Sashe 59
Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Murmushi ya yi, yana jin daɗin yadda Zubaida ke da buɗaɗɗen amana gare shi. Ya shiga cikin album yana kallon hotunanta, hoton ranar auren su, hotonta da mahaifinta, da wasu na al’ada. Yana ta murmushi yana tuna kyawawan lokutan baya.
Sai kawai idanunsa suka tsaya kan wani hoto, hotonta ita da wani mutum, amma fuskar mutumin ba ta bayyana sosai ba. Murmushinsa ya ɗan ɓace, zuciyarsa ta buga.
zuciyar da cike da tambayoyi, Sooraj ya shiga sashen chat. A can ne ya tsinci kansa cikin mamaki. Yawancin sakonninta suna cike da maganganu na batsa, waɗanda suka fi yawa da mutane da yawa.
Ya shiga cikin tattaunawar da ta fi ja masa hankali. wacce take tsakanin ta da Junaid.
Bayan ya duba sakonnin baya, zuciyarsa ta tsinke lokacin da ya ga message daga Junaid yana nuna cewa ta zubar da cikin jikin da ta sa yayi mata ba tare da saninsa ba kuma ta nemi gafarar Sooraj.
Idanunsa suka ƙara kaɗawa, suka yi ja saboda tsananin bacin rai. Hannunsa ya yi sanyi, ya jingina da kujera ya rasa ko ya yi ihu ko ya yi shiru.
Bayan ɗan lokaci na tunani mai nauyi, Sooraj ya ɗauki wayarsa ya kira abokinsa Umar.
Bayan Umar ya ɗaga Sooraj ya ce.
“ Umar, gobe da safe ka zo fada. Muna da magana mai muhimmanci,” ya faɗa cikin muryar da ke nuna ba wasa yake yi ba. Sannan ya katse wayar.
Mamaki ne ya kama Umar ganin irin kiran da Sooraj ya yi masa. Hakan ya sa Umar ya yi tunanin cewa tabbas akwai abinda ke shirin faruwa ko kuwa akwai abinda ke tafiya ba daidai ba.
Bayan haka, Sooraj ya kira Sarki, sannan ya sanar da shi cewa za'a yi meeting gobe. Sannan ya fito ya faɗa wa su Zahra da Zubaida cewa gobe su shirya, za su taru a fada domin tattaunawa.
Kowa ya shiga cikin mamaki . “Wannan wace magana ce haka za a yi?” Cewar Zahra.
Zahra ta shiga tunanin ko akwai wani sabon rikici ne, yayin da Zubaida ta ji wani sanyi ya ratsa jikinta, zuciyarta na bugawa ba tare da ta san dalili ba.
Daren ranar, gidan Sooraj ya kasance cikin yanayi mai ɗauke da shiru. Kowa yana cikin ɗakinsa, amma babu wanda zuciyarsa ke a nutse.
Zahra tana kwance a kan gado, tana juyawa ba tare da ta iya samun barci ba. Tana ta tunanin ko wannan muhimmin taro za'a yi gobe.
A ɗaki dabam, Zubaida ta kasa zama lafiya. Zuciyarta na bugawa da karfi, hannayenta na zufa. Ta san sirrin da take ɓoye wa, sirrin da zai iya rushe rayuwarta gaba ɗaya idan ya bayyana. Ta rika ɗaga wayarta tana duba sakonni, tana share wasu, amma duk da haka tana jin kamar a banza ne.
A masarauta kuwa, bayan kiran wayar Sooraj, Sarki ya shiga mamaki. Bai saba jin muryar Sooraj a cikin irin wannan yanayi mai ɗauke da damuwa ba.
Ya kira Mami, Saratu, da Talatu ya sanar musu cewa gobe akwai taro da dole kowa ya halarta.
Dukansu suka shiga tunanin ko wannan na da alaka da harkokin masarauta ko kuma wani lamari na cikin gida.
Washe Gari a Fada
Da safe masarauta ta cika da motsi fiye da yadda aka saba. Masu gadi suna kai komo, manyan fadawa suna shirin taron da Sarki ya kira. A babban falon fada aka shirya kujeru cikin tsari kujerar Sarki a tsakiya, sannan duk sauran zauren ya kasance a cike da fitilu masu haske.
Su Sooraj sun iso fada da wuri, Sooraj kuwa fuskarsa a ɗaure, yana riƙe da wayar Zubaida a hannunsa. Bayan ‘yan mintuna, Zahra tana ɗan kallonsa da mamaki, tana ƙoƙarin gane dalilin kiran taron. Zubaida kuwa tana ƙoƙarin rufe damuwarta da murmushi.
Bayan su Umar sun shigo cikin nutsuwa, amma a gefensa akwai Amrah, wacce ke sanye da doguwar riga mai launin shuɗi da rawanin kanta. Idon wasu ya faɗa a kanta, suna tambayar a ransu me yasa Umar ya kawo ita.
Sarki ya kalli kowa a falon sannan ya ce da muryarsa mai cike da iko.
"Na kira ku domin jin maganar Sooraj. Yana da wani abu da yake so ya bayyana a gaban masarauta."
Sooraj ya miƙe tsaye, ya yi ajiyar zuciya, sannan ya ce:
"Na kira wannan taro ne saboda an ci amanata. Kuma wanda ya yi hakan yana nan a cikin wannan falon."
Sai ya juya ya kalli Junaid da ke tsaye a gefen falon, yana kallonsa kai tsaye.
"Junaid," in ji Sooraj, "Me yasa zaka ci amanata, ka shiga harkar matata, sannan ka yi lalata da ita har ma da wannan cikin da take dashi yanzu?"
Kallon mamaki ya cika fada Zahra ta rufe baki da hannu, Zubaida kuwa ta durƙusa tana girgiza kai tana hawaye.
Kafin Junaid ya iya cewa komai, Umar ya yi magana.
"Na san duk abin da ya faru. Kuma gaskiya zan faɗa a gaban Sarki. Junaid bashi da laifi babu abin da kuka zarge shi da shi da ya faru.".
Kowa ya juyo yana kallon Umar, ciki har da Sarki da Sooraj.
Nan Sarki ya ce. "Umar, ka bayyana gaskiyar abin da ya faru nan take, saboda wannan magana ba za ta tsaya a rikici kawai ba."
Umar ya gyara zama cikin falon fada, ya dube su Sooraj da Sarki da sauran ‘yan masarauta. Muryarsa ta yi nauyi kamar wanda ya ɗauko wani babban abu daga zuciyarsa.
"Da farko, Sooraj, ka kwantar da hankalinka. Gaskiya tana nan, kuma yau dole ta fito fili. Abin da zan faɗa ba sauƙi bane, amma yana da muhimmanci ka sani."
Ya ɗan ja numfashi sannan ya ci gaba:
"Kwanakin baya, na ga Zubaida tana fita daga masarauta. Na bi ta da kallo har sai na haɗu da Junaid yace min shi ma fita zai yi bayan fitarsu. Wannan abu ya sa na fara tunani a zuciyata, saboda haka na yanke shawarar bin bayan su."
"Na biyo Junaid har suka shiga wani hotel. Bayan sun zauna suna tattaunawa, ni kuma na zauna a gefe ina sauraren duk abin da suke faɗa. Duk maganganun da Zubaida ta yi masa, da yadda Junaid ke nuna damuwa, duk na ji."
Umar ya ɗan yi shiru, kowa a falon ya zurfafa cikin sauraro.
"Bayan na koma gida, na je ɗakin Junaid. Na tambaye shi gaskiyar lamari. Sai ya bani labari cewa, tun suna makaranta, Zubaida ta kasance budurwarsa, suna soyayya. Amma a lokacin sha’awa kawai take ji a gare shi, tana neman ya bata haɗin kai, amma shi ya ƙi bata haɗin kai."
"Ranar birthday ɗinsa, Zubaida ta kawo masa wani special cake a matsayin kyauta. Ya ci, amma daga baya ya fara jin kansa yana juya wa kamar wanda aka yi wa wani abu. Bai san inda kansa yake ba har sai da ya farka ya ga tana kuka tana cewa ya yi mata fyaɗe."
Cikin falon, murmushi mai ɗaci ya bayyana a fuskar Junaid, yayin da idanuwansa suka cika da baƙin ciki.
"Junaid ya rantse min cewa babu abin da ya yi mata. Wannan ya sa na ɗauki mataki na tafi hotel ɗin da aka yi birthday ɗin. Na nemi CCTV footage. Bayan na duba, sai na ga wani abin mamaki."
Umar ya ɗan waiwayo yana kallon kowa da ido.
"Hoton CCTV ya nuna cewa bayan Zubaida ta kawo cake ɗin, wani mutum ya shiga ɗakin bayan ta kwantar da Junaid saboda rashin hayyacinsa. Shi ne ya yi lalata da ita, ba Junaid ba. Bayan mutumin ya fita, ne Junaid ya dawo hayyacinsa, sannan Zubaida ta yi masa sharrin cewa ya yi mata fyaɗe".
A falon, aka ji tsit, sai numfashin mutane kawai ake ji.
Nan Umar ya ce. "Duk da cewar a shari'ar Muslunci indai haka ga mace tayi zina ana da buƙatar hujjoji mutane guda huɗu domin tabbatar da cewa tabbas ta aikata. amma saidai babu wannan huɗun ni ɗaya ne kuma CCTV camera baya ƙarya shi ya bayyana komai. Sannan shi ne asalin gaskiya".
Sooraj ya yi shiru na ɗan lokaci bayan Umar ya gama bayani, numfashinsa yana fita da sauri. Idanunsa sun yi ja, ransa yana tafarfasa.
"Zubaida, duk wannan sharri da kika yi wa Junaid kina sane da irin illar da kika jawo? Kin yi wa mutumin nan barna a suna, kin ƙeta masa martaba! Kin sa ni na zarge shi da abin da bai aikata ba."
Zubaida ta zube a ƙasa tana kuka, hannunta a haɗe tana roƙo.
"Wallahi na yi kuskure, shaiɗan ne ya ruɗar da ni. Ban yi niyyar lalata rayuwar kowa ba. Don Allah ka yafe min Sooraj."
Sooraj ya girgiza kai cikin ɓacin rai
"Yafe miki? Bayan kin sa wani ya sha wahalar abin da bai aikata ba? Yanzu da a ce Umar bai gano gaskiya ba, da har yau muna kallon Junaid a matsayin mai cin amanar aure da kuma masa kallon rashin mutunci. Wannan ba ƙaramin abu bane!"
Zubaida ta ƙara kuka, tana rawar jiki. Amma Sooraj ya miƙe tsaye, muryarsa na nuna ƙarshe.
"Daga yau babu aure tsakanina da ke. Na sake ki saki uku. Ki koma gidanku, ki nemi gafarar Allah da kuma Junaid wanda ki ka yi wa wannan babban sharri."
Ta saki ƙara mai tsuma rai, tare da faɗi ƙasa, yayin da aka ruga aka riƙe ta.
Sooraj ya juyo wurin Junaid, zuciyarsa cike da nadama.
"Junaid, na yi maka babban zargi, na ɗauke ka kamar mai ci amanar aure. Na yanke hukunci a raina ba tare da na bincika ba. Don haka ina roƙon ka, a matsayin ɗan uwa, ka yafe min."
Junaid ya ɗan yi shiru sannan ya ce cikin nutsuwa:
"Na yafe maka Yahya. Abinda ya faru darasi ne ga dukkanmu, cewa dole a binciki gaskiya kafin yanke hukunci sannan ita da taje ta yi zina Allah ya gafarta mata".
Sai Sarki ya yi gyaran murya, yana kallon kowa a falon.
"To, yanzu da gaskiya ta bayyana, dole a yi hukunci bisa shari’ar Musulunci. Zubaida ta yi ƙazafin zina ga wanda bai aikata ba, wanda hukuncin sa a shari’a shi ne bulala tamanin a bainar jama’a. Bayan haka, za a mayar da ita gidan iyayenta. Wannan hukunci zai zama darasi ga duk wanda zai kuskura ya yi irin wannan aiki a cikin masarautar nan."