← Book details Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 65

Sashe 10

Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin masarautar su ya shiga ba tare da ya kalli kowa ba ya shiga part ɗin sa tare da ɗauko maƙullin da ke cikin littafn da Mrs Lailah ta bashi tareda shi littafin sannan ya fito daga ɗakin. Nan ya ci karo da Mami da kuma mai martaba. Kallonsa Mami ta yi ta ce. "Ina Zahra take fatan babu abin da ya same ta?".

Kallon Mami Sooraj ya yi farin ciki lulluɓe kan fuskar shi ya ce. "Mami kin san wace ce Zahra?, tana ɗaya daga cikin yaran Mrs Lailah".

Zaro idanuwa waje Mami ta yi cikin farin ciki da jin dad'i ta ce. "Kana nufin Zahra ƴar Lailah ce? Alhmadullihi rabbil alamin!, Gaskiya nayi farin ciki sosai da jin wannan maganar, ban taɓa kawo wa a raina cewa Zahra ƴar Mrs Lailah ba ce, wannan wane irin abun al'ajabi ne".

Kallon ta Sooraj ya yi. "Yanzu aka tana cikin daji ita da ƴan uwanta, kinga su kuwa, kammaninsu ya ɓaci ba za ki iya taɓa gane su ba saida ƙwayar idanuwansu". Yanzu aka zan kai musu wannan littafin ne inda za su gano dukiyar mahaifiyar su sa kuma hujjojin da suke ciki".

Cikin farin ciki mai martaba ya saka masa albarka sannan ya yi masa addu'ar neman tsari daga mutum ko aljan sannan daga bisani ya fice daga gidan.

Duk abin da suka ce a kunnen Gimbiya saratu da talatu wanda suke manne jikin gini kamar wasu chewgum.

Kallon juna suka yi sannan suka shiga cikin part ɗin su. "Wai me suke nufi ne, naji ana maganar Zahra ƴar Mrs Lailah ce. Ba Mrs Lailah ba ce aka ce tana safaran mata shekaru baya da suka gabata wacce aka ce ta silarta yara sun mutu ba, kuma an ce tana da kuɗi sosai domin tana da kamfanunuwa a ƙalla guda goma a faɗin duniya kuma ta mallaki gidaje da estate ko ba ita ba ce". Cewar Talatu.

Amsa Gimbiya Saratu ta ba ta da cewa. "Ƙwarai da gaske ita ce nan ba wani ba nayi mamaki da na ga an ce Zahra ƴarta ce. Koma dai mene ne idan ta yi tsami zamu ji.

********
Ɓangaren Sooraj kuwa bai ɗauke shi lokaci mai yawa ba ya isa inda suke sannan ya miƙa wa Zahra littafin da maƙullin.

Kallon bangon littafin suka yi suka ga hoton daji da dabbobi a ciki. Yayin da a jikin littafin aka rubuta cewa. "Wannan ba gamagarin littafin ba ne da kowa zai iya karanta wa, iya ƴan uku ne kaɗai za su iya karanta wannan littafin kuma su ne yaran Mrs Lailah.

Ajiyan zuciya gaba suka sauke yayin da Safira ta ce. "Kenen iya mu uku ne kawai za mu iya shiga cikin wannan dajin, gaskiya ni tsoro nake ji hanya zan iya kuwa?".

Kallonta Zahra ta yi ta ce. "In ba za ki iya ba, ba dole ba ne, ni na shirya wa ko wane irin chakwakiyar da za mu fuskanta tun da ku kuna da baiwa za ku taimaka mana dan aka dole muje wannan dajin domin kankaro kima da darajar mahaifiyar mu a wajan mutane, idan kuwa bamu yi hakan ba to sam mu ɗin ba yaranta ba ne ba, dan aka dole mu shirya domin zamu fuskanci nasara da kuma faɗuwa da kuma mutuwa". Nan take su ukun suka haɗa baki wajan faɗin. "A shirye muke domin fuskantar kowace irin kalubale indai a kan mahaifiyar mu ne to babu abinda ba za mu iya ba".

*KUYI HAKURI DA JINA SHIRU TSAWON KWANAKI WAYATA CE TA SAMU MATSALA GABA ƊAYA AMMA ZAMU CIGABA IN SHA ALLAHU🙏🙏🙏🙏🙏

LIKE, COMMENTS, AND SHARE FISABILILLAH 🙏

ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞💞
ZINARIYAR JAJIRTATTU

بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎

*BOOK 2*
PAGE 6️⃣7️⃣▶️6️⃣8️⃣

Nan take suka haɗa hannayensu guri ɗaya tare da damƙe su.

Murmushi Aliyu ya yi sannan ya ce. "Yanzu tun da an samu littafin da maƙullin dajin ne kuma ya rage mana mu nemo inda yake".

"Aka ne, maganar gaskiya bai kamata mu cigaba da tsayuwa a nan ba kamata ai a ce mun fara neman inda dajin yake". Umar ya faɗa yana mai kallon su baki ɗaya.

Kallon su Safira ta yi ta ce. "Amma na shiga ƙoƙanto!".

Kallonta suka yi baki ɗaya suka haɗa baki wajan faɗin. "Wane ƙoƙanto kuma?".

Amsa ta ba su da cewa. "Me ya sa mahaifiyar mu ta kai dukiyarta cikin dajin?, sannan mene ne alaqar ta da wannan dajin?, ta ya ya za'a ce iya mu kaɗai za mu iya shiga cikin wannan dajin bayan mu babu wani da zai shiga, toh wane sirri ne a cikin dajin da zai kasance iya mu kaɗai ne za mu iya shiga?, shin akwai wani abun cutarwa ne a ciki ko kuwa akwai wani abun al'ajabi wanda yake faruwa ga mutum idan ya shiga?, tabbas wannan ba iya kacin gaskiyar al'amarin ba ne dole akwai wani sirrin da mahaifiyar mu ta ɓoye ba ta sanar da mu ba".

Kallon ta Zahra ta yi ta ce. "Kamar ya wani sirri?, ki ka sani ko ta yi hakan ne saboda waɗan da za su yi mata zangon ƙasa su kwace dukiyarta?, ina tunanin ta yi hakan ne kawai saboda kare dukiyarta, sannan kuma daga baya mu kuma muje mu kwashe su".

Girgiza kai Safira ta yi ta ce. "A'a wannan ba gaskiya ba ne, tabbas an ɓoye mana wata gaskiya, ina tunanin a wannan abun akwai lauje cikin naɗi".

Kallon su Umar ya yi ya ce. "Koma dai mene ne ya biyo baya, domin a halin yanzu bamu da lokacin ɓatawa, idan ma so ki ke ki samu bayanai dangane da dajin sai ki bari idan kin haɗu da mahaifiyar ta ku sai ki tambaye ta, mu da ki ke tambaya babu wanda zai iya baki amsa domin bamu san komai ba dangane da wannan dajin". Ya ƙarashe maganar yana mai kallon Safira.

Tsaki Zahra ta buga sannan ta ce. "Malam Umar ka rabu da ƴar iyayi kawai, neman abin fakewa take shi ne take wani cewa akwai wani sirri, wane sirri ne in ba munafurci irin naki ba. Ni fa na tsani iyayi, idan kin san ba za ki iya zuwa ba ai ba'a yi miki dole saikin je ba ko ana dole ne?".

Tsaki Safira ta ja ta ce. "Hmm mutum baka kula shi ba amma lallai saiya shiga harkar ka sai kace dole. Ni fa kinga ni nan bani da lokacin da zan tsaya ina musayar yawu da ke, domin idan aka kalle ni, aka kalle ki an sa class ɗin mu ba ɗaya ba domin ni nafi ƙarfin tunanin ki yarinya, you are just a baby okay".

Dariya Zahra ta kwashe da shi sannan ta ce. "Allah ko?, to sannu baturiya, sai faman cewa ki ke class ɗin mu ba ɗaya ba amma kuma ciki ɗaya muka fito kuma gaba ɗaya ku biyun nan na riga ku zuwa duniya dan aka ko kina so, ko bakya so dole ki girmama ni domin na riga ki shaƙar iskar duniya".

Girgiza kai Sooraj ya yi ya ce. "Wai ke Zahra bakin ki baya taɓa mutuwa ne wai?, gaba ɗaya na rasa mene ne abin da ke damunki, mu muna nan muna ta yadda za'a dawo da hujjoji ku kuma kuna nan kuna shirme, wallahi idan baku yi min shiru ba, gaba ɗaya zan ɗaure mu na zane ku a nan wajan, iskanci kawai".

"Oho wallahi na gani na bari ƙwalelen agalawa, babu yacce aka iya da mu". Cewar Zahra tana mai turo baki gaba.

Tafa hannu Aliyu ya yi yana mai sakin dariya ya ce. "Wai ke Zahra baki da wani baiwa ne sai tada fitina da yin masifa?, sauran ƴan uwan naki sunce suna da baiwa amma ke na rasa gane wace iriyar baiwa Allah ya baki aka, duk kin bi kin cika mu da surutu. Indai wannan shi ne baiwar ta ki to samm ba ta yi ba".

Takowa Zahra ta yi ta nufi inda Aliyu yake ta ce. "Kai dan sanda banason shishigi da ƙwala kai a faranti, ni ba waccan Safira ko me take da suna bace, idan kayi min abin da bai yi wa raina dad'i ba sai dai kaji bugu a bakin ka. Toh ni dai na faɗa maka gargaɗi nake baka ba shawara ba".

Ji suka yi an ƙwallah wata razananniyar ƙara mai matuƙar firgitarwa!. Nan take gaba dayansu suka toshe kunnuwansu.

Kallon juna suka yi sannan Umar ya ce. "Daga ina wannan ƙara take fitowa?".

Amsa Amrah ta bashi da cewa. "Ina tunanin daga chan wajan ne". Nan take Amrah ta fara bin hanyar inda suke jiyo ƙara, yayin da su kuma suka mara mata baya.

Chan suka hangi wata bishiyar kuka mai matuƙar tsayin da kuma girma. Yayin da kuma bayanta rijiya ne mai matuƙar zurfin gaske, wanda koda wasa ba za ka iya gano ƙarshen ta.

Ƙarasawa inda rijiyar take suka yi sannan Zahra ta dubi bangon littafin da ke hannunta. "Tabbas ga zanen rijiya a nan, ina fa tunanin nan ne dajin da ake nema, to ta ya ya zamu shiga cikin wannan rijiyar mu da ba kifaye ba kuma harta kai mu cikin daji?, gashi naga ma rijiyar babu ruwa ko ɗigo a ciki".

Kallon juna suka yi yayin da kowa ya shiga cikin tunani. Ɗago wa Amrah ta yi hawaye na sauka kan ƙuncinta.

Dubanta suka yi gaba ɗaya sannan suka ce. "Me ya faru?".

Share hawayenta ta yi ta ce. "In dai zamu shiga cikin rijiyar nan to dole wani a cikin mu ukun sai ya mutu".

Zaro idanuwa waje gaba ɗayan su suka yi yayin da gaban kowane su ya yanke ya faɗi!.

"What!, kina nufin a cikin mu ukun nan dole ne wani saiya sadaukar da rayuwar domin ya ceci ta mu rayuwar?". Cewar Safira

Girgiza kai Amrah ta yi ta ce ƙwarai da gaske dole ɗaya daga cikin mu saiya mutu".

Nan take Zahra ta saki wata irin tusa mai shege ƙara. Toshe hancin su gaba ɗaya suka yi suna mai kallon Zahra.
Chapter 10 · 0% Book details