← Book details Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 74

Sashe 9

Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ihu ta kurma zata yi magana umma ta gwabe mata baki se kuka da take yi kaman ranta ze fita, kasa shiru tayi tace
"Abba dan Allah karka aura min ya Yusuf wallahi bana son shi"

Abba na kallonta da mamaki yace
"se wa kike so?"

Tace
"Abba hamza yace ze turo iyayenshi in ya dawo daga tafiya don Allah Abba karka aura min yaya Yusuf"
Cikin tsantsar yarinyata take zancen, Abba yace

"Eh lallai wannan ko waye ne ya ɓata min hidayat, aurenki kuwa har Abada ya haramta a gareshi wallahi billahi"

Duk yadda hidayat taso fahimtar da Abba be fahimta ba saboda Yusuf ya riga ya sharewa kanshi Fage, Abba ya riga yayi amanna Yusuf na kaunar ta kuma ba ze cutar da ita ba.

Ganin zata iya birkicewa yasa Abban ma ya yanke za'ayi bukin da na Khausar da saura wata guda in ya so ta karasa secondary É—in a É—akinta.

Hmmm a wata gudan nan mutuwa ne kawai bata yi ba, hidimar gidan babu abunda basu sakar mata ba, ga cin zali, ga muguntar Yusuf, ga auren dake ta matsowa duk duniya kuwa babu wadda ta tsana irin Yusuf.

Hamza ya dawo ya zo gidan sede Abba ya ja mishi federal warning a kanta be hakura ba musamman da yaji wadda Abban ya zaɓa mata, haka ya dinga turo mutane Abba ya ki sauraran su karshe iyayenshi suka ce ko ita ce autar mata ba zasu kara komawa gidan neman mishi aurenta ba.

Rana bata karya ranar Juma'a aka sheda daurin aurenta da Yusuf wadda ya sakata doguwar suma, Seda ta sha jini har Leda biyu sanadiyar bukin nan, se a lokacin kuma Abba ya bar fushin da ya ɗauka da ita me tsanani da be taɓa yi ba.

Kwatanta irin zamanta da Yusuf ɓata lokaci ne, Tsananin azabar Rayuwa, yunwa, matsi, mugunta, musgunawa babu abunda bata fuskanta, ga zina da a kullum take Rokon Allah kar ya sakawa yaran mutane a kan nata yaran, tun tana damuwa har ta dena, kayan ɗakinta da ya fi na khausar kullum suna hanyar gidan da ɗauki ɗaiɗai suka karar da komai na gidan nata.

Ita bata san wani amarci ba se baƙar azabar sex irin na Yusuf, bata yi wata biyar ba ciki ya bayyana nan Yusuf yace bata isa ba shi baya son yara.

Duk yadda ya so ta zubar ki tayi se azabanta ya karu, duka kam har bata san sau nawa ta sha a hannunshi ba, ze daki cikinta har se ya so kashe ta Amma da Allah yayi Usman me zuwa duniya ne Seda ya zo, kan haihuwar Usman Abba ya haÉ—u da kaddarar hatsari inda ya kwanta ciwon da shine yayi ajalinshi, da sana'o'in da take ta samu ta hada mishi abunda ya kamata ita tayi mishi huduba da suna Usman.

Usman na da shekara da watannin da basu wuce uku zuwa biyar ba ta sake samun wani cikin, Yusuf be farga ba seda cikin ya shiga wata biyar, irin dukan da ya mata Seda tayi ta bleeding kaman bazata haife ta ba, da taimakon Allah itama ta haifeta ita ma itace duk wahalar yarinyar uban be san dasu ba, ya kuma yi rantsuwar abincinshi basu da rabo ita kaɗai yake ciyarwa banda yaran. Wallahi ko makiyinta bata mishi fatan rayuwa irin tata. Tunda ta haifi Aisha be sake kusantarta ba se wata rana da ya sha abubuwan shaye shayenshi lokacin Aisha na shekara biyar ya faɗo mata inda kaddarar wannan cikin ya samu, zaginta a kullum yake daga an taɓa ta se ciki..

KOWA YA GA ZABUWA...
(DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

*PAGE 7*

*FREE BOOK*

Abba yayi nadamar hukuncin shi gareta yafi abunda ya fi a kullum se ya zub da hawaye in ya ganta, rashin kula da rashin suturu duk sun haÉ—u sun maidata tsohuwar da bata kai ba, yayi nadamar rashin sauraren ta kuma a kullum in har zata je gareshi ta kan karanci irin rokon gafararta da yake da idanu, shine kaÉ—ai take kalla tayi farin ciki ta kuma buga kirji tana da wani a duniya shima yanzu ya tafi, bango mafi girma a rayuwarta ya zube tas bata da karfin fara wani tubalin bare ta sake gina makamancinshi a rayuwarta...

DAWOWA LABARI

Cikin wani irin yanayi take kukan, kuka ne wadda duk wadda ze kalleta ze san akwai abu mafi girma da ya sameta na rayuwa ganin yadda ko la'akari da jama'ar dake kai kawo bata yi, wata mata ce ta matso ta tare da dafata tace

"baiwar Allah kiyi hakuri! Duk tsanani yana tare da sauki ki duba condition naki it's not good for you da irin wannan kukan da kike"

Kallon matar take da idanun rayuwa daaÉ—i yake miki ni tawa rayuwar bata da sauran anfani banda na yarana, ba tare da tacewa matar kala ba ta mike ta nufi gate tana tafiya kaman iska ze É—auke ta, da Kallo matar ta bita cikin tausayawa duk yadda akayi matarchan tana cikin depression me girma.

Har ta isa gida bata dena zub da hawaye masu zafi ba, a kofar gida ta ga Usman da Aisha zaune da gudu suka zo suka mata oyoyo, tana share hawaye wani na bin wani ta rungumesu itama, cikin sanyin murya tace
"Usman me yasa baku shiga ko wurin Asabe bane kuka zauna a kofar gida tun yamma?"

Aisha tace
"ba mun je ba su Lantana suka koremu wai tunda bamu da gado mu bar musu gida"

Bata sake cewa komai ba, hannunta na rawa ta fiddo key sede ta kasa buɗewa se Usman ne ya karɓa ya buɗe suka shiga, akwai wutar nepa alwala tayo suma duk suka yi cikin karfin hali a zaune haka ta miƙa sallar magrib da isha da ake ta kira.

Bayan sun idar tana jin yaran na azkar sede ita bakinta be iya yayi ba se a zuciya take binsu, bayan sun gama Usman yace
"Mama baki da lafiya ne?"

Aisha ma tace
"Mama kina ta kuka Ko Abba ya biki ya bugeki ne a unguwar da kika je?"

Rungume Aisha tayi ta saki sabon kuka, duk yaran ma se suka soma kuka, da kyar ta dakatar da kanta tace

"Usman, Aisha ina kun san Abbana na gidan umma?"

Aisha tace
"Umman Abbanmu wacce itama take dukanki?"

Lumshe idanu tayi tace
"Aisha ba na hana ki cewa ana dukana ba?"

Shiru yarinyar tayi, se Usman yace
"Abba da be da lafiya mama?"

Kai ta gyaÉ—a tace
"shine yau ya rasu, ya tafi ya barni Æ´aÆ´ana bani da kowa se ku se kuma Allah...."
Ta fashe da wani irin kuka.

Aisha tana shafa bayanta Usman na share mata hawaye, sun jima a haka Kan Aisha tace
"Mama malam yace haramun ne in mutum ya mutu a yi mishi kuka ko Ya Usman?"

Usman yace
"Eh Mama, muma ya ce mana duk hawaye da ze diga daga fuskanka kaman azabar wuta kake karawa wadda ya mutun"

GyaÉ—a kai tayi tace
"Na dena! Na dena kunji?"

Kai suka gyaÉ—a mata tace
"daga yau in kun yi sallah karku manta saka Abbana a Adu'a kun ji?"

Kai suka sake gyaÉ—awa, Usman ya je ya É—auko musu abincin da seda ta girka musu kan ta tafi wurin Abban nata, shi ya zuba musu Aisha ta É—auko cokali sede duk yadda suka yi da Maman tasu ta kasa ci ko kaÉ—an.

Ita kadai ta san irin azabar da take ciki na nakuda, yadda cikinta ke yi kaman ze barka fata ya fito, gumi kawai take HaÉ—awa cikin dauriya irin na wadda ya Rayu cikin azaba ya girma cikin azaba tayi ta zama har suka gama cin abincin tana ta Kallonsu.

Bayan sun gama ta kalli Usman tace
"Usman je ka kiramin Asabe don Allah"

Fita yayi yaje gidan ya dawo ya samu abu kam fa kara tsanani yake don ko buÉ—e idanu se tayi da gaske suke buÉ—uwa, yace
"Mama Su Habiba sun koreni"

Lip ɗin ta dake cikin haƙorinta ta saki da kyar tace
"ka ce su taimakeni nakuda nake yi"

Aisha na rike da Hannunta tana kuka ya fice, Seda ya jima kan ya dawo yana zub da hawayen halin da ya zo ya tarar da maman sun yace
"Mama kowa ya ki zuwa ya taimaka mana, duk korata suka yi Zulai har da cewa ki mutu ma in kin ga dama, Mama ai ba zaki mutu ba ko?"

Kai ta gyaÉ—a cikin dauriya tace
"In shaa Allah, ka fita....ka samo napep don Allah ka kula Abban mama"

Ficewa yayi da gudu, Aisha ta kalla tace
"É—auko jakan baby da na HaÉ—a"

ÆŠaukowa tayi jakan gwanjo ne ta sayo ta HaÉ—a Æ´an abunda baza'a rasa ba, a ciki akwai dubu uku uwar kudin jarinta kenan da dama gawayin zata sake sayowa, ko da Usman ya dawo kan ta samu ta mike Seda tayi da gaske kafafunta sun kasa motsi, da kyar da taimakon Allah da dafa bango ta samu ta fito suka shiga adaidaitan bayan ta saka Usman rufe gidan cikin karfin hali.

Me adaidaitan se Kallonsu yake cikin tausayawa yace
"ko a unguwa babu wadda ze iya raka ki asibiti kan Æ´an uwanki su zo? Yaran nan ai sun yi kananan kai ki haihuwa"

Hawayen da ya zubo mata ta kai hannunta  da shima nauyi yake mata ta share tace
"Bani da kowa se Su se Allah"

Shiru yayi ya ja machine É—in, har suka isa asibitin da anan ne take awo babu wadda ya ce komai, sun sauka yaki karbar kudin haka ya tafi, da taimakon yaran nata suka shiga asibitin sede abun takaici babu wani wadda yayi attempting attending É—inta tunda ba masu kudi bane, tunda ba wasu suka sani ba bare a san su.

Ko da suka samu ta zauna Aisha ce tayi gudu ta rike hannun wata senior nurse da bata kula dasu ba tace
"Aunty mamana zata mutu don Allah ki cire mata babyn nan"
Chapter 9 · 0% Book details