← Book details Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 65

Sashe 33

Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Share hawayenta ta yi sannan ta ce. "To ka saurare ni kaji, wallahi in ka ga na rabu da kai to mutuwa ce ta yi ajali na, kuma muddin ina da sauran numfashi a duniya ba zan taɓa barin ka auri Zahra ba, saina sa an kashe ta, na sa kaji irin ƙuncin da naji, kuma ko ka ƙi, ko ka so saika aure ni dole. Ita kuma Zahra ni ce nan wacce zan yi ajalinta. Za ka ga ni".

Ta faɗa tare da juyawa da zimmar tafiya. Da sauri ya janyo hannunta sannan ya dubi idanunta ya ce. "Naga so ki ke ki tafi gidan yari, wallahi muddin Zahra ta ji koda ciwon kai ne to ki sani cewa ba zan rabu da ke ba. Ki je ki samu duk wanda za ki samu amma ki sani cewa auren Zahra babu fashi sai anyi, in kuwa ban auri Zahra ba to babu abin da zai sa na aure ki. Ni dama kiyi wa kanki faɗa, ki nemar wa kanki mafita, ki auri mafi alkhairy a gare ki, domin ni ba zan zamo miki alkhairy ba saima hanyar baƙin cikin ki, domin kuwa bana sonki. Wasu sunce ƙiyayya tana iya juyewa ta koma soyayya, amma ni hakan ba zai taɓa faruwa ba domin ƙiyayyar da nake miki ba za ta taɓa gushe wa daga cikin zuciyata ba".

Yana kaiwa nan ya fice daga ɗakin. Yana fita Zubaida ta faɗi tare da fashe wa da matsanaciyar kuka.

Kai tsaye part ɗin Mami ya nufa, yayin da ya tarar Mami ta gama shirya komai. Ɗauka ya yi tare da yi wa Mami sallama sannan ya nufi asibiti. Saida ya ɗauke lokaci mai tsayi kafin daga bisani ya kai asibitin. Nan ya tarar Zahra ta buɗe ido.

Kallonta Sooraj ya yi ya ce. "Zahra kin farka, ga abinci nan Mami ta haɗa miki kici. Girgiza kai kawai Zahra ta yi sannan ta karɓa ta fara ci.

Murmushi Sooraj ya yi ya ce duk da cewa baki da lafiya amma kina iya cin abinci". Ya faɗa yayin da yake ƙara jin kamar ana ƙara masa wutar son Zahra a zuciyar sa.

***********
WASHE GARI
washe garin ranar ta kama Monday yayin da su Miss Lailah suka shirya tsaf domin tafiya kotu.

Kotu suka nufa yayin da jama'a suka taru a ƙofar kotu domin ganin anyi wa Lailah adalci.

Shiga cikin kotu suka yi tare da zama.

Nan court clerk, wato jami'in kotu ya ce. "Kira da murya mai ƙarfi, alkali mai shari'a zai shigo kowa ya miƙe!".

Nan kowa ya miƙe tsaye, shigo wa alkali ya yi, ya zauna a kujerarsa. Nan ya bada umarnin a zauna. Nan kowa na cikin kotun ya zauna.

Nan alkali ya ce. "Za'a ƙara sauraren shari'ar shekarun ashirin da suka gabata a yau tsakanin miss Lailah Abdullahi da kuma Govnor Musa Muhammad. Shin ɓangarori biyu suna nan?".

Nan jami'in kotu ya ce. "Eh suna nan".

Nan alkali ya ce. "Zamu fara da mai ƙara, lauyan mai kara ka shirya?".

"Miƙe wa Safira ta yi ta ce. "Ya mai girma mai shari'a, lauyan ta baya nan amma ni zan maye gurbin sa".

"A matsayin ki na wa?". Cewar alkali. Nan Safira ta bada amsa da cewa. "Ni yarta ce kuma nima fannin doka na karanta. Nan ta nuna takardunta na zama cikakkiyar lauya tare da takarda zama lauya daga body na Nigerian bar association (NBA). sannan kuma tare da nuna rejista ɗin ta na zama memba na wannan kotu.

Nan alkali ya bata damar ta zo ta tsaya domin kare miss Lailah.

Nan alkali ya ce a gabatar da shaidai farko. Nan Alhaji Abdullahi ya fito tare da shiga akwatin sheda sannan haka rantsar da shi.

Nan haka miƙa mai Alqur'ani sannan haka ce ya saka hannun dama kana ya rantse zai faɗi gaskiya kaɗai. Kamar yadda kotu ta buƙata haka Alhaji Abdullahi ya yi rantsuwa.

Nan alkali ya tambaye shi dangane da abin da ya sani game da wannan ƙarar.

Nan Alhaji Abdullahi ya bada bayanin komai dangane da abinda ya faru tsananin shi da Musa da irin mu'amalar da suka yi har izuwa wannan lokaci. Nan lauyan Gov. Musa ya dinga rubutu.

Nan alkali ya tambayi lauyan gov. Musa na cewa yana da tambayoyi.

Nan lauyan gov. Musa ya ce. "Eh mai girma mai shari'a, ina da tambayoyi guda biyu".

Nan alkali ya bashi damar faɗa.

Nan lauyar Gov. Musa ya ce. "Ya kamata a bayyana hujjoji domin tabbatar da maganar da ya faɗa, sannan shi ya kasance mijinta ne zai iya kare ta. Muna buƙatar wani bashi ba".

Objection my Lord. "Wannan mutumin yana ƙoƙarin faɗin cewa miji yana kare matarsa ne, wato yana nufin abin da ya faɗa game da ita ƙarya ce. Kotu tana da damar bawa duk wanda yake da shaida ko da kuwa uwa ce ko uba. A gaban kotu kowa yana da ƴancin faɗin shaida da gaskiya, ba tare da la'akari da ko an san shi ko a'a ba. Koru tana bukatar gaskiya gaskiya fiye da wani abu. Doka ta bawa kowa damar bayyana gaskiyarsa a kotu, ba tare da kowa ya duba ko mutum ɗan gari ne ko ba shi ba".

Nan kotu ta bayar da damar Alhaji Abdullahi ya cigaba. Nan Safira ta ɗauki littafin da miss Lailah rubuta dangane da abubuwan da suka faru tare da miƙa wa alkali. Nan alkali ya karɓa tare da karanta wa. Nan ko ina na kotun ya ɗauki shiru tamkar babu wanda ke a cikin wajan.

Yayin da ta kuma ɗaukar sauran hujjoji tare da karanto shi a gaban kowa da kowa. Bayan wasu lokuta. Alkali ya yi rubutu sannan ya dubi lauya mai kare Gov. Musa ya ce. "Shin kana da abin cewa?".

Girgiza kai lauyan ya yi ya ce. " I have no objection my Lord". Ya faɗa tare da zama kan kujerarsa.

Nan Safira ta ce. "A ƙarƙashin sashe na 375 na dokar laifuffuka ta cirminal code act, yin sharri na iya zama laifi. Idan mutum ya wallafa bayanan ƙarya da sanin cewa ƙarya ne, zai iya fuskantar hukuncin ɗaurin shekara biyu a gidan yari, idan kuma an yi ne da nufi domin ɓata sunan mutum ko kuma ya haifar da tashin hankali, ana iya ƙara tsaurara hukunci. Kisan yara mata yana cikin laifukan da ake hukunta su. Dan haka muna son wannan kotu mai adalci ya hukunta wanda ya yi laifi sannan wanda aka tuhuma a wanke shi".

Nan alkali ya yi rubuce-rubuce sannan ya ce. “Bayan sauraron wanɗan nan hujjoji kotu za ta yanke hukunci a zama na gaba ranar Litinin".

MU HAƊU A PAGE NA GABA🙏🙏🙏🙏

KADA KU MANTA DA LIKE, COMMENTS, AND SHARE FISABILILLAH 🙏🙏🙏🙏🙏🙏

ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞
ZINARIYAR JAJIRTATTU

*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎

*A'ISHA M.B*💞💞

*BOOK 2 PAGE9️⃣4️⃣▶️9️⃣5️⃣*
________________________
Jin hakan da suka ji alkali ya ce ya sanya kowa miƙe wa tare da fita daga cikin kotun.

Ɓangaren Gov. Musa Muhammad kuwa kama shi ƴan sanda suka yi tare da yin waje da shi. Daga nesa ya hangi miss Lailah na ƙoƙarin shiga jikin mota. Wafce jikinsa ya yi daga na ƴan sanda sannan ya nufi inda miss Lailah take tare da faɗa wa kan gwiwowinsa. Da sauri su police suka bi bayansa.

"Dan Allah Lailah ki gafarce ni, na san na aikata babbar kuskure wanda zai yi yuwa ki iya yafe min, ki taimaki wannan bawan Allah, bana son naje kurkuku, nayi muku alƙwarin cewa zan koma mutumin kirki, sannan kuma waɗan da na zalunta na je na nemi gafarar su". Cewar Gov. Musa yayin da hawaye ya hawaye ya wanke kan fuskarsa.

Murmushi wanda ya fi kuka ciwo Miss Lailah ta saki, sannan ta ce. "Shin ka san ahali nawa ne ka sanya cikin ƙunci da baƙin ciki na rayuwa?, ta ina za ka fara neman yafiyar su?, ta kai na?, ko kuwa ta kan yara ashirin da kayi sanadiyar mutuwar su za ka fara neman yafiya?, ka san irin halin da na shiga?, haka na dinga gararanba a titi ina neman taimako, kai a lokacin kana ina?. Kana gida kana jin dad'i, dama abinda ka shuka shi za ka girba. Yanzu ni na yafe maka, toh yara ashirin da kayo sanadiyar mutuwar su sannan ka sanya iyayensu kuka da baƙin ciki kana da tabbacin za su yafe maka?. Ni yanzu bana da ta cewa, aikin kotu ne ta yi wa waɗan da aka zalunta adalci".

Karɓar maganar Alhaji Abdullahi ya yi daga bakin miss Lailah ya ce.

"Kai ɗan siyasa ne, tsaya ka saurare ni, wannan ba magana ba ce ta a yafe maka. Wannan magana ce ta gaskiya, ta damuwa, ta kiraye-kirayen da jama'a ke yi cikin shiru da hawaye. Kana da iko a hannu, kana da kujerar da mutane suka yarda ka zauna a kai domin ka kare su, ma tallafa musu, ka gyara musu rayuwa. Amma me kake yi da wannan ikon?, kana kashe bayin Allah, kana ɓata musu rayuwa, kana safaran yara mata ƙanana, kana sanya su dole domin yin fasiƙanci. Duk domin me?, domin kana da iko a hannu?, ko kuwa domin kujerar da kake kai wacce za ta wuce?. Kai ka sani, dunita ba wurin dauwama bace. Mulki da kuɗi basua taɓa ana mutuwa. Zaka tafi kamar yadda kowa ke tafiya, amma abin tausayi ne idan mutane za su yi murna da mutuwarka saboda zaluncinka a gare su. Shin mene ne amfanin duk hakan?".

Hawaye ne ya soma bin kan ƙuncin Amrah, share hawayenta ta yi sannan ta ce.

"Me ya sa ka kasance haka mara imani?, me ya sa zuciyarka ta tsananta fiye da dutse?. Ka raba uwa da ƴaƴanta tsawon shekaru ashirin, wannan uwa ba ta tsaya ta gama ganin ƴaƴan ta ba, ba ta shayar da su ba, ba ya rungume su ba, ba ta ji muryar su ba, duk saboda kai. Kai da ka ke fa iko na gyara wa amma sai ka zaɓi ka rusa. Wannan zalunci ne da har dabbobi ba su iya aikatawa. Me ka ke nema da hakan?, wane irin zuciya ne da kai da baka tausayin mutane?, wane irin mutum ne kake so duniya ta sani da sunanka".

Sannan ta ƙara da cewa.
Chapter 33 · 0% Book details