauka ƙosai ne kuma na ɗauka ke mutum ce. Amma ki ka yaudare ni da ƙosai. Ashe ƙazanta ce".
Nan take ran matar ya ɓaci. A fusa ce ta barar da komai na wajan tana huci ta ce. "Abincin namu ki ke kira da ƙazanta tunda aka ne to dole ne saikin cinye wannan kashin ƙadangaru tas".
Zaro idanuwa waje Zahra ta yi ta ce. "Ina ci ta gaigawaye ni, ina ci mai tatsine ta dawo duniya".
Jin hakan ya sa matar ta buga tafi. Nan take wasu tsofaffin matan suka bayyana tare da igiyoyi a hannun su.
Da sauri Zahra ta ja da baya tare da nuna su ta ce. "Mene ne ku ke shirin aikata wa?".
Nan take wasu daga cikin su suka kama hannun Zahra tare da janyo ta sannan suka ɗaure ta a jikin bishiya.
Dariya matar ta kwashe da shi sannan ta ce. "Ba abincin mu ki ke kira da ƙazanta ba, to zamu ga ta yadda za ki kiɓuce mana". Matar ta faɗa tana mai ɗaukar kashin ƙadangaru.
Taɓe baki Zahra ta yi kamar za ta yi kuka ta ce. "Aba fisabillillahi dan Allah kada kiyi min aka wallahi zan mutu idan naci wannan, kinji ƙawalliya romon jaɓa".,
Dariya matar ta yi ta ce. "Babu abin da za ki ce domin nima ƴar uwata daɗin baki ta yi min harta tafi duniyar ku, har yau ba ta sake dawo wa ba, yanzu a kalla kwanaki ashirin".
Kallonta Zahra ta yi ta ce. "Aba ƙawalliya romon jaɓa kwanaki ashirin ai ba yawa za ta dawo dan Allah ki sa su kunce ni".
A fusa ce matar ta ce. "Ba ina nufin kwanaki ashirin ba irin naku a namu duniyar shi ne kwanaku ashirin amma a wajan ku ina nufin shekaru ashirin".
Zaro idanuwa waje Zahra ta yi ta ce. "Kambala'i shekaru ashirin, chabb gaskiya ta daɗe kamm".
Nan take wani dabara ya faɗo wa Zahra. Nan ta saki murmushi sannan ta ce. "Ohhh wai kina nufin dama gurasa ƙawar ki ce?".
Kallonta matar ta yi ta ce. "Ba gurasa ba ne sunanta, sunanta Farira ita ɗin ƙanwata ce".
Shiru Zahra ta yi cikin ranta ta ce. "Ashe Farira ne sunanta". Ɗago da kanta Zahra ta yi ta ce. "Ƙwarai kuwa na san Farira sosai a birni mun haɗu da ita yanzu aka ma ita ce ta aiko ni izuwa gare ki".
Saki fuskarta matar ta yi murmushi ɗauke kan fuskarta ta ce. "Da gaske ki ke?, kina nufin kin haɗu da Farira?, amma ta ya ya?".
Murmushi Zahra ta yi ta ce. "Ki fara sakawa a kunce ni tukun saina faɗa miki".
Nan dattijuwar ta kunce ta yayin da tsofaffin matan suka ɓace.
***********************
Waige-waige Amrah ta fara yi tare da miƙe wa tsaye, sannan ta kai hannunta kan gurin da ta ji ciwo nan ta ga gurin ya ɓace. Mamaki ne ya kamata . Kawar da kanta ta yi tare da basar da kanta sannan ta cigaba da tafiya.
Tafiya ta yi mai nisan gaske sannan ta samu guri ta zauna. Waige-waige ta soma yi amma ba ga komai ba. Chan ta hangi wani dutse mai suffar mutum tare da ido yana zubda hawaye.
Miƙe wa tsaye ta yi mamaki ɗauke kan fuskarta sannan ta nufi inda wannan dutsen yake. Da mamaki ta ke bin dutsen da kallo sannan ta ce da dutsen. "Me ya sa ka ke yin kuka?, dama dutse yana motsi ne?".
Da mamaki kuwa ta ga dutsen ya fara magana kamar haka. "Eh ina motsi ni ɗin na kasance aljanin ruwa ne shi ne na aikata laifi a ka maida ni dutse. Idan da a ce za ki iya taimako na ki tura ni izuwa cikin ruwa, da nayi farin ciki sosai kuma kema zan taimaka miki, wajan neman abin da ki ka zo nema".
Girgiza kai Amrah ta yi ta ce. "Tom zan taimaka maka, amma ta ya ya ne zan iya ɗaukar ka bayan kai babba ne, kuma a wane ruwan ne zan saka ka na kasa gane wa".
Amsa dutsen ya bata da cewar. "Ba ɗauka na za ki yi ba, tura ni za ki yi sannan sai mu bi hanyar da take kallon dama, ki cigaba da tura ni, in mu zo wajan ke da kanki za ki gani".
Girgiza kai Amrah ta yi. Kamar yadda ya buƙata aka ta shiga tura wannan dutsen da iya ƙarfin ta. Yayin da ta bi hanyar dama kamar yadda dutsen ya ce.