Sashe 50
Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mantawa yayi da yana fushi da Hidayat a take yayi unblocking layinta ya fara kira...
***
"Rashida kiyi hakuri ki bar fushin nan haka kiji wani labari! Tun kwana biyar baya nake son sanar dake sede bamu samu zama ba"
"me zaki gayamin bayan abun takaici da kunyar da kika aikata?"
Dariya sossai hidayat tayi don kwanakin nan walwalanta na daban ne, bata taɓa jin sanyin farin ciki me tafiya da natsuwa me kwantar da hankali ba se a tsakankanin nan, kwarai Raed daban ne cikin maza, dukda baya tare da ita yana kashe ta da soyayyar da bata tunani ko a labari akwai wadda ya kusanto irin tashi.
"Shi wadda kike taya fushin ya ma mance an yi abun yana cikin walwala da kwanciyar hankali ke kina nan kina cin magani"
Da sauri Rashida ta kalleta tace
"ban fahimce ki ba?"
Wuri guda hidayat ta kurawa idanu tace
"Rashida wallahi ban san sa'adda soyayyar Raed tayi mun mugun kamu ba, ban farga ba seda ya furta min, ban kuma tabbatar ba seda ya janye jikinshi daga gareni na kwanaki kusan takwas fasalta miki irin damuwar da na shiga a sannan ɓata lokaci ne, ban hakikance cewa idan babu shi rayuwata tana cikin hatsari ba seda ya fara dafa ni da zazzafar soyayyarsa me narkar da zuciya, Rashida ina me tabbatar miki ban taɓa son abu makamancin soyayyar da nake yiwa Raed a yanzu ba.."
Ihu Rashida ta kurma tana rungumeta cikin farin ciki tace
"kaji min matar nan! Shine kika barni ina nan ina ta fushina ku kuna nan kuna ƙonewa! Zan rama ne"
Dariya kawai hidayat tayi, Rashida zata sake magana wayan hidayat ya ɗauki ƙara, duk idanu suka mayar kai se a lokacin Hidayat ta tuna da ya hamza ma ashe fushi yake da ita tun daga ranar da Raed yayi proposing mata.
Kallon Rashida tayi da idanun ya zan yi dashi tayi, rashida tayi shrugging kafaÉ—a, bata dauka ba kaman yadda be hakura da jera mata kira ba.
Seda ta dawo gida ta É—auki call nashi..
"Hidayat! Kiyi hak'uri"
Tace
"no baka min komai ba"
Yace
"idan da ban yi miki komai ba da baki ƙi ɗaga wayana a ringing na farko ba, na san kuma kina gani"
Shiru tayi mishi, yace
"Hidayat ko wanene dole ne ya shiga damuwa makamancin wadda na shiga idan yaga ana mai barazana akan soyayyarsa, baƙin cikin da nake ciki ya hana in saurare ki, da gaske Raed proposing miki rannan yayi?"
Ajiyar zuciya ta sauke tace
"Ya hamza ya zainab? Har yanzu bata sauka ba?"
Lumshe idanu yayi ya buÉ—e yace
"ta sauka, ta samu da namiji"
Cikin farin ciki tace
"Alhamdulillah! Allah ya raya mana ya dayyaba"
Yace
"Ameen! Hidaya Albishir"
Tace
"Goro fari Kal"
"Hajiya ta amince da aurenmu! Zainab ma ta amince da kasancewarmu family guda"
Ya faÉ—a cikin farin ciki.
Rassss haka gaban hidayat ya faÉ—i, dankari! Yanzu ya zata yi? Me zata cewa ya hamza? Ta ina zata fara? Ya Allah, ta ambata tana lumshe idanunta.
"Hidayat!"
Ya kira sunanta don tabbatar da tana kan layin sede bata iya ta amsa ba.. A sanyaye ya É—aga wayan daga kunnenshi ya kalla yaga yana reading ya sake mayarwa ya ambaci sunanta....!
#Vote
#share
#comment
        🖤Gureenjoh🖤
KOWA YA GA ZABUWA...
  (DA ZANEN TA YA GANTA)
بسم لله الرØÙ…Ù† الرØÙŠÙ…
FATIMA MUHAMMAD GURIN.      Â
     (Gureenjo)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
FOLLOW ME ON Wattpad @Gureenjoh6763
AND ON AREWA BOOKS @gureenjo
Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*
           *PAGE 33*
*FREE BOOK*
**Aunty safeeya da maman sadiqðŸ˜ðŸ˜ wannan page É—in naku ne kuyi yadda kuke so dashi son soâ¤ï¸**
"Ya hamza don Allah ina so ka saurare ni da kunnen basira, karka fassarani da abunda yake ba tsarina bane tsarin Allah ne, Raed ya taimaka min a sadda bana cikin hayyacina ina kan gadon mutuwa ta da baƙin cikin rayuwa da kuma baƙin cikin ɗa namiji, da taimakon Allah da na Raed aka yi mini aiki cikin sa'a, a sannan yarana were stranded shi ya taimaka ya basu natsuwa da kwanciyar hankali, a sadda mahaifin Usman ya kashe min yaro na fito titi bani da maraba da mahaukaciya Raed shine ya zo ya taimaka min zuwa asibiti he did his best Amma kwanan Usman ya riga ya kare ya tafi, Raed shine ya ciyar a wannan wurin makoki har aka watse wadda uban da ya haifeshi be iya mishi ba bayan yayi ajalinshi, taimakon wannan bawan Allahn be tsaya iya nan ba, bayan Yusuf ya wulakanta ni iyayenshi sun koreni...mugaye suka so hallaka min yarinya su hallaka rayuwata Raed shine ya bayyana ya taimaka mana, ya dawo min da murmushi da farin cikina, ya bani dama me girma a rayuwarshi, ya maida ƴaƴana tamkar nashi ina zaune a gidan Raed ne da sunan aiki amma kudaden da yake kashewa ni da yarana yafi karfin albashina na shekara, please put yourself in my shoes kana tunanin akwai wani abunda wannan bawan Allahn ze nema daga gareni in kasa mishi?"
Wani irin bakin miyau hamza ya hadiye, yana jin wani irin turirin zafi na ratsa jini da jijiyarshi, zuciyar shi tayi baƙi kirin.. Be iya magana ba ta cigaba.
"Kayi hakuri da abunda zan faÉ—a yanzu, idan duk aka jingine sadaukarwar Raed ga rayuwata beside all that ina son shi, ba zan ce ga sadda na fara ba sede na san cewa a yanzu Raed shine farin cikina, kayi Hakuri ka cigaba da zama a matsayin yayana na riga na ba Raed ragamar rayuwata....."
Katse ta yayi yana zub da hawaye yace
"Hidayat ba se kin ce ban kai Raed kuÉ—i ba, ba se kin sanar dani Raed ya fini suna da tashe ba, ba se kin tabbatar min da cewa Soyayyar da kika fara nuna min tun a baya yaudara bace, ashe fakewa kawai kika yi da hajiya... Hidayat ba zan iya hakura dake ba, wlh ko duk abunda na mallaka zan iya baiwa Raed a matsayin sadaukarwar shi gareki ya bar mini ke, don Allah karki hukuntani da rabuwa don ba zan Jura ba"
Hawayen da ya zubo mata ta share...
"Mutum baya auran matar wani ya hamza, kana da ilimin addini ka sani komai ya faru already a rubuce yake, kar son zuciya ya sa ka fassarani a baibai, kuɗi kuma ba ze taɓa sayan sadaukarwar R....."
FaÉ—uwar abu taji da karfi, se taji ihun Hajiya tana kiran sunan Hamza, ruÉ—ewa tayi bata kashe wayan ba tana ji hajiya na ihu tana kiranshi da jijjiga shi, tana ji har sadda aka fita dashi asibiti kan ta kashe ta kife fuskanta bisa tafin hannunta tana zub da hawaye cikin damuwar halin da ta jefa hamzan ciki.
Ta jima anan kan wayanta ya sake É—aukar kara ta duba se taga layin zainab ne don tayi saving..
ÆŠagawa tayi tare da sallama, zainab na kuka tace
"Hidayat don Allah kiyi hakuri da abunda nayi miki, nayi shi ne out of bacewar tunani da hankali, na auri hamza ne ba don yana so na ba se don soyayyar da ni nake mishi, a farkon aurenmu ya duba kamata da cancantata ya fara bani kulawa har zuwa sadda na samu cikinshi hankalina a kwance yake, sede daga sadda kika bayyana cikin rayuwarmu na rasa gane kan Hamza, na san halin matan yanzu a yadda hamza ya gigice a soyayyar ki se nayi zaton aikin asiri ne hakan yasa na kira na miki barazana ga mamaki na har yau baki fadawa hamza ba, don a yadda yake sonki na san da kin faÉ—a mai da watakila zamana ya kare a gidanshi, wannan dalili yasa kunyar abunda na miki ya baibayeni har nake jin zan iya kiran ki in baki hakuri sede ban yi hakan ba don hankalina be kwanta ba se yanzu na samu dama, don Allah kiyi hakuri.."
Hidayat tayi murmushi tana gyara zama Dukda murmushin ba wai ya kai ciki bane..
"Babu damuwa ni dama ban rike ki ba, kowacce mace akwai hanyar da take ganin ya fiye mata wajen bi don kare martabar aurenta, abunda kawai nake so in tunashe ki shine...A duk sadda hankali ya ɓata hankali ke nemo shi, ni karan kaina ina ta so na kiraki don ni na daukeki ne a matsayin matar yayana zan kuma iya baki shawara, ko gaba hakan ba daidai bane don yana zubar da ƙima, ba irin kishin da matan annabawa da sahabbai suka yi kenan ba, a masali wata ce a shoes ɗina zata kira ta gayawa Hamza ƙimar ki ze zube a idanunshi, hakanan tunda akwai gigin karin aure a kanshi ze iya kawo karshen zaman ku sbd a duk sadda namiji ze yi aure to fa se kin yi hakuri kin kau da kai, lokaci kalilan ne kina zaune komai ze zo ya wuce kaman ba'a yi ba, ina kuma so na shawarceki yawan kai kara na fitarwa miji soyayyar mace sbd a kullum ze zamana baku da abun hange se laifukan junanku.. Fatan ban yi miki shisshigi ba"
Murmushi zainab Ta saki tace
"ko É—aya, Seda na zauna nayi maganan da mahaifiyata ta fitar dani haske yadda kika yi min kan na san nayi kuskure, shiyasa nake shirin gyara.. Ya hamza na cikin wani hali yanzu haka maganan da nake miki muna asibiti ne, likita yace zuciyarshi ya kumbura kuma idan yana cigaba da shiga damuwa ze iya fashewa mu rasa shi hakan yasa na kira in roki arziki, don Allah kiyi taimako ki amincewa aurenshi mu zo mu gina rayuwa me kyau, bana so É—ana ya tashi cikin maraicin uba yanzu ne ya fara rayuwa don Allah"
Ajiyar zuciya me karfi hidayat ta sauke cikin damuwa tace
"Zainab zuciyata bata yiwa hamza soyayyar aure, hasalima akwai wadda nake so barin shi kaman cutar wa ne a gareni da kuma shi karan kanshi da iyalan shi don suma suna bukata ta"