Sashe 28
Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nan take annurin da ke kan fuskar Mrs Lailah ya ɗauke ya koma damuwa. "Da a ce irin halin ka mahaifin ka yake da shi, da ya ji daɗin duniya, Allah sarki Khadijah, tabbas kayo halin mahaifiyarka domin ta kashe mace mai kirkin gaske. Allah ya kai rahama da kwanciyar hankali cikin kabarin ki, tabbas a da Musa ya kasance mutumin kirki, amma daga baya sheɗan ya rinjayi zuciyarsa ya ka sa bambance daidai da kuma ba daidai ba". Maida kallonta ta yi kan Alhaji Abdullahi tare da sakin murmushi ta ce. "Karka damu ni na yafe maka kaji, na yafe maka domin babu abin da kayi min na riga na san cewa duk Musa ne ya tsara komai, sannan kaima Baba ba laifin ka ba ne ba, a lokacin kana cikin fushi ne wanda zai yi wuyq ka iya sauraro na hakan ya sa ka yanke hukunci cikin fushi, dan haka gaba ɗaya na yafe maku, yanzu ahalin za su dawo yadda suke a ɗa".
Nan take farin ciki ya mamaye zuciyar kowannensu
Rungume ta Amrah ta yi cikin farin ciki, yayin da ita ma Safira ta yi hakan. Da sauri Grandma ta isa inda Mrs Lailah take tana mai rungume ƴarta cikin soyayya sannan ta fara kukan farin ciki".
Babu abin da Mrs Lailah ke faman yi sai hawayen farin ciki, yau ga ta ga dangin ta, komai nata ya dawo gare ta saura ƴarta ɗaya wanda take fatan ita ma ta dawo gare ta.
Murmushi Umar ya yi ya ce. "Wannan shi ake kira da, what goes around comes around".
_____
"Ni fa naga kamar matar nan ta ƙaro wulaƙanci, yanzu naga ta daina tsoron mu, ya kamata mu koya mata hankali fa". Cewar Saratu.
Murmushin mugunta Zubaida ta yi ta ce. "Ku bari na fara auran ɗan ta a nan ne zamu gasa mata aya a hannu, dole na siyi maganin mallakar miji ko ta bita zaizai wanda koda mahaifiyar sa ce ta kira shi ba zai saurare ta ba, sai ni kaɗai". Tana kaiwa nan gaba ɗaya suka kwashe da dariya.
Junaid kuwa komai da zubaida ta faɗa ya ji hakan ya sa shi shigowa cikin ɗakin da suke a ciki, sannan ya dubi kowanensu ya ce."Kuji tsorom Allah fa, wannan ba rayuwa bace, wannan abin da ku ke ta faman yi babu inda za ta kaiku sai hallaka, kuna abu tamkar dabbobi".
Kallonsa Gimbiya Saratu ta yi a fusa ce ta tsinka masa mari, tare da buge bakin shi ya ce. "Mu za ka gaya wa kabli da ba'adi?, karka manta ni fa mahaifiyar ka ce, wallahi idan ka yi ƙoƙarin gaya wani ko sarki abin da Zubaida ta faɗa saina lahira ya fika jin dad'i, shege ɗan iska kawai wanda bai san darajar mutane ba, da wani yaron kirkin ne tuni ya haɗa hannu da mahaifiyar sa sun kori wannan Mami da ɗanta daga masarautar nan amma saidai kai babu abin da ka iya sai gulma, wai kai mai gaskiya".
Girgiza kai Junaid ya yi ya ce. "Ba za ku fahimta ba, amma lokaci zai zo da Allah zai kawo wanda zai yi maganin ku, na tabbatar muku cewa lokaci zai zo da za ku durƙusa ku faɗa kan gwiwowin ku kuna neman yafiya daga waɗan da ku ke zalunta".
Da sauri Saratu ta kai hannu za ta ƙara masa mari, ganin hakan ya sa ya fice daga ɗakin.
"Shashasha ai da ka tsaya ka ga yadda ake yin ta, shege munafiki kawai!".
______________
Sooraj kuwa bai tsinci kansa a ko ina ba sai a wani tsibirin da ban.
Buɗe idanuwansa ya yi a hankali yana mai neman ta inda zai hangi Zahra.
Chan ya ganta a durkushe ta yi ruff da ciki. Da sauri ya miƙe tare da nufar inda take.
"Zahra!". Ya ambaci sunanta murya ƙasa.
Da sauri Zahra ta ɗago da idanuwanta tare da ɗora su a kansa. Zabura Zahra ta yi tana mai miƙe wa tsaye ta ce. "Me ya kawo ka wannan dajin Yarima?, ka fara maye ne?, maza kayi gaggawar barin nan kafin so zo idan ba haka ba za ka mutu".
"Babu inda zani, domin na zo nan ne dan tafiya da ke, idan kin ga na bar nan ba tare da ke ba to mutuwa nayi".
Dafe kanta Zahra ta yi a fusa ce ta nufo inda yaje ta ce. "A kan me ya sa za ka zo ka sanya kanka a hatsari saboda ni?, ni ɗin fa iya ƴar aikin ka ce kawai, me ya sa za ka zo, maza ka juya ka bar nan".
Janyo ta Sooraj ya yi jikinta yayin da numfashin sa da nata ke gogan na juna, wani yarr ya ji lokacin da ya janyo ta jikinsa. Kallon cikin idanuwanta ya yi ya ce. "Ke ba iya ƴar aiki na ba ce, ke ɗin kin zamto wani ɓangare na jiki na ne, ke ɗin rayuwata ce Zahra. Ki sani cewa na zo nan ne dan ina mutuwar sonki, kuma koda rayuwata zan bada dan na ceci taki rayuwar zan yi hakan".
Jin maganganun sa ta yi tamkar saukar aradu.
Babu zato ta ji an janye Sooraj daga gare ta tare da ɗaga shi sama.
"Sooraj!". Ta faɗa da matuƙar ƙarfin gaske.
"Kada ku cutar da shi, shi ɗin babu abin da ya yi muku, na roƙe ku ku ƙyale shi".
Dariya halittun suka yi sannan suka ce. "Tunda ya shigo to shima ya zama gawa". Suka faɗa tare da ɗaukar adda da zimmar sare kan Sooraj.
Nan take Zahra ta saki wata razananniyar ƙara! Wanda ya sanya halittun suka yi saurin sakin Sooraj. Tashi sama Zahra ta yi yayin da ta ware hannayenta sannan iska da bishiyoyin da ke cikin wajan.
Cikin wata iriyar murya wanda kamar ba nata ba ta ce. "Na rantse duk wanda ya yi ƙoƙarin taɓa shi saina kashe shi".
Da sauri suka ja da baya yayin da suka gayyato sauran halittun cikin jeji nan take. Kowannensu ya zagaye Zahra da kuma Sooraj.
Mamaki ne ya kama Sooraj ganin yadda Zahra ta sauya lokaci ɗaya. Cikin ransa ya ce. "Tabbas ina ganin baiwar ta ne ya tashi".
A fusa ce ta kurma wani ƙara wanda ya sanya jikin halittun ya soma ƙonewa.
💃💃💃💃💃💃💃💃
KUYI SHARING DOMIN SAMUN UPDATE KAN LOKACI.🤸♀️
KADA KU MANTA DA LIKE, COMMENTS, AND SHARE FISABILILLAH 🙏🙏🙏🙏🙏🙏
بسم الله الرحمن الحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!
*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎
*BOOK 2 PAGE8️⃣8️⃣▶️8️⃣9️⃣
_________________________
Nan take halittun tsibirin suka fara aman wuta domin su ƙona su Zahra. Saidai da mamakin su kuwa suka ga wutar tana juyowa kansu.
Nan take gaba ɗayansu suka rushe suka zama toka.
Jiri ne ya ɗibi Zahra ta faɗi ƙasa.
Da sauri Sooraj ya isa inda take tare da ɗaga ta sannan ya ɗora kanta kan kafaɗarsa. Taɓa jikinta ya yi ya ji ya ɗau zafi sosai, kallon fuskarta ya yi ya ce.
"Kina lafiya Zahra?, babu dai abin da ya same ki ko?". Shiru kawai Zahra ta yi masa domin gaba ki ɗaya ba ta cikin hayyacinta.
Ganin ba za ta iya tafiya ba ya sanya Sooraj ɗaukar ta chakk tamkar ƴartsana sannan ya fara tafiya da ita. Ganin hadari ya soma haɗuwa kamar za'a yi ruwan sama, hakan ya sa ya ƙara saurin tafiyarsa tamkar zai tashi sama.
Haka ya cigaba da tafiya ba tare da ya san inda yake nufa ba, bai ankara ba ya ji an zuge da ruwan sama.
Waige-waige ya soma yi ko zai samu wajan ɓuya har a gama ruwan sama, saidai da mamakin sa kuwa komai da ke cikin wajan ya zama sifili domin ko ganye baka iya gani saboda wajan gaba ɗaya ya washe.
*************
Fito wa Mami ta yi daga cikin ɗakin ta tare da nufa hanyar dining saboda yunwa da ke cinta. Chan ta hangi su Samira su barbazar da abinci a kan dining duk sun ɓata wajen sai ka ce jakuna.
Ƙarasawa wajan Mami ta yi ta dube su ta ce. "Wannan wace iriyar ƙazanta ce, wannan ai almubazaranci ne, ya za'a yi a ce wasu suna nema basu samu ba ku kuna wasa da shi?, wannan fa ba rayuwa bace, idan za ku gyara ku gyara domin wannan halin na za ta haifar muku da ɗa mai ido ba".
Kallon juna Samira da su Fasma suka yi. Nan take suka babbake da dariya, kallon baki da hankali Samira ta bita da shi sannan ta ce.
"Toh ke ina ruwanki?, naga dai ba ke ki ke siyan abinci ba, to hakan bai kamata ya dame ki ba, idan mun gadama mu zubar ko mu bawa karnuka, so ki ja jikin ki ki fice daga wajan nan, kinga dai ɗanku baya bayan ko kuma sarki yana part ɗin sa, dan haka bamu ƙi mu haɗu muyi miki ɗan banzan duka ba".
Girgiza kai Mami ta yi tare da sakin murmushi wanda ya fi kuka ciwo sannan ta dube su ɗaya bayan ɗaya ta ce. "Ina tausaya wa rayuwar ku, ba laifin ku ba ne ba, laifin waɗan da suka haife ku ne. Sannan ni ba zan biye muku ba domin na wuce na tsaya ina musayar yawu da ku saidai nayi da uwayenku".
Tana kaiwa nan ta nufi hanyar kitchen da zimmar dafa abinci. Ba ta ankara ba ta ji an zagayo gabanta a tsaya. Chak Mami ta tsaya tana mai bin Gimbiya Saratu da kallo.
Mamaki ne ya kamata ganin ta a daidai wannan lokaci. "Saratu mene haka kuwa za ki zo ki tare min hanya?, ni kinga bani da lokacin ire-iren waɗan nan abubuwan, kawai ki bani hanya na wuce".
Riƙe ƙugu Gimbiya Saratu ta yi tana mai faɗin. "Kina tunanin dan kin mari talatu shi ne ki ke tunanin nima za ki iya yi min hakan?, wai da me ki ke takama ne?, gaba ɗaya naga kwanan nan idanuwanki sun buɗe kema kin waye, waye ya wayar miki da kai haka?. Wato mu ne bamu iya bada tarbiya ba, da har za ki buɗi baki ki ce ba laifin su Samira ba ne laifin iyayeyen su ne?, hanya matar nan baki fara fita yin karuwan....