← Book details Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 74

Sashe 7

Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana kai nan ya juya ze fita da gudu ta sha gabanshi tace
"ni ka mara akan wanchan Æ´ar shegiya..?"

Kara zabga mata mari yayi yace
"idan har zaki cigaba da kiran hidayat da irin sunayen nan hannuna ba ze gaji da hukunta ki ba"

Ihu ta kurma tace
"Wallahi ba zan tafi ba se da hujjah, ba zan bar gidan nan ba har se ka ban hujjar tafiya"

Yace
"hujja kike so? OK ki je na sake ki saki É—aya"

Hannu ta sa a kai ta kurma ihu
"akan ts...." Fasa faÉ—ar tsinanniyar tayi ganin ya sake É—aga hannu tayi saurin cewa
"yanzu akan hidayat ka sakeni Abubakar? Akan wannan yarinyar?"

Yace
"ba saki kaÉ—ai ba, zan auro wacce zata kula da ita tunda ina da damar hakan"

Me umma zata yi! kuka wiwi kaman yarinya Alhj ya ce ze yi aure, a haka ya fita ya barta, a kofar É—akin ya samu sauran yaran be kula su ba ya fice abun shi, suna ji suna gani umma ta HaÉ—a akwati ta fice.

A ranan a sashen Abba hidayat ta kwana bayan tafiyan umma ma fita yayi ya sayo musu gasashen kaji da su ice cream ya biya super market ya sayi sabon lunch box hadadde, Washegari a sashenshi ta ci abincinta suka fito mota a tare, yaran basu É—auko mata lunch box ba ya kalli khausar bayan sun gaishe shi yace
"koma ki É—auko wa hidayat basket É—inta"

Juyawa tayi bakin ciki kaman ya kashe ta, haka ta je ta É—auko ta kawo musab dake zaune a gaba ya kalla yace
"mus'ab koma baya"

Fita yayi ya koma baya da kanshi ya saka hidayat a gaba yace
"as from today wurin zamanta kenan Habibu driver duk ranar da ka kuskura muka haÉ—u ko daga nesa ne ban hange ta É—aga gaba ba a bakin aikin ka, sannan duk ranar da ta sake fita ba lunch box baka gayamin ba shima a bakin aikin ka"

Yana kai nan yayi musu waving bayan ya ba kowa kuÉ—in break É—inshi suka fice.

A mota sun yi shiru ne sbd sun san ko an koma habu ya faɗawa Abba in ya tashi dukansu babu umma me karɓansu, a school ne suka Taran mata suka mata kacha kacha Aunty khausi har niyyar dukanta tayi aka raba su.

Wasa wasa satin umma uku Abba kaman be san da zaman ta a gidansu ba, gidansu irin gidan hayan nan ne masu É—akuna dayawa, magana har ya soma yi mata yawa ga takura gashi bata samun sakewa kaman tana gidanta, tasha alwashi Kala kala akan Hidayat, tun tana Tunanin Abba ze zo ya É—auke ta har ta sadakar ta fara kama kafafu da manyanshi bayan sati daya aka samu suka zauna.

Ya gindaya mata sharuÉ—a akan hidayat ta ji ta amince ta bashi hakuri sossai kan ya amince ta dawo, a lokacin har wani fari da kumatu hidayat ta kara irin kulawar da Abba ke bata ko yaranshi be baiwa ba, ya mata sayayya ba na wasa ba Dukda ya kan HaÉ—a da su khausar sede nata fa na daban ne.

Tunda umma ta dawo bata shiga sabgar hidaya ba haka itama, shakkan umma da take yasa bata bari ma su haÉ—u, bayan dawowanta da sati biyu aka tura Abba wani aiki a France ya tattara ya tafi tare da kara jadaddawa umma kula da Hidayat ya kuma tabbatar mata ko tsawa me karfi umma tayi mata ta gayamishi in ya dawo.

Umma ce zaune tana Tunanin abunda zata yiwa hidayat don Wlh abunda ta mata ba ze taɓa tafiya a banza ba, wasa ma ake ace ta hakura komai ya wuce, hidayat ɗin ita wacece? Hmm

Bayan ta gama nazari ta tashi tayi kitchen, ruwan ta me kankara ta samo ta fito tayi gaban TV ta samu cable su Surayya na kallonta, tayi É—akin su a kwance ta samu hidayat bisa shimfiÉ—arta tunda Abba ya fice take a haka a É—arare ta san umma kaman yunwar cikinta, tana cikin tunani kawai taji ruwan sanyi a jikinta bata gama dawowa daidai ba ta fara jin saukan cable, ihu ta kwala ta fara kokarin gudu sede umma ta fi karfinta haka ta rike ta Tsam ta hau jibganta kaman Allah ya aiko ta, Seda tayi mata laga laga kan ta janyota parlor.

"Fahariyya kawo min wuƙa"
Wani irin zaro idanu hidayat tayi anan ta fara
"Umma Don Allah kiyi hakuri, umma karki kashe ni wallahi ba zan sake ba, umma kiyi hakuri.."

Idanunta rufe take ta baiwa umma hakuri ta ruɗe ta gigice, bata kara sarewa ba seda fahariyya ta kawo wuƙa umma ta saka khausar kama mata kafafu, fahariyya ta kama hannayenta suka Mikar da ita Salamatu da Surayya suka danne ta da kyau, kaman zata shiɗe take rokon umma kar ta yanka ta.

"Zaki sake ko da ambatan sunana a gaban Abba?"

Da sauri ta girgiza kai tana cewa
"A'a a'a umma ba zan sake ba"

"A'a zaki sake gwara in yanke ki tsab in birne ya dawo in ce kin gudu"

"Ki rufa mun asiri umma ki taimakeni karki kasheni, Wayyoooo..!"

Umma ta gyara wuyanta ta saka wukan nan, kokawa hidayat ta fara yi da numfashinta don tsoro, a take fitsari ya kufce mata, umma kuwa ko ajikinta ta didara mata wukan nan a take ya shiga wadda yayi daidai da sumewar hidayat.

Yusuf da ya turo kofa ya shigo kenan daga Maiduguri ganin abunda suke shirin yi yasa yayi sauri ya karɓeta, ɗaukanta yayi zuwa asibiti suka watse da dariya umma harda hawaye, su Surayya na kwatanta yadda hidayat ɗin take yi.

Daga wannan rana da aka yiwa hidayat É—inki a wuya ko muryar umma taji se jikinta yayi reacting, wani irin tsoron ta take ji kaman rai, su kuma suka samu abun yi.

Yusuf shi de baya hana su Idan ba ya ga dukanta da gaske gasken zasu yi ba, sannan shi baya mata Dukda yana da zafin zuciya sossai.

Ko da Abba ya dawo ko ya tambaye ta ana mata wani abu da gudu take cewa a'a, a haka hidayat tayi rayuwa, tana da shekara goma ta fara musu girki.

Idan be yi daaÉ—i ba zata daku kuma ta cinye, ko zata amayo hanjinta se ta ci, a hankali a hankali suka sallami me aikinsu gabaÉ—aya, zata yi breakfast a ci tayi shara, su tafi school su dawo kan islamiyya tayi musu abincin rana tayi wanken wanken safe, kullum se an dake ta a islamiyya sbd letti, tana dawowa zata yi na dare tayi wanke wanken rana, ta wanke musu uniform duka.

Bata da maraba da baiwa a gidan, abunda har yau ta kasa ganewa shine a idanun Abba yusuf kaman ya maida ta ciki amma a bayan idanunshi babu ruwanshi da ita Dukda baya duka ko zaginta, sbd yawan damuwa da yawan kukanta yasa har mutanen layi kan gane tana cikin damuwa.

Bayan wani lokaci!

tana da shekara goma sha huÉ—u a lokacin Dukda khausar ta gama secondary har an sanya mata rana ma amma har a lokacin hidayat ce ke bautar gidan, wanke wanke take da sauri sbd ta riga tayi letti a islamiyya, tsautsayi ya saka ta fasawa umma cup na tangaran kirjinta da suke a cike Dukda yarantanta ta dafe a fili ta furta

"innalillahi wainna ilahi rajiun"

Bata rufe baki ba umma ta shigo kitchen É—in, mari ta saukar mata hagu da dama nan ta hauta da wani irin faÉ—a, kasa bata hakuri tayi ai ko umma tace dawa Allah ya HaÉ—ata ai dama ta lura kwanan nan hidayat É—in ta fara kwaso halayen rashin kunya zata yi maganinta ta fitar mata dashi a kanta, duka ta yi mata kaman zata kashe ta.

Bayan ta gama wanke wanken da kyar ta fito, ta sanya uniform sbd in ta zauna a gidan ma ba natsuwa zata samu ba, tana tafiya kaman iska ze yarda ita lokaci lokaci ta kan share hawaye, banda raÉ—aÉ—i babu abunda fatar jikinta ke yi.

Bata hankara ba taji an sha gabanta.
"Baiwar Allah! Hawayenki ko kogi ne ina Tunanin yana gab da yankewa"

Baya ta matsa tana kallon shi don bata san shi ba.
Yayi murmushi yace
"is ok don't be afraid, sunana hamza I'm a military officer kullum idan har zan tsaya anan a irin wannan lokaci na kan tsinkayi wucewarki cikin zub da hawaye hakan ya kwaÉ—aita min jin matsalar ki Ko Allah ze sa in iya taimakonki"

Kallonshi kawai take, this is the first time wani yake mata magana cikin kamala da tsantsar kulawa, in aka cire Abba da ummi ƙawarta, tabbas tana bukatar comfort kuma daga gani Ɗayan nan ta aminta dashi sede labarin ta na da tsai.

"Labarina bashi da wani armashin saurara babu abunda ze kara maka banda damuwa da tunani, so ka ga babu amfanin ji"

Kallonta yake da mamaki yace
"amma tukuna shekarunki nawa?"

Tace
"sha huÉ—u"

Kara wara idanu yayi wadda har ya sakata murmushi yace
"amma shine kika iya zaro zance haka?"

Tana murmushi ta kauda idanunta daga kanshi tare da harÉ—e hannu tace
"lokuta da dama ba mu muke iya abubuwa dayawa a gashin kanmu ba se abunda rayuwa ta koya maka kake iyawa, rayuwata ba irin ta kowa bace hakan yasa bana sa'a da sa'anni na a fannin komai na rayuwa"

"wow please what's ur name?"
Tace
"HIDAYAT"

#like
#share
#comment

                   🖤Gureenjo🖤

KOWA YA GA ZABUWA...
   (DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

                      *PAGE 6*

*FREE BOOK*

"Hidayat! Ni kuwa zan so sanin wannan labari ko zan amfana da wani darasi na zamantekwar rayuwa"
Zata yi magana suka Haɗa idanu da Yusuf dake bautar ƙasa yanzu, irin kallon da yake aika mata yasa tayi saurin wucewa Dukda be taɓa dukanta ba sede ta san yana da manufa me girman gaske a kanta.
Chapter 7 · 0% Book details