← Book details Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 74

Sashe 59

Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Princess wannan ma Abbanki ne, shine babban amini na minister of finance na yanzu"

Dukawa tayi ta kara gaida shi tana murmushi shima ya amsa cikin fara'a yana mata barka da haduwar su da mahaifinta, Abinci ta zuba musu dukkansu biyu don tana ji Abbanta na maganan tun bayan da ya fito sallar asuba yayo nan don tun jiyan be san yana asibiti ba.

Raed da Daadida da kuma yaran suka wuce É—akin Baba Buba, se bayan fitansu Abbanta yace
"Yayanki hamza ma yana samun sauƙi ɗazu ya bar nan!"

Tace
"Abba bari na kai mishi abinci ko?"

Yace
"eh ya kamata! Don ban ga hajiyar shi ba banda tabbacin ta zo ko bata zo ba, matarshi kuma na jego"

Kai ta gyaÉ—a kan ta É—auki basket É—in ta fice bayan ya gayamata room number, da sallama ta shiga É—akin yana zaune kan gadon ya zubawa gini idanu, duk ya rame ya lalace kaman ba hamza ba.

Kallo É—aya ya mata ya É—auke kai, ta karasa ta zauna bisa kujera kan tace

"Yaya ina kwana? Ya jiki?"

Kallonta yayi kan yace
"lafiya na gode!"

"Ba dae fushi kake da hukuncin ubangiji ba yaya? Duk abunda fa kaga ya samu bawa muqaddari ne daga Allah kila taka jarabawar kenan, don Allah ka kwantar da hankalinka ka samu lafiya ko hankalin Abba ma ze kwanta! Yanzu ka fara rayuwa saboda yanzu ne ka fara tara iyali please be yourself for the sake of Allah, Abba and ur little child"

Hawaye masu zafi ne suka zubo mishi yace
"Meyasa se ni za'a hukunta da laifin mahaifiya....."

"Shhhh Astagfirullah! Karka yi saɓo mana yaya! Ka jingine duk wata damuwa a gefe ka sa a zuciyarka ni haramiyarka ce, ko da Raed ko ba Raed babu aure a tsakaninmu ko da mu biyu kaɗai muka rage a aduniya, don Allah ka komawa Allah duk abunda ya sameka harda sakaci wurin neman zaɓin Allah"
Ta karashe a tausashe.

Kai ya gyaɗa mata, jakanta ta buɗe ta fiddo counter ta bashi, ya karɓa yayi mata godiya.. Abinci ta saka mishi tana zaune a gabanshi har ya ci mai yawa, bayan ya sha kunun gyaɗar ya gama yace

"Amma me kike Tunanin hajiya tayiwa mahaifiyarki da zafi haka? Hajiya wasn't herself tun jiya kaman akwai abunda ya taɓa ta, she called asking for some huge amount of money daga account ɗin Abba ban bata ba na dae bata abunda zan iya daga nawa account ɗin, like she was desperate!"
Ya faÉ—a wondering don abunda ya hana shi bacci kenan Tunanin me hajiya zata yi da makudan kudin da ta ambata tana so.

Hidayat tace
"Ka dena Tunanin duka wannan yaya! Ka fara samun lafiya tukuna ka ji?"

Kai ya gyaÉ—a, se aka turo kofan da sallama É—ago kai tayi se suka HaÉ—a idanu da Zainab.

Ganin hamza zaune yana danna counter yasa ta karaso tana kallon hidayat tace
"Hidayat??"

Dariya hidayat Tayi tace
"ya aka yi kika gane ni haka da wuri Auntyna?"

Murmushi zainab tayi tace
"jikina ne kawai ya bani ke ce hidayat! Sannu da zuwa yaushe a gari?"

Hidayat tana karɓar yaron na bayan zainab tace
"Na kwana biyu amma se jiya na haÉ—u da yayana, masha Allah wannan yaron ai ni yayo yaya hamza kalli kaga don Allah bamu yi kama ba?"

Murmushi yayi ya san so take tayi cheering É—inshi ya manta komai ya É—auke ta as sister, shima se ya daure yace
"sossai ma yaro in be É—auko goggonshi sakike ba wa ze biyo to!"

Dariya suka yi har zainab, hidayat tace
"Aunty zainab kin shiga wurin Abba kuwa?"

Tace
"eh Seda na gaishe shi na shigo nan"

Hidayat tace
"ko bakon ya tafi?"

Tace
"A'a yana nan"

Hidayat ta miƙe rungume da yaron tana duba wayanta tace
"OK, bari na shiga Da Rashida ta gaida shi, ummi ma tace tana hanya"

Bata jira Cewar zainab ba ta fice..

Kallon Hamza Zainab tayi tace
"kaina ya kulle! Yaushe hidayat ta San Abba haka da har zata gayyato mutane gaida shi daga zuwa dubiya itama? Like yadda take maganan kaman akwai sanayya ko wani abu"

Murmushi me ciwo yayi yace
"Hidayat is my half sister zainab, mahaifinmu É—aya muma se jiya muka sani"

****

Tana fitowa ta isa enterence na ward É—in ta shigo da Rashida suna hira, É—akin Abba direct suka yi suna shiga da sallama Abokin Abba yace

"Rashida?"

Wara idanu tayi tace
"Daddy!"
Se ta saka dariya tace

"Daddy dama ka San Abban hidayat?"

Yace
"eh shine best friend ɗina da na kan baku labari baku taɓa zuwa duba shi bane sbd bakwa zaman Nijeria"

Rashida tace
"Daddy and hidayat is my friend mun haÉ—u a school a Paris, kaga Ikon Allah ko?"

Abba yace
"ai ba'a mamaki da ikon Allah"

Gaishe shi Rashida tayi tana ajiye Ledar hannunta, ya amsa da kulawa yana tambayar ta school... Suna cikin gaisuwa se ga ummi itama ta zo room number hidayat ta faÉ—a mata ta karaso itama da karamci Abba ya tarbeta suka gaisa sossai har yake cewa shi ya samu lafiya ma yau gida ze karashe wuninshi.

Duk suka yi murmushi, hidayat tace
"Abba bari na karasa dasu su gaida Baba"

Kai ya gyaÉ—a yace
"na shiga da safe nake jin abunda likita ya faÉ—a, Allah dae ya bashi lafiya amma kam yana jin jiki"

Amsawa suka yi da Ameen, kan suka fice zuwa É—akin Baba Buba suna tafiya Hidayat na musu introducing juna.

Da sallama suka shiga, yana kwance as usual cikin jin jiki, Raed na tsaye yana waya amma tunda suka shiga idanunshi ke manne bisa kanta, murmushi kawai ta sakar mai ta kauda kai, yaran na zaune bisa center carpet dake É—akin sun saka ma Buba idanu suna kallo sbd yadda yake rattabo zantuka, Daadida na zaune bisa kujera.

Gaisawa suka yi da Daadida kan suka gaida Raed suka kuma gaida Baba Buba, yaran suka gaida su.

"Yaran nan kun ji ko? Wai ba zan sha ko ruwa bane har nan da sati biyu, ko kurɓi ɗaya fa... Wallahi yunwa nake ji, kishi nake ji!"
Cikin tausayawa hidayat tace

"Baba saboda lafiyanka ne in shaa Allah komai ze wuce"

Yace
"uhmm Æ´an nan yunwa bai da daaÉ—i, ashe haka nayi ta azabtar da Muhammad da yunwa ban kyauta ba! Ban kyauta ba wallahi"
Duk fa da kyar yake iya fusgo maganan.

Rashida tace
"baba save ur energy yawan maganan nan yana kara rage maka lafiya ne, ka dinga Ambaton Allah in shaa Allah komai ze zo da sauki"

Kallon Daadida yayi yace
"Mama kin ce akwai Æ´ar Aisha da ta zama matar Raed anan? Waccecce don Allah in nemi yafiyar ta ko zan samu sassauci?"

Hidayat tace
"ni ce baba! Kuma na riga da na yafe maka, Allah ya yafe mana baki É—aya"

Hawaye yake zubarwa da miyau yana cewa
"Allah sarki Aisha!"

Yini sur suka yi a asibitin da su Rashida, ummi da Rashida kaman sun shekara da sanin juna, anan take ganin wasu daga cikin en uwanta ta ɓangaren Abba, duk wadda ya zo Abba ze aika a kira ta ko wurin ya hamza ko wurin baba ko chan waje Inde suke zaune ta zo yayi musu introducing juna, ba laifi kuma kowa na maraba da ita cikin farin ciki.

Yamma Lis aka sallami Abba, hamza ma da Hidayat bata barshi ba ta saka shi yayi ta karatun Alqur'ani da azkar jikinshi ya É—an yi karfi yace sede a sallame shi, shima aka sallame shi.

Duk wadda ze shiga duba Baba Buba se ya zub da hawaye sbd kowa ya shiga se ya faÉ—a mai yana jin yunwa, Raed ya mai alkawarin kaza da youghurt me sanyi duk randa likita yace ya ci abinci, abun nashi kaman iska yanzu ze yi ta magana anjima in ciwon ya buge shi se nishi, cikin da ya kumbura kaman balon balon likitocin suka yi mishi Mini-surgery suka saka wani roba ta gefen yana zub da ruwan dake taruwa a cikin banda wari babu abunda yake.

Fitowanta kenan tayi sallar magrib ta idar aka fara kiran layin wayanta, dubawa tayi ta Mikawa Hidayat take cewa
"duba min sunan wanene?"

Hidayat tace
"Daadida ai ba suna lamba ce"

Daadida tace
"kayya! Tun fa jiya ake kirana da lamba in na ba wannan farar baturiyar(Norah) se tace layi ne kawai bazan dauka ba in sun gaji swa barni na shaki iska Haba"

Hidayat tayi picking ba tare da tacewa daadida komai ba ta kara a kunnenta...

#Vote
#share
#comment

                  🖤Gureenjo🖤

KOWA YA GA ZABUWA...
   (DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

FOLLOW ME ON Wattpad @Gureenjoh6763

AND ON AREWA BOOKS @gureenjo

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

                      *PAGE 39*

*FREE BOOK*

"Assalamu Alaikum muna magana ne da Maman Buba?"

Hidayat tace
"Wa'alaikumussalam warahmatullah jikarta ce! Allah yasa lafiya kuke nemanta?"

Mutumin cikin gurɓataccen hausan shi yace
"Lafiya ba lau ba! Tafe muke da abu me muhimmanci kuma muna so mu ganta ne ido da ido!"

Hidayat tace
"Amma a ina kuka samu layinta? Sannan wani irin muhimmanci abun yake dashi da bazaku iya faÉ—a a waya ba?"

Mutumin yace
"hooo É—iyar nan, mun samu layinta ne wurin matar Buba Badi'ah, da kyar ta bamu bayan mun biya ta dubu biyar mun sayi layin, abunda muke Tafe dashi kuma yafi karfin waya yarinya... Mu musulmi ne munshe la'ilaha illah lahu don haka bamu san me cutarwa ba!"

Shiru hidayat tayi kan tace
"Ina Zuwa!"

Kashe wayan tayi ta kalli Daadida tace
"Daadida ko kina da wasu en uwa ne a ruga ko wajen Nigeria?"

Daadida tace
"ko É—aya! Halan shirme aka miki a wayan?"

Hidayat tace
"sun samu layinki ne a wurin Badi'ah bayan sun bata har dubu biyar, sun ce magana me matukar muhimmanci suke tafe da ita suna son ganin ki ido da ido"
Chapter 59 · 0% Book details