← Book details Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 74

Sashe 21

Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

BuÉ—e back seat tayi ta saka tana Kallonsu har suka fice, ciki ta dawo ta samu Miss Mary na aikinta na shara da goge goge, sannu ta mata ta haura a nan suka karya da abunda yaran suka bari, wanka suka shiga sukayi tare da sauya kaya ta zauna ta sake fara karanto abubuwa da yaran suke so da wadda basa so..

Ta Tabbatar se tayi da gaske kafin yaran suyi blending da ita har wani shakuwa ya shiga tsakaninsu, yaran suna bukatar uwa tsayayya in ba haka ba rayuwarsu akwai matsala babba..

ÆŠakin su ta gyara musu tsab kan ta fara duba abunda zata É—aura musu na lunch Seda tayi ta kallo tana maimaitawa kan ta zo ta fara cikin taka tsantsan, wuraren É—aya ta gama ta shirya a dining, tana gyara kitchen É—in taji shigowar su babu ko sallama, fitowa tayi tace
"girls annabi yace idan zaka shiga wuri dole Kayi sallama ga ahalin wurin kuma amsawa dole ce ga dukkan musulmi da yake wurin, kunga sallama na da kyau kenan hakanan In kayi sallama kana da lada me yawa kunga wadda kuma ya tara lada ne kaÉ—ai ke shiga aljanna"

Duk kallonta suke baki hangame kan Nora tayi tsaki ta wuce, Farrah kuwa dake jin yunwa dining tayi, abincin hidayat ta zuba mata ta diba zata kai baki hidayat tace

"pray first"

Se ta lumshe idanu hidayat bata ji abunda tace ba banda in Jesus name daga karshe, wara idanu tayi tana rike spoon É—in da sauri a fili tace
"Na shiga uku!"

A tsorace Farrah ke kallonta tace
"Farrah please say bismillah, u r a muslimah so be acting like one wannan É—abi'ar ba namu bane"

Seda ta kalli hidayat É—in kaÉ—an kan tace
"bismillah!"

Ta fara cin abincin, ajiyar zuciya hidayat ta sauke tana dafe kanta ba karamin aiki ne a gabanta, haka suka yi da Norah ma da ta fito cin abinci amma ita bayan tayi bismillahn se jikinta ya É—an yi sanyi wadda hidayat bata san na menene ba..

Da dare ma kusan yadda aka yi da safe suka yi don Seda babansu ya fita dasu amma yanzu harda Aisha ya kira suka fita, bayan sun dawo a gajiya suka kwanta bacci landline ɗin ɗakinta ne yayi ƙara da sauri ta ɗauka yace yana son ganinta..

Gabanta na faɗuwa haka ta ɗauki hijab ɗin ta ta saka, hanyar waje tayi tana jin sanyi sanyi na neman rufe ta bata son ɓata mishi rai har yayi mata faɗa gashi daga fara aiki yau har tayi laifi, bata ganshi a parlor ba hakan ya ƙara faɗuwar gabanta..

Kofan dakin shi tayi ta tsaya daga bakin kofa tayi knocking mintuna biyu yace "Come in" cikin hadaddiyar voice É—inshi me kaurin nan, hannunta har rawa yake ta sa a handle tare da murdawa ta sanya kai kamshin da ya buge ta da sanyi Seda ya sakata lumshe idanu...

#like
#share
#comment

                    🖤Gureenjo🖤

KOWA YA GA ZABUWA...
   (DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

                      *PAGE 15*

*FREE BOOK*

Abunda idanunta ya faÉ—a kai ne yasa tayi hanzarin É—aukewa tana runtse idanu, mace a kan jikinshi? Daga gani ma ba musulma ba?
Innalillahi wainna ilahi rajiun.. Wani irin rayuwa suke yi a gidan nan?..

Tayiwa kanta tambayar tana iya kokarinta wurin hana jikinta  ɗaukar rawar da ya fara, zaune yake bisa couch na ɗakin me taushi sanye da pants/boxers wadda be kai gwiwa ba kana iya ganin murɗaɗɗiyar jikinshi gabaɗaya, wadda gargasa yake nan kwance lublublub, a kan faffaɗar kirjinshi wata kyakyawar yarinya ce daga ganinta bata san me wani talauci ba, ta ci gayu ga nails an yi fixing dressing rabi jiki a waje kwata a rufe..

Daga idanunshi yayi ya sauke a kanta se ya É—an tsaya yana nazartarta ganin yadda tayi wuri wuri, jikinta na rawa idanunta a runtse, magana yake shirin yi Wayanshi ya sake daukar kara..

"Handsome pls pick this phone samu mu huta da ringing.."

Dauka yayi cikin yanga ba wai don Kimorah tayi magana bane yasa yake so ya É—auka no kawai ya ga ya kamata ya É—aukan ne ya É—aga..

"Daadida please.. Don't spoil my mood yanzun nan, I don't really know what's ur problem mutumin nan tun farko fari yace baya so na, yace he hates me nd hates everything abt me and I also fucking hates him..! You lied to me akan baki da lafiya u made me went to Nigeria but at last u saw what happened... I promise idan baki dena min maganan mutumin nan ba zan yanke duk wata alaka da zaki sameni ta waya am damn tired with ur stress..."

Shiru yayi yana sauke numfashin masifar da yake yana jin muryar matar na Kuka cikin kunnuwanshi wadda yake ji har tsikar jikinshi na tashi, yana son ta har ranshi itace mace guda da yake jinta har tsakiyar zuciyarshi kuma ita ce kadai ta rage mishi bayan yaranshi sede abunda take so daga gareshi shine yake kara nesanta su, be taɓa ganin macen da bata zuciya akan abu ba se akan Daadida she spent years tana abu guda bayan babu haske..

Zata yi magana yace
"I have to pray, good night"
Daga haka ya yanke wayan.

Mikewa yayi ya wuce toilet, Kimorah da take ta kallon Hidayat tun fara Wayanshi tace
"ke! Wacece ke?" Cikin harshen turanci don baturiya ce..

"New nanny!"
Tsaki ta ja tana kallon irin kyaun fuska da na sura da Hidayat É—in ke dashi Dukda a cikin hijab take, wani abu ne ya tsaya mata a wuya, haka kawai hankalinta be kwanta da nannyn ba.

"Go to Paul ki ce mishi ya baki food É—in ki kawo min am starving"

Fita tayi Paul shine cook ɗin masu aikin gidan kuma shine yake yiwa Oga abinci, ƙasa ta sauka a kitchen na kasan ta same shi tace ga abunda wata dake ɗakin oga ta ce..

Yana murmushi yace
"Kimorah.. Is her name she's the only fiancee of oga, ita kaÉ—ai ta ciri tuta a cikin dubban matan da suke crushing a kanshi from different part of the world"

Kai kawai ta gyaÉ—a, banda faÉ—uwa babu abunda gabanta yake.. Zuciyarta ke tirsasata shiga hurumin da ba nata ba sede fa idan ta tuna da tarihin nan na mutanen annabi Musa waenda aka hana su kama kifi ranar Asabar se ranan Lahadi da kuma sauran ranakun se su je su ajiye abun kamun kifin ranar Juma'a se ranar Lahadi da safe se su zo su É—auka wai su zasu yiwa Allah dabara..

A cikin mutanen sun kasu ne kashi uku, kashi É—aya sune masu kamawar, kashi na biyu su ne waenda suka gani ana yi sun kuma san ba kyau se suka ce Babu ruwan mu, kashi na karshen kuma sune waenda suka gani suka kuma yi magana..
Da Allah ya tashi se ya hukunta masu yi É—in da waenda suka gani suka ce babu ruwan mu, a musulunci babu maganan ba ruwanka idan kaga É—an uwanka na abunda ba shine ba ka faÉ—a mishi karka yi fushi ka cigaba da faÉ—a mishi har Allah yasa ya gyara Allah shi kadai ya san sakamakonka a ranar gobe..

Karɓar tray ɗin tayi ta koma sama, a gefe ta ganshi sanye da wata jallabiya me kyau da daukar idanu navy blue kirar Kasar Qatar ba karamin kyau ya mishi ba barin ma da ya saka hulan nan na taɓani kaji hadisi.. Sede abunda ya girgizata har ya so sakata sake tray ɗin shine yadda yake gabatar da sallar cikin rashin natsuwa da kuma watsar da ka'idoji masu yawa na sallar..

Innalillahi wainna ilahi rajiun ta dinga maimaitawa ba karamin abun tashin hankali bane gareta ganin namiji har namiji ga kuɗi har kuɗi ga kyau sede babu addini, yana mutuwa yau wuta fa za shi... Hawaye ne ya fara kwaranya a fuskanta cike da tsoron Allah lallai in ka tsinci kanka a wani jarabawar ka gode Allah sbd naka me sauƙi ne..

Da alama la'asar, magrib da isha ya hada don har ta gaji da tsayuwa ta duƙa a ƙasa, bayan ya idar ya kira sunanta wadda ya sa gabanta wani irin dokawa.

"Miss hidayat!"

"Na'am sir"

Yace
"Na tashi ban san wani farin ciki ba har Seda na samu yaran nan nawa guda biyu na san wani abu wai shi farin ciki, they are all I've got a duniya, ɓata musu kaman ɓata min ne, ina tausayin ki hakan yasa kika kai har yanzu a gidana kiyi kokari kiyi blending da yaran nan within a short period of time in ba haka ba you will loose this job"

Kanta kasa ta sa hannu ta share hawayen da ya zuba mata, kan tace
"in shaa Allah zan yi iya kokarina kayi hakuri pls"

Kuka na daga cikin abunda Sam baya so, ganin yadda hawayen wani ke bin wani yasa ya kau da kai yana lumshe idanunshi masu yanayi da me jin bacci, yace
"tomorrow ki shirya Aisha they will be going together with Farrah na yi mata komai, interview zasu mata su bata uniform and rest"

Bata san sadda murmushi ya subuce mata ba har dimples É—inta na bayyana ga kuma hawaye a idanunta, sossai taji daaÉ—i ta dinga mishi godiya..

Sake dauke kai yayi yace.
"U can go"
Ta mike ta fito..

ÆŠakin Farrah tayi ta samu tayi bacci, gyara mata kwanciya tayi ta kashe wutan ta fito ta shiga É—akin Norah..

Zaune ta sameta tana kallo, a hankali ta zauna bakin bedside É—inta tace
"Norah..! Please ki bani mintuna biyu cikin lokacinki ina so zamu yi magana"

Seda ta É—an kalleta kan ta É—auke kai kaman bazata bada hankalin nata ba se kuma ta tsayar da kallon tace
"am all ears"

Hidayat tace
"Norah kin san wanene Allah?"

"Almighty God?"

Ta tambaya, tana wara idanunta..

Kai hidayat ta gyaÉ—a, Norah tace
"the creature of everything I guess"
Chapter 21 · 0% Book details