← Book details Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 74

Sashe 18

Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga inda ta ɗan duƙa tana jin tsawar da aka mishi wadda ya saka shi lumshe idanu se kawai ya zare wayan ya kashe gabaɗaya.. A kausashe yace
"I see no reason da zan bi abunda kike so woman... He hates me nd I fucking hate him more"

Yana maganan yana danna wayan da sauri ya kara a kunne..

"Buy me a ticket of any available flight to Paris now!"
Ba tare da ya jira amsa ba ya kashe tare da wurga wayan kan kujera yana ji ana ta kira sede be sake kallon ko ta ɓangaren ba.

Ita dae hidayat a tsorace take da mutumin nan wani irin mafadaci ne wannan Allah na? Ta ayyana a ranta tsoron mishi magana ma take, in ka kula da kyau zaka ga yadda jikinta ke rawa..

Da kyar ta iya cewa
"Ina kwana!"

Be amsa ba se ta dauka baya jin hausa jin yadda yake turanci, sannan ko yayi hausar ma ba fita take da kyau ba ta sake cewa
"good morning!"

Se a lokacin ya ɗago se idanunsu suka faɗa cikin na juna, janye nata tayi tana jin kaifin idanun nashi a jikinta kwarjininshi duk ya cika parlorn.. murya chan ƙasa yace

"morning!"

Tace
"Dama.. Ina so ne in maka godiya bisa taimakon da kayi mana, ubangiji ya raya zuri'a, Allah ya saka da alkhairi ya sa a mizani."

Lumshe idanunshi yayi yana tuna Usman, lokaci daya yana mamakin yadda ta iya turanci don da turanci tayi maganan, akwai abubuwan da suka É—aure mishi kai a kansu sede bashi da lokacin saurara ko bincike tunda be shafe shi ba.

Kai ya gyaÉ—a mata kawai, wasa da fingers É—inta ta cigaba da yi feeling uncomfortable kan tace
"mu zamu tafi.. Allah ya biya da gidan Aljanna"

Aisha da bata san ya aka mata wanka ba sanye da hoodie na kamfanin Nike purple color tayi rau rau da idanunta..

Harara Hidayat ta zabga mata wadda ya sakata mikewa ta nufi Hidayat É—in hannunta ta kama tace
"se anjima"
Suka nufi kofa abun su...

#share
#like
#comment

🖤Gureenjo🖤

KOWA YA GA ZABUWA...
(DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

*PAGE 13

*FREE BOOK*

*Adda Haneefa and herlieymertouh this page is for you😍🥰❤️*

"Ina zaki je with this 2 little kids? Wai ni kam are you in ur right senses? How can you be so reckless abt ur kids well being? Do u really want them death as Usman?"
Maganan ya mugun dakarta, hakan ya sakata tsayawa Chak...

Me yake nufi? Zuciyarta yayi matukar zafi, ashe wani ze iya ganin laifinta akan yaranta? Yana É—auka sakacinta ya saka kullum take cikin matsala? Bata ga laifin shi ba don ba shine a shoes É—in hidayat ba, bata ga laifin shi ba saboda be san wacece hidayat ba..

Hawayen da take zubarwa ta sa hannu ta share, ba tare da ta juyo ba tace

"I never wish anything bad to them, na yarda akwai sakacina wurin rasa Usman sede ya zanyi? Ina zanje? Wurin wa zan je? Duk ban sani ba, bani da kowa bani da komai taya zan fara duk ban sani ba...! Don Allah ka gayamin ta ina zan fara???"
Ta karashe tana zubewa kan gwiwowinta tare da fashewa da kuka me tsananin cin rai, idan ta tuna sanadiyar kare mata duka Usman ya tafi se taji kaman ta kashe kanta ta huta sbd dacin zuciya...

"Who are you?"

Ya watso mata tambayar yana kallonta fuskanshi da little bit tausayinta da ya fara kama zuciyarshi daga ganin yadda take kuka she's terrified, and restless.

Kasa magana tayi se kuka, Aisha na duke a gabanta tana goge mata duk hawayen da suka zuba, hakan se ya motsa zuciyarshi...
Ganin kaman bata da niyyar amsa mishi tambayar yasa yace cikin cool voice

"I just wanna help, nd I cannot trust you with the work am gonna give you in har baki gayamin wacece ke ba!"
Yayi maganan yana maida idanunshi kan system É—inshi, zafi zafi yake operating system É—in a hankali yaji maganan ta cikin sanyi da karaya ta fara bashi labarinta tun daga farko yadda ta tashi ta ganta har zuwa kawo yanzu..

Tun yana yin typing ɗin sauri sauri har ya dawo a hankali a hankali daga karshe hannayenshi ne kawai zube bisa keyboard ɗin, ya lumshe idanunshi be taɓa jin labari makamancin wannan ba, yana Tunanin nashi labarin shine mafi munin labari ashe ba haka bane..! Ashe nashi azabar kaɗan ne shi namiji ne for that matter gashi yayi building career ɗinshi yayi kuɗi fiye da uban nashi..

Ashe akwai mutane haka? What a world are we living in.. Ya rabb.

Duk wannan Tunanin a zuciyarshi yake saboda kukan da take yi jin tsikar jikinshi yake a matukar tashe, har rawa zuciyar shi yake... Yarinya karama ce sossai wacce sa'anninta suna nan suna building career É—insu but nata is already shattered..

"How... How can I help you?"

Fuskanta da ya kumbura ta share, tace
"I want revenge!"

Da sauri ya É—ago ya kalleta jin yadda tayi maganan daga muryarta zata san har cikin zuciyarta abunda take nufi kenan..

"Da kaina nake so in bi ma Usman hakkin shi... Usman died bcs of me! Usman ya tafi saboda kare min duka how can I forget that?"

Kallonta ya cigaba da yi ba tare da ta kalleshi ba ta sake cewa

"Ina so in nemi aikin yi ko wani iri ne wadda za'a dinga biyana da wahalana, I want to study I want to be a barrister ta yadda zan dawo rayuwarsu kaman dirar mikiya!"

Lumshe idanunshi yayi, yana nazari he can trust her with his kids sede su Norah fa? Ya san su sarai they don't want people from Nigeria.. But bari ya bata chance he loves her kids sbd wayaun su da tarbiyar su...

"Can you nanny my kids? As a job?"

Kanta ƙasa sbd idan har ze kalleta ita bazata iya Kallonshi ba, kai ta gyaɗa tace
"in shaa Allah, zaka sameni yadda kake so wurin baiwa yaranka kular da ta dace!"

Kaman ya ce mata they are not regular kids, rayuwarsu irin na Turai ne sbd ko wata babu wacce ta taɓa yi a Nigeria a cikinsu sede yayi shiru, she says she can then let's see...

Waya ya janyo yayi kira...
"Patric I wanna see u now"

Ba'a yi mintuna talatin ba se ga Patric, already hidayat ta koma ciki cook É—inshi ya aika ya kirata.

KuÉ—i ya zubewa Patric yace
"take them to super market, they should buy anything like komai na bukata she will be Norah nd Farrah nanny so please guide her u knew their taste... From there u take her to immigration office for international passport and start processing her visa we r leaving together"

"Yes sir!"
Patrick ya amsa.. Tare da cewa
"shall we go ma'am?"

Kai ta gyaÉ—a suka fice ta so ta ce mishi ko ta gode ne sede fuskanshi tsoro yake bata, rashin sakewar fuskan tayi yawa gashi da I don't care attitude don har suka fita ko Patrick É—in be sake É—aga kai ya kalleshi ba..

Da ɗaya daga cikin Zafafan motocin shi suka fita, ita dae a muzance take jinta Dukda hijab ɗinta ba abunda ya same shi sede fa ta san rayuwar nan da ta shigo ya fi karfinta, nanny..! Allah andi yaran har nawa ne.. Rayuwar ƙasar waje kuma ya ze kasance mata?

Sayayya na fitan hankali Patrick ya sa matar tayi mata, suna da spa a wurin ya sa suka mata facial and body scrub, dayake ta cewa matar duk dressing da za'a hada mata ba ta son me bayyana tsiraici se matar tayi mata haɗi masu kyau, har da su suits sede ba me kama jiki ba sannan da baby hijabs ko veils, har veils ɗin seda ta koya mata different design na yafa su sbd Patric ya gayamata yaran zasu iya mata mugun raini idan ta je a yadda ta je and they can deny her as nanny baban su kuwa be taɓa turning against their decision ba..

Kayan da taje da su Patrick yasa aka watsar, har junior sayayya shi daban, ita akwati medium da kit É—inshi ash na zamani, na Aisha medium na yara pink me hoton frozen, se Junior wani jaka ne me kyau har da carriage na yara wadda ake daure su a gaban nan ya sa aka saka musu sbd ya san turawa basa goyo kaman yadda mu muke yi, man shafa, turaruka duk na matsakaitan kuÉ—i ya sa aka sa mata..

Fitowa suka yi hidayat sanye da peach English gown da yayi mata kyau sossai me dogon hannu, gyalen tayi mishi yafin Æ´an kasan Oman sanye da Junior cikin carriage ta gabanta, hannunta rike da Aisha da bata chanza daga kayan Farah da Raed ya saka mata ba..
In ka kallesu zaka É—auka asalin su masu kuÉ—in ne kyaunta yayi mugun bayyana Dukda ramar da tayi da kuma fatan ta da yayi duhu kaÉ—an..

Immigration office suka je aka yi mata passport abun ka da kuɗi awanni biyar aka basu zasu karɓa, Patrick ya maida su gida da sayayyarsu yayiwa Raed bayani a waya don ya riga ya bar parlorn..

Hidayat na ɗaki sede har washegari ko kofa bata leƙa ba, abunda yayi keeping ɗinta busy kuwa shine System da Raed ya aiko cook dashi da takarda da biro abubuwan da yaranshi suke so ne da waenda basa so, yadda suke yin breakfast, lunch, dinner.. School ɗinsu da komai dama duk.nanny ɗinsu da zata bar aiki zata yi documenting komai ta tura mishi yadda next nanny zata ɗaura daga nan, tun yamma take abu ɗaya har washegari nan ta fara sarewa, daga gani yaran nan ba kananun ƴan gata bane irin su kuma ta tabbatar they would be rude.. Sede zata yi hakuri da komai saboda cikar burinta..
Chapter 18 · 0% Book details