← Book details Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 74

Sashe 74

Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Da kyar ta jira Raed ya dawo ta fesa mai suka yi ta jin daaÉ—i.

8YEARS LATER

Tsaye tayi hannu a kwankwaso tana kallonsu
Norah da ta zama matashiyar kyakyawar buduruwa ta hautsina gabaɗaya parlorn wai tana neman Nose percel ɗinta da Junior ya ɓatar, Farrah da Norah kuwa wai suna gwada water gun ɗin Najwa da Maher katti dasu ƴan mata, shi kuwa bawan Allah Nawaf na zaune gaban TV yana kallon avengers yayinda Junior ke cin abinci.

"Lallai ma Yaran nan wai me kuka maida ni? Ji parlorna kaman na mahaukata? Norah, Farrah, Aisha da girman ku?"

Duk natsuwa suka yi don sun san halin mommyn tasu bata musu da wasa kaman Daad, kallonta suke yi sanye da decent suit da mayafi se after dress hannunta rike da brief case.

"Sorry mommy"

Harara ta watsa mishi tace
"Acici ba, ai kai kam idan aka ce yau ba abinci duniya an bonu da kai Junior"

Da sauri Nawaf ya tashi yace
"mommy welcome"

Tace
"zo babana damo sarkin haƙuri"

Rungumeshi tayi shine farkon É—an da ta haifa da Raed, wadda yake shekara takwas yanzu tana matukar kaunar yaron saboda hakuri da sanyin halinshi kuma sunan mahaifinta sannan Usman É—inta Raed ya mayar, tana kallon Norah dake final year medicine tace
"Ina yarana?"

Farrah tayi saurin cewa
"suna bacci mommy"

Bayan Usman(Nawaf) da four years ta sake haifan twins Mairamu da Abubakar sunan iyayenshi shiyasa suka musu inkiya da Najwa da Maher.

Tace
" Naji, ku tabbatar kun tattara min parlor tsab kan in shiga in fito in ba haka ba zan ga me Bi na final wasan Daddy"

Da gudu suka hau tattare, ita kam É—aki ta shige yau Raed yake wasan shi na karshe daga shi ritaya ze yi su koma Nigeria amma zasu bar Junior saboda shine ya É—au kafan Raed kwallo yake so kaman hauka har yanzu ba'a ce mishi junior zallah se Raed junior, yana makarantar horas da yara en kwallo.

Cikin awa biyu suka fito a haɗe kaman ka sace, hidayat ta saka wani blue palazo se rigar Al nassr Yellow da blue bayan rubuce da sunan jarumin ta,ta kama daidai cikinta da pin ta baya yadda ya zauna mata kaman dama chan haka aka yo shi, jersey scarf blue ta zagaye kanta dashi se wani hill silver, ta riƙe jakanta na kamfanin D&G blue idanunta sanye da sunglasses Sam bata tsufa kyaunta da kyaun halin ta a kullum shi kowa ke yabo, ga iya ɗaukar wanka.

Tana yawan zuwa Nigeria ita kam sbd a chan tayi call to bar Sannan ta kan karɓi case musamman ta je Nigeria shiyasa kowa ke fatan mijinta yayi retire su dawo don za'a ga jajirtacciyar barrister me faɗa akan irin abubuwan da ake yiwa mata a Gidajen mazaje da ma kan hanya.

Yaran kowa ya ci wanka cikin Al nassr jersey da kalolin wankansu, Motoci uku suka yi zuwa babban filin wasan, hidaya na jan nata, Norah ma na jan nata se driver na jan na karshe, a gaba gaba aka jera su har aka fara wasa da zafi zafi.

Yana cin kwallon farko ya É—ago yana kallonta yayi mata alamun zuciya da hannunshi alamun ya sadaukar mata da kwallon, murmushi me kyau tayi ta mishi blowing kiss ya dafe zuciya yana murmushi kan ya cigaba da wasa, haka seda ya sha ball uku yana mata dedicating a haka wasa ya tashi.

Saukowa suka yi filin aka fara hotuna ana taya shi murnar retire, karramawa da ya samu ba'a magana, yana cikin tarihin Kasar Saudia a harkar kwallo na har abada don babu irin nasarar da be samar musu ba, Seda aka kusa tashi se ga Abba, Maami da en biyunta dake da 8yrs suma Zayd da zayyad, da gudu su Maher suka je suka rungumesu suna kira uncles.

Se ga Ummi da ta auri wani ambassador suna zama US ita da yaranta uku biyu mata É—aya namiji, chan se ga Rashida ma da nata familyn tana auren babban hafsin soja na Nijeriya yaranta biyu.

A take media ta É—auka
"Love❤️🫶Moh Raed dedicated his final goals and shows her his heart during his last match in history, later she and the children descended from the stands onto the field🥹🫶"
Hotunan su se yawo yake platforms

An sha hotuna an kuma sada zumunci, inda daga karshe suka wuce gida kwana biyu suka kara suka juyo Nijeria aka maida Junior hostel har kuka yayi gidansu na nan kaman na Paris don su kan je vacation.

Mahaifin mamansu ya rasu Allah be yi ze karɓi musulunci ba, Hajiyar Hamza ma ta cika bayan ta shafe shekara bakwai tana fama da lalura karshe har cisgar naman jikinta tayi tayi kan ta tafi inda ake girban abinda aka shuka.

Ko da suka dawo Nijeriya gabaÉ—aya an chanza tsarin gidansu zuwa wani na daban hadadde, su umma sun zo yi musu murna khausar na auren wani dattijo itace matarshi ta huÉ—u, se fahariyya dake auren wani police su biyu ne matan nashi se Surayya da ko shekara bata rufa da auren wani ma'aikaci redio suna sana'ar su har abada kuma suna godewa Hidayat suna sanya mata albarka.

Kannen Raed ma duk sun yi aure, waenda suke gidan mazajensu ma be Barsu ba seda ya tabbatar a ko yaushe babu abunda suka nema suka rasa da taimakon sana'o'insu.

Bayan sun natsu ya fara harkar business É—inshi ka'in da na'in, ita kuma hidayat ta fantsama ta zama topic da kowani namiji azzalumi yake tsoro, sossai ta jajirce wurin zama mace me kamar maza.

Bayan wasu watanni Raed ya gane dangin mahaifiyarshi, mahaifiyarta da kuma yannenta maza biyu se kanwar ta mace É—aya sun dawo neman Mairamu aka kwatanta musu gidan Raed da taimakon sisters É—inshi na nan gembu suka isa Kano.

Sossai yayi farin ciki Daadida ta nace sede su zauna tare ba se an sake nemar musu wani gida ba, mazan ya saka su cikin business É—inshi.

Kwance take a kirjinshi tana bashi labarin wani mutumin da aka yanke mai hukuncin shekara biyar gidan yari da tara me yawa akan irin zaluntar matarshi da yayi cikin azabtar wa.

Yana shafa bayanta yana sauraron ta yana murmushi yace
"in dae da irin ku Hidayah maza ba zasu zalunci mata ba, su kan manta cewa macece ta haifesu ta kuma raine su har suka zama abunda suka zama, a ko yaushe mace abar tausayi da kulawa ce, Allah ya cigaba da dafa miki matata, kwarai ina kaunarki,zuciyarki tsarkakakkiya ce shiyasa Allah be taɓa bari kin taɓe ba, I love you hidayah today and always karki manta da hakan"

ÆŠagowa tayi tana shafa hancinshi tace
"A da ban san kaina ba, kai ka tsince ni ka zamar dani mutum wacce kowa ke alfahari da ita, da kowani namiji irin ka ne da mata basu sha wahala ba a duniya you are not just my favorite person you are my everything Muhammad Raed, I cannot breathe when you are not near. I love you"

Ta karashe tana kissing lips ɗinshi, ya juya ta ƙasanshi yace
"wai me sirrin ne?"
Yayi maganan yana dage mata gira da sauri ta rufe idanunta tana dariya sossai...

TAMMAT BI HAMDILLAH ABUNDA NA RUBUTA DAIDAI ALLAH YA BANI LADAN ABUNDA KUMA NA YI KUSKURE INA ROKON ALLAH YA YAFE MIN, ALLAH YA KAWO MU KARSHEN WANNAN LITTAFI GODIYA ME DUMBIN YAWA A GAREKU DAUKACIN MASOYAN KOWA YA GA ZABUWA.....

GODIYA NA MUSSAMMAN ZUWA GAREKU

FAV SIS(HANEEFA MOHD GURIN)
MAMA TANKO SHANONO
AUNTY SAFEEYA
UMMULKHAIRI
MAMAN SADIQ
MAMAN KHALIL
MAMAN ALI
SIS JIDDAH ADAM
AUNTY FARIDA
MOM MUNEEFA
AMEERATUH
SIS AISHA USMAN KUSHERKI
MAMAN AYSHAT
SIS SADIYA UMAR ADAM
SIS KHADIJA QUEEN
SIS FIRDAUS

DA MA WAENDA BAN KIRA SUNA BA KU SANI WALLAHI NA JI DAAÆŠIN TAFIYAR NAN DAKU KUMA INA MATUKAR GODIYA BISA HAKURI DA KUKA YI DANI.

ALLAH YA HADAMU A DIDDIGAR ƘAYA... 🥰😍❤️

                 🖤Gureenjo🖤
Chapter 74 · 0% Book details