← Book details Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 74

Sashe 52

Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A kwana ɗaya da suka kara a Paris fasalta irin yadda suke kashe juna da soyayyarsu ɓata lokaci ne, sede dukkansu sun fahimci ba karamin soyayya da shakuwa bane ya shiga tsakaninsu, Yaransu har sun fahimta kuma sossai suka yi murna, washegari suka shirya trip ɗinsu suka yi airport harda Rashida sbd ya nemi ta bi su daga nan se ta wuce Nigeria ga mamakin ta se taga pjet, yau Rashida xa'a hau private jet se farin ciki take su ya sun su se air hostess da captain suka ɗaga sararin samaniya yana rungume da Junior....

*I have been smiling like mumu🤧**

#Vote
#share
Comment

                 🖤Gureenjoh🖤

KOWA YA GA ZABUWA...
   (DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

FOLLOW ME ON Wattpad @Gureenjoh6763

AND ON AREWA BOOKS @gureenjo

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

                      *PAGE 34*

*FREE BOOK*

*My Meerah😍❤️ wannan page ɗin naki ne se yadda kike so za'a yi😘*

Wannan tafiya shi ya zama silar chanzawar rayuwarta gabaɗaya, tafiyar da ya zama silar farin cikinta da samun dawamammiyar kwanciyar hankali, ingantacciya kuma nagartacciya, kwarai Allah ya riga ya mata zaɓi..

Jirgin su be sauƙa a ko ina ba se King Abdulaziz international Airport jeddah, ko a mafarki bata taɓa mafarkin zata ziyarci ɗakin Allah ba, se gata nan a ciki tsamo tsamo kusa da manzon Allah, hawaye ne ya zubo mata daidai sadda suka Haɗa idanu bayan ya gama sauka, da idanu yayi mata alamar hawayen na me? Girgiza kai kawai tayi, tare da kankame hannun Rashida.

Motoci na musamman ne suka zo suka dibe su zuwa masaukinsu, hotel ne me zaman kanshi wadda daga tsaruwarshi da securities É—inshi kama daga mutane da na'urori zaka san ya wuce na ya ku bayi, flat ne na musamman a inda suke É—in parlor da É—akuna huÉ—u, kuma kowanne self content komai da komai akwai a gyare yake tsab.

Baccin gajiya duk suka yi kan su tashi ya musu order na abinci kala kala, nan suka baje a parlor suka ci daga nan suka fita don kallon garin jeddah kan su wuce, dayake Rashida ta san Saudia sossai hakan yasa ya kyale su ya tafi harkokinshi daga karshe seda ya dangana da Riyadh sbd wasu meetings don Saudia suna so su saye shi...

Be dawo ba se washegari amma ko wani lokacin cin abinci za'a shigo musu dasu gasu nan se wadda kowa yayi ra'ayin ci, washegari da yamma ya dawo a daren ya kira wayanta yace mata yana so su É—an fita amma su biyu kawai..

Shiryawa tayi cikin jallabiya peach and red kirar Kasar Oman ya ji ado kam, se bata yafa gyalen ba ta É—auki Red gyale tayi wrapping ta sa red flat shoe, da Rashida suka bar yaran suka fito yana sanye da kananun kaya as usual riga da wando, da kanshi ya buÉ—e mata bayan motar ta shiga, shima ya zagaye ya shiga bayan kusa da ita motar ta bar harabar hotel É—in.

"Hidayah!"
Ya kira sunan cikin husky masculine voice É—in nan nashi wadda seda taji a jikinta rabon da ya kirata da Hidayat ya jima.

"Na'am paapi!"

Ya waiwayo gabadayanshi gareta yana kallonta yace
"alfarma nake roko na san kaman nayi sauri sede ina ganin menene anfanin soyayya idan ba hakan ba, ina son ki kina so na mun fahimci juna bamu da kowa se kawunanmu da yaranmu, don Allah ki bani dama in sake shiga rayuwarki na dindindin"

"paapi ka wuce duk wata alfarma ko roko a gareni, duk abunda ka yanke mana ko zaka yanke mana na tabbatar me kyau ne kuma baze cutar damu ba so na baka dama.."
Ta faÉ—i itama tana kallon shi.

Lumshe idanu yayi ya buÉ—e yana sakin murmushi yace
"Gobe zamu wuce madina, kaman yadda kika sani a aikin Umura zuwa madina is optional duk wani aiki na Umura a Makkah ne kuma a Makkah ya kare, gobe in Allah ya kaimu idan mun isa masallacin manzon Allah za'a É—aura mana aure don ina so ki isa ga É—akin Allah da martabar Aure bisa kanki..!"

Kallonshi kawai take se hawaye ya fara zubo mata, me yafi wannan? Anya akwai wadda ze sakata farin ciki a duniyan nan bayan Raed, ita hidayat ce za'a É—aurawa aure a madina! Ya Allah ina Yusuf, ina umma da su Surayya su zo su ga yadda rayuwarta ya inganta, ta nagartu da samun cikakken masoyi wadda yafi maza dubu a gareta, ita kam me zata mishi ta saka mishi bayan tsabtatacciyar soyayya da kauna marar algus?

"Die hard! Why are you shedding tears? Kin san bana son kukanki ko?"

Hawayen ta share cikin wani murya dake nuna farin ciki, mamaki da kuma sallamawa tace
"Hawayen farin ciki ne, lallai na zama mace mafi sa'a a duniya! ni ce annabi ze shaida aurena...."

Kuka ne ya ci karfinta, tace
"ko a haka ka barni kayi min komai a rayuwata paapi, na gode kwarai Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa ya kaimu gobe lafiya! Ina kaunarka sossai da sossai"

Murmushi ya sakar mata, yace
"ana Aidan uhibbuki hubban khasira(I love you more)"

Murmushi suke sakarwa juna na kauna yana ji ina ma akwai aurenshi a kanta da yayi mata rarrashi yadda ya kamata, zata yi magana taga sun iso Airport kuma mutane suna ɗan fitowa hakan yasa ya fiddo face mask ɗinshi ya saka ya fita hannunshi ɗaya cikin aljihu ya zagaye ya buɗe mata ta sauko suka nufi ciki a tare, in ka gansu bazaka taɓa cewa suna da yara a gida ba, sun yi mugun dacewa barin ma da yake fuskan hidayat kaman gonar auduga sbd farin cikin da take ciki a yau...

Ko da suka isa arrivals tsayawa suka yi yana É—an mata magana, idanunta ne suka sauka kan wata dattijuwa bazaka kirata tsohuwa kai tsaye ba sbd daga shiganta zuwa yadda take tafiya zaka tabbatar da akwai cikakken hutu da natsuwa a tattare da ita, sanye da Atampha riga da zani da hijab É—inta hannunta rike da sandarta tana tahowa, bayanta masu É—aukan kaya ne ture da akwatinta, tsantsar kama da taga suna yi da Raed ne yasa ta kalleshi se taga yana yiwa matar murmushi kan ya kalli hidayat yace

"finally! meet Daadida!"

Fuskanta ne ya kara washewa da fara'a da sauri ta taka ta nufi Daadida, tana zuwa kawai ta rungumeta se ta fara hawaye, Daadida na murmushi ta É—ago ta tace
"Hidayat! Yau dae Allah yayi na ga jikata, masha Allah tabarakallah!"

"Sannu da hanya Daadida kin zo lafiya?"
Cewar hidayat É—in.

Tace
"Alhamdulillah hidayat, sannu kinji tabbas kin cika mun alkawari na, kuma mafarki na ya tabbata, kin zama fitila a gidan Raed Allah ya miki albarka"

Da Ameen ta amsa tana murmushi, yace cikin yanayin shagwaba
"ni kuma fa?"

Dariya suka yi Daadida tace
"kaima Allah yayi maka albarka"
Ya saki murmushi yace
"yanzu na ji zance"

Wucewa suka yi zuwa motar da ta kawo su, aka sanya mata kayan ta a baya, hidayat ce ta buÉ—e mata kofa ta shiga shi ya shiga gaba hakan yasa hidayat ta koma É—aya gefen inda ya zauna É—azu ta zauna, suka bar Airport É—in.

Kwarai Daadida dattijuwar arziki ce, daga zuwan su gidan zuwa tayi wanka taci abinci ta huta duk kusan suna tare da Hidayat ko wani motsi tayi zata tambaye ta abunda take so, suna yi kuma suna hira cikin hikima Daadida ke wayar mata da kai take kuma nusar da ita menene aure, abunda ba'a mata ba a zaman ta da Yusuf, dukda wasu ta sani sbd islamiyya, wasu kuma ta sani sbd experience É—inta na aure sede ba duka ba, wannan na nagartacciyar tsohuwa ne me cike da hikima da sanin makamar aure da na rike miji a gargajiyance.

Yaran basu shaku da Daadida sossai ba, dukda haka sun yi mata maraba sun kuma gaida ta tana ta masifar da wanchan pastorn ne baban mamansu da tuni sun cike wurin da hayaniyar ganinshi amma Raed ji yaranshi a gabanta, Norah kam ma tun lokacin rasuwar mahaifiyarsu bata sake ganinta ba se yau don bata zuwa Nigeria.

"Ai ya kamata daga nan Nijeria Zaku yi bari uban naku ya dawo ma"

Dariya kawai Rashida da Hidayat suka yi ashe da gaske take bayan ya dawo ta tabbatar mishi daga nan duka tare zasu tafi da Hidayat akwai abubuwan da take son ayi mata, be Musa ba yace Allah ya kaimu.

Washegari karfe É—aya na rana a cikin garin madina ya musu, kusan irin hotel da suka zauna a jeddah anan ma haka suka zauna, garin madina gari ne me cike da tarin ni'ima da albarka, jinta take wasai gata ga manzon Allah, har hawaye Seda ta zubar zuciyarta a cike da farin ciki, rashida na taya ta da su Norah.

Kaman yadda ya faÉ—a bayan sallar azahar al'ummar annabi suka shaida É—aurin auren *HIDAYAT ABUBAKAR DA MUHAMMAD RAED* akan sadakin sisin É—anyen gwal wadda idan za'a musanya kuÉ—in shi da Naira ba kananun kuÉ—i bane, kuka sossai tayi na farin ciki, Annabi ya shaida Aurenta kwance cikin kabari, zata isa ga ubangijinta da martaba da darajar aure a kanta ko a mafarki bata kawo kanta nan ba.

Kwanansu biyu a madina suna ziyarce ziyarce, suna zuwa inda annabi ke kwance ta fara mishi sallama kan ta fara jero mishi salati tana zub da hawaye cikin tattausar murya sbd ba'a so ka É—aga murya kaman yadda ya zo a Suratul Hujurat, dukda a kwance yake sede yana ji kuma yana amsawa.

Daga nan suka garzaya Makkah, duk fa Daadida bata yarda hidayat ta keɓe da Raed ba, shima be matsa ba don tun bayan da aka ɗaura auren da ya dawo ya sanyata jikinshi yana zub da hawayen farin cikin mallakarta itama ta kankame shi tana mishi godiya Daadida ta janyeta suka yi ɗakinta daga ranar ko hannunta be kara tabatawa ba sbd Daadida da tayi uwa tayi makarbiya..
Chapter 52 · 0% Book details