← Book details Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 65

Sashe 46

Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nan ta ɗago da kanta daga cikin bargon. Nan take gaban Sooraj ya yanke ya faɗi!, da sauri ya ja da baya. Take hankalin sa ya yi mugun tashi z ganin yadda fuskar Zahra ta kumbura ta yi jaa alamun kuka tayi".

Da sauri ya isa inda take sannan ya fara share mata hawayenta ya ce. "Na shiga uku dan Allah kiyi haƙuri, ni kaina bada son raina na mare ki ba, I'm so sorry please, ba zan sake marinki ba kinji".

Saurin ture hannunsa Zahra ta yi ta ce. "Kada ka ƙara taɓa ni, ka fita ka ƙyale ni, yau na gama tabbatar da maganar da ka faɗa cewar baka so na, wallahi ka bani mamaki, kuma Allah sai ya yi mana hisabi..... Da sauri ya haɗe bakinsa da nata guri guda wanda ya sanya Zahra shiru ba tsammani.

Sauri take domin ta cire bakinta daga nasa amma hakan ya citira. Nan take ta fashe da wani marayan kuka. Ganin hakan ya sa Sooraj sakin leɓenta. Riƙe leɓenta Zahra ta yi ganin yadda yake mata zafi da raɗaɗi ya sanya ta faɗi. "Allah ya isa na wallahi mugu kawai, kuma wallahi saina faɗa wa Mami abin da kayi min tun da kai ka zama abinda Malam ya ana ni faɗa".

Sooraj kuwa bai san sanda ya fashe da dariya ba ganin yadda ta jigata. Girgiza kai kawai ya yi ya ce. "Kin san Allah, idan baki min shiru ba sai na zo na yi miki abinda ya fi hakan".

Jin hakan ya sa Zahra ta yi gumm kamar mutuwa ta gifta.

Murmushi ya yi ya ce. "Good girl ashe dai kina jin magana, yanzu na gano lagwan ki, duk sanda ki ka min abu ba daidai ba ta wannan hanyar zan bi na dinga koya miki hankali".

Haɗe rai Zahra ta yi ta ce. "Ai wallahi ba isa ba, ko ka manta wacece ni?".

Murmushi Sooraj ya yi tare da ƙoƙarin yowa kanta. Ganin hakan ya sa Zahra ta buga tsalle kana ta shige banɗaki ta ƙulle. Dariya ya kwashe da shi ya ce. "Haka ce bakya ji". Ya faɗa tare da barin ɗakin.

Jin cewa ya fita ya sanya Zahra fito da daga banɗaki tana mai sauke ajiyan zuciya ta ce. "Haka kurum na zauna ka cire min leɓe ka cuce ni a banza. Ni wallahi ƙyanƙyami ma nake ji, aikin banza kawai". Ta faɗa tare da koma wa toilet ta ɗauki brush domin wanke bakinta.

__________________________
"Wai ni kamm Junaid yaushe za ka kawo min suraka gidan nan?, kai ma ya kamata a ce kayi aure fa". Cewar Mami.

Murmushi Junaid ya yi ya ce. "Mami kenen, ai ni ban shirya ba yanzu sai dai nan gaba kamm, dan yanzu wacce nake so karatu take yi, sai ta kammala tukun zan kawo ki ganta". Ya faɗa tare da miƙe wa ya ce. "Ni yanzu zan je na kwanta zuwa safiyya zamu yi magana".

"Toh mu kwana lafiya". Cewar Mami. Nan Junaid ya amsa da "Ameen".

Sannan ya fita daga cikin ɗakin ta. Shiru Mami ta ɗan yi na wasu lokacin domin a fuskar Junaid samm babu walwala ta fuskanci cewar kamar yana cikin damuwa. Basar wa ta yi kana ta fara shirye-shiryen bacci.

______
Washe Gari
Tunda gari ya waye Zubaida take ta faman amai babu gaggauta wa, inda hankalin Sooraj ya bi ya tashi. Ya yi da ita su je asibiti a duba ta, amma samm Zubaida taƙi amince wa. Ganin hakan ya sa ya buƙaci Zahra ta zo ta taimaka mata wajan gyara wa Zubaida part ɗin ta.

Girgiza kai Zahra ta yi jin wani irin rainin hankalin da haka zo mata da shi. "Lallai ma, wato ni ce zan je na gyara mata ɗakin ta, gani ƴar aiki ko?". Kallonsa ta yi ta ce. "Ai ba sunana saratu ba balle ka ce naje na gyara mata ɗaki, ita ta san me ke damunta, babu ruwa na da abin da ya shafe ta, kowa ya kama kansa".

Roƙon ta Sooraj ya shiga yi, yayin da Zahra ta ce wallahi ba za ta yi ba. Babu yadda ya iya haka ya haƙura ya koma part ɗin Zubaida. Kallonta ya yi nan ya ji ta bashi tausayi, ko ba komai ita ɗin ƴar ƙanin mar martaba ce. Dubanta ya yi ya ce. "Sannu kinji bari naje na kira a gida a kawo min kayan aiki na in ya so ni da kaina na duba ki".
Girgiza kai Zubaida ta yi ta ce. "A'a kada ka damu zai tsaya, na sha wani maganin tsaida amai in sha Allah zai tafi, ina tunanin abincin da na ci jiya ne ya ɓata min ciki, amma komai zai yi sauƙi".

Shiru kawai Sooraj ya yi domin baya tunanin wannan amai da Zubaida ke yi na abinci ne. Fita ya yi ya bar mata ɗakin.

Bayan fitar Sooraj Zahra ta shigo cikin ɗakin kana ta bita da kallo. Girgiza kai Zahra ta yi ta ce. "Duniya rumfar kara, gaskiya duniya ta zo ƙarshe, wai a ce matar aure da cikin wani a jikinta ba na mijinta ba, tirrr da irin wannan ƙazamar rayuwar, ke yanzu ya za ki yi idan ya gano ina ɗauke da cikin wani a jikin ki?".

Kallonta Zubaida ta yi cikin raunatacciyar murya ta ce. "Dan Allah Zahra kada ki faɗa wa kowa please, na san ma babu wanda za ki faɗa wa".

Taɓe baki Zahra ta yi ta ce. "Toh idan ma na faɗa ribar me hakan za ta haifar mun?, ni yanzu zuwa nayi na ɗan taimaka miki wajan ƙimtsa jikin ki, bawai da zuwa nayi na miki gyara ba, atohh dan ba ni na aike ki ba, ke ki ka kai kanki da kanki inda haka manna miki ciki, gashi an barki da wahala, shi wanda ya miki ɗin ma yana chan hankalinsa kwance. Tukun na ma wai waye ya miki wannan cikin faɗa min?".

Fashe wa da kuka Zubaida ta yi ta ce. "Wallahi ba da san raina nayi zina ba, tirsasa min a kayi, raping ɗina ya yi, gashi ya cuce ni ya gama da ni". Ta faɗa tana mai fashe wa da kuka.

Nan jikin Zahra ya yi sanyi. Dubanta ta yi ta ce. "Wane ne?, ni kuma zan taimaka miki wajan ganin an hukunta shi".

Share hawayenta Zubaida ta yi ta ce. "Shi ɗin ya kasance........ Maganarta ne ya tsaya sakamakon ringing da wayarta ke yi. Ɗaukar wayar ta yi nan ta ga number Mami a kai. Ɗaga wa ta yi tare da kara wa a kunnenta ta ce. "Hello Mami ina kwana".

Daga ɗayan ɓangaren Mami ta ce. "Lafiya kalau ƴata, yanzu Sooraj ya kira ni yake sanar min cewa wai baki da lafiya".

"Eh wallahi Mami amai nake yi tun da safe". Cewar Zubaida.

"Yanzu zan tawo in sha Allah me ki ke son na dafa miki kici?".

Girgiza kai Zubaida ta yi kamar tana gabanta ta ce. "A'a Mami ba sai kin zo na, na fara jin sauƙi kuma gashi Zahra tana tare da ni".

Nan Mami ta buƙaci Zubaida ta bawa Zahra waya. Nan ta bawa Zahra wayar yayin da suka taɓa hira kana daga bisani ta ce wa Zahra ta kular mata da Zubaida daga ƙarshe ta katse wayar.

Miƙe wa Zahra ta yi ta ce. "Bara naje na haɗa abincin karin kumallo ina nan dawo wa". Ta faɗa tare da fita daga part ɗin ta.

ALƘALAMIN
A'ISHA MB
ZINARIYAR JAJIRTATTU
[8/21, 8:01 AM] AYEESHER MB💞💞💞: 🔥KUNDIN CINIKAYYA🌍

A’ISHA M.B 💞
BOOK 2 – Page
1️⃣1️⃣2➡️1️⃣1️⃣3️⃣

Zahra tana barin ɗakin Zubaida da niyyar had’a karin kumallo, zuciyarta cike da rudani da tausayin abinda ta ji. “Ya Allah, idan har Zubaida bata da laifi, ka bayyana gaskiya,” ta furta a hankali yayin da take tafiya.

A bangaren Sooraj kuwa, yana zaune a cikin parlour yana ɗan karanta wani rubutu akan wayarsa. Amma zuciyarsa bata zaune ba. Tunanin marin da ya yi wa Zahra ya shiga birkice masa kwakwalwa. "Ko da tayi laifi, bai kamata na mareta ba. me ya same ni haka?" Ya furta a hankali yana jin tsoron abinda zai iya biyo baya.

Zubaida na kwance a kan gado, hawaye na zubo mata. Kalmar da Zahra ta faɗa na ci gaba da ɗinbin zuciyarta – “Mutum da auren sa amma yana ɗauke da cikin shege?”

“Ya Allah, idan aka gano gaskiya me zan ce? Me zai hana su kore ni ko su...?” Ta fashe da kuka. Nan take ta yanke shawarar cewa muddin tana numfashi, dole ta nemo wanda ya ci amanarta domin ta samu mafita ko 'yanci.

Na take zuciyarta ta yanke mata hukunci
"Dole na faɗa wa Zahra komai, ita kaɗai nake jin zata iya taimaka min".

Da Zahra ta gama, ta jera abincin a faranti sannan ta nufi part ɗin Zubaida. Amma sai ta tsaya a ƙofar ɗakin kafin ta shiga.

Zubaida na jin shigowar ta ta ce cikin rauni,
“Zahra, don Allah zo ki zauna, akwai abu mai muhimmanci da nake son faɗa miki.”

Zahra ta ƙarasa cikin ɗakin a hankali, tana kallon Zubaida da idon tausayi.
“Me ke faruwa?". Zahra ta tambaya cikin dakiya.

Zubaida ta lumshe ido sannan ta ce.
“Wanda ya yi min hakan ba wani bane illa...”

Nan ta dube ta ta ce . "Wai wa?". Sai a lokacin Zahra ta lura Sooraj ya shigo cikin ɗakin. Da sauri suka basar da maganar. Kallonsu Sooraj ya yi da idon zargi ya ce. "Wai me ku ke faɗa ne?".

"Bakomai". Zahra ta furta.

WASHE GARIN RANAR .
Kai tsaye Zahra ɗakin Sooraj ta nufa domin ta gyara kasancewar jiha Mami ta faɗa mata ta yi hakan.
Dakin Sooraj tamkar dakin sarki ne, komai yalwa, tsafta, da tsari. Fararen tiles masu sheƙi, bango mai walkiya, gado mai girma da siliki, sai sanyi da ƙanshi na royal vanilla.

Zahra ta shigo a hankali hannunta rike da cleaning rag, tana sanye da doguwar riga mara ado. Fuskar ta a lumshashe cikin tunani da rashin kwanciyar hankali. Bata saba zuwa cikin ɗakin ba – sai yau. Amma zuciyarta ta cika da raɗaɗin da ba ta fahimta ba.

Tana goge mirror da nutsuwa, sai idonta ya sauka kan wayar infinix mai launi blue wayar Zubaida. Tana gefen madubi, kamar an aje ta a gaggauce.
Chapter 46 · 0% Book details