Sashe 63
Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Juyawa muka yi zamu bar wurin tayi wani tsalle ta sha gabanmu ko damuwa da cikinta da ya É—an fara fitowa bata yi ba tace
"Ina Zaku je? Wai me kake nufi ne?"
Hannu ya sa ya matsar da ita yace
"wuce baiwar Allah"
Na wuce ya biyo ni zuwa karamin sashen dake daga gaban wannan É—in, da sauri ta kuma shan gabanmu tace
"É—akin ka zaka kai ta?"
Yace
"eh tunda nan kam ba naki bane baki da hurumin hanani ko yi mini iko"
Bori sossai tayi tayi wadda wasu ba zan iya tunawa ba akan kilan cikin ma nashi ne dangina suka koro ni na dawo mishi da abunshi in ba haka ba ina ze sameni da sassafen nan, babban damuwarta kankantar shekaru da kyau na Dukda sossai ya ɓuya sbd wahala.
Daga karshe ganin da gaske sashen shi ze ajiyeni tace ta hakura in zauna sashen ta, haka muka koma ta bani extra room, be barni ba seda ya tabbatar na ci abinci nayi sallah, ina gabamawa nayi pillow da jakana as usual na hau bacci.
Dukda kasancewar Amina mace ƴar uwata sede ko sau ɗaya bata taɓa jin tausayina ba a zamana da ita Dukda taga banda cikakken lafiya da hankali, bayin ta babu pampo se wurin wanke wanke, da safe zata saka ni diban ruwa in cika mata randunan bayi, in yi wanke wanke kan ta bani abin karyawa, abincin rana wani lokacin se yamma idan Alhj ya dawo mutum me tsananin mutumci da karamci ze ɗauki nashi ya bani Dukda barazana da matarshi ke mishi a kaina iri iri.
Na zauna na tsawon sati uku a gidan bana yiwa Kowa magana tun ruwa da nace ina so ban sake cewa kowa tak ba, da dare Alhj ya kan zauna ya tambayi suna na, mijina, garin da na fito ko wasu en uwana amma babu abunda nake iya ce mishi ko nake tunawa.
Wata rana na tashi da nakuda bayan na ɗibi ruwa ina a na karshe cikina da bayana suka riƙe sossai, ban iya karasawa ba bokitin ya faɗi nan tsakiyar parlor ya jike Mata ɗaki, wani irin bangaza tayi mini ta hau zagi na babu irin sunan cin mutuncin da bata kirani ba har marina Seda tayi akan se na gayamata gaskiya mijinta ne uban ciki na?
Ina fama da wahalar nakuda hakan yasa duk abunda take yi É—in ban ma san tana yi ba, ta saka ni na share mata ruwan da na zubar ina cije baki da komai a tsugune na yi aikin ban iya komawa É—aki ba nan tsakar ranan na faÉ—i ina shan azaba, matar nan bata fito ba bare ta kulani na fi awa uku a wurin har jini da ruwa suka fara bin kafafuna ga rana ana yi na jike sharkaf da zufa, da taimakon Allah Allah ya turo Alhj Dukda yaranta na nan suna kai kawo sede kallo babu wacce tayi min.
Hankali tashe ya kirata ta zo ta taimaka min mu tafi asibiti tace ba da ita ba, lokacin da aka yi abunda aka yi ba'a gayyace ta ba se yanzu, haka ya taimaka min sbd babu yadda ze yi muka je mota ya kaini asibiti, da kyar suka karɓe ni seda suka yi faɗa sossai akan rashin kulawa da sakaci da aka yi gashi ba wurinsu nake zuwa awo ba.
Bayan baƙar wuyan da nasha na haifo yarinya mace, ina haifanta kuma na fara wani kalar bacci kaman wacce ta bugu, su suka mata komai har nono suka bata ba tare da na sani ba.
Se washegari da yamma bayan sun gama bincikensu suka bani sallama, tunda na farka kuma se hauka na muraran ya bayyana, ba zan ce na riƙe yarinyar ba sbd Alhj tsoron bani ita yake kar na yarda ta.
Muna dawowa Amina ta sake tada sabon bore, Seda suka kai ruwa rana kan na shiga É—akin da suka saukeni, da farkon dare ya kawo min yarinyar yace
"Baiwar Allah ya kamata kiyi magana ko sunanki ne mu sani! Babu daaÉ—i yadda Amina take adressing naki da sunaye marar kyau"
Kallonshi nayi kaman zan ce wani abu se nace
"Aisha! Aisha!!"
Ina ta maimaitawa Seda ya gaji yace
"sunanki Aisha?"
Kai na gyaÉ—a yace
"daga ina?"
Ban yi magana ba se jaka na buɗe na fiddo box na miƙa mai nayi murmushi, karɓa yayi yana Juyawa kan ya ɗago nayi bacci fita da yarinyar da ko kukanta ni ba zan ce ga yadda yake ba yayi, madara ya sa aka sayo mai ya bata a tare suka kwana.
Karfe Taran dare naji ana tashina, É—ago kai nayi na kalli Amina ta zaro min idanu tace
"tashi tsohuwar munafuka ki fitar min daga gida.. Ai nayi kokari tunda kika yi sama da sati uku"
Mikewa nayi a tsorace na rarumo jakana na rungume, fisgewa tayi tana cewa
"uwar menene ciki da kike mammaƙeta haka?"
Zazzagewa tayi zobuna na suka zubo waenda suke gwal ne masu kuÉ—i a lokacin guda biyu, É—auka tayi tana Juyawa ta kalleni tace
"kam bala'i!! Wato Alhj ya iya saya miki gwal kina karuwarsa ni matar gida be sayawa ba?"
Girgiza kai nake ba tare da nace komai ba, mari ta sauke min tace in zo in fitar mata daga gida kan ta kulle idanu ta buÉ—e zobunan kuma wlh bazata bani ba tunda da kuÉ—in mijinta aka saya.
Kuka nake son yi ta fincikoni tare da toshe min baki ta ja ni har wajen gate ta cilla ni na faɗi har Seda goshina ya fashe da dutse, raina ne ya ɓaci ban sani ba ko aljannun da aka Haɗa ni dasu ne ko yaya kawai ina mikewa na dau hanya ba tare da ko waiwaye ba.
Seda nayi tafiyar da ban san na awa nawa ba gari dae yayi shiru kan na iso wani rumfa inda buzaye suke zube sun hura wuta, anan na shiga cikinsu na kwanta basu ganni ba seda safe, sun tsorata macen ta tashe ni, ina farkawa mijin yace kar kowa ya min magana, wasu Adu'a ya dinga yi min kan yace
"Baiwar Allah!"
Na kalleshi sede ban yi magana ba, yace
"hoo innalillahi wainna ilahi rajiun duniya ina zaki damu jama'a? Laure wannan mata na shikin masifa tana matukar bukatar taimako"
Matar tace
"to me gida ba se ayi wani abu ba?"
Yace
"yo ai ba ze yiwu anan ba duk abubuwan suna chan gida gashi kudu muka nufa"
Tana kallona cikin tausayawa tace
"kayi hakuri mu koma Nijar me gida! Wannan baiwar Allah duk inda danginta suke na tabbatar suna shikin tashin hankali"
Haka gamji da matarshi Laure suka fasa wannan tafiya suka tafi dani Nijar, na sha wahala sossai wurin adapting rayuwarsu, nayi jinya me yawa wadda har na kan yi wata ba tare da na san inda kaina yake ba, abun ya zo ya fi karfin Gamji Seda ya HaÉ—a da neman taimako a wasu nahiyar na Nijar.
Tsawon shekarun ashirin ina fama da jinya don se haukan yayi kaman yayi sauƙi se kuma ya taso, na samu lafiya shekaru uku baya inda komai ban manta ba, na basu labarina gabaɗaya saboda sun zama kaman yayyina sun riƙe ni da amana matuka, basu taɓa saka lomar wani abu a bakinsu ba tare da na saka ba, ko da suka ji labarina wadda ina zuwa wurin barin jinjirata da ba zan iya tuna fuskanta ba se kuka da firgici su rufe ni, ta ina zan fara neman ta? Kuma ta yaya? Wlh ko sunan Wannan bawan Allah da ya taimakeni ban sani ba bare unguwar da yake a birnin Kano.
Mun kara delay na shekara uku kan mu zo ne sbd tsananin rayuwa da gamji yake ciki ya sayar da duk dabobbin shi wasu yayi asarar su duk ta hanyar neman min lafiya don aljannun sun sha kashe mishi garke gabaÉ—aya sbd ni akan ana mishi gargadi ya Rabu da ni da rayuwata babu ruwanshi.
Da muka samu kuɗin suka taru kuma fita ƙasar Nijar ya gagareni seda muka yi ta biyan wasu kudade kan muka iya fitowa, mun kwana Kano kan muka nausa Gembu seda muka samu kab labarin abunda yake faruwa gidan Buba kan muka nemi layin mama, matarshi Badi'ah ta bamu shine muka kira, ko da muka iso Kano da neman taimako muka samu me adaidaitan da ya ɗauko mu zuwa wannan gida don ko biyar bamu tsira dashi ba kuma..."
Shiru tayi tana share hawayen fuskanta, tana me cigaba da shafa kan Hidayat da take ta kuka har da majina, Abbanta da ya hamza ma kuka suke yi duk dauriya irin ta maza, sossai jikkunansu yayi sanyi babu wadda ya iya magana se muryar Hajiya Balaraba suka ji ta fara cewa
"Hahahahahhaha ba kin dawo ba! Dama ya faÉ—a kina dawowa se na haukace ai kaikayi koma kan mashekiya ne! Aisha ke azzaluma ce, ina zaman zamana da mijina tun kan yayi kuÉ—i har yayi arziki shine ya tsallake ya auro Æ´ar gembu waenda ba inda labarin kyaunsu be je ba! Yana so ni balaraba in zama bora ya sa kyakkyawa gaban mota Hahahahahhaha"
Ta sosa kai ta sake gyara zama kan tace
"ni ce nan na je wurin neman taimako aka taimaka min ake sakar miki da ciwon ciki me tsanani da kuma zuban jini duk kwananki...! Hahahahahhaha kin ɗauka ban sani bane har da bani labari.... Ai wannan malamin ma ba malami bane ruwan asiri na yayi ta baki as magani ke kuma wawuyar kika yi ta amfani dasu har asirin warin jaɓa ya shige ki..."
Kallon maman Rashida tayi tana kwalalo idanu tace
"ke Adama ke munafuka ce! Har abada a matsayin hoto na so Aisha ta zauna gaban Usman se kika min zamba cikin aminci kika karya mun magani ba tare da na ankare ba.... Boka na yace min tunda har wannan ya karye babu yadda na iya sede in fara HaÉ—awa da kissa irin ta mata su zasu na aiki har gunki ya basu nasara..."