← Book details Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 74

Sashe 19

Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abunda bazata riƙe ba se ta rubuta a cikin hardcover da ya haɗo ta dashi, shi ya san yaranshi in bata musu ba se su hautsina mishi lissafi, and yana tausayinta apart from the nanny be san me zata musu na kuɗi da ze iya biyanta ba..

A cikin 3days komai nata ya kamalla, kuma har kwana ukun nan bata sake sanya shi a ido ba, Aisha dae tana mata wanka zata fice se dare cook ke dawo da ita wani lokacin kuma ta dawo da kanta kan magrib, farkon abunda ya fara É—aga mata hankali shine idan Aisha ta dawo ta tambaye ta.

"Kin yi sallah?"

Se yarinyar tace
"A'a"

Hidayat tace
"me yasa kina ji ana kiran sallah bazaki tashi kiyi ba? Ko bakya ganin daddyn nayi ne da zaki zauna bazaki yi sallah ba Aisha fa."

Se yarinyar tace
"Mama ai shima be tashi yayi ba..!"

Hidayat bata kara magana sbd tsoro da fargaba da take shiga, Aisha bazata yi karya ba amma me yake hana shi yin sallah? Ko de ba musulmi bane? Toh ya akayi sunanshi Muhammad kuma..!

Kwakwalwanta a sarƙe yake har ranar da zasu tafi, Adu'a kawai take Allah ya sa wannan rayuwar ya zame mata mafi alkhairi kar ya zama wani baabin mummunar kaddarar kuma daga cikin shafuskanta na rayuwa..

Sanye take da shirt nylon tare da palazzo trouser me faɗi se ta saka kimono marar nauyi wadda be gama kaiwa ƙasa ba aka yi wani style daga kasan ba karamin kyau tayi ba dake mayukan da take anfani dasu masu kyau din ne ga cima me kyau da take samu, ta shirya Junior cikin kananun kaya farare da ya amshe shi sossai yaron ba de kyau ba..

Aisha a wurinshi ta shirya cikin kananun riga da wando kanta ba É—an kwali tana shigowa hidayat ta kama ta ta saka mata after dress saman kayan tare da sa mata baby hijab se tayi wani kyau abunta..

Fitowa suka yi suka tsaya daga bakin kofa, ba'a yi minti biyar  da tsayuwar su ba fitinannen kamshinshi ya fara musu sallama kan tsayayyen figure ɗinshi ya bayyana tafiya yake cike da ginshira da wani kalar ƙasaita hannayenshi sanye cikin aljihu..

Sanye yake da crazy Jean blue me kyaun gaske ya ɗan kama shi se wani silk shirt me zanen art emerald green me guntun hannu, kafafunshi sanye cikin emerald green combus daga gani ka san ba na karamin kuɗi bane, kanshi sanye da same color face cap ya saka baƙin sunglasses da facemask sbd ɓadda kama, ɗan kunnenshi se walkiya yake hakanan zoben azurfa dake hannunshi..

Agogonshi na Fendi dake ɗaure a hannunshi na hagu ya kalla it's almost time ba tare da ya kalli ko ɓangaren dining da cook ɗin shi ya shirya mishi abinci ba ya riƙe hannun Aisha da taje wurinshi da gudu suka nufi waje yana kallon dressing ɗin ta da ya mishi kyau, ko inanta a rufe se ɗan karamin baby face ɗinta, dab da ze fita hidayat da ta biyo bayansu tace

"Good morning sir"
Yace
"morning"
Suna karasa fita, Patrick ne ya buÉ—e bayan zazzafar Porsche É—inshi suka shiga, yayinda hidayat ta shiga gaba ya ja suka fice daga gidan dama tun É—azu ya saka kayayyakin su a booth sanin ogan shi ba tafiya da kaya yake ba..

Saboda shigan dake jikinshi babu wadda ya gane shi a Airport ɗin ma har suka shiga VVIP, ita dae hidayat banda bat bat bat babu abunda zuciyarta ke yi, bata taɓa ganin jirgi ido da ido ba se gata yau ita ce zata shige shi, daga ganin inda suka shigo ma ta san cewa ba wurin regular mutane bane zama yayi kaman a parlornshi briefcase da Patrick ya rako shi dashi har seat ɗinshi ya janyo ya ciro system ɗinshi ya hau operating yayinda Aisha ke zaune kujeran dake facing nashi tana mishi tambayoyi yana amsawa a takaice  anan hidayat ke gane wasu abubuwan..

Har za'a tashi ya ɗan kalleta bata ɗaura seat belt ba and a labarin da ta bashi he's quit sure bata taɓa hawa jirgi ba abunda ya fara kwantar mishi da hankali a tafiya da ita shine bata da hayaniya, button na gefen shi ya danna se ga one of the cabin crew ta shigo..

"How can I help you sir!"
Tayi tambayar cikin tsananin girmamawa da taka tsantsan, kallon hidayat yayi yace
"give her the safety guide"

Da sauri tace
"ok sir"

Wucewa tayi wani cabinet ta ɗauko ta zo ta baiwa hidayat cikin girmamawa, karantawa hidayat ta fara se taji ma ana maimaitawa ta loudspeaker ɗin jirgin, da sauri tayi yadda aka ce da belt ɗin tare da gyara junior ta rufe idanunta har jirgin ya ɗaga sararin samaniya, shi da kanshi ya riƙe Aisha har aka daidaita ya tashi ya maidata Ɗayan kujeran ya gyara mata don already sun kashe wutan jirgin nasu..

A Lagos suka tsaya for about an hours Dukda basu sauka ba su bata dae san sauran mutanen jirgin ba kan suka sake É—agawa sun tafi sun tafi har taji ta gaji, ga ciwon kai ga jiri da take ji, shi kam ko don ya saba ne aikinshi kawai yake abun shi, ita kuma Aisha tayi bacci, chan cabin crew ta zo ta tambayeshi me yake so ya faÉ—a, se ta matso ta tambayi hidayat rasa me zata ce tayi se tace ta kawo mata anything Nijerian dish..

Abincinshi ne ya fara zuwa har ya gama tsakura ya fara kurɓan coffee, junior da ya gaji ze fara rikici ne ta ɗaga tana ɗan mishi rawa da waka se yaron ya bangala dasori yana dariya, a hankali ya sauke idanunshi kan yaron, dariyarshi gwanin kyau, farar ɗaya yaji ƙaunar yaron fiye da yadda yake ƙaunar Aisha, yana so yace ta kawo shi sede bakinshi yayi nauyi, yadda take mishi wasan ya kalla hakwaranta dake jere farare tas a waje hakan ya ba dimples ɗinta duka biyu Daman loɓawa..

ÆŠauke kai yayi ya cigaba da kallon Junior cike da sha'awa daidai lokacin aka kawo mata abinci, ajiye mata aka yi sede junior baze barta ta ci ba don ya iya janye janye gashi se son sauka yake yana ta tsalle yaron is full of energetic..

"Can't u give the child to his father so that u can eat peacefully?"
Cabin crew É—in tayi maganan, rikicewa hidayat ta so yi ta fara kame kame.

Tsam Raed ya miƙe ya zo ya saka hannu ya karɓe shi yana chilla shi sama yaro kam ba se ya bangala dariya ba shima murmushi yayi yace mata

"his name?"

Tace
"junior"
Baki ya taɓe ya nufi kujerar shi dashi wasa yake ta mishi, har ta gama cin abinci aka kwashe abubuwan ta kishingiɗa a take bacci ya sureta, yaron ya gyara a kirjinshi suka kwanta a haka idanunshi a lumshe..

Tafiyar 6 hours ten minutes ya kawo su Paris sun gaji tilis, barin ma hidayat da Aisha da basu saba tafiye tafiye ba, a hankali suke saukowa idanun hidayat na buɗuwa da tsananin kyaun Airport ɗin na Charles de Gaulle(CDG) Aéroport de Paris..

Wasu rantsatsun baƙaƙen GLS 460 4matic baƙaƙen sidik ne suka yi parking gabansu guda biyu bayan sun fito daga terminal ɗin masu ɗaukan trolleys ture da chart ɗin dake ɗauke da kayan su Hidayat, kofofi biyu daga ciki suka buɗu wata kyakyawar matashiya da zata yi 14yrs ce ta fara fitowa sanye da leggings da shirt pink kafafunta combus ne pink se gashinta da ya sha gyara kan karama wacce bazata wuce Aisha ba ta fito itama irin dressing ɗin yayarta ne jikinta rige rige suke yi sede turus suka dakata ganin Daddyn nasu riƙe da wani yaro da basu sani ba..

A tare suka ce
"Daaaaad!" Da wani expression a fuskansu..

Hannunshi É—aya ya wara musu Farah taje ta shige yayinda Norah ta ja gefe tana kallon Hidayat da kuma Aisha ta sake kallon junior da baban su ke rike da shi tace
"daad Qui est-ce?(Who are they?"

Ba tare da ya kalleta ba yace
"ur new nanny nd her family"

A tare suka ce
"Whattt?"

Ɗan ɓata fuska yayi yace
"manners girls and parlez lentement, s'il vous plaít"(speak slowly please)

Ya faÉ—a yana shiga motar da aka buÉ—e mai, duk a tare suka kalli Aisha da Hidayat da suke ji sun muzanta don kirkiri yaran suka nuna basu musu ba, hidayat bata san sadda ta wara idanu ba jin sun ce
"Disgusting...!" A tare suka yarfa hannu suka shige motan da baban su ya shiga...

#like
#comment
#share

                    🖤Gureenjo🖤

KOWA YA GA ZABUWA...
   (DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

                      *PAGE 14*

*FREE BOOK*

*Afuwan today I wasn't myself abubuwa sun cunkushe min ayi hakuri da wannan*

No.1.3 Le Marais
4th Arrondissements, Saint Thomas d'Aquin.

Shine sunan home Address da taga sun yi horn daga bakin hadaddiyar gate É—in, gabaÉ—aya layin gidajen ba kananun Gidaje bane, Gidaje ne da suka haÉ—u suka kuma gaji da haÉ—uwa daga nan inda suke suna kallon Effile tower dab dab dasu kaima ka san me zama kusa da Effile tower ba karamin abun duniya ya tara ba..

Harabar gidan kaɗai abun kallo ne, riƙe da hannun Aisha suka sauko kaman yadda aka buɗewa Moh Raed ya sauko rungume da Junior, ma'aikatan gidan ne a jere cike da tsantsan girmamawa suke mishi welcome..

Hannu kawai ya É—aga musu ya juya ga wata farar baturiyar mata yace
"Miss Mary this is the new nanny, show her around..!"

Cike da girmamawa tace
"Noted sir..!"

Daga haka ya miƙa mata junior ta zo ta karɓe shi cikin taka tsantsan, Juyawa yayi ya wuce rike da hannayen girls ɗin nashi kowacce na zuba shagwabanta da complain ɗinta..

"You welcome, am miss Mary I am the house keeper, can I please show you around Miss...."

Hidayat tayi murmushi tace
"Hidayat.. Thank you nice meeting you"
Chapter 19 · 0% Book details