← Book details Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 74

Sashe 24

Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau Asabar wankin da Hidayat ɗin tayi a washing machine ta sauka kasa don son shanyawa, bata taɓa ma zuwa ta ɓangaren igiyoyin nasu ba se yau, bayan banda shuke shuke da katuwar Mikano ɗinsu se ƴar lilon dake kada kanshi da kanshi cikin kyakyawar field dake shimfiɗe da grass carpet se wasu kujeru haka na shan iska babu abunda yake wurin.

A natse take shanyar har Farrah ta zo ta wuce ta gefenta bata tanka ta ba, chan bayan inverter ɗin ta tafi se gata da wani katoton police dog brown color me baƙin baki banda dilalar da miyau babu Abunda bakinshi yake.

Wani irin faɗi gaban Hidayat yayi gashi su kaɗai, yadda Farrah bata ƙaunartan nan tana da tabbacin in ta gane tana tsoron kare zata sakar mata shi wannan karen kuwa yadda yaken nan se ya cinye ta tsab..

Ganin da gaske nufota suke yasa ta fara ambaton Allah, jikinta na daukar rewa suna isowa wurin kuwa karen ya fara zuwa wurinta yana shunshuna ta, duk yadda take kokari wurin ganin bata firgice ba hakan be yiwu ba, wani ƙara ta saki tana kiran Sunan Allah a take karen yayi kanta bata tsaya ba ta saka gudu wadda ya sa Farrah tuntsirewa da dariya..

A gigice hidayat ke zagaye wurin karen na bin ta, kokarin barin wurin take se ta harÉ—e ta nufi faÉ—uwa wadda yayi daidai da isowar Raed wurin sbd tun ihun farko ya ji kuma ya ji haushin kare ya kuma san Bingo ba sanin hidayat yayi ba idan kuwa hakane cizonta ze yi..

Cikin hanzari ya sanya hannayenshi biyu ya riƙe mata kafadu don hanata faɗuwa sede dayake a gigice take bayanta take kokarin Juyawa taga ko karen ya iso ta aiko ganin gashi ga ita yasa ta sake sakin ihu tana runtse idanu hawaye wani na bin wani duk ta ruɗe shima se ta ruɗa shi, da sauri ya janye ta ya maidata bayanshi ta kama Rigan shi ta riƙe kamkam kam..

"Bingo!"

Ya kira sunan karen ganin shima kokarin bin hidayat É—in yake, sarkar wuyan shi ya kama yace
"is ok, she's not a bad person oya back to your cage"

Juyawa karen yayi ya fara gudu yana karkada bindi, hakan ya saka Raed kokarin juyowa sede Hidayat ta ki sake Rigan shi har lokacin idanunta a runtse hawaye wani na Bin wani, daga yadda suke tsaye yana jin bugun zuciyarta..

Idanunshi ya kai kan yadda ta riƙe mishi riga kamkam hakan ya saka shi sakin murmushi..

"Ya tafi fa!"
Yayi whispering yana sake kallon É—an karamin farin hannunta dake rike da riganshi, da sauri ta saki tana matsawa baya..

Juyowa yayi ya kalli fuskanta yadda yayi kaca kaca da hawaye É—an karamin bakinta red se motsi yake alamar Adu'a take, hakan ya sa be san sadda wani murmushin me yanayi da dariya ya sake subuce mishi ba a fili yace

"duk wannan tsoro ne?"

Da sauri ta juya ta nufi ficewa daga wurin don abubuwa dayawa ne suka haɗu mata, ga tsoro dake barazanar sumar da ita ga kusancinsu dake haifar mata da wani yanayi marar misaltuwa ga kunyan yadda yaga take kuka sbd kare ga kuma wani dariyar da yayi da bata taɓa ji ko gani daga gareshi ba sbd shi mutum ne me ƙarancin fara'a..

Shi kuwa Juyawa yayi har lokacin yana murmushi ganin wai kuma kunya taji, faÉ—a ya fara yiwa Farrah don ya san ita ta fito dashi se ta kama kuka wai yana fififita nanny sama da ita daga karshe rarrashi ya koma sbd yana son yaranshi fiye da misali..

A daren ranar tana kitchen tana tattare abubuwan da tayi anfani dasu na abincin dare ya shigo, ƙasa ta soke kanta tare da cewa
"Barka da shigowa sir, akwai abunda kake bukata ne?"

Girgiza kai yayi ba tare da ya kalleta ba yace
"no cigaba da aikinki"

Fridge yaje ya É—auki ruwa sbd na parlor ya kare ya kuma kira Paul akan a kawo, har ya kai kofa yace
"ehen when u r done meet me at my room"

Kai ta gyaÉ—a, har ya fice bayan ta gama ta wanke hannayenta tare da nufan É—akin shi da take jin hayaniyar junior da su Norah, a kan couch ta same shi yana duba system da ya ajiye akan center table yaran kuwa suna kan carpet suna wasa da Junior yayinda Farrah ke kallon cartoon a TV É—in É—akin...

A ƙasa ta zauna ɗan nesa dashi kanta kasa sbd daga shi se shorts jikinshi ba riga kaman yadda ta ga yake kaunar zama haka, banda murdaddun muscles ɗinshi da shafafen cikinshi har kwantacciyar gashin dake jikinshi babu abunda take iya kallo..

Wasu takarda ya Mika hannu ya ɗauka tare da mika mata, a ladabce ta karɓa yace
"it's for ur studies, kin samu gurbin karatu a Paris science et lettres"

Wani irin sanyin daaɗin da bata taɓa ji bane ya rufe ta, cikin tsananin farin ciki ta fara mishi godiya, murmushi kawai yayi ta juya tana nunawa su Norah da Aisha suma murna suka taya ta..

Haka Hidayat ta kwana yiwa wannan bayan Allahn Adu'a, wasa wasa abu kam ya zama gaske se ga hidayat a one of the best universities na duniya, karatunta be hana ta kula dasu Farrah yadda ya dace ba..

Tun kan asuba zata fara HaÉ—a musu breakfast ta saka musu na makaranta ta zo tayi wanka ta gabatar da sallar asuba ta je tayiwa Farrah wanka ta zo tayiwa Aisha da Junior duk su shirya, a sadda zasu fita tafiya makaranta kuwa a sannan itama zata fita tafiya school, bus take hawa kuma Alhamdulillah ba karamin fahimtar karatunta take ba..

Da yamma take yiwa su Norah karatun Qur'ani da Æ´an tarihin annabawa, wadda Farrah bata cika maida hankali ba amma Norah na matukar so, Junior kuwa har ya fara buÉ—e baki a Æ´an watannin nan da suka yi yanzu watanshi takwas da sati biyu, da Daddy ya fara buÉ—e baki wadda yake gani kaman shine Mahaifinshi..

A ɓangaren career ɗin Raed banda cigaba babu abunda yake gani, don sede idan baya cikin wasa za'a kira musu faɗuwa, ji dashi ake sossai a PSG har wasu clubs ɗin na fafutukar sayanshi...

Kwatsam wani ranar Laraba Raed da kanshi ya fita dasu da yamma sbd rikicin da Junior ke yi yasa yace duka su zo su je su sha iska kadan, Norah ce ta saka Hidayat dole suka fito..

Sanye take da red palazzo trouser se white shiffon shirt me dogon hannun ta yafa red mayafi se ta saka white Shoe, duk cikin irin sayayyar da in har ya fita da yaran tare suke fita se ya ce itama ta É—auka..

Yaran duka suna zaune cikin wata kyakyawar runfa bayan sun yi ordering ice cream flavor ɗin da kowa yake so, bayan an kawo se Farrah ta ɓarar wa Aisha da nata wadda ya so sakasu faɗa shine Hidayat ta bata hakuri ta mike ta fice don samo mata wani..

Ta fito kenan riƙe da ice cream ɗin shi kuma ze shiga wani karo suka ci ba tare da duk sun ankara da juna ba..

"Subhanallahi..!"
Shine abunda ya fito daga bakinta wadda ya saka shi saurin kallonta don be tsammaci jin sunan Allahn a irin wurin ba..

Karab idanunsu ya faÉ—a cikin na juna.

#like
#share
#comment

                  🖤Gureenjo🖤

KOWA YA GA ZABUWA...
   (DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

                      *PAGE 17*

*FREE BOOK*

"Ya Hamza..!"
Ta faɗa tana wara dukkan idanunta da ta saka musu kwalli waje, duk da yadda ya kara girma da jiki ya tara kasumba gwanin burgewa hakan be hanata shaida shi ba a kallo ɗaya sbd shine mutum na farko da ya fara nuna mata ƙauna a duniya bayan Abba kuma kullum yana ranta..

Shi kuwa kokarin ce mata sorry yake amma ganin ta kira sunanshi yasa ya É—an dakata tare da sanya mata idanu na seconds se kuma ya waro su gabaÉ—aya yace
"Hidayat!"

Dariya suka saki a tare yace
"what a coincidence! Hidayat me kike yi a Paris? Taya kika zo?"

Tana murmushi tace
"labari ne mai tsawo"

Yace
"then mu je mu zauna se in ji da kyau, aurenki fa?"

Kanta ta É—an dukar tace
"ya mutu"

Wani sihirtaccen murmushi ya saki tare da Juyawa ta bi bayanshi Sam ta mance ma da Aisha jiran ta take da ice cream ɗin da ya ɓare again, wurin wasu kujeru guda biyu suka je suka zauna yana tsokanarta akan ta ƙara girma tayi kyau tana ta dariya..

Daga inda yake zaune sanye da designers Riga da wando na kamfanin Versace idanunshi sanye da designer shade na Swarovski ba karamin kyau yayi ba barin ma sabon diamond ear ring da ya sauya dake ta kyalli, tun da ta mike ya tsinci idanunshi a kanta har ta shige be dauke ba, daidai fitowanta da karon da suka yi duk a kan idanunshi..

Ganin suna dariya da magana alamu sun san juna yasa ya ɗauke kai yana jan tsiririn tsaki, agogonshi ya kalla se ya ɗauke kai again, Aisha dake zaune ya sake kallo ya ɗaga kai ya kalli sun nemi wuri sun zauna suna ci gaba da dariya, wani irin ɓacin rai ne ya bijiro mishi da be san na menene ba, miƙewa yayi kaman ze nufi inda suke se ya fasa ya shiga shagon ya sayo wani ice cream ɗin ya zo ya ba Aisha duk yana kokarin hana idanunshi kallon ɓarayin da suke..

Ita kuwa Shap ta ma mance dasu, a hankali take ba Hamza labarin abubuwan da suka faru tun tana dauriya har ta fara kuka tana zuwa wurin rasuwar Abba ta dakata tana hawaye sossai, handkerchief hamza ya ciro ya mika mata ta saka hannu zata karɓa se suka Haɗa idanu..
Chapter 24 · 0% Book details