← Book details Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 74

Sashe 40

Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wannan kallon ma ya kamata ta mishi nashi karatun don ya fita musulunci.. Ze yi magana kenan kimorah da ta shigo tuntuni tace

"what the hell is going on here? So Raed that's the reason? This filthy nanny is the reason why you are giving me hard time?"
Yadda take magana da masifa ne yasa duk suka zuba mata idanu.

Da sauri tayi kanshi zata taɓa shi kaman wadda yaga wuta yayi sauri mikewa yana ja baya yace
"don't! Don't you ever lay ur finger on me"

Wani irin kukan kura tayi tayi kan Hidayat....

#Vote
#share
#comment

                    🖤Gureenjoh🖤

KOWA YA GA ZABUWA...
(DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

*PAGE 26*

*FREE BOOK*

Fisgota yayi da karfi kan ta ƙarasa kanta ya nuna ta da yatsa yace cikin harshen turanci
"karki kuskura ki fara abunda bazaki iya ba... Now! Get out of my house...!"

Idanunta gabaÉ—aya ta waro tace
"what do you mean?"

"I mean it's over between us.."

Kuka ta fashe dashi a zuciye ta wuce room da ta kwana ta janyo kayan ta ta fito ta sauka da gudu tana kuka.

Tsaki yaja yana É—auke kai daga kallonta se suka HaÉ—a idanu wani irin numfashin tsoro take ta saukewa, kanta ta mayar kasa tare da cewa
"Seda safe"
Bata jira amsar shi ba ta wuce

Washegari shi ya sauke ta a makaranta Dukda dae ba wani hira suka yi ba bayan gaisuwa sede fuskanshi a sake ba kaman sadda yake fushi ba kuma sossai taji daaÉ—in hakan.

****

Roba me É—auke da garin kunu kaÉ—an da kuma kullin tsamiya da gyaÉ—a ta dire mata.
"Tashi ki yi min kunu karki yarda tsamiya yayi yawa kuma ya nuna kar yayi ruwa"

Kallonta Surayya tayi zata yi magana suka HaÉ—a idanu da Umma ta girgiza mata kai alamun kar tayi.

Miƙewa Surayya tayi ta ɗauki robar kunun ta yi bakin murhu tana mitan..
"Kece matsiyaciya da kike shan kunu in ba da yanzu rayuwa ya chanza ba ai ko sunan kunu ba'a kira mana gida daga custard se oat"

Tak bata ce ba ta samu kujera ta zauna, a cike take da su dukkansu kuma kaÉ—an take jira kab ta saita musu zama, umma dake zaune cikin Asabar da Lahadi na kodaddiyar Atampha ta zabga tagumi tana Tunanin Abba

A lokacin da yayi mutuwar son tayi karatu ko don bayan ranshi tayi amfani da aikinta wurin kula dasu sede Sam ta ƙi tana ganin yana dashi ko ya mutu ba zasu yi rashi ba, ya sha gayamata dukiyar gado iska ce tsab se ta iya bin me shi cikin lokaci ƙankani, ya sha gayamata rayuwa ba tabbas sede duk tayi watsi da hakan.

Yau a yanzu wa gari ya waya? Da Kausar taƙi karatu ma ita ce ta bata goyon baya haka Abban ya hakura ita kuma fahiriyya a sadda zata auri mijinta da take aure ya shaida musu ba karatu a gidanshi Abba ya ƙi bada ita ba karamin bore suka yi ba haka ya hakura ya zuba musu idanu, ita Surayya da take ɗan karatun an kore ta saboda rashin kokari gatan da ta nuna mata na Hidayat take yi mata komai ciki har test da exams ya ja mata.

Yusuf bashi da maraba da mahaukaci, wanchan kuma bata ma san duniyar da yake ba..! Wata ashariya da hafsatu ta saki ne ya katsewa Umman tunani.

Mari ta gaure Surayya dashi tace
"don uwarki wanchan dake zaune haka na baki umarnin dama min kunu?"

Surayya tace
"Wallahi ba de uwata b..."

Kwashe ta da tayi ya hana maganan karasa fitowa, se ga Surayya a ƙasa wanwar dama gata kaman karan kaɗa miya, danne ta hafsatu tayi bata damu da zafin kunun ba ta fara ɗura mata tana cewa
"yau se nayi maganin bakin rashin kunyar nan..! Zaki san ni kika yi kokarin zagi"

Ga tsinkakken kunu, ga Shakura, ga tsami saboda tsamiyar da ta labta don mugunta ga rashin sugar da zafin kunun duka ya HaÉ—ar mata shidewa take sede ko a jikin hafsatu, ba ta sake ta ba seda taga kunun na fitowa har ta hanci ga idanunta kaman garwashi ko da ta sake ta mikewa tayi ta fara kwara amai tana tari kaman zata mutu.

Idanu kawai umma ta zuba mata hawaye na gangaro mata a idanu tana tuna sadda suka yiwa hidayat É—uren custard, lallai annabi yayi gaskiya da yace yadda kayi haka za'a yi maka.

Surayya bata gama tari da aman ba suka fara jin hayaniya a kofar gida, tsaye umma ta mike ganin an shigo da Yusuf ranga ranga jiki jina jina.

"Lafiya me ya faru?"

"Ki Ja wa wannan mahaukacin É—an naki kunne ko kuma ku samu mari ku É—aure shi yau duka kawai ya samu gobe kuma ina ga sede bindiga..."

"Ban gane ba bawan Allah me yayi?"

Wani daga cikin waenda suka shigo da shin yace
"zaki gane ne a sadda aka shigo miki da gawarshi in ba mahaukaci ba daga ganin É—an DPO rike da hannun Babanshi ya ruga ya chakwame yaro yana kiran sunan wani Usman, yaro ya firgice anyi anyi ya saki É—an mutane ya ki ya kwankwame shi seda DPO yasa yaranshi suka lallasa shi kan ya saki yaron don azaba, to wlh gobe yayiwa soja haka harbe shi ze yi ba ruwanshi.."

Yusuf din umma ke kallo har suka fita, ba karamin duka ya sha ba se hawaye ke zuba a idanunshi.

Ta kalli Surayya da ta lallaɓa ta miƙe ta shige ɗaki, ta san matarshi na ji sede bazata fito ba ko in ta fiton ma sede ta kara mishi akan ciwon da nata tashin hankalin.

Murhun da Surayya bata kashe ba taje ta É—aura ruwan zafi ta zauna ta zabga tagumi har yayi ta surka kaÉ—an ta zo tana matse mishi yana ihu tana share hawaye cike da Tunanin mafita.

*****

"ya hamza..!"
Zainab ta kirashi.

Firgigit ya dawo daga duniyar da ya shiga yace
"uhm baby hidayah"

HaÉ—e rai tayi ji wani salon iskanci, zata fara magana ya tuna barnar da yayi se yayi sauri cewa
"Don Allah kiyi haƙuri! Faɗamin menene?"

Harara ta zabga mishi ba don maganan da take son faÉ—a mai ba da ta bar wurin don yanzu zancen hidayat kaman ruwa yake a wurinshi, motsi kaÉ—an se ya ambace ta ta rasa wani kalar kyau hidayat É—in ke dashi da ze susuce a kanta, ta rasa da wani irin Boka hidayat ke tsafi da zata kanainaye mata miji ta hanata zaman lafiya a gida, kab duniya in kace wa ta tsana to hidayat ce..

"Ina so in na haifi namiji a saka mishi sunan Abbana.. Idan kuma macece se ta ci sunan Hajiya ka yarda?"

Kallonta yayi na mintuna kan yace
"idan macece sunanta Hidayat.. zainab"

"mene? Sunan wanchan karu...."

Wani irin tsawa ya daka mata
"karki kuskura ki sa in nuna miki ɗayar kala ta, wallahi a duk sadda kika sake yin kuskuren danganta hidayat da mummunan kalma se na lahira ya fi ki jin daaɗi in kina Tunanin wasa ne kuma ki gwada... Sannan ina so ki rubuta ki ajiye in har nine uban abunda  ke cikinki in har dae mace kika haifa babu fashi sunanta Hidayat..!"

Ya faɗa cikin zafin ran da hajiya ke sa mishi tension ɗin kuma sanadiyar zainab shiyasa take matukar bashi haushi, ya tsani mutum me kai ƙara anyhow zainab kuma tambarin ta kenan.

Be gama Tunanin ba Wayanshi ya fara kira dubawa yayi yaga hajiya, ya tabbatar zainab tayi aikin da ta saba, tsaki ya ja yana ƙara ji tana fitar mishi a rai, kaman ba ze ɗauka ba se kuma ya ɗaga

"Sannu isasshe..! Wato dayake hidayat ɗin itace uwarka shine zaka tada wa matarka jijiyan wuya akan ɗan cikin da ita ta ɗauki rainon kayan ta kuma zata sha wahalar nakuda ko? Wallahi hamza ka kiyayi ɓacin raina. Wai da wani irin Boka wannan hidayat ɗin take takama ne?"

Yace cikin muryar da ke nuna lallai ranshi a bace yake an taɓa hidayat.
"Hajiya hidayat baiwar Allah ce don Allah ki dena danganta ta da Boka, kiyi hakuri kuma amma na riga nayi rantsuwa in dae har mace zainab ta haifa sunanta Hidayat."

Kasa magana hajiya tayi daga karshe tace
"na yarda asiri gaskiyar me shi, wato ni kake sa'in sa da yau ko? To ba matsala zan ga uban da ze yarje maka auren ita hidayat ɗin take ko wa.. Sannan in har  ni na haifeka ka tsallakeni ka sakawa ɗiyar ka sunan wata bazawara wallahi zaka gane baka da wayau, shashasha kawai"

Kit ta kashe wayan.

Takaici ya saka shi jin kaman ya sa hannu a kai yayi ta ihu, wallahi shi karan kanshi be san yaushe ya fara yiwa hidayat ɗin irin wannan son ba, gashi Allah ya ɗauki ran kakanshi wadda ya taɓa yi wa hidayat gyaran hannu da ya san kwarai ze shige mishi gaba wurin ganin ya mallake ta.

Gidan ya tafi don in ba Wurin Abban shi yaje ba baze samu natsuwar da yake buƙata ba, in ka ganshi kaman ba hamza ɗan gayu ba, ya tara kasumba wadda ya saka ramarshi fita, da Tunanin kasancewar hidayat inuwa ɗaya da Raed yake kwana yake tashi, ko ball yaga ake yi da PSG in har ya kyalla ido ya ga Raed ya ga irin kyaun sura da baiwa da Allah ya mishi se yaji kaman yayi hauka.

A gaban Abban ya zauna yana rike da hannun shi ya fara faÉ—a mishi abunda hajiya tace kaman Abban na ji.

Har ya gama yayi shiru, shi ba me yawan abokai bane Dukda yana da su ɗin sede be da maganan da ze sa ya iya baza musu duk wani sirrin shi, yana matukar kaunar Abban shi kaman yadda yake tuna sadda yake ƙarami Abban ke matukar ƙaunar shi ya san shi ze fahimce shi, Hajiya don tana mace ne ta kasa fahimtar shi.
Chapter 40 · 0% Book details